Daudar Gora Book 2 page 53

 


Book two( 53)

Wata shegiyar dariya ya saki idanunsa kan takardar da aka aiko masa ta sake zaman shari'ar yau. Ya kai hannu ya yarce ruwan wankan dake kan goshinsa zuwa fuska. Tun safiyar jiya basa gidan shi da Miran Jasim. Sai yau ne shi yake dawowa Miran Jasim kuma da daddare.


       Wayar landline dake gefe gadonsa ya dauka,yay yan danne-danne yana da ga tsayen da yake. Ana dauka ya kwashe da dariya, sai kuma ya kai zaune a bakin gado. "Yaya dai kawun mai sharia kaima an kawo maka takardar ne?".


         Wani irin shegen tsaki Miran Jasim yaja da ga can. Ya ce, "Bar wawa dan wahala mana. Shifa gani yake kamar ya wani kai anan. Muje zuwa idan ya isa sake zaman wata shari'ar da ga wannan. Zamuyi maganinsa ne shida shegiyar yarinyar nan mai bakin akkunaye".


       Sake kwashewa da dariya Miran Arshaan yayi, tare da fadin, "Ai boka dan gurguzu yayi,tunda muka fita muka dawo masarautar nan babu wani shege da yay magana shima bai isa

yinta ba yau".


       Dariya suka kwashe da ita a tare kamar wasu mahaukata...




_Tofa, mi Fir 'auna da hamana suka shiryo ne

haka🥱😂🚴🚴🚴🚴



Yau kam a tare suka fito zuwa dining room. Amintaccensa ya zube kansa a kasa yana gaishesu cike da girmama. Iffah ce kawai ta amsa masa cikin kulawa. Gogan nata kam lips kawai ya motsa ya wuce abinsa. Da kansa ya ja mata kujera, itama sai ta ja masa tana kallonsa da murmushi. Shi dai bai murmushin ba, amma ya juya idanu cike da salon birgewa. Koda amintaccensa ya taso domin hada masa abinci kamar yanda ya saba dakatar da shi tai. Sai ma ta sallamesa akan yaje idan sun kammala sai ya dawo.


      Sai da ta gama bubbude duk kwanikan wajen sannan ta kallesa alamar mi yake so? Kaifafan idanun nan nasa ya zuba mata, sai kuma ya daga yatsarsa manuniya a hankali ya nuna ta.Baki ta tura gaba tana wani kyaf-kyaf da idanu."Ni abinci nace fa". Yanda tai din sai ya bashi dariya. Amma sai ya gimtse abarsa ya dauke kai Itama sai ta tabe baki ta dauke nata kan dan ta fahimci yau kuma yan mislinacin ne da mulki a kansa. Zabar abinda taji tana so a ranta tai kawai ta zuba musu ta ajiye komai gabansa da fadin bismillah. Abincin kawai ya zubama ido yana jinsa wani daban yau din. A da sai daiamintaccensa ya hada masa, yau kuma gashimatarsa ce, abinda ya jima yana mafarki. Rayuwa kenan mai farko da karshe.


     A nutse suka fara cin abincin, Iffah na satar kallonsa da jinjina mulki da kasaita. Yanda yake cin abincin ma kansa abin birgewa ne. Suna gab da kammalawa kanta yay wani irin sara mata. Da sauri ta kai hannu ta dafe tana ambaton sunan ALLAH. Kallonta yay shima da mamaki, sai kuma ya riko hanunta da ta dafe kan da shi. Dago idanunta da sukai wani irin jajaja cikin kankanin lokaci tai ta kallesa. Shi har sai da ma yaji tsigar jikinsa ya tashi, amma sai ya dake kasancewar shima akwai nasa abebadan a kansa. Da ido ya mata alamar minene? Dan da gaske yau miskilancin ne a kusa. Ji yake motsa lips din ma yay magana babban aiki ne.


A hankali ta furta, "Kaina ke dan mun ciwo


Tun yaushe?".


    Ya fada a fusge. "Da safen nan ne fa. Amma ba wani ya matsa bane karka damu. Dan ALLAH ka barni na fara tafiya kotun nan sai kai kuma ka taho da ga baya".


     Idanu kawai ya tsira mata. Ita kuma ta langabe kai gefe alamar roko. Dauke idonsa yay kawai da ga kanta batare da ya ce komai ba. Ya lima yana zargin akwai junnu a jikin yarinyar nan, yanzun ma kuma abinda yake zargin kenan. (Ya arrahaman, komai na yarinyar nan sake sakashi a rudani yake). Sai kuma maganar data fada masan yanzu ta shiga masa kaikawo a rai. Ya barta ta fara yin gaba kafin shi na nufin akwai wani abu kenan. Shikam yaga takansa da wadan nan ahali nashi. Wani abu kenan wani ya sake masa ko kuma dai aljanun nata ne ke neman raina masa hankali. Cikin rashin bama abin muhimmanci ya cigaba da cin abincinsa, sai dai kuma abinda ta fada kuma ya faru a wacan ranar na masa kaikawo. Iffah dake binsa da kallo kamar zatai magana sai kuma ta hadiye kayarta tana sakin nannauyar ajiyar zuciya da jan jikinta

baya.


      Komai baice mata ba, sai da yaga ta mike. A can kasan makoshi ya furta "Ina zuwa?".


    Agogo ta nuna masa. Kallon agogon yay ya dauke ido. Batare da ya sake kallonta ba ya ce ,Kina bukatar masu rakkiya ne?".


"A'a".


Ta bashi amsa a takaice.


'"Amma kin san bazai yuwu kije ke kadai ba. Kije akwai masu jiranki a can kasa".


          "Nagode".


       Da kallo kawai ya bita ganin yanda ta sauya lokaci guda. Ga fuska ta wani daure tamau babu alamar wasa. Shi sai ma ya fara jin ko dai itace aljanar da kanta.





          *Yau kam da alama shari'ar zatai zafi. Dan kotun tacika fie da zaton mai hasashe. Abinda Kuma zai birgeka duk ahalin masarautar ne.Cikin wani irin takun kasaita da izza da ya jawo hankalin duk wanda ke cikin kotun Iffah ta shigo da shi. Ga hadimai na take mata baya. Tayi matukar kyau cikin shigar jikinta, ga wani irin kyawu da fuskarta ta kara sai shining takeyi fiye da hasken tauraruwa zarah. A zahiri ita tafiyarta takeyi normal, amma ga masu kallonta babu abinda suke gani tattare da ita sai tsantsar izza mai ban mamaki. Wani abin birgewa da tai ya kayatar da was a wajen shine kai tsaye inda Malikat Haseenat take ta nufa. Takai kasa cike 17:42

yanzu bayan Tajwar Eshaan da Malikat haseenat sama da ita a duniya.




Shigowar mai gayya mai aiki tasa tunaninsa katsewa…. a take kotun tai tsitt kowa ya mike domin girmamawa. Taku yake cikin tsantsar kasaita da izza data zame masa jinin jiki. Ga wani irin kamshinsa mai kada zuciyar mai shaka na tashi. Yammatan wajen da suka dade da folawa a sonsa tuni zukatansu suka shigar narkewa, duk da babu abinda ake gani bayyane a fuskarsa. Dan ya sakayata hatta da idanunsa saye suke cikin eyeglasses dake nuna blue daga waje. Addu'ar neman tsarin ALLAH da ga duk wani abin cutarwa ya karanto lokacin da yake kaiwa zaune a hadaddiyar kujerar da ke a mallakin zamansa. Ya dan saci kallon sashin da yake tunanin ganinta. Tana a wajen kuwa, sai dai abin mamaki ita sam bama shi din take kallo ba.Ajiyar zuciya ya dan sauke a hankali wadda ko amintaccensa da ke gefensa da masu tsaro guda hudu haggu da damansa basu isa ji ba.


      Bayan an tabbatar da kowa ya natsa Sayeed Hanifud-Din ya mike ya dubi jama'a.

"Alhamdullahi muna godiya ga ALLAH da ya sake dawo damu zama na uku akan wannan shari'a. A zaman daya gabata wadda ake kara ta amsa laifinta, sai dai ta Bama wannan kotu mai adalci damar bincike mai zurfi akan tushen shugaba na wanna daula. Inda wannan kotu mai adalci ta amshi korafinta har ta bada dama ga masu bincike. Matsala ta ratsa ta yunkurin son halaka Zawjata-almilk da akai, inda dalilin haka aka samu tazarar daga wanna zama har sai da ta samu lafiya. To yanzu dai alhmallh, wanna zama a wanna gabar duka zai ta'allaka ne ga jin bayani da ga bakin shugaban jami'ai da aka danka wanna bincike garesa. Shugaban jami'ai bismillah".


      Sai da ya mika gaisuwa ga Shahan-shan cike da girmamawa kafin ya juya ga jama'a. "Assalamu alaikum kamar yanda aka bamu damar bincike a gaban wannan kotu mai adalci mun gudanar. Mun bibiyi tushen samuwar madara da kaita sashen Zawjata-almilk. Inda bincikenmu kuma ya kaimu har ga wanda ya shigo da wannan madara mai dauke da dafin macizai a ciki. Karna cikaku da surutu waka bakin mai ita tafi dadi. Ina rokon alfarmar wannan kotu da ta bani damar gabatar da Dafiq in Ghalib a gabanta".

   

    "An baka".


Cewar Sayeed Hanifud-Din.


Kallon juna Miran Arshaan da Miran Jasim sukai suka saki murmushi. Sai kuma sukai saurin duban wanda jami'ai ke kokarin shigowa dashi kirazansu na wani irin mummunan harbawa.Kokarin mikewa Miran Arshaan yay da sauri Miran Jasim ya danne masa hannu jikinsa na rawa. Iffah da ke kallonsu ta saki murmushi,cikin Sa'a kuwa suka hada do da Miran Jasim.Ido daya ta kashe masa da dauke kanta tana dan wani cizar lips cike da salo.


        Dattijo da jami 'ai suka shigo da shi bazai wuce shekaru hamsin da takwas a duniya ba. Cikin nutsuwa ya gurfana gaban Shahan-shan yay gaisuwa, bai o motsa ba da ga zaman kasaitarsa. Dattijo Dafiq in Ghalib ya gyara tsaiwarsa yana fuskantar kotu. Dubansa Sayeed Hanifud-Din yayi ya ce, "Dattijo waye kai?".Cikin dan rawar harshe ya ce, "Dafiq ibn Ghalib. Ni masanine akan macizai. Ina zaune a kauyen Bansh".

    "Miye alakarka da daular ruman?".


   "Alakata da Daula ruman alakace irin ta kowanne dan kasa. Wato fadan shugaban kasata adali".


      "Amma duk da haka ka iya bada dafin macizan da za'a cutar da shi?"


         "Ko kusa ba haka bane, ko wani naga zai cutar da hadimin wannan daula bama shugabana ba sai inda karfina ya kare ai. Ni dai a ranar daren wata laraba wani bawan ALLAH ya sameni akan shi din jami'in ne na hukumar bincike akan sanin nau'in dabbobi masu dafi.Yazo kuma wajena ne da bukatar samun kalolin dafin macizai zaiyi bincike a kansu. Da farko naso naki, dan nasan dan adam na wannan duniyar ba abin yarda bane. Amma sai ya nuna min katin shaidar aikinsa. Hakan yasa na yarda da shi na dauka na bashi"……….✍️


No comments

Powered by Blogger.