Daudar Gora Book 2 page 62
Chapter: 62
...…….Tofa dan-dan-dan, da alama dama irin wannan damar Iffah ke jiran samu, dan cikin
kankanin lokaci duk da darene masarautar ta dauki dumi, yayinda aka kwashi Ameera Haifah da Jasrah zuwa asibiti, Miran Arshaan kuwa da jikinsa ke tsumar toro gaba daya ya gama
gigicewa, dan sai zuwa yanzu ya dawo a hayyacinsa. Tuni kuwa ya tsure da ganin abinda ya aikata, sai kawai ya bige da borin kunya.
Sudai jami'an babu wanda yace da shi komai,sun tattara komai akan sai zuwa da safe za'a kai
maganar ga Shahan-shan. Abu dai mafi daure kai shine miye tsakaninsa da Ameera Haifah din
har haka a irin wannan tsohon daren, dan a kala fa karfe biyu na dare kenan.
A lokacin da duk ake waccan dambarwar anan ta-kurya ce ke ganawa da manomin ganyayyakin shayin Shahan-shan. A cikin badda kamarta take, dan haka shi bai san wacece ba.Hasalima magana da Jazaa sukeyinta ita dai tana hakimce komai batace ba. Da farko yaso ya, amma ganin wata lukutiyar jakkal da zinare ga barazanar halaka zuri'arsa kunne tuni ya mika wuya akan an gama. Malikat Bushirat tai murmushin basawa ta dauke kanta.Kwalayen ganyen shayin da uwa ta kawo kan ya fara kaiwa sashen Shahan-shan din kafin wanda zasu noma ya tsiro nan ma Jazaa duk ta ajiye masa su har uku..
Hummm🥱🚴
Zaune take bayan idar da sallar asuba, yanda ta kurama waje daya ido zai baka tabbacin tunani take. Sai lokaci zuwa lokaci da takan saki murmushi, harda cusa kanta cikin kafafunta kamar mai jin kunyar wani da ke gabanta. Ta dan jima a hakan kafin ta mike kamar wadda aka tsikara idonta kan agogon dakin. Tasan yanzu kam yana Gym ne tunda har ya kai yanzu bai shigo ba. Itama tsaf ta shirya cikin kayan motsa jiki ta, sun mata matukar kyau da fidda ainahin surarta komai dam. Dan wani bana ta saka a kanta siriri kalar kayan sannan ta daura talda daura after dress saman sport wears din. Shiru tai tana bin Gym din data shigo da kallo, babu kowa komai ma a kashe yake, da alama banan yazo ba. Fuska ta dan bata da tura baki gaba, har zata koma sai kuma ta tuno randa ta samesa a can sama yana wasan takobi shi da Miran Arshaan. "Yes!" ta fada tana wani kashe ido daya da yin juyi sannan ta nufi can cikin takunta na nutsuwa
Shelanta sunanta da na'urar kofar tayi kamar yanda ta saba duk wanda zai gitta ta cikinta ya sashi dakatawa da jujjuya takobin ya juyo a hankali. Tuni hadiman wajen sun jujjuya bayansu sukam. Yanda take takowa garesa kamar wata tarwada yasa shi gagara cigaba da abinda yake yi.
"Good morning
Ta fada cikin rashin tsoron nan nata na bayyane tana daura yatsanta saman tsintsiyar hannunsa ta zano a hankali ta dire kan kyakykyawar takobin da ya rike rikon kasaita da kwarewa. Da kallo kawai ya bita batare da ya amsata ba. Itama sai bata nuna tasan yana kallonta ba ta zare takobin a cikin hannun nasa fuskarta da murmushi. kin sakar mata yay, sai ma cike da salo yay wani irin juyata bata ankara ba ta dawo saman jikinsa takobin a wuyanta sai dai bai daura a kan fatar jikinta ba. Iffah jitai zatayi fitsari na neman kufce mata tsabar yanda ta tsorata har yana jin yanda jikinta ke tsuma. Dan dukowa yay kansa a kafadarta bakinsa saitin Kunnenta ya furta, "k takamarki tsokala ko?".
Idanunta da ke kawo kwalla ta shiga kikkifatawa da girgiza masa kai a hankali. Cikin rawar harshe ta ce, "Eshaan Akhi na tuba".
"Daga baya kenan".
Ya fada yana kara matsar da takobin jikinta gaf.Sake tsurewa tai. Shiko sai faman danne dariya yake.
"Ki fanshi kanki".
Da sauri ta ce, "Da mi?".
Dan lumshe idanunsa yay ya bude yana mai busa mata numfashinsa a wuyan. A dan salon tabe baki ya ce, "Komai ma".
"Shike nan, shike nan naji na amince, amma dan ALLAH ka janye sau daya fa ake mutuwa, rai daya ne". Yanzu kam kasa daurewa yay sai da murmushi ya subuce masa. Ya janye tare da dauke hanunsa dake saman cikinta ya juyota suna fuskantar juna. Hawaye fa da gaske sun cika mata idanu. Da kyar ya iya gimtse dariyarsa. Idanunsa ya maida ga hadiman wajen da suka juya bayansu tun dazun, dasss daga yatsunsa sau biyu, cikin abinda bai sakkani ba sun bar wajen a ka barsu su biyu. Da baya-baya yaja zuwa table din gefensu kadan,wata takobin ya dakko a cikin kyakykyawan kufanta ya dawo gabanta, hanunta ya riko ya daura mata takobin sannan ya zare abayar ta ya ajiye tare da mata alamar bismillah. Kamar ba ita ta gama hadiyar hawayeba yanzu ta wani dubi takobin shima ta dubesa ta dan murguda baki. Kansa ya maida gefe yana murmushi, tare da ajiye tsinin tasa takobin bisa kasa ya fara zagayata. Yana a tsaye daga bayanta ya juya takobin cikin salon tsokanarta kawai a bazata yaji tama kanta garkuwa. Idanu ya dan waro waje, da bin takobin da kallo kawai ta zuke ta maida masa harin. Cikin zafin nama ya kare kansa shima mamakinta na nan kasheshi.
"Dama kin iya wasan takobi?".
Ya tambaya da mamaki idanunsa cikin nata Murmushi ta sakar masa da kara zukewa ta kai masa suka ta kasa. Nanma baya yay cikin zafin nama yay wata irin bahaguwar zukewa. Dariya tayi da dire takobinta ta fara zagayashi kamar yanda ya mata dazun, cikin salon dage gira da kashe masa ido daya ta ce, "Zaka cigaba da tsayawa tambayar a ina na iya ne na kaika kasa?". Tsaiwarsa ya gyara da kyau yana murmushi da kamo lips dinsa na kasa ya tura ( paki suka cigaba da zagaye juna. Sai kowa ya yinkuro cikin ragabza akai tsaiwar zakaru. Cikin kwarewa da nuna bajinta ga kowa suka cigaba da wasan mamaki na nan kashe Tajwar Eshaan a zuciya. Duk da ya fita kwarewa yanda ta iya din itama na bashi mamaki matuka.Sai dai ya bita da salon saffa-saffa yanda bazai cutar da ita ba dan karfinsu ba daya bane
Tamkar wanda aka jeho kawai sukaji sallamarsa a kusan tsakkiyar wajen, dan kamar sai da ya matso gab da su ne ma yake sallamar.Da ga shi har Iffahn juyowa sukai, musamman Iffah da kamar wadda ta ma firgita, dan jikinta har rawa yake wajen neman abinda zata yafama jikinta, tsabar yanda ta rikice tama ki ganin after dress din nata. Bata san yanda akai ba, tayaya ma kawai jinta tai a jikinsa, jin kamshinsa ya sata kankamesa da sauri tana kokarin boye kanta.
"Miya kawoka nan babu neman izini? Kabar wajen nan Aam!!" ya fada a matukar tsawace shima yana kankameta da juyawa da ita suka bama Miran Arshaan da yay mutuwar tsaye baya.
"I say out!!!".
Ya sake fada da wata irin mummunar tsawa mai karaji da har jikinsa na girgizawa, ga idanunsa sun yi wani irin kadawar masifa kamar wanda ake kadama gangi. Miran Arshaan har tuntube yake yi tsabar firgicewa da tsawar Tajwar Eshaan din. Bai taba sanin yaron nan dan bala'i bane irin yau. Next surar yarinyar nan ta matukar kidimashi, ashe abinda Jasim kenan ya gani kullum yake cikin sambatu da santin yarinyar, shi manemin matane tun yana da kananun shekaru, yayi mu'amula da mata kabila daban-daban a duniya da bai san adadi ba. A sanda yake ji da rashin ji har order din mata suke ta online, yaga matan ma da sukafi Iffah kira amma wannan jikin dabanne. Ji yake yama kasa cigaba da tafiyar yanda jikinsa ke bari, sai kawai ya samu bango ya manne yana sauke numfashi gudu-gudu. (Humm)
Yanda Iffah taji zuciyarsa na bugawa da sauri- sauri kamar zata ballo kirjinsa ta fito ga tsawar da yayma uncle din nasa ya matukar sake rudar da ita fiye da tsoron ganinta a yanda take da tai gudu. Kanta ta shiga jujjuya masa da kankame hanunsa, sai kuma ta dan dago ta kalli fuskarsa. Ta wani irin kadawar masifa jazur hakama idanunsa gaba daya sun juye mata cikin canjawar kammani. Dole ta maida idanunta kasa jikinta na rawar toro da yanayin nasa. Jitai kawai ya wani irin fisgar hanunta zuwa hanyar kofar da ta shigo, bai tsaya da ita ko ina na bedroom. Yarfar da hannun yay yayi shigewarsa bathroom. Da kallo ta bisa hankalinta a tashe itama, dan ita kadai tasan kalar wutar masifar data gani a cikin idanunsan. Raya mata zuciyarta ta dingayi kawai tabar dakin nan karma ya fito ya sameta...
Koda ya fito bayan tsahon lokaci da ya dauka a bayin bai nema Iffah ba dan yana bukatar kadaici saboda ya shiga bacin rai, shi mai kishi ne, tabbas yanada matukar kishin da yake ji akan yarinyar nan zai iya badda mutum. Wata irin tsanar Miran Jasim da Miran Arshaan yake ji irin wadda bai taba ji a kansu ba a dukkan abubuwan da suka aikata masa a baya, ga wani irin sara masa da kansa yake yi na ciwo. Jikin window ya karasa hannunsa goye a bayansa batare da ya cire ko bathrobe din jikinsa ba yana kallon sararin samaniya da ke hada was irin manyan bakaken giza-gizai na hadari, du da safiyar tayi sosai garin yaki washewa sai ma rinewa yake sake yi kamar za'ai wata sabuwar magriba. Kiran waya ne ya shigo, ya share kamar bai jiba, aka sake kira nan ma kamar zai share sai kuma ya nufi wayar a fusace ya daga. Sai dai yay shiru baice komai ba. Da ga can Sayeed Fayzul-haq ya gaishesa cike da girmamawa.Haushin kowa yake ji, duk da bashi yay lefin ba ya samu rabonsa. Dan maimakon amsa gaisuwa a dake ya ce, "Ya akai". Dan rikicewa Sayeed Fayzul-haq yayi, amma sai cikin dauriya da sake kankan da kai ya shiga masa bayanin abinda ke faruwa tsakanin Miran Arshaan da Ameera Haifah tun a daren jiya. A zafafe ya ce, "Kaima jami'ai magana su kamashi a hadashi da dayan sakaran, a saka na'urar daukar magana cikin akin kurkukun kuma.Itama Haifah din Doctors su sallameta idan babu wata matsalar data shafi lafiayarta jami'an tsaro su rufeta",. Daga haka ya ajiye kan wayar yana huci. Duk yanda yake kokarin rike kansa da bin komai a sannu ya fahimci ba haka makiyansa suke bukata. Fushinsa suke son gani, ainahinsa suke bukatar ya nuna musu. Ya barsu da yarinyar nan ne kawai domin shi din shugaba ne, shugaba kuma da hadiyewa aka sansa, amma tunda so suke shi ya fito musu a Eshaan In Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb din sa to yanzu ne wasan zai fara..
Leave a Comment