Daudar Gora Book 2 page 69


 69

.....WASHE GARI ta kasance ranar da zasu koma kasar ruman. Da safe bayan Tajwar Eshaan ya gama ganawa da Sultan na saudiya sunyi sallama amintaccensa da

Sayeed Tasadduq-Husain da sai daga baya yazo ya samesu a saudiyyan da wasu mutane biyu suka samesa. Cikin girmamawa suka mika gaisuwa, kafin Sayeed Tasadduq-Husain ya mika ma Amintaccensa file din hannunsa. Amsa yay da sauri yaje gaban Tajwar Eshaan din shima ya ajiye.


   "Wannan shine result din binciken ALLAH ya kara ma adalin shugabanmu lafiya da nisan kwana. Sannan wadan nan sune sukai binciken. Sun kuma kasance kwararrun likitoci ta wanna fanin".


   Da sauri daya a cikinsu ya karbe zancen Sayeed Tasadduq-Husain din cikin harshen turanci, "Idan mukai bincike so daya ba'a samun kuskure, amma domin cire tantama sai da mukai wanna sau uku. Abu daya yake tabbatar mana shi namijin mahaifinta ne, mace kuma ba ita ta haifeta ba. Bayan muni sau uku mun sake bayarwa was asibitocin ga results din nan dai duk abu guda suke bayarwa".


     Baice komai ba, sai amintaccensa ne ya amsa da

yawunsa. Da ga haka sukai masa sallama Sayeed Tasadduq-Husain yay musu rakkiya. Duk abinda akeyi Iffah na daga kofar falo na biyu ne tsaye zata fito zuwa sashen Uwargidan Sultan da zasuyi sallama. Duk da bata san manufar zancen ba sai duk taji ta tsargu, amma kasancewar yanzu an koyi wasu halaye musamman akan hadiye abu koda ta fito wucewarta kawai tavi tunda yasan da fitar tata.. Koda taje can kuma abun nata mata kaikawo har tana jin kwadayin son sanin abinda ke a tattare da file din da son sanin akan wama ake maganar da har sai anzo wata kasa za'ai binciken bayan kowa yasan kasar su suna daya a cikin masu kwararrun likitoci a duniya. Sai kuma a ka kara yin sa'a lokacin da take dawowa sashen ta samu Sayeed Tasaddug-Husain da Tajwar Eshaan din suna maganar again. Cikin kasaitar nan tasa da magana a fisge yake sanar masa. "Ayi musu komai da ya dace, nan da kwanaki biyar bayan anyi salla sai ku biyo bayanmu, dan ina son ku iso ne randa zamu koma zaman shari'ar".


"Umarninka da cikawa shine abin jiranmu Insha ALLAHU"


  Iya abinda Iffah kenan ta iya ji ta shige. Lokacin da ya shigo dakin zai shirya tata fatan ya shigo da file din amma sai ya shigo babu komai. Kuma bai mata maganar ba. Amma koda suka kammala shirinsu suka fito Sultan da kansa yau ma da yayansa maza biyu da uwargidansa sukai musu rakkiya har airport Iffah harda kwallarta hakama Uwargidan Sultan abinka da sabon mata bayan shigarsu jirgi sun zauna tana a jikinsa yana lallashinta sai ga file din nan ajiye a gefensa. Ta danyi mamaki amma sai ta basar, sai dai zuciyarta na sake tabbatar mata da koma akan wa file din ya kunsa yanada matukar muhimmanci ga mijin nata. Jirginsu na dagawa babu dadewa barci ya kwasheta…...




* KASAR RUMAN




Duk da saukar dare sukai tako ina a airport din zagaye yake da matakan tsaro. Kai da gani kasan mai kasar ruman dinne da kansa zai sauka. Ta bangaren masu tarbarsu kuwa manyan masarautar ne masu fada aji. Ga wasu lafiyayyun motoci ababen birgewa ga mai kallo. Sosa barcine a idon Iffah dan yanzu kam bata da aikin da yafi wannan. Hakan yasa ta kasance a kusan rabin jikinsa lokacin da suke fitowa, Dole duk wanda ke wajen yay kasa da kansa cikin jin nauyi. Shika gogan nasu ko'a kwallar rigarsa rungume yake da ita hankali kwance yana daga musu hannu daya alamar amsa gaisuwarsu har zuwa motar da aka ajiye domin su kawai. Sai da suka shiga har aka rufe sannan hadiman da sukal masu rakkiya ke fitowa a jirgi suma. A wannan tawaga musamman ta matan Diwa ce kawai zuciyarta ke a tsarkakake game da nado labari, amma sauran duk yan daukar rahoto ne. Sai dai kuma basu samo yanda suke so ba sam kasancewar su/Iffah'r sun musu wahalar ma gani ba kamar yanda su Uwa sukai tunani ba.


   Tun daga airport har cikin masarauta jami'an tsaro ne, a cikin masarautar ma tarba suka samu da taima Iffah dadi, dan harda Malikat Haseenat da Daneen Ammarah da kanta. Sal wata da Iffahr bata sani ba amma suna kama da Daneen Ammarah sosai kuma tana kama da Jaddah. Haka kawai taji a ranta itace Daneen Waheeda da aketa fada. Lokacin da take dagowa da ga rungumar da taima Malikat Haseenat zata rungume Daneen Ammarah idanunta suka sauka kan wata kyakykyawar farar budurwa sol tana balla mata harara. Bata santa ba, dan haka ta dauke idanunta ta maida hankali ya Daneen Ammarah din cikin rashin damuwa. A hankali ta saketa ta nufi Daneen Waheeda da ke tsaye tana kallonsu kusa da Malikat Ashwaq fuskarta babu yabo babu fallasa. Gabanta ta rissina ta gaisheta tare da Malikat Ashwag din. Amsa mata tai da dan murmushin yake sakamakon kallon da Malikat Haseenat ta watso mata. Sai kuma ta nufi Malikat Bushirat ta rungume, itama dai gain kallon da ake musu ne yasata shafa kanta tana yake, Jasrah kam saita boye bayan Malikat Bushirat din dan da gaske kunyar Iffah take ji. Murmushi Iffah tai itama ta rungumeta, dan koba komai kafin faruwar hakan al ta nuna mata soyayya ta gaskiya..


   Tuni shi Tajwar Eshaan ya shige ciki, dan haka itama Malikat Haseenat ta kama hanunta tana facin,"Kinga zomuje kema ki huta kunyi buda baki a jirgi babu nutsuwa". Da ga haka ta nufi ainahin sashenta da ita dan an sake masa gyara na musamman. Bayan wucewarsu abubuwa da yawa sun faru a cikin masarautar, ciki hard jajircewar Malikat Bushirat akan komawar Iffah sashenta. A zahirance dai babu wanda ya kawo komai a ransa game da hakan, sai Malikat Haseenat ce ma take gain Malikat Bushirat din na son hakanne da tunanin Iffah ta kanainaye mata Eshaan, ta kuma san sai dai Bushirat din tayi ta gama Iffah da Tajwar Eshaan sun riga sun gama zama abu daya. Ga tabbaci nan ma a yau ta sake gani, dan duk mai hankali da zai kalli Iffah'r a yau yasan tana tare da juna biyu. Komai nata ya canja, ga kyau data kara da budewa. Yanzun ma Malikat Bushirat na gain sun nufi can ta saki wani lafiyayyen murmushi tana fadin, (yes) a zuciyarta alamar akwai abinda suka kulla a sashen kenan.


   Ko dar Iffah bataji da komawarta sashenta ba. Sai ma farin ciki data tsinta kanta a ciki. Ga hadimanta duk an dawo mata da abinta, a ganinta ma ita wannan wata dama ce da zatai yakinta da kyau a yanzun. Wanka ta farayi bakinta dauke da addu'a, kasancewar duk tayi sallolinta tun a jirgi shirin kwanciya kawai tai ta haye gado abinta sai ko barci.





    Cikin barci take jin kamshinsa na sake shige mata hanci, a zatonta mafarki take, sai tai kokarin yin juyi abunta. Jinta jikin mutum a gaske ya sata bude idanunta da kyar. Akan kyakykyawar fuskarsa ta sauke idanun nata. Tashi tai a dan zabure ya rikota, maidata yay ya kwantar yana mai tura yatsunsa cikin gashin kanta, sai kuma ya matso da fuskarsa saitin tata ya daura goshinsa kan nata hancinsu na gogar juna.


   "Yaushe kazo?"


 Ta fada cikin muryar barci. Shiru kamar bazaice komai ba, sai da ya mula dan kansa sannan. "Dama zaki iya barci babu ni a tare da ke?". Kankamesa ta sakeyi tana sakin ajiyar zuciya, itama a hankalin ta furta, "Kawai dan banda yanda zanyi ne".


"Toni gani nayi yanda zanyi ai".


   Ya bata amsa yana sake matseta cikin jikinsa kai kace amshe masa ita za'ai. Luf ta kwanta kuwa suna sauke ajiyar zuciya a tare. Sai kuma ya hade bakinsu a hankali. Da ga haka labarin ya sauya salo...


  Karfe uku nayi ya gudu, sai farkawa tai taga babu shi a dakin. Murmushi kawai tayi ta tashi zuwa bayi tai brush da tsaftace jininta ta fito. Madara mai dumi kawal tasha matsayin sahur. Duk da barcin dake cin idanun nata sai bata kwanta ba tayo alwala ta danyi nafilfili da karatun Alkur'ani. Bata tashi a wajen ba sai da tai sallar asuba, Tana idarwa kwanciyar ta sake yi, bata tashl ba sal azhar. Tayi mamakin barcin da tayi, amma kuma sanin yanayin da take ciki da rashin isasshen barcin da bata samu a Saudiya ba yasa ta fahirci akwai ramuwa dole dama.


   Tsaf tai shirinta cikin kyakykyawar abaya kamar ka sace ta ka gudu. Dama ga ko'ina ya sake fita da fitar kwarjini da kyawun haiba na ciki. Cike da girmamawa a gareta hadimanta ke zubewa Rasa gaisheta lokacin data fito. Nuni tai musu da su tashi, cikin sanyin da ciki ya haifar mata yanzu ta basu izinin mata rakkiya zuwa sashen Malikat Haseenat da ga nan su wuce na Malikat Bushirat. Da girmamawa suka arsa mata tai gaba suna take mata baya. Duk da akwal tazara a tsakaninsu bata shiga motar da aka ajiye domin ta ba tunda ta fito, A kafa ta taka hadimanta na take mata baya. Dolene ta birgeka, dan yanda ta fito da kafan ma sal ta kara kima a idanun hadiman. Ta ko'ina kuwa ta gitta hadiman ne ke zubewa mika gaisuwa, hannu kawal take daga musu fuskarta da dan murmushi dan sam bata daureta ba. Yayinda Amintacciyar hadimarta ke amsa musu da baki ita kuma.


   Tun kan shigowarta aka sanar da Malikat Haseenat da ke zaune Daneen Ammarah da Daneen Waheeda tare da ita. Sai Iftihal diyar Daneen Waheeda dake zaune a can gefe tana latse-latse a laptop. A nutse ta shigo bakinta dauke da sallama. Dan haka suka dago a tare. Sai dai kuma a hankali Iftihal taja sirrin tsaki da maida kanta ta cigaba da abinda take yi. Babu wanda ya jita, sai dai Iffah kam taga kallon da tai mata sarai. Amma tai kamar ma ita bata ganta ba ta nufi Malikat Haseenat da ta bude mata hannu fuska duke da murmushi alamar tazo gareta. Ita din ta nufa cike da kunya, ta durkusa a gabanta tana murmushi da gaisheta. Cikin murmushi Malikat Haseenat ta ce, "A'a kinga Hafidah tashi ki zauna keda ke fama da kanki, ALLAH dai ya raba lafiya".


   Sosai kirjin Daneen Waheeda ya buga, yayinda Daneen Ammarah ke murmushi kawai tana bin Iffah'r da kalion kasan ido, Bayan ta gaishe da su duk cikin girmamawa Daneen Ammarah ta nuna mata Daneen Waheeda. "Ga wata maman taki nan tazo kuna Saudiyya, nasan kin san dai sunanta da labarinta tun kafin yau". Fuskar Iffah cike da murmushi ta jinjina mata kai. Kafin ta kara gaishe da Daneen Waheeda din da zancen cikin nan va sata sumar zaune, cikin murmushin yake ta kai hanunta kan Iffah'r ta shafa. Daneen Ammarah ta sake waiwayawa ta nuna mata Iftihal da tai kamar ma bata san mi ake ba "Wannan yar uwarki ce ita kuma, sunanta Iftihal, itace first born a wajen mamanki. Tanada kanne maza har uku".


   Murmushi kawai Iffah tai sai dai batace komai ba kamar anda itama Iftihal din ko dagowa batai ba. Yanda tai din kuma sai ya zafi Daneen Ammarah. Ita kanta malikat Haseenat dai tayi shiru ne amma fuskarta ta nuna jin zafin abinda Iftihal din tayi. Ita kam Iffah ko'a kwalar rigarta, hankalinta kwance suka cigaba da hirarsu da Daneen Ammarah da Jaddah...✍️


No comments

Powered by Blogger.