Daudar Gora Book 2 page 55

 


Book2 (pg55)

Il

A

..Wani irin fadawa tai saman gado cike da farin ciki tana sakin siririyar dariya. Babu abinda take hangowa sai idanun Miran Jasim da na Malikat Bushirat harma da Miran

Arshaan. Tai wani irin juya ta sake juyawa a gadon sai kace tarwada. "Kina lokacinki Fhareedah bint Zayyan". Ta fada a fili tana sake kyalkyalewa da dariyarta kai kace an mata albishir ne da dawowar su Baby kasar ruman. Yanda take ji kam kamar ta tashi tayita taka rawa. Daya da ga cikin burikanta ya cika, ya cika a gabar da ALLAH ya bata abinda baya cikin lissafinta. Tabbas zama mallakin Shahan-shan baya cikin lissafinta. Lissafinta na daukar fansa ne kawai,fansar jinin yan uwanta da bazata iya yafewa ba. Sai dai kuma dukkan labarin ya canja, ya canja da canjawar shigowar su Miran Jasim cikin tattakinta batare data tsaro da su ba. Shigowar Tajwar Eshaan in Haysam Abdul-majeed matsayin wani abu mai daraja a ciki labarinta batare da ta rubuto da hakan ba nan ma. "Ya rabba" ta fada a zahiri tana lumshe idanunta da sukai wani tar-tar na haske fuskarta na kara kawatuwa da murmushi mai kayatarwa.


"Miyasa kika boye min?".


Bata fahimci mi yake nufi ba, dan haka ta idanunta da jan cikinsu ke dan raguwa a hankali ta zuba masa. Bazata iya jurar kallonsa cikin ido ba dan haka ta dauke su ta maida gefe. "Ban san akan mi kake magana ba Sultan".


Sai da ya dan furzar da hucin baci ran da yake ta dannewa, a dan fuse ya furta, "Jasim! Miyasa kika boyen ya sameki a kurkuku da maganar banza?"


     Shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma ta motsa cikin sauke ajiyar zuciya ta ce, "Kayi hakuri, a lokacin ban san ta yanda zan tunkareka ba. Ban kuma san ta yanda zaka fahimceni ba. Kuma ai ALLAH ya kareni da ga sharrinsa tunda ga shi yau gaskiya tayi halinta".


Shiru baice komai ba, dan zuciyarsa tafasar kishi take har yanzu akan wanna kalmar, tafi komai tsaya masa a zuciya fiye da abinda Miran Jasim din ya aikata masa dan ya jima da sanin dama suna farautar rayuwarsa. Sai maganar rashin fitowar sunan Miran Arshaan shima na masa kaikawo, kamar zai mata magana akan hakan sai kuma dai ya hadiye kayansa da tunanin ko Miran Jasim din ne kawai ya fiddo mata da nasa hali. Amma in bai manta ba ranar a kalamanta ta masa nuni ne da mutane biyu ko yace fiye da daya. Hakan na nufin bayan Jasim din akwai wani kenan. To miyasa ta boye? Bashi baice komal ba ya dal cigaba da kallonta. Kusan minti daya sannan ya motsa da cigaba da don takawa a hankali cike da kasaitar nan tasa. gabanta yaja ya tsaya, tare da zare hannunsa dake cikin aljihun wandon jeans dinsa ya mika mata. Idanunta ta dago ta kalli hannun da ke fari tas da shi, ga jini nata kaikawo a tafin kamar ba namiji ba. Idanunsa ya dan lumshe da budewa a lokaci guda yana gyada mata kai alamar ta daura nata. Kamar mai jin tsoron hakan ta dago natan ta dora a cikin nasan. Sake lumshe idanun yayi kamar wani wanda maganadisu ya taba,batare da ya bude ba ya dagota ta mike tsaye itama. Matsota yay kawai jikinsa ya rungumeta tsam-tsam. Sassanyar ajiyar zuciya ta saki nutsuwa na ratsata, sai kawai ta kankamesa itama tare da kwanciya luff a faffadan kirjinsa tana shakar daddadan kamshin turarensa mai saka zuciyar mai shaka nutsuwa

_Oh oh su Iffah an waye an manta da mu dangi

Mammah duniya abin tsoro ce why, duk da mun jima da sanin Jasim baya kaunar Abni sai yau din da komai ya fito fili ya bani mamaki. Har zuciyata iya abinda nake kallonsa da shi shine nuna adawa kawai ga mulkin tunda shine burinsa. Amma why ban taba kawo zai iya shirya halaka rayuwarsa ba haka. Wace irin rayuwa ce wannan wai dan uwanka jininka ya zabi cutar da kai akan abin duniya mai yankewa. Wai ina mahaifinmu da ya zama sanadin kawomu duniyar ma? A da shine a wannan kujerar, amma ya shude kamar ba'ayisa ba, aka daura dan uwanmu, shima ya shude kamar baiyi ba, idan sukai hakuri shima wataran bashi bane anan din. Bazan boye miki ba Mammah,zuciyata ta fara min sake-sake da kokwanto akan rasuwar Haysam Akhi, haka Zawjata-almilk da muka rasa, anya kuwa hakan baida alaka da su Jasim Akhi ya karba makamancin tayin da muka jima da tsigesa a cikin jininmu?. Dan zuciyata ta fara rabuwa biyu bayan zargin mushirakar can data dade da shudewa a tarihinmu kamar akwai wata mai irin al'amuranta a yau zagaye da wani namu".

Malikat Haseenat da ke ta faman jinjina kai taja ajiyar zuciya mai karfi tare da fesar da iska zazzafa da ga bakinta. "Tabbas duniya ta cancanci zama abar toro kam Ammarah, nima kuma kamar ke zuciyata ta fara rawa, ta fara rawa da wannan gabar har inajin ni kaina ban yarda da kaina ba. Tabbas mushirikar can ta shude ita da tarihinta, amma sai zuciyata ta gagara nutsuwa da hakan duk da tsahon shekarun nan da suka shude da kasancewarta.Babu abinda Jasim bazai iya aikatawa ba,musamman idan na kalla irin mugun zaman da mukai da mahaifiyarsa a masarautar nan. Dan haka shima kam yanzu abin tuhuma ne. Sai dai akwai wani furuci da yarinyar nan tayi yafa tsaya mun a rai, tun dazun kuma yake mun kai kaWO….

"Wane furuci kenan Mammah?".

"Furucin bibiyar gawar Zawjata-almilk ta karshe da muka rasa, inda ya zama sanadin haduwarta da Jasim. Lallai ina bukatar ganawa da Zawjata-almilk".

      Shiru Daneen Ammarah tai tana kallon Mammah, sai kuma ta nisa itama zuciyarta na mata kai kawo akan hakan. Eh tabbas wannan furuci abin a bibiya ne, dan sai a mahanga ya ke da nasaba da abu biyu. Shi kansa Jasim suspect ne a wannan case din shima. Duk da dai duk Zawjata-almilk na baya da suka rasa ransu suke fara zuwa su ganta kafin kowa.

Firgigita ta daw hankalinta sakamakon tabatan dan Malikat Haseenat tayi, taja ajiyar zuciya mai nauyi da sauke numfashi. "Yi hakuri mammah, why na tafi wata duniyar tunan nima. Za'ai bincike ga Ibnati dinne? Ko kuwa ya kike nufi?".

Kai Malikat Haseenat ta jinjina da fadin, "Fara nemo min ita a waya".

*Har yanzu Iffah na kwance a kan gado cike da farin ciki da nishadi kira ya shigo a landline din dakin. Wayar ta kalla kamar bazata tashi ba. Sai kuma ta mike lokacin da take gab da yankewa ta daga. Kin yin magana tai, sai da Daneen Ammarah tai sallama sai kuma duk ta rude. "Lah Mamy kece, Barka da wannan lokaci a gafarceni". Murmushi Daneen Ammarah ta saki mai sanyi da ga can tamkar Iffah'r na gabanta, tana matukar kaunar yarinyar nan ta yanda ita kanta ma bata san adadi ba. A hankali ta nisa da sakin ajiyar zuciya ta ce, "Ba komai Ibnati, Mammah ce ke bukatar magana da ke daman". Tamkar Iffah na gaban Malikat Haseenat ne cike da girmamawa ta gaisheta duk da yanzun nan suke rabuwa da ga zaman kotu. Da ga can ta amsa mata cike da nutsuwa da dattakonta, kafin ta aura da fadin, "Mijinki ya shigo ne?". A hankali Iffah da kalmar ta bama kunya da yi mata nauyi ta ce, "A'a Mammah".Murmushi Mamma ta sakeyi da gyada kai da fadin, "Idan har bakya wani uziri bayan sallar isha'i ina son ganinki". Cike da girmamawa ta ce,

"To Mammah insha ALLAHU".

Shiru tai tana kallon wayar bayan ta yanke.Zuciyarta sai faman mata kaikawo take da tunani kala-kala. Sai kuma ta dage gira da dan tabe baki tana ajiye kan wayar ta mike. Ficewa tai da ga dakin ta nufi can saman ginin dan wajen na matukar kayatar da ita. Tana kaunarsa fiye da kowane waje a masarautar.

"Abu Harith kana lafiya kuwa? Tunda muka baro kotu ka kasa zaune ka kasa tsaye. Duk da dai nasan abinda dan uwanka ya aikata ga wannan bawan ALLAH dole ya tabaka, amma sai nake ga damuwar taka da rudanin kamar sunma fi na kowa. Ka tuna nima fa dan yar uwata ce dat rikeni tamkar uwa, sannan shugabanmu baki daya. Mu dukanmu ya sakamu muka haukace akan baiwar ALLAHr yarinyar nan da bataji ba bata gani ba. Why har kunyar haduwa da ita nakeji yanzu. ALLAH sarki Mammah tai ta son nuna mana gaskiya muna bijirewa, duk da 

nuna mana gaskiya muna bijirewa, duk da ALLAH ne shaidata kai ne ka dinga kara tunzurani har idanuna sukai makancewar kasa hasashen komai gashi na kare da dana sani" 

Kallonta kawai yake tana zabga zance ko hadiyar yawu batayi, bata san jima yake tamkar ya shakota ba tsabar takaici da takura masa da tai. Shifa shi kadai yasan irin kalar tashin hankali da rudanin da yake ciki akan al'amurin nan. Da farko yayi zaton hadiminsa na aikine bisa aikinsa na tsawon shekaru da ya daurasa a kai akan bibiyar dan uwansa, sai dai kallon da yarinyar nan Iffah tai masa sanda suke fitowa daga kotun ya matukar saka zuciyarsa neman bugawa. Idan har ya canka dai-dai lokacin da take shigewa *_Next.…_* ta rubuta masa akan iska fa. Wannan kalmar itace ta tsaya masa a zuciya taki fadawa sai faman kaiwa da komowa take.....

"Ya ilahi Abu Harith!!".

Jasrah da ke hargowar kwala kiran sunansa ta katse masa tunani. Cikin bacin rai ya nuna mata kofa alamar ta fice masa. Rai bace take dubansa itama, har taji ta kasa hakuri ta ce,"Kamar ya na fita bayan kuma magana muke?Wai shin kodai kaima da naka kashin ne a jiki banda labari, dan wannan yanayin naka kam ya fara sakani a rudani..

"Jasrahhh!!!".

Ya fada cikin karajin da ya sakata zabura. Cikin wata irin birkicewa da bata taba fuskanta da ga garesa ba ya sake nuna mata kofa. "Wihy idan baki fita min ba sai na kwashe fuskarki da maruka. Banza kawai kin dameni, ki barni naji da abinda ya isheni ban san wawanci".


      Ba karamin tsorata Jasrah tayi ba kam, dan wutar bala"i ta gano kuru-kuru cikin idanunsa da kan fuskarsa. Cike da sassarfa ta nufi hanyar fita ranta a bace da tsawar da yay mata.... Tana gama ficewa yaja wani shegen wawan tsaki da raka bayanta da harara ya ce,

"Tinkiya kawai, ban san damuwa",. A wani irin zafafe ya koma jagwab cikin kujerar ya zauna yana dafe kansa da ke sara masa da karfin masifa. Dai-dai nan kira ya shigo wayarsa. Sharewa yay bai dauka ba har ta tsinke, sai kuma ga wani ya sake shigowa. Tsaki yaja da finciko wayar daga aljihu da niyar kashewa gaba daya yaci karo da sunan Ameera Haifah baro-baro. Kamar bazai daga ba nan ma sai kuma ya amsa a fusace da kaita kunnensa. "Ke kuma miye kike wani kirana a wannan lokacin bayan kin san mi ake ciki".


Da ga can cikin muryar tashin hankali ta ce,"Dolene na kiraka Arshaan. Dan tabbas akwai matsala. Matsala babba why. Na kasa gane komai, ka saka zuciyata a rudani gaba daya game da abinda ka aikata a kotu. Shin mi hakan ke nufi? Taya komai da muka aikata mu ukkoma kansa shi kadai? Kai ne kai hakan kokuwa hatsabibin yaron can ne ya kulla mana gadar zare ta hanyar yar iskar yarinyar can. Wihy kaina ya kwance gaba daya, dan ALLAH ka zaba mana wajen haduwa yanzu da gaggawa kar zuciyata ta buga".


"Da zata buga din ma da kowa ya huta.Please malama ki kyaleni bana bukatar magana da kowa okay". Kittt ya yanke wayar batare da jiran cewarta ba."Ashe zan kasheka na kashe banza idan kace zaka zamar min matsala Arshaannn!!!".


Ta fada cikin karaji da cije lips dinta jikinta na rawa. Wayar ta cilla saman gadonta ta cigaba da kaikawon da take tun dazun a cikin dakin. Tunda ta baro kotu ta gagara zaune ta gagara tsaye.Tasan in har Miran Arshaan ne ya shirya komai ga Miran Jasim hakan na nufin itama bazata tsira ba dan tare sue kulla komai. Idan kuma Tajwar Eshaan ne ya ganosu kama Miran Jasim kawai ba komai bane garesu face talala. Don dole ma akwai wani abu da ya kamata ta sani, dole ta sanshi a yau din nan yanzun nan basai gobe ba. Idan Miran Arshaan ya cigaba da wofantar da tuhumar da take masa to lallai zai ganta yanzu a sashensa kuwa. Sai dai duk ma abinda matar tasa zata zarga ta zarga. Ko kuma in ma barewa zatai why sai dai ta bare da su su duka amma bazata taba barin Miran Arshaan ya sha ba shima ko ya kaita kasa kamar yanda ya kai Jasim. A fusace ta sake fisgar wayarta ta hau rubuta masa dogon text message jikinta sai tsuma yake. Ga uwar zufa ta mata sharban kamar wadda taci gudu a cikin dokar jejin da babu komai sai sahara mai zafi da ta dauki zafin rana.

Yi take kamar zata tsumbula cikin wayarta dake a hanunta. Ihu kawai ya rage ta kurma akan kiran Daneen Waheeda da take faman yi tun bayan fitowarsu kotu amma bata daga ba.Ta bata lokaci da tunanin zatai kiranta in ta gani amma babu alamar hakan zata faru. Kuma asha ba shima ko ya kaita kasa kamar yanda ya kai jasim. A fusace ta sake fisgar wayarta hau rubuta masa dogon text message jikinta sai tsuma yake. Ga uwar zufa ta mata sharban kamar wadda taci gudu a cikin dokar jejin da babu komai sai sahara mai zafi da ta dauki zafin rana..

Yi take kamar zata tsumbula cikin wayarta dake a hanunta. Ihu kawai ya rage ta kurma akan kiran Daneen Waheeda da take faman yi tun bayan fitowarsu kotu amma bata daga ba.Ta bata lokaci da tunanin zatai kiranta in ta gani amma babu alamar hakan zata faru. Kuma a kalla kira na goma sha bakwai kenan take mata.Banda text message da zai iya zama biyar koma fiye da hakan.


Kamar almara aka daga wayar, cikin rawa da kakkarwar jiki ta kaita kunnenta tana fadin.


No comments

Powered by Blogger.