Daudar Gora Book 2 page 9


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (09)
.........Yanda ya umarcetan haka tayi akan Iffah, dan dole ta kasance a tare da ita har zuwa lokacin da ya bukaci ta kai tare da itan. Komai dake faruwa kuma akan idanunsa ne, sai bayan wucewar Daneen Ammarah da kusan mintuna talatin ya ɗauka Alkur'aninsa ya fito cike da takun nan nasa na izza da ƙasaita ya nufi ɗakin. Zama yay a kujerar da ke gaban gadon shanyayyun idanunsa a kanta, ya mata kallo na wasu mintuna tamkar mai nazari kafin ya fesar da ɗan huci ya ɗauke kansa. Alkur'anin ya buɗe yana mai ƙara tabbatar da nutsuwarsa gaba ɗaya garesa sannan ya fara raira karatu cikin daddaɗar muryarsa da bama kowane harafi hakkinsa cikin ƙwararren larabci yanda ya kamata.

      Ya ɗauki tsahon lokaci yana karatun, kafin ya tsagaita ya rufe ya ajiye. Kujerar da yake zaunen ya sake matsarwa gab-gab da gadon, tamkar wanda baya so ya kai hanunsa kan bargon ya ɗan yaye kaɗan. Kauda idanunsa yay da ga kallon inda suka sauka ya maida a fuskarta, ɗan bakin tsiwar nan duk ya bushe. Ya ɗan ja wasu sakanni a kallon nata, sai kuma ya kaudar yana sake tsuke fuska ya fara karanto addu'oi yana tofa mata. Haka ya kasance tare da ita har gabannin asubahi, dan sai da katafaren agogon masarautar ya buga cikar ƙarfe uku dai-dai sannan ya bar ɗakin ya koma nasa. Dole ya kai kwance dan shima ba jikin nasa ya gama komawa normal bane, a yanzu hakan ma jiri-jirin da ya fara ji yana rinjayarsa ne ya sakashi haƙura ya dawo nan ɗin.......


★★... WASHE GARI ★★....


     Ƙoƙarin rufe system ɗin gabansa yake dai-dai da shigowarta da sallama doctor Afif na take mata baya kasancewar hadimanta basu da hurin biyota har nan. A kallo ɗaya zaka fahimci ɓacin ran da ke shimfiɗe kan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Doctor Afif ya gyara mata kujerar da ke gaban gadon jiyyar Tajwar Eshaan ɗin, sai da ta zauna ya juya ya fice tare da zuge musu ƙofar gilashin duk da wajene da bana shiga kowa da kowa ba.

       A hankali ya ɗan risinar da idanunsa alamar girmamawarsa gareta, sai kuma ya motsa lips ɗinsa a tausashe ya furta “Amincin ALLAH ya tabbata a gareki ya Ammie-na”.

   Duk da ɓacin ran da ke zagaye da zuciyarta hakan bai hanata ɗan sakin murmushi ba, ta kai hannunta kan nasa ta riƙo, itama cikin sauƙaƙa harshe da nuna kulawa ta amsa. “Tare da kai Bin Haysam Abdul-majeed. Ya ƙarfin jikinka?”.

      Suna mafi soyuwa da yakan so ji da ga bakin mahaifiyarsa, sai dai kuma a duk sanda ya jisa da ƙarfin izzar harshenta ya kan saurin gane ɓacin ranta a bayyane. Ganin damuwarta kam shine abu mafi ƙona zuciyarsa dan shi karan kansa bai san irin tarin ƙaunar da yake ma mahaifiyar tasa ba. Kaɗan ya gyara kishingiɗar da yay har lokacin idanunsa na kanta, ya juya yatsunsa da ke riƙe da nata ya maida nasa a ciki, a sannu yake tausa mata gaɓɓansu da kulawa da lallashi batare da ya sake cewa komai ba. Tsahon mintuna suna a haka har ta fara sauke ajiyar zuciya alamar saukar fushin nata. Ganin ta koma kamar yanda yafi buƙatar ganinta ya ɗan sake mata murmushi.

      “Nafi buƙatar ganin murmushin akan ƙyaƙyƙyawar fuskar Ammie-na a kowace daƙiƙa ta numfashi na. Akasinsa kan ƙona zuciyata fiye da yanda wuta ke narkar da kitse.”

   Kalamansa koda a taƙaice suke zinarai ne a zuciyarta, shi ɗin yafi hasken diamond walwali da ƙyalli a cikin idanunta a duk sanda take dubansa, ta so abubuwa da yawa kafinsa ciki harda mahaifinsa sai dai shi tamkar shafine dake shafe dukanin fejin sauran fejikan baya a littafin rayuwarta. Kafin ka buɗe a bangonta shine, a shafin farko da shi take shimfiɗa, tsakkiya da ƙarshe shine mafi girma a ababen yabonta da ƙaunarta. Ta sake sakin murmushi zuciyarta na sake risina da ga fushin da ta baro sashenta a ciki. 

        Malikat Bushirat wata irin mace ce da gane halinta sai wanda ya santa, tana da abubuwan ban mamaki ta na da kuma na ban tsoro harma dana ban sha'awa da suka kasance mafi rinjaye a yimata ado. Hamshaƙiyace ta gasken gaske dan ko'a cikin manyan matan dole a kirata *_ZAKANYA UWAR ZAKIN ƘASAR RUMAN_*. A yanzun ma halin dattakon nata ta nuna, ta hanyar shanye dukan tarin abubuwan bakin nata ta cigaba da bama ɗanta magajin mijinta mai amsa suna shugaban sarakunan ƙasarta kulawa har zuwa lokacin data gamsu zata iya magana da shi babu fushi a harshenta. Ta tsatstsaresa da idanunta masu kaifi irin na uwa, yayinda shi nashi ke a rissine gareta risina irin ta ɗa a gaban mahaifiya. 

         “Na kasa gane komai da ga Mammah dangane da al'amarin yarinyar, a sanina ita ke fara hukunta duk wanda ya zaɓi cutar da kai koda da mummunar magana ne, kuma koda ni da na haifeka ce. Amma a wannan lokaci sai ta zaɓi bama mai son kawar da numfashinka kariya batare da fahimtar da ni kaina hujjarta akan hakan ba. Shin taya ake tunanin zan iya haɗa numfashi a ƙarƙashin runfa ɗaya da wadda ta shirya kawarmin da abinda bani da madadinsa ko samin madadinsan ba har abada? Taya ake tunanin zan iya kawaicin barinta da cigaba da kallonta a matsayin Zawgatu al-ibn duk da yunƙurinta na son ganinta ta tarwatsani da tai? Idan har igiyar aurenka da ke kanta ne katangar da ake iya min nuni da ita bango gareta ina son ka rusheta, ka yanketa, yankewa ta har abada ibn Haysam Abdul-majeed. Dan hakan shine kawai zai iya bani nutsuwa na manta da komai”.

         Da ɗan ƙarfi ya matse idanunsa yana mai sakin numfashi a harɗe, sai dai mai kallo da ido bai isa fassara kamilar fuskarsa ma'abociyar annuri da kwarjini ba hatta ita dake amsa sunan mahaifiya a garesa.....

    “Yanke hukunci cikin fushi da rashin haƙuri akan bincike ba itace ɗabi'ar shugaba nagartacce ba”. Daneen Ammarah ce dake tsaye mai maganar tana ƙoƙarin shigowa ɗakin, da alama ta ji dukkan kalaman Malikat Bushirat ɗin. Bai motsa ba, hakama bai buɗe idanun nasa ba harta ƙarasa shigowa garesu, sai dai ya sauke wata irin ɓoyayyar bahaguwar ajiyar zuciya acan cikin maƙoshinsa. Jin shiru ya ratsa ɗakin ya sashi buɗe idanun sannu-sannu. Dukansu cikin ɓacin rai suke kallon juna kowa najin ya isa yana kuma da ƙarfin iko akan yaƙin. Abune da babu wanda zai ce ya taɓa gani a tsakaninsu sai a wannan lokaci, ciki kuwa harda shi kansa. Daneen Ammarah ta sake katse yanayin nasu ta hanyar ɗora hannunta a kafaɗar malikat Bushirat da alamu suka nuna ta gama kaiwa maƙura a fusata..

        “Úht!”. 

     (sunan data kan kirata da shi wani lokacin) 

      “Ban sanki da garaje ba, ban sanki da kasa fahimta ba, ban sanki da munana zato ba. Ban sanki da dagiya ba. Ina roƙonki ki danne, ki jure, ki zama mai ƙarfafa gwiwar mai ƙarfin da ba ƙarfin akafi son ya gwada ba kai tsaye, saboda amsa sunansa na shugaba. Bazan musa miki sunan Fareedah matsayin mai laifi ba, amma zan so ki kasance a yanda na sanki wajen tabbatar da gaskiya akan kowane ne kafin zartar da hukunci. Muma ba burinmu hana a hukunta ta ba, ko fifitata sama da gudan jininmu kuma shugabanmu ba, so muke kawai abi tsarin da ya dace da dokar shari'a da muke fata bayan ita za'a iya tono waɗan da ma suke aikata ɓarnar baya mai barinma gudan jininmu baƙin fenti da tabo a rayuwarsa da rayuwar mulkinsa. Ki fahimci Mammah ba fifita Fareedah take sama da abinda ta cancanci fuskanta bane, kariya take bata matsayinta na tamkar makamin da zai iya zama zaren da zai jamu ga duk ɓoyayyun masu laifin da muke fatan kamawa a cikin hannayenmu. Shin baki ji a ranki wanda suke aikata ta'asar baya nada nasaba da na yanzu ba? Baki ji a ranki yanke mata hukunci a kallonta ita kaɗai mai laifin tamkar basu ƙwarin gwiwar cigaba da aikatawar bane koda kuwa a yanzu basu da hannu kan abinda yarinyar ta aikata? Shin baki tunawa shi shugaba ne ba mai azaba ba?. Da yawan mutane gani suke sakacinsa da ƙin bama abu muhimmanci koda mai muhimmancin ne halayyarsa, sai dai yanda yake yi shine cikar zama cikakken duk wani shugaba. Shugaba da shanyewa aka sansa koda ɗacin na ƙona makoshinsa, da haɗiyewa aka sansa koda raɗaɗin na azabtar da hanjinsa, da ɓoyewa aka sansa koda girman al'amarin yafi girman zuciyarsa, da nazarta aka sansa koda ƙarfin yafi ƙarfin ɗaukar ƙwaƙwalwarsa. Ba ko yaushe yake ihu ba, ba ko yaushe ake gane ainahinsa ba, ba ko yaushe ake iya karantar zuciyarsa ba koda a ƙwayoyin idanunsa ne.....” ta ɗan ja numfashi ta fesar a hankali da cigaba da faɗin, “Idan har mu a karan kammu zamu kasa fahimtar kammu taya wanɗanda ke zagaye da mu zasu fahimcemu?. Idan har uwa zata iya shanye wa da daurewa akan halayyar ƴaƴanta da duk girman adadinsu bazasu haura ashirin ba mai zaisa shugaba mai mulkin ƙasa baki ɗaya kamar ruman za'a so ganin zahirinsa a dole dan kawai farin cikin wani ɓangare ko munanama wani ɓangare? Tayi laifi an yanke mata hukunci, daga baya gaskiya ta bayyana bata da laifi ko tursasata akayi ko wani dalili da zai iya wanketa koda ace ba shine yay hukuncin ba, to shi ne za'a kalla da tabon gazawa? Wa za'a munana? Wa za'a aibanta? Wa za'a munanama kima da mutunci? Amasar itace shugaban nan dai Umm-Jasrah. Dan ALLAH na roƙeki ki kwantar da hankalinki kar wasu su dinga amfani da fusata fushinki domin cikar nasu burin, ki cigaba da zama a yanda na sanki inba hakaba wasu zasuyi amfani da hannayenki wajen shafama kanki da kanki fentin da babu wani ruwan da zai wankeki ya wanke wanda ake son amfani da soyayyarsa a zuciyarki. Bayan ke uwa ce, kema ɗin shugaba ce.....”

         Har cikin rai da ɓargo zantukan Daneen Ammarah sun matuƙar ratsata, sai dai basu ruguje kaso ashirin cikin ɗari ɗin matsayin da take kallon Iffah da shi ba har a yanzun, amma taji ta kuma amince zama mai haƙurin bin matakin da ya dace ɗin wajen hukuntata, hakanne kawai zai bata salama kasancewar ta wadda bata ɗaukar ƙiyayya da sauƙi ga duk wanda ya nuna mata, hakama soyayya. (Hakan kuskure ne Malikat Bushirat, karka zafafa ƙiyayya, kar kuma ka zafafa soyayya dan wataran duk zasu iya canja kansu a gurbin juna), sai kuma ƙudirinta na biyu babu gudu babu ja da baya zata tabbatar da shi koda babu yardar kowa a daular ruman har shi kansa Tajwar Eshaan ɗin........✍️


  

       (Nace, “Humm”)   

*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*_LITTAFI DAYA: 400_

_LITTAFI BIYU: 600_

_LITTAFI UKU: 800_

_LITTAFI HUDU :1000_

_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI

ACCESS BANK

0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN 


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar  1250CFA

Books hudu  1050CFA

Books uku  850CFA

Books biyu  650CFA

Bookk daya  450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*

No comments

Powered by Blogger.