Daudar Gora Book 2 page 57

 


Chapter: 57


"Kinci abinci?".


Kanta ta girgiza masa alamar a'a.


"Mi yasa?".


"Banajin yunwa ne".


Shiru bai sake cewa komai ba har kusan minti daya. Hannunsa da ke kan bayanta ya dago ya daura saman goshinta data kwantar jikinsa, kan da zafi sosai har ma yana iya jinsa.


"Na miki addu'a?".


Nan ma kan ta daga masa. Komai bai sake cewa ba shima. Sai matsawa da su da yay zuwa gadon, tana a jikin nasa ya kai zaune itama ya zaunar da ita a cinyarsa. Addu'a ya fara mata a kan idanunta a lumshe, bayan ya kammala ta kwantar da kanta a kafadarsa tai luff tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Nan ma sun jima a zaman shiru kafin ya kirata muryarsa a can kasan makoshi.


"Mrs Eshaan?".


"Uhmyim".


Ta amsa itama can kasa batare data dago kanta da ke a kafadarsa ba.


"Miyasa kika boye min?".


Bata fahimci mi yake nufi ba, dan haka ta dago idanunta da jan cikinsu ke dan raguwa a hankali ta zuba masa. Bazata iya jurar kallonsa cikin ido ba dan haka ta dauke su ta maida gefe. "Ban san akan mi kake magana ba Sultan". Sai da ya dan furzar da hucin baci ran da yake ta dannewa, a dan fuse ya furta, "Jasim!

Miyasa kika boyen ya sameki a kurkuku da maganar banza?"


Shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma ta motsa cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, "Kayi hakuri, a lokacin ban san ta yanda zan tunkareka ba. Ban kuma san ta yanda zaka fahimceni ba. Kuma ai ALLAH ya kareni da ga sharrinsa tunda ga shi yau gaskiya tayi halinta".


Shiru baice komai ba, dan zuciyarsa tafasar kishi take har yanzu akan wanna kalmar, tafi komai tsaya masa a zuciya fiye da abinda Miran Jasim din ya aikata masa dan ya jima da sanin dama suna farautar rayuwarsa. Sai maganar rashin fitowar sunan Miran Arshaan shima na masa kaikawo, kamar zai mata magana akan hakan sai kuma dai ya hadiye kayansa da tunanin ko Miran Jasim din ne kawai ya fiddo mata da nasa hali. Amma in bai manta ba ranar a kalamanta ta masa nuni ne da mutane biyu ko yace fiye da daya. Hakan na nufin bayan Jasim din akwai wani kenan. To miyasa ta boye? Bashi da mai basa amsa baya kuma bukatar son ji da gareta yanzu dan ransa duk babu dadi yake ji.Itama da kanta ta fahimci hakan, dan fuskarsa a tsuke take fiye da sanda suka fita kotun. Sai duk take jin kuma babu dadi. Dan haka kawai take jin tausayinsa. Idan har zai shiga damuwa saboda halin wancan karen uncle din nasa, yaya zai kasance kuma a randa zai san mahaifiyarsa da kanta ke halaka masa matan aurensa da duniya ke kallonsa a mai halakasu tsahon shekaru. Kai kai wannan al'amarin fa na taba mata zuciya why sosai matuka. Ajiyar zuciya ta dan sauke a hankali, sai kuma ta kai hanunta saman lallausan gashin sajen fuskarsa ta shafa. Murya can ciki ta ce, "Kayi hakuri? Ka amsa da hannu biyu jarabawace. Badan UBANGIJI baya sonka ba ya jarabeka da su. Shi kansa mulkin ma da kake kai ai jarabawa ce. Kai numfashinmu ma kansa jarabawace a garemu, dan UBANGIJI ya azurtamu da shine domin yaga zamu kasance masu bin dokokinsa ne ko kuwa masu bijire masa". 


Idanunsa da ke lumshe tun sanda ta daura hanunta saman fuskarsa ya bude a hankali, sunyi zajur fiye da yanda ya shigo da su a dan birkice. Hannun ya kamo yana kallonta, cikin tsananin kasala ya daura lips dinsa a tsakkiyar tafin ya sumbata. Sai da ta matse jikinta tsabar la jininta yay wata irin yamutsawa har brain. Yunkurawa tai da nufin tashi a jikinsa ya hanata hakan, sai ma fuskarta da ya kamo cikin tafukan hannunsa ya manne lips dinsu waje guda. A tare suka saki ajiyar zuciya Iffah na rumtse idanu da karfi. A tsorace take matuka,amma ta danne ta karfin tsiya domin taimaka masa ya samu nutsuwar zuciya kamar yanda Mammy ta mata nasiha akan a duk sanda taga ya shigo da fushi tai kokarin gain ta cire masa wannan fushin da damuwar ta hanyar jansa jikinta da hira da raha ko nasiha. Idan kuma ya nuna bukatar wata hidimtawarta ko ita ta fahimci akwai abinda ke sakashi shagala ko kwaranyewar damuwarsa da wuri to tazama jaruma wajen aikatawa kota bashi hadin kai. Tunanin a iya abinda yake yi din baza'ai gaba ba ya sata sakar masa jiki harta fara bashi hadin kai. Gaba daya ta sake rikita masa lissafi, dan abune da bai zaton samu da ga gareta ba anan kusa haka. Tuni idanunsa sun rufe ya juyesu a gadon ya shiga yamutsata yanda yake so cikin nutsuwarsa, dan a rayuwa komai na Tajwar Eshaan babu gaggawa a ciki, koda kuwa yana a wani yanayi ne da zai iya canjawa sai kaga a zahirance babu wanna canjin a gaggawa garesa. Dan nutsuwa da kasaita a jinin jikinsa take yawo da harbawar bugun zuciyarsa. Jin al'amarin ya fara zarce karamin tunaninta tuni ta fara son kwatar kanta. Sai dai kuma babu hanyar samun wanna damar da ga jarumin ,Shin yaya lafiyar giwa da ma. Balle kuma ita da kanta ta balle likin. Duk yanda taso tuna masa dinkin dake a tare da ita babu alamar yana ma iya jinta balle fahimta. Burinsa kawai yake kokarin cimmawa a cikin rufewar idanu..






(* Tsun-tsun da ya ja ruwa (?))





***








Da karfi, karfin karfi yake buga kansa a bangon dakin kurkukun mai tsananin duhu da ta iya karamin windown kawai ake iya gain dan ziririn haske. Gaba daya zuciyarsa ta bushe, zafi

yakeji a cikinta mai tsananin tururi dake kona zuciya. Shi shi Jasim ibn Abdul-majeed Aliy Qutb ne wata karamar yar iskar yarinya yar cikin cikinsa tai sanadin kawowa cikin kurkuku. Shi Arshaan da ya koya sanin kansa a wajensa zai yima cin amana? Shi hadiminsa da ya dauka tsahon shekaru yana kyautatama zai ci Amanarsa a gaban makiyansa. Wace irin wannan, mai tsananin duhuwa da babu lissafinta a cikin duka lissafe-lissafensa. Ta yaya shi Jasim in Abdul-majeed Aliy Qutb zai yi irin wannan faduwar bakar tasan a gaban karfin ikon dan makiyansa kuma makiyinsa.



Cigaba da buga kan yake da karfinsa yana ihu mai tsananin karaji da ya saka masu tsaron dakun kurkukun nasa da Tajwar Eshaan ya bada umarnin bama tsar mai tsananin tsauri tsora.Cikin karfin hali daya a cikinsu ya dan leko, ta dan hasken da ya hasko da ga karamin windown ya hango fuskar Miran Jasim da tai wani irin jage-jage da jini dan ya fasa goshinsa.A zabire yay baya yana zazzaro idanu. Yan uwansa ya sanarma, babu bata lokaci sukai kiran shugaban jami'ai suka sanar masa dai-dai da yanke jikin Miran Jasim da jini ke rinjayarsa va fadi kasa....






Rungumeta yay tsam-tsam a cikin jikinsa idanunsa a lumshe. Jin kukanta yake har tsakkiyar zuciyarsa. Dan kuka take sosai fiye dana daren shekara jiya kasancewar yau fami yay akan ciwo.



"Ni ka kaini wajensu Ummu".


Ta fada cikin kuka. Yanda tai magana tana sake barke masa da kuka ga hawaye shabe-shabe harda su majina ya sa yaji dariya na yunkuro masa. Kamar ba yanzu ta gama iyayi a kotu ba,dan duk abinda ta dingama Miran Jasim akan idonsa ne tsaf. Amma jiba yanzu a dan abinda bai taka kara ya karya ba ta koma abin tausayi.Ya fahimci sai ya dage matukar dagewa akan dorata a irin layin da yake bukata ta hau inba hakaba ragguwa za'ai, bakinne kawai cike da zance da tsiwa. Bashi da burin sake wani auren bayan ita, dan haka dolene ta shirya karbarsa a duk sanda yazo. Murmushin da ke neman kufce masan ya hadiye da kyar da saka hannu yana goge mata fuskar data kwabe da hawaye. Cikin dadisashiyar muryarsa data kara komawa can kasan makoshi a fusge ya furta, "Am sorrybazan kara ba".


"Wlhy zaka kara, ranar ba sai da kace bazaka sake ba amma yau ka kara, ni bazan sake zama a sashen na a kasheni kwana na bai kare ba". Ta kara barke ma sa da kukan tabara.


Yanzu kam kasa rike dariyar yayi, dole ya Murmusa har jerarrun fararen hakwaransa masu da siririyar wushirya na bayyana a zahiri Bashi da zabin da ya wuce sake rungumeta a jkinsa tsam-tsam yay murmushinsa iya san ransa. (Shi kam wannan Fitinanniyar yarinya ALLAH ya bashi, kuma yana so da kaunar abinsa fiye da zaton mai hasashe). A zuciyarsa

yake maganar yana bata sumbata masu kyau a wuya. Kafin ya mike ya dagata cak zuwa bathroom. Idanunta ta rumtse sosai da kankamesa ita a dole karya gammata jiki kar kuma ta gansa itama.


Gashi yay mata mai kyau bayan ya duba yau baiyi barna ba dan ciwukan wancan ranar ma sun warke sai abinda ba'a rasa ba, taimaka mata yay tai wanka, hawaye kuwa da ya ga ba dainawa zatai ba bai sake ce mata komai ba kansu. Da zasu fito cewa tai ita why bazata iya ba sai dai ya dauke ta. Baice komai ba, illa murmushi da yay a zuciyarsa ya dauke ta cak suka fito tana faman tura masa karamin bakinta.Ga idanu sunyi luhu-luhu na kukan da tasha.


"Idan baki bar turamin bakin nan ba zan maimaita ni babu ruwana". Ya fada yana tsane mata laimar ruwan kanta da towel. Narai-narai tai da fuska zata sake masa kuka ya daura yatsansa saman bakinta ya ce, "Shilli!! Harda kuka ma". Babu shiri ta hadiye abunta da maida bakin da sauri. Murmushi ya saki da cigaba da tsane  mata gashin…. kiran da ya shigo ta sashi dakatawa su duka suka dubi wayar, kamar bazai daga ba dan har tana gab da tsinkewa sai kuma ya kai hannu ya dauka batare daya matsa da ga gabanta ba ko dauke towel din da ga kanta.


Cikin girmamawa shugaban jami'ai ya shiga gaishesa da ga can, a takaice ya amsa masa murya a dake kamar bashine ke hidimtawa yar yarinya ba. Da ga can shugaban jami'ai ya kara nutsuwa sannan yay masa bayanin abinda ke faruwa. Shiru kamar bazaice komai ba kafin ya nisa a dan fisge da maganar nan tasa kasa-kasa ya ce, "Doctor Afif ya je ya dubasa a cikin kurkukun". Daga haka ya yanke kiran.

  

     Kallonsa Iffah tai da jajayen idanunta, gaba daya ya sauya kamar bashi ba ya koma mata Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed da ta fara gani a sashen Mammah. Muryarta a dashe saboda kukan da tasha ta ce, "Miya faru?".Kamar bazai kulata ba yana cigaba da goge mata kan tsahon minti biyu kafin ya motsa lips da kyar ya furta "Jasim"……….✍️


No comments

Powered by Blogger.