Daudar Gora Book 2 page 52

 


Book two ( 52)


Duk da barcin dake cikin idanunsa tattaresa yay ya ajiye gefe guda ya tattara dukan hankalinsa kan littattafan da Malikat Haseenat tabashi. Inda zuciyarsa ke zallon zuwa kawai ya nufa bayan ya dan karanta tarihin mafarin komai. Babu bambanci da

wanda Mammah ta bashi, dan haka ya ajiye gefe da burin sai ya nutsu zaiyi komai daki-daki. Bai san adadin shekarunta ba, amma sai ya kiyasta da adadin shekarun da yake kallonta da su. Yaci karo da kusan hudu da yay dai-dai da hasashensa, a ciki uku na mata daya na namiji, gefe ya maida na namijin, ya dauka wayarsa yana kallon natan da na sauran matan uku kozai dace da wanda zasuyi dai-dai. Wani irin masifar harbawa zuciyarsa tayi gain tambari na karshe bashi da banbanci da natan. Bayanin dake kasan tambarin na tabbatar da dashi aka haifeta, a duk ma wanda aka haifa a tsakanin lokacin ita kadaice wadda aka haifa da shi sauran duk yimusu shi akayi. An haifi mai tamarin a daren ranar juma'a 22 a shekarar 2003 uku ga wata.Sai dai ita kuma ta rasu ne bayan haihuwarta da kwana uku. Wani irin kai hannu yay saman kansa ya yamutsa sumarsa yana ambaton sunan ALLAH. Ya akai haka? Ta yaya ma? Idan har ya tabbata ita din ce ya akai take raye bayan ance kuma ta mutu? Idan kuma wadan can dinne Iyayenta tayaya suka bar masarautar ma?bata mutum ba suka boyeta sukace ta muturn? Kai ina akwai dai abinda ya kamata ya sani, farkoma shekarunta ita. Sannan sanin asalin iyayenta.Lokaci yayi da zaisa a maidosu kasar ruman.

**

Kanta sara mata yake da cio mai azaba. Ga wani irin ja da idanunta sukai. Kofar da suka fita kawai ta tsurama ido tamkar suna a wajen har kusan awanni uku bayan fitarsu. Sosai take jin kuna mai radadi a zuciyarta. Har yanzu ta kasa yarda a ido biyu take, ta kasa yarda a zahiri komai ke faruwa, ta kasa yarda ita ta-kurya wata ta tsaya a gabanta tai mata wannan in kashir.Ta kasa yarda ita ta kurya yau wani ke tabbatar mata yasan itace silar mutuwar matan danta. Ta kasa yarda, ta kasa yarda da komai.


            "Ta-kurya!!".


    Muryar UWA ta shiga cikin kunnenta a bazata.Firgigit ta kai dubanta ga inda taji sautin kuryar.Ita dince kuwa, zaune cikin kujerar nan tata.Yanda fuskarta ke tsuke hancinta na fidda hucin bacin rai sai ta kara muni ga mai kallo. Idanunta jajurta kara budewa akan Malikat Bushirat itama kallonta kawai take babu alamar jikinta na aiki bayan fitar numfashi.


         "Kin bani kunya ta-kurya. Kin bani kunya da har kika kasance a haka kan wata karamar barazana da ga yar cikinki. Ashe bazaki iya yakin ba kika amsa takardar gayyata? Dama duk baki shirya zuwan irin wadan nan ranakun

ba…


      "Uwa ya kike so nayi? Ya kike so na kasance?.Ni fa yarinyar nan ta kalla cikin idona ta fadamin abinda bayan ni da ke babu wanda ya sani a kaf duniya. Ni yarinyar nan ta shiryama makirci a gaban dana dana zama sanadin zuwansa duniya, wanda dukkan gwagwarmayata akansa ne da tabbatar da wanzuwarsa a matsayin da yake yanzu, wanda da shi take ado, da shi take takama da jin kanta ita har takai mace abar kallo. Uwa shiyyasa nace miki ki kasheta tun a farkon farawarta amma kik....


           "Na fada miki na kara fada miki kashe wannan yarinyar kai tsaye ba abune mai sauki ba. Domin akwai wani boyayyen al'amari da yake zagaye a kanta. Tsaye nake kuma akan ganoshi dare da rana dan ba dake kawai ta shirya yakin ba har dani nan kaina. Sai dai abinda bata sani ba ni nafi karfin iyawarta, zan kuma tabbatar mata da hakan nan kusa. A cikin sharuddanmu kin tafka kurakurai da yawa ta-kurya, ciki harda kasa bamu alkyabba da ke a sashen mai babban daki. Tun a ranar farko kin kasa shayar da yarinyar nan madara, bayan gagara yimata wankan turare da saka mata alkyabbarmu. Kinyi yunkurin kasheta da hanunki bayan na sanar miki hakan babban kuskure ne amma kika ki jina. Kinyi kuskuren kasa saka ido har aka kaita sashen Ajlaan bada saninki ba. Kinyi kuskuren kasa hadiye abubuwa da dama dangane da ita.Wadan nan abubuwan dama wanda ban lissafaba sun taimaka mata wajen bude kofar samunki ta inda bakiyi zato ba. Babban na karshe daya bude komai kasancewarta da jininki matsayin abu guda, bayan kuma tun a farko mun sanar miki mune zamu bama Ajlaan matar aure mai kwaranye kishinsa...


         "Na amsa dukkan laifina gareki Uwa, ina kuma mai neman afuwa da agajinki karki barni na fadi kasa a gabar da makiya ke burin ganin bayana. Ki fadi mi kuke bukata na diyyar laifukana komai wahalarsa zan zama mai cikashi da gaggawa ni bazan kasance mai butulci irin wanda akai miki a baya ba. Ina son yarinyar nan tayi nadamar sanin kanta ma balle ni a karan kaina".


      "K mai kokarin cika sharudda ce ta-kurya shiyyasa bana iya dogon fushi da ke. Kije an miki, sai dai ki shirya dan shirinmu na yanzu zai zama a saman a bayane. Zaki biya diyyar kurakuranki da jinin bakaken shanu goma, na rakuma goma, na bakaken karnuka goma suma. Jariri sabuwar haihuwar kwana uku kamar yanda akai a wancan karon mai tambarin masarautar nan. Bayan sati guda zaki cika mana da jinin barin ciki na mata biyu masu sabon shigar ciki dan watanni hudu. Tare da namijin hadimi sabon aure shima da yay kwanciya da mace sau daya. Da ga yau madarar da Ajlaan zai koma sha zata dinga fita da ga hanunki ne, akwai shayi da yake sha a kullum kisa a nemo miki mai masa nomansa ya noma da wannan irin amaimakon wanda yake noma masa, dakin zai dawo tafin hanunki komai sai da umarninki zai aikata shi. Tana makirci da danki a tsakkiyarku,kenan sai kibi ta karfin ikon shi da ke a hanunki da ga yau. Zamu sama mata amintacciyar hadima, dan haka ta koma sashenta da zama.Muna akan bakanmu, waccan yarinyar zata shigo domin da ga gareta kawai muke bukatar magajin daular ruman kiyi gaggawar gain an kulla aurensu. Da ga shi har ita ki tabbatar sun sha wannan ruwan, shine zai hanasu sake kasancewa da juna har abada".

   

       Cike da farin ciki Malikat Bushirat ta amsa tana jera godiya ga uwa cikin gurfana. Ji take a daya duk wani bacin ranta da tashin hankali sun kwaranye kamar ma ba'ayi ba


         "Uwa sai dai akwai hadimin nan daya sakata a ruwa, Saiful-malik ya tabbatar min yana haninsu".


        "Wannan bashi da wani muhimmancin da zai dameki, dan baisa ke wacece ba ai".


         "Amma Uwa ita ai ta sani, baki ganin zata iya yin yanda kowa zai fahimci ni din ce?".


       "Bata isa sanarma kowa ba koda shi Ajlaan ne, dan akwai soyayyarki a zuciyarsa fiye da yanda duk wani mai hasashe ke zato

Nidai bilynku na ce, "humm" πŸ₯±)

      Ta farka sau daya vin fitsari taga baya dakin,17:38

Ta tarka sau daya yin titsari taga baya dakin, sai hakan ya kara mata nutsuwa. Sai dai kuma Can tikin dare ko tace gabanin asuba taji a mata wata irin runguma data sakata farkawa a firgice. Gabanta faduwa yay lokacin data tabbatar da shine. Muryarta har kakkarwa take na son magana. Sai dai ma kafin ta furta ya ce mata "Shilli!!" dole ta hadiye tai luf. Yamutsata ya dingayi da jagwalgwalata yanda yake so, ta riga ta gama kaiwa makura a rudewa. Sai dai bai mata komai ba har aka kwala kiran salla ya mike a gadon ya nufi bathroom. Kusan mintuna goma tana nan kwance lamo da share hawayen da tasha na tsoro ya fito da alamar wanka ma yayi.Luff tai bata motsa ba har ya gama tsane gashin kansa ya wuce wajen canja kaya. Wuff tayi ta tashi zuwa bayi, lokacin da ya fito cikin shirin massalaci ya nufi gadon da shirin tadata ya samu wayam. Shi yama zata barin akin tai, sai kawai ya fice abinsa gudun kar ya makara kuma.
         Koda ya dawo da ga salla Gym ya wuce abinsa cike da kokarin danne abinda ke damun gangar jikinsa da ruhinsa. Wani irin mugun motsa jiki ya ringayi na tashin hankali duk dan ya samarwa kansa nutsuwar manta abinda ke bijiro masa. Sai dai maimakon samun nutsuwar da yake bukata hankalinsa ne make cigaba da tashi. Ya dauki tsawon awa biyu a Gym din kafin ya fito ,ya koyi zufa sharkaf kamar wanda iyo a cikin ruwa.Tana tsaye gaban gadon tana canja bedsheet ya shigo da sallamar nan tasa ciki-ciki. Dan juyowa tai kadan ta dubesa sai kumata dauke kanta. A can kasan makoshi ta ce,

"Good morning".


"Ya kike?".


    Ya fada a takaice yana cigaba da mata kallon mamaki. Kamar zai share dai ya kasa hakuri."Waya saki wannan aikin?". A dan shagwabe tace, "Ni na sa kaina, shike nan mutum bazai motsa jikinsa ba sai dai komai ai masa ni banaso". Takowa yay gabanta gab sosai, tare da riko hanunta da ke rike da filo.Dagowa tai ta kallesa.Zata maida ya girgiza mata kansa. Dole ta hakura, sai dai tai kasa-kasa da idanunta.Shikam dai idanunsa kyam kan kyakykyawar fuskarta da yau dai ta gama komawa normal kamar komai bai faru ba, ya dan matsa hannuna hankali yana dan huro iskar bakinsa kan fuskar tata. "Akwai muhimman ayyuka da yawa da zaki motsa jiki ai ba sai wannan ba Niger".


         Fuskarta a dan narke ta dago idanunta da kyau tana dubansa, "Wannan ma fa Mammy tace ni ya kamata na dingayi yanzu ba amintaccenka ba. Nima kuma kaga dai a gida Ummu ko mu bata yarda mu gyara cakin Babiy,ko Bata da lafiya sai tace bari ta danyi ko sama-sama".


     Gaba daya ta sake narkar da shi a halin da yake ciki, bai ma san sanda ya furta, "Kowane salonki kasheni yake autar mata". Yanda ya fada a narke da kai hannunsa ya shafo jikinta sai taji kunya. Da sauri ta juya masa baya tana rufe fuskarta da tafukan hanunta. Shima murmushin yayi ya ajiye filon yana nufar bathroom. Sai da taji shigewarsa sannan ta bude idanunta ta cigaba da aikinta. Haka kawai take jin kanta cikin wani irin nishadi yau.

"Mammah wai yau ma zakije zaman kotun nan kema? Naga kamar kina jin kafar nan sosai fa?".

     Dan murmushin karfin hali Malikat Haseenat ta saki idonta akan Daneen Ammarah mai maganar. "Karki damu ai bawani ciwo take mai yawa ba. Ke dai yi sauri ki bani kunun nan nasha, kin sanshi dan ka'ida ne akan bin lokaci".

    Yar dariya Daneen Ammarah tayi kawai, Da ganta itama zaka fahimci tana cikin farin ciki. Daga ita har Malikat Haseenat din tun jiya fuskokinsu sun kasa daina murmushi, da dare kam zama sukai suka ding hirar Iffah. Su kansu sun kasa gane ta yanda akai yarinyar ta shiga ransu matuka har haka, kuma take ma kara shiga a kullum musamman ma ita Daneen Ammarah din da kwanakin nan taketa mafarkai da ta kasa gane kansu……………✍️


No comments

Powered by Blogger.