Daudar Gora Book 2 page 60


 Chapter: 60


."An haifi ciki lafiya, kuma da namiji sanbalele da yaci suna *_Eshaan_*, Eshaan kyakykyawan yaro mai lafiya da ban sha'awa ga kowa, ga

shiga rai. Wata irin makauniyar soyayya Bushirat ke nuna masa har takai Ni kaina sai nayi da

gaske nake ganinsa, hakan da take yasa Waheeda yimata tas kafin ta dan canja aka

dinga kawomin shi nan. Ya taso yaro mai wayo, miskili da baka iya gane abinda yake so ko baya

so sam. Shi ko irin abokan wasan nan na kuruciya Eshaan bayayi, yafi so ya zauna shi kadai shiru ko yayta karance-karancen

abubuwa musamman a litattafan tarihin wannan daula da suka shude. Sai dai yana

matukar son wasan doki da basket ball, da wasan takobi, idan kuma yana tare da Kakansa

ko mahaifinsa zaki dingajin maganarsa ko babu yawa. Al'adar wannan masarauta da Miran mai jiran gado ya kai shekaru bakwai zuwa goma

ake kaishi can wani boyayyen waje ya rayu har sai girmansa, ko kuma sarki ya zabi murabus

kafin ya mutu shi ya daurasa, idan kuma bazaiyi murabus ba za'a dawo da shi cikin masarauta

da iyalansa dan su basa wuce shekaru ashirin basuyi aure ba gaskiya. Shiyyasa sai kiga yaro

ya taso mahaifinsa bai wani tsufa ba. Da farko Bushirat ta tsaya tsayin daka akan baza'a rabata

da danta ba, nima kuma na bata goyon baya dan banji dadi ba sanda aka rabani da Haysam,

sai dai was tsurface-tsurfacen tsafi da Uwa ta fara kawowa a kansa yasa nace a kaisan, ta

nuna bakin cikinta sosai akan hakan da nayi, har tai gargadi mai girma akaina da cewarta ni na

cika shiga mata hanci ni da zuri'ata. Sam wani kurarinta da tsubbace-tsubacenta basa bani

toro, dan da UBANGIJI NAna dogara akoda yaushe. Dan haka na cigaba da dagewa har sai

da Tajwar Abdul-majeed ya yarda aka kaisa kasar Cuba. Haukane kawai Uwa da Bushirat

basuyi ba, sai dai kamar ALLAH ya saka tsorona ne a zukatansu ni ban sani ba. Dan duk

hatsabibancin uwa iyakarta borenta a kaina a bayan idonane, taci alwashi sosai a kaina dalilin

dauke Eshaan har ma abin ya dinga daure mun kai amma sai na daukesa aikin banza dan bata

isa mun abinda bai kasance jarabawata ba. Komai ya lafa kowa ya cigaba da harkokinsa aka shiga watan azumin ramadan. Azumi nada

kwanaki bakwai sai Tajwar Abdul-majeed ya sameni akan zan masa rakkiya ya duba Eshaan da ga can muje umrah da shi bayan salla sai mu

maidasa Cuba mu dawo gida. Ban kawo komai a raina ba na shirya mukai wannan tafiya har da Haysam. Munyi-munyi Ammarah ta bimu taki,

ashe lokacin ta samu wani saurayi ne ya kuma mata alkawarin dinga zuwa shan ruwa wajenta. Sai da na nuna bacin raina kan rashin son binmu 12:47

Sai da na nuna bacin raina kan rashin son binmu a zatona bata son taje ne su hadu da yar uwarta, sai da ta zauna ta fahimtar dani. Naji dadi sosai, dan tace tana son bashi damane ta karanci halayyarsa anay in bikin sallah ai aurensu

kawai. Muni farin ciki da hakan, mun kuma mata fatan alkairi."


   Malikat Haseenat tai shiru tana jan ajiyar zuciya, yayinda Iffah kejin kaguwa matuka da

son jin cigaba, sai dai batayi magana ba har sai da Mammah ta cigaba dan kanta bayan tasha

ruwan zam-zam dake gabanta.


"'Tafiyarmu itace mafarin kaddarar Ammarah,sannan itace mafarin yakice uwa da ga wannan zuri' ar, sannan itace mafarin yin kuka garemu

dama duk al'ummar kasar ruman, sannan itace mafarin hawan Haysam karagar mulki matsayin

madadi ga mahaifinsa. Bayan wucewarmu umarah, bisa yarjewar Jasim UWA ta sakasu yin yankan nan dai dana sa Tajwar Abdul-majeed bijire mata akansa, ta kuma basu umarnin daura auren daya daga cikin kannensu da wani bawa

ko cikin talakawan gari. Son zuciya da sanin makomar dan da ake so a samar ko ya ta

wannan hanyar suka aurar da Ammarah ga dan mai dinka kayan dokin masarautar, domin a

ranar sunzo kawo kayan kwalliyar dokuna na bikin al'ada dake tunkarowa. Babu waya a

lokacin balle ta sanar mana ko wani ya sanar mana,hasalima sunyi auren ne a sirrance sai ita

da suka dauka suka kai wa yaron bisa tirsasashi Ya kusanceta in ba hakaba zasu kashe dukkan

ahalinsa da shi kansa. Dolene ya tsorata ya aikata abinda suke bukata yana kuka itama

tanayi. Shi UBANG|JI mai hikima ne, sun taya ya kuma isar musu bisa ikonsa, badan baya son

Ammarah da wannan bawan ALLAH bane, ba kuma dan yana son nuna Uwa a saman kokarin

mu bane. A'a wannan itace kaddararsu. Kuma ALLAH ya rubuta sai an samar da wannan abun haihuwar ta wannan hanyar. Sai dai alhmallh, ina godema ALLAH da sake gode masa, dan kuwa koba komai ta hanyar biyan sadaki da sheda aure abinda ya farun ya faru. Mun dawo muka

tadda Ammarah a wani irin yanayi, dan kuwa ta birkice musu matuka, a lokacin kowa ya sake

tabbatar da iska a tare da ita. Muni kuka ni da Mahaifinsu da dan uwanta sosai, mahaifinsu

kuma ya fusata a wannan karon har ya kulle Jasim a kurkuku tare da duk wanda suka goya

masa baya akan aikata aikin, yayi kiranyen uwa amma taki zuwa, an sa malamai domin mata

kiranye nanma taki zuwa. Har takai an hada da bokaye irinta amma amsa daya suke bamu tafi

karfinsu. Hankalinmu ya tashi matuka, musamman bayan wasu watanni da ciki ya bayyana ga Ammarah, gashi lafiya taki samuwa gareta, tama koma wata iri kamar mai ciwon

hauka, ta daina magana da kowa, sai kuka,abinci ma sai an tsaya kanta take ci.ALLAH ne kawai

ya zama kariya ga wannan ciki har zuwa ranar haihuwarsa. Tajwar Abdul-majeed ya sakka

a nemo masa mijin da suka aura matan, sai dai anje ba'a dace da samunsu ba, wai sun bar asalin kauyensu a wani dare. Iya nema da bincike kuma ba'a dace ba dole aka hakura. A daren wata juma'a ALLAH ya sauki Ammarah

lafiya, sai dai tasha matukar wahala kafin ALLAH ya kawo haihuwar. Ta haifo yarinyarta mace kyakykyawa, sai dai babu ta inda take kama da ita sai tambarin tabon tawadar ALLAH da zuri'ar wannan gida ke da ita, bamu san mahaifinta ba kuma balle musan ko da shi take kamar. Mun amsheta hannu biyu, sai dai zagaye take da addu'ar neman kariyar UBANGIJI da ga sharrin uwa. A randa aka haifi yarinyar a ranar ALLAH ya

kawo wani mai magani.

Malikat Haseenat ta saki murmushi mai ciwo.Tare da fadin "kin san wani abu?" kai Iffah da ke sharar hawaye ta girgiza mata. Malikat Haseenat ta sake sakin murmushi. "Mai maganin nan hatsabilin kansa ne, dan kira daya yayma uwa a randa ya cika kwana uku a masarautar nan a take ta bayyana gabansa

gaban kowa wujiga-wujiga. Ya tabbatar mata shi ba azzalumi bane, da sai ya wahal da rayuwarta ta yanda bata isa sake numfashi a duniya ba, amma ko'a yanzu bazai kyaleta ba sai ya nakasa rayuwarta ta yanda bazata kara tunanin cutar da

Wani ba. Ya sakata ta warware duka wani tsafi data aikata zagaye damu batare da mun sani ba, sannan ya bude dukkan surukanta a gabanmu yay mata korar wulakanci da gargadi

mai tsaurin gaske. Sosai ta dinga kuka da neman gafara da tabbatar masa ta zubda

makaman yakinta bazata sake ba a barta taci gaba da rayuwa damu amma yaki saurarenta.

Majiya karfin hadimai aka saka suka kwasheta zuwa can tsakkiyar dokar jeji mai tsananin rintsi da hadari suka jefar da ita. Wannan shine mafarin barin uwa tare damu, sai dai kuma a

wannan dare ALLAH yay ma jaririyar da Ammarah ta haifa rasuwa, washe gari shima

Shahan-shan Abdul-majeed yabar duniya sakamakon bugawar zuciya da saran macijin da aka rasa tushensa, sai kuma ya kwana da tashin hankalin abubuwan da Uwa ta dinga sakasu sunayi na shirka da yanda bayan ya tsawatar wasu suka zagaye sunayi ciki harda dansa

Jasim. Abdul-majeed ya rasu, uwa ta shude,jinjirar Ammarah ta koma. Haysam ya zama

Shahan-shan. Bayan duk faruwar wadan nan abubuwa da shudewarsu zukata suka hakura

abubuwa suka fara komawa dai-dai. Saurayin nan da Ammarah ta shirya gabatar mana matsayin miji ya dawo da burin aurenta duk da ba'a boye masa komai da take ciki ba. Yace yaji

ya gani, dan ko a baya da ya janye jikinsaJasim

a samesa da gargadin karya sake zuwa an mata aure. Bayan kuma yaji an saketa dan auren kwata-kwata na sati biyu ne ya sake dawowa amma aka hana mishi ganinta ma kwata-kwata.

Ammarah taso bijirewa, dan har lokacin bata dawo dai-dai ba, amma naita lallabata da mata

nasiha ni da yar uwarta hatta hakura aka daura aure. Sai dai sam auren bai wani je ko'inaba ta

fito, sakamakon wata sabuwar kaddarar data afka mata, a duk sanda mijinta zaije gareta sai a

sauya halittar matancinta ta koma ta namiji.Dole babu yanda zaiyi ya rabu da ita ta dawo

gida, daga nan bata sake aure ba, daga nan bamu sake jin labarin uwa ba, daga nan bamu

sake jin labarin bawan ALLAHn nan da ya taimake mu ba akan Uwa ba, daga nan Jasim ya

nuna mana ya tuba, sha'anin mulkin Haysam ya cigaba da tafiya a tsaftace dan a masa

gargadin nisantar duk wan mushiriki akan al'amurin mulkinsa..Hawaye sosai Iffah takeyi na tausayin Daneen Ammarah, da tausayin su Malikat Haseenat dan labarin nan ya matukar girgizata, al'amari haka

kamar a wasan kwaikwayo, wannan wace irin duniya ce mai cike da son zuciya. Kowa burinsa

ya kasance a sama, mai nasara bisa nasarar dan uwansa, kai kai rayuwar gidan sarauta dabance,

dabance a cikin duk wani rikicin gidaje da zuri'arsu. YaYanda Iffah ke kuka sai Malikat Haseenat ce ta koma lallashinta. Sai da ta

tabbatar ta samu nutsuwa sannan ta mikar da ita. "Hafida-ti, kinga tashi ki tafi dare yayi maybe ma mijinki nacan na jiranki".


Cikin share hawaye Iffah tace, "Ai bai san ma na taho nan ba".


Idanu sosai Mammah ta waro da fadin "Ya ALLAH, aiko kinyi laifi, maza wanko fuskarki muje na miki rakkiya to".


Bata musa ba taje ta wanko fuskar, Malikat Haseenat ta mika mata wata yar kyakykyawar

jaka tana murmushi. "Kije da wannan, duk abinda ke ciki kiyi kokarin dinga amfani da shi

kamar yanda na rubuta, ki yawaita shiga ruwan zafi har ki saba da daina jin ciwon".


Kai Iffah ta sunkuyar cike da jin kunya, sambatai tunanin Mammah din zata gane ba yau,

musamman yanda take dauriyar dai-daita tafiyarta duk da zafin da take ji……..✍️


No comments

Powered by Blogger.