Daudar Gora Book 2 page 54


 Book2 (54)

......."Ko zaka iya gane mutum idan ka sakeganinsa".

      "Sosai ma kuwa. Dan akwai ma cctv footage na abinda duk ya faru a tsakaninmu batare da shi ya san inada camara a wajen ba." ya kare maganar yana duban shugaban

jami'ai. Ya fahimci mi yake nufi, dan haka ya mike ya mikawa Sayeed Hanifud-Din flash da ke a hannunsa, anan take kuwa aka saka flash jikin lap-top aka kai gaban Tajwar Eshaan, sai ko ga duk abinda ya fada din dalla-dalla.


       An shigo da wanda ya amso dafin macizan, wanda ya kasance amintaccen hadimi ne ga Miran Jasim, kowa ya sani kuma a masarautar nan, dan tun yana a matashin saurayi ma yake tare da hadimin, shine ke masa duk wasu ayyuka na sirrinsa dama na mugunta. Ai Miran Jasim baima san yay wata iriyar zaburar tashin hankali ba jikinsa na kakkarwa. Yayinda gaba daya kotun ta dauka yan kananan magana har sai da aka tsawatar. Sayeed Hanifud-Din da shima dai gaba daya jikinsa yay sanyi da al'amarin ganin daga inda ya fito, dan koba'a fada ba komai a bayyane yake. Fuskantar hadimin da gaba daya ya fita hayyacinsa a hannun jami'ai yay. "

"Bama bukatar wani kwana

ja da ga gareka ko ja' in ja, fadar gaskiyarka na nufin zaka iya samun sassauci, zabar yin taurin kai kuwa ya rage naka. WANENE YA

SAKA?".

A hankali hadimin ya dago ya dan dubi inda

su Miran Jasim suke, idanu suka hada da Miran

Arshaan da yake masa kallon kasa-kasa yana

wani dan motsa yatsunsa. Ajiyar zuciya ya ja a

hankali, kafin ya maida dubansa ga Sayeed

Hanifud-Din. Kai tsaye babu wata kwana-kwana ya ce, "Shugabana Miran Jasim ne ya sakani


      A take kotun ta dauki wani irin hun karajin Miran Jasim da ya zaburo kan hadimin nasa, sai da jami'ai suka rirrikesa. Yayinda jama'a suka hau salati suma har sai da aka tsawatar. Hadimin ya cigaba da fadin, "Sai dai ni ban san mizaiyi da ita ba, amma a gabana ya zubashi a cikin madara ya bani madarar yace na kai sashen Zawjata-almilk nace daga sashen uwar masu gida. Bani da ikon cemasa a'a, amma navi niyyar kin kaiwa sai dai nasan zai iya sawa a bibiyeni idan nai hakan zai halakani kuma, dan haka na cika umarninsa amma ni duk tunanina ma Zawjata-almilk din zai ba. A ranar nata kokarin ganin samun ganawa da ko amintaccen adalin shugabanmu ne amma hakan bai faruba,da ga karshe ma sai naji wai ashe shine za'a bama madarar ta hanyar Zawjata-almilk ba kamar yanda nai tunanin itace zai bamawa din

ba. Kuma zan fadi gaskiya, ba laifin Zawjata-almilk bane ba asiri yay mata kan duk yanda yaso haka zaiyi da ita, daga baya itama zai kasheta.


        Duk yanda akaso samun nutsuwar kotun kam hakan ta gagara. Salati kawai kake ji da la'antar Miran Jasim da akeyi. Iffah ta saki wani irin shegen murmushi tana mai kallon Miran Jasim da yay sumar tsaye. Sai kuma ta maida kan Miran Arshaan da gaba daya yay sharkaf da zufa. Wata dariya ta kyalkyale da shi a zuciyarta tana fain (tun banzo kanka ba) a zahiri kam baka isa fassara yanayinta ba.


      A bangaren Miran Arshaan kam ya dauka makircinsa ne yay tasiri kan Miran Jasim. Dan kuwa hasalima shiya tura hadimin ya shiga jikinsa duk tsawon wanna shekarun da suke a tare, dan kawai ya san duk wani motsinsa Abinda bai sani ba a yanzu hadimin ba aikinsa yake ba aikin Iffah yake yi, ita kuma ta zabi tattara laifin ga Miran Jasim a karan kanta saboda haka ta tsara binsu daddaya, shi kuma zata cigaba da jansa a kasa har zuwa gabar da take so..


      Wata irin daddagewa da fashewa da kuka da Miran Arshaan yay ne ya katse mata tunaninta. Ta zubama drama din tasa ido dan ya wani daddagene ya fashe da kuka yana duban Miran Jasim kai kace dada duniya har zuciyarsa ne. "Jasim! Jasim Akhi mu zakama haka? Kai da kanka zakaci amanar dan uwanmu ka zama jagoran shirya halakashi. Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un.…. Mi kake bukata ne? Miye dan uwanmu bai mana na gata ba a wannan duniyar? Ya rikemu tamkar yanda Abie (Tajwar Abdul-majeed) zai rikemu, amma mu mu kasa rike jininsa daya tilo a duniya da bashi goyon bayan mulkin da ALLAH ya daura masa. Dama na jima ina zargin kana kwadayin mulkin nan ne,ban tabbatar da hakan ba sai randa aka samu kayan tsafin daka saka a kujerar da adalin shugabanmu yake zama, kaki zuwa kuma wajen meeting da ga karshe ma bakin cikin an ganoka ka nema halaka iyalinka" ya sake fashewa da kuka.


      Wata irin mahaukaciyar shaka Miran Jasim da jikinsa ya hau kakkarwa ya kaima Miran Arshaan da kyar kuwa aka bangaresa yana fadin sai ya kashe Miran Arshaan din.


   Duk da wannan dambarwa mai gayya mai aiki Shahan-shan na zaune ne yana binsu da kallo ta cikin gilashinsa. Shi kansa a wannan gabar sai ya shiga dan rudani, dan a iya bibiyar rayuwar uncle's din nasa da yake yi tun lokacin da ya fara zarginsu a tare suke aikata komai sai dai a sirrance ne kam. Kuma ita kanta Iffah ta sanar masa su biyu ne ai, amma yaya akai hakan ta kasance komai ya juye kan Miran Jasim shi kadai.


     Tamkar Sayeed Hanifud-Din kam yasan mike ransa ya ambato sunanta. "Ko Zawiata-almilk nada wani karin bayani akan alakarta da Miran Jasim da har hakan ta kasance tsakaninsu?".


    Shiru kamar Iffah bazata motsa ba, sai kuma ta yunkura da kyar fuskarta jage-jage da hawaye. Handkherciff din da Malikat Haseenat ke miko mata ta amsa ta goge fuskar sannan ta fuskanci kotu bayan ta saci kallon Tajwar Eshaan da takeji a jikinta kallonta yake, dan tun dazun takejin kaifafan idanunsa a kanta. Hakama Malikat Bushirat kallonta takeyi. A nutse cikin nuna rauni ta ce, "Ni ban san mizan ce ba, amma abinda na sani kawai bani da wata alaka da shi nikam, hasalima ban sanshi ba a zahirance sai a randa aka nunani gaban dai iyayen wanna gida mai albarka. Kuma ko'a ranar bazan iya cewa ga kamaninsa ba. Sai a randa Zawjata-almilk farko ta rasa ranta ne dai-dai da rasuwa sayeed Khairul-Bashar na nufi sashen mai girma Shahan-shan hankali tashe dan ina son tabbatar da abinda al'umma keta fade akan shine ke kashe matansa. Ina tsaka da dube-dubena akan gawar suka shigo tare da shugaban jami'ai, Ni kuma sai naji tsoro na buya, bayan an fita da gawar ashe shi ya ganni shine ya dawo da baya. Na tsorata amma sai ya ce na nutsu muyi magana, zai rufamin asiri amma yana so muyi aiki tare. Ya dan mun maganganu dai da yawa. A ranar ya kawo min maganganu masu rudarwa, mafi girma a cikinsu nunamin video cewar adalin shugabanmu ne ya halakamin iyayena da tsafin maciji kamar yanda naga alamar saran maciji a jikin Zawjata-almilk da ta rasu, ya kuma sanar min nima na tsira zanyi ba dan haka nima nayi takaina. Nazo mu hada hannu mu yakesa dan baza'a hukuntashi ba. Ni a lokacin maimakon cemasa wani abu ma rudani na shiga da tashin hankali akan iyayena,dan haka bamma gama saurarensa ba, ganin bana a hayyacina ya tashi ya fita. Sai kuma A ranar 9 ga watan 2 dai nanma na samu kiransa misalin karfe takwas a dare. Nayi matukar mamakin hakan, dan bai boyemun ba ya sanar min aiki fa yake son miyi tare kamar yanda ya a waccan ranar amma zai sanar min abu. Ban katsesa ba nace ina saurarensa.Yasanar min magana bazata yiwu ta wayar landline ba, amma ga number dinsa na kirashi direct video call. Har lokacin ban kawo komai a raina ba, duk da dai inajin toro ganin shiga uncle dinsa ne, idan na fadama wani bama za'a yarda dani ba. Dan haka nabi umarninsa na kira din dan bangama sanin yanda akeyi anan din ba. Tun daga wannan ranar ban sake fahimtar komai ba da ga yanda yake bibiyata sai da nakai madara ga adalin shugaban wannan kasa ya sha. Daga nan na fara fahimtar makirci ne musamman yanda ya dage akan sai an kaini kurkuku. Bayan an kainin kuma ya bini har can yana fadamin maganganun banza harda na rashin da'a". Ta fashe da kuka mai cin rai, wanda a yanzu kam da gaske kukan take, dan kalmar KARUWA da Miran Jasim ya ce zai maidata na mata radadi har yanzu a cikin rai.


       Dolene yanda Iffah ke bayanin yasa kaji hawaye yazo maka, kuma ko kai waye sai kaji ka yarda da ita. A nan din ma fa rudewa kotun ta sake yi, yayinda Miran Jasim ke hargowar sai ya batar da ita, sai ya shafe babin rayuwarta baki daya ita da Miran Arshaan da sukaci amanarsa. Babuma wanda ke saurarensa sai ALLAH wadai da ake jifansa da shi da tausayin Iffah da gaba daya yau kowa ya fahimci an mata makirçin ashe ,Dama can wasu da yawa tunma a ranar data aikata suke fadin bayin kanta bane, tayi kankanta da aikata laifin ita daya. To sai gashi yau kam komai ya fito filin ALLAH. Kotun tai bala'"in daukar turiri har sai da Tajwar Eshaan da kansa ya tsawatar. Dan danan kowa ya nutsu kotun tai tsitt. Ya dauka tsahon mintuna uku babu alamar zai ce wani abu, kafin ya nisa da kyar cikin maganar nan tasa a fuse kamar wanda akaima dole. Da kyar ya iya danne zafi da radadin da zuciyarsa ke masa kanjin wai uncle dinsa yama matarsa magana ta rashin da'a,amma ta boye masa.


       "Alamu da kalaman Jasim in Abdul-majeed Aliy Qutb sun tabbatar da duk abinda aka sanar anan game da shi ya aikata. Sai dai duk da haka wannan kotu mai adalci zata bashi damar sanar damu dalilinsa na aikata duk wannan a zama na gaba. Za'a tsaresa a kurkukun da Zawjata-almilk tai rayuwa har zuwa ranar da kotu zata sake bukatar ganinsa a gabanta. Wannan kotu kuma ta wanke Zawjata-almilk da ga zargi, tare da bada damar kawo bokan da yay sihirin gaban shari'a shima. Tanada damar shigar da kara itama a karan kanta game da amfani da ita da Jasim yayi. Daga karshe ni Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb ina shigar da kara nima bisa yunkurin kashe min MATA da akayi har karo biyu ta hanyar yimata allurar guda da jefata cikin ruwa..." da ga haka ya mike anutse cike da salon nan nasa yayinda ya bar jama'ar kotu gaba daya a yanayin mutuwar zuune da kalamansa na karshe. Malikat Haseenat kam murmushi ta saki mai sanyi da kayatarwa, hakama Daneen Ammarah. Yayinda zuciyar Malikat Bushirat ke bugawa da wani irin sauri-sauri a cikin kirjinta dake yin kamar zai bude.


         A bangaren Iffah kam idonta akan Miran Jasim ne, a cikin iska ta rubuta *_FINAL_* da yin alamar yanka wuya ta kashe masa ido daya…….✍️


_Mai RUMAN sai kayi takanka kaima to, dan da

gaske Iffah kaza zata koma uwar tone-tone🥱_

No comments

Powered by Blogger.