Daudar Gora Book 2 page 45

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (45)

........Sai da ya tabbatar ta samu isasshen gashi sannan ya taimaka mata tayi wanka, har lokacin bata daina hawaye ba. Idan kuma ya ɗan motsata da ƙarfi ko yaya ne sai ta saki siririyar ƙara da ƙara ƙarfin kukanta. Babu abinda ya ke iya jera mata sai kalmar “Sorry, I am sorry”. Bai san tunzura mata zuciya

kalmar haƙurin nan take sake yi ba. Koda ya saka mata bathrobe shima sai da ya cire kayan jikinsa dan duk sun jiƙe. Yanzu ma cak ya ɗagota zuwa ɗaƙi, ganin lokacin salla ya ƙwace da yawa ya ɗakko mata rigar jallabiyarsa ya saka mata, veil ɗin ta na jiya ya naɗa mata sannan ya saka mata sallaya ya sake ɗakkota da ga kan sofar da take kwance ya ajiye kan sallayar. Ta kasa tsaiwa yanda ya kamata tsabar yanda ƙafafunta kansu sukai mata tsami, sai da ya dinga lallaɓata sannan tai dauriya da ƙyar, lokacin da take kaiwa ruku'u da sujida yana jin yanda kukanta ke ƙara ƙarfi alamar a wahalce take, zaman tahiya kam ta kasa zama da ƙyau. Duk sai hankalinsa ya ƙara tashi, dan ya fahimci lallai akwai matsala. Tana yin sallama ta zame kwance tana rusar kuka da kiran Ummu ta zo ta taimaketa. A gabanta yazo ya durƙuso tare da kamota jikinsa, yanda ya motsatan yasa ta ƙanƙamesa sosai.

         “Please stop crying babie”.

     Ya faɗa da wata irin murya mai tsananin sanyi da taushi yana rungumeta da ƙyau idanunsa a lumshe. Duk yanda taso tsaida kukan ta kasa, dan ciwo takeji sosai a jikinta. Ga kanta na mata wani irin ciwo mai azaba shima. Ga zazzaɓi mai zafi sosai. Gaba ɗaya ta birkice kamar ba Iffah'r Babiy mai shegen tsiwar nan da tsaurin ido ba. Dama irinsu bakin ne kawai ba iya jurar wahala sukai ba (lols😆).

        Bawan ALLAH Shahan-shan gaba ɗaya ta susutashi ya daina gane komai, yanda take kukan jinsa yake har tsakkiyar zuciyarsa dan shi mutum ne mai tausayi tun da can ma. Amma akan fuskar babu alamar wani abu kamancin hakan tattare da shi, yayi masifar dakewa kamar komai ma bai faru ba. Ɗagata yay daga wajen ya kaita saman kujera dan gadon gaba ɗaya ya ɓaci gashi farin bedsheet. Rirriƙesa tai da sauri alamar bazata iya zaman ba, dole ya ɗan kai gaban kujerar durƙushe yana riƙe da ita. 

        “Faɗamin minene ke damunki?”.

      Yanda ya zuba mata fitinannun idanunsa ba shiri ta shiga ƙoƙarin ganin ta haɗiye kukan, da ƙyar ta iya furta, “Zafi yake wajen, zafi mai azaba kamar sanda k.......” sai kuma ta kasa ƙara sawa ta fashe da kuka.

      “Stop crying please, bara na duba naga ko kinji ciwo ne”.

     Da sauri-sauri ta shiga girgiza masa kai tana matse jikinta waje guda da faɗin, “Ni bazaka gammun ba, ka kiramin Ummuna”.

          Hannunsa ya ɗan kai bisa goshinsa ya murza. Sai kuma ya sake ɗago kan a hankali, har yanzu durƙushe yake gabanta tamkar ba Shahan-shan ba. Cikin ƙara tausasa murya da shima har yanzu bata gama dai-daita ba ya kai hannu saman fuskarta ya tallafo da duk hannayensa, babban yatsansa yasa yana share mata hawaye. “Kiyi haƙuri, ki zaɓi wanda zan kira miki bayan Ummu, dan ko tana a ƙasar nan bazan iya haka gareta ba, bazan so ta ganki a haka ba. Faɗamin wa kike so na kira miki bayan ita? Ammie, Jaddah, ko Mammy, ko Aunty Jasrah? Ko na baki wayar ki zaɓa wanda kike so yazo?”.

        Kanta ta ɗaga masa hawayen na cigaba da kwaranyowa. “Okay tom bar kukan, Ni bana son ganin hawaye nan suna sake raunani, rauni na kuma yana nufin sake maimaita abinda nai a daren jiya ko kina so a ƙara?..”

         Har zabura take tana girgiza masa kai wani sabon kuka na taso mata, amma sai tai saurin danne bakinta da hannayenta duka biyu tana ƙoƙarin haɗiyewa. Tausayi ta bashi da dariya, amma sai ya dake abinsa yana yi a cikin rai. Dan da gaske badan kar ya kashe musu yarinya ba babu abinda zai hanashi sake kai mata ziyara. Shi kaɗai yasan mi yake yaƙin dannewa da ga safiya zuwa yanzu, kawai dai abar kaza cikin gashinta. Ɗan kwantar da ita yay da ga zaman karkacewar da tayi, ya miƙe ya ɗauko ɗaya da ga cikin wayoyinsa. Gabanta ya sake zuwa ya dirƙusa ɗin dai maimakon zama da ya saba yi, ita inba a gaban UBANGIJINSA ba yayin bauta masa bata taɓa ganinsa durƙushe haka gaban wani ba. Duk da bawai yayi wani durƙuso bane na ƙasƙanci. Hasalima yanda yay ɗin sai ya ƙawatar irin masoyi a gaban masoyiyyarsa ɗin nan da suke cikin tsananin shauƙi ma juna. Contact ɗinsa ya shiga sannan ya miƙa mata wayar. Karɓa tai tana sake kumbura fuskar nan da tai jazur duk a suntume musamman idanunta. Kalmarsa ta zai ƙara ne ya sata danne hawayen tilas badan ta gaji da kukan ba. Number Mammy ta lalubo, taja wasu sakkani kamar mai tunani ko tsoron kiran sannan tai dialing. Bugu biyu zuwa na uku kuwa aka ɗaga. Da sauri ta rumtse idanunta hawayen da take riƙewa na ɓulɓulowa. Da ga can jin anyi shiru Malikat Haseenat da ta ɗauka wayar kasancewar Daneen Ammarah ta shiga wajenta sanar mata Malikat Bushirat babu lafiya tace ta haɗa mata ruwan wanka shine ta bar wayar gefenta, ita kuma ganin number Tajwar Eshaan yasa ta ɗauka da tunanin ko shima zancen Malikat Bushirat ɗin ne. Amma sai kuma taji anyi shiru ga kuma kamar ana jan ajiyar zuciyar kuka da ake ƙoƙarin dannewa yana son fita. 

        “Assalamu alaikum”.

   Ta faɗa a nutse cike da dattakonta. Kamar an ƙwalama Iffah farantin silver saman kai da sauri ta ɗauke wayar a kunnenta ta miƙa masa kukan da take dannewa na kufce mata. Bashi da zaɓin amsar wayar shi ya kai nasa kunnen, tunda har aka riga aka ɗaga bashi da hurumin cewa zai yanke sai ya sakata a tashin hankali. Wayar ya kai kunnensa yana mikewa da yin sallama cikin sassanyar muryar nan tasa mai cike da nutsuwa da kame kai. Malikat Haseenat ta lumshe idanu da sakin ajiyar zuciya ta amsa masa. Cikin mamaki yace, “Jaddah ke ce? Ina Mammyn?”.

         “Tana haɗamin ruwan wanka ne. Ina fatan lafiya dai ko naji kamar ana kuka da farko?”.

      Ji yay duk yama kasa cewa komai, a karo na farko na rayuwarsa yaji yana jin nauyin kakar tasa. Amma sai ya daure da ƙyar acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Fhareedah ce Jaddah. Dama muna buƙatar Mammyn ne anan”.

         Malikat Haseenat tsohuwar ƙwarai mai ran ƙarfe da cikar kamala. Sai kawai ta saki murmushi batare da ta nuna ma ta fahimcesa ba tace, “Oh to bara ta fito sai a sanar mata”.

       “Uhum”.

   Ya faɗa ciki-ciki. Bata sake cewa komai ba itama ta yanke wayar... Nannauyan numfashi ya sauke yana ɗan murza goshinsa. Sai kuma ya kalli Iffah da ta rufe idanu hawaye na cigaba da tsiyaya. Shi kam yama rasa gane kan wannan kuka, amma ya fahimci harda shagwaɓa da ragwantakar tsiya sai shegen tsiwa bakinta babu mai iya kadata a zance. Amma gashi a ɗan tabatan da yay da bai wuce ko ƙwayar zarra da ga abinda ke tattare da shi ba ya sauke take wannan rakin. Lallai ashe akwai aiki gabansa dan ba'a fara komai ba wannan sharar gona ce. (🚴🚴Taɓɗi).

       Tashi yay ya yaye bedsheet ɗin gadon dan yayi ma kansa alkawarin gyara sirrinsa da kansa. Gudun karma ya barsu a gani closed dinsa ya wuce da su ya adana. Sai kuma yama ga su bar ɗakin kawai, dan haka ya zo ya ɗauketa zuwa ɗakin kusa da wannan ɗin ya rufe wannan...


      Cikin abinda baifi mintuna goma ba sai ga kira da ga amintaccensa. Bayan gaisuwa da yay masa cike da tsantsar girmamawa ya nema wa su Daneen Ammarah iso. Duk da yaji mamakin jin kamar su biyu ake nufi kai tsaye ya bada umarnin ya shigo da su room 3. Karo na farko kenan bayan ita da ke matsayin matarsa da wani zai shigo jerin bedrooms ɗin sa na saman nan gaba ɗaya. Dan ko su matansa da duk aka kawo nan suka rasa ransu a hawa na huɗu ake ajiyesu. Iffah ce ta farko da ta taɓa hawowa hawan ƙarshen nan. 

         Ba shi kawai ba, hatta da Iffah da tayo gayyar sai da ta daburce da jin sautin muryar Malikat Haseenat na sallama. Amma jarumin naku sai yay ɗam da fuska daɗa duniya bai aikata komai ba babu alamar ko gezau tattare da shi. Sai dai kasancewar sa mutum mai tsananin kunya sai ya kasa yarda ya haɗa ido da Malikat Haseenat ɗin. Dan ita kaɗai ta shigo Daneen Ammarah na falo ta kasa shigowa. Bata san dalili ba kawai taji bazata iya ba, dan zuwan ma sai da Mammah ta tilasta mata harma yanda ta nuna ya bama Malikat Haseenat ɗin mamaki matuƙa dan kunya ce a bayyane kamar wadda zatai gamo da surukinta.

           A hankali ta cigaba da gara kekenta cikin ɗakin idanunta na yawo kan Tajwar Eshaan da tun kallo guda da yay mata bai sake ba da Iffah da ke duƙunƙune a gado cikin bargon da ta sashi ya lulluɓa mata saboda rawar sanyi da takeyi. A gaban Iffahn ta dakata, a hankali cikin dattakonta da ƙasaita ta kira sunanta da kai hannu ta janye bargon data lulluɓe har kanta da shi. Ɗan zabura Iffah tayi, sai kuma tai saurin maida kanta tana hawaye. Tausayi yarinyar ta bata, dan duk wanda ya kalleta yasan tana cikin wani halli. Batace komai ba ta juya kallonta ga Tajwar Eshaan da ke ɗan satar kallonsu...

       “Barka da safiya Jaddah”.

   Ya faɗa a taƙaice yana wani ƙara fuskewa abinsa. Itama sai tai kamar bata fahimci komai ba ta ce, “Barkan ka dai. Mike damunta haka jikinta zafi zau ga fuska duk ta kumbura idanu sun ɗashe yarinya duk ta fita a hayyacinta”.

         Wayyo shikam ina ƙasa ya ɓuya ciki ko zai kuɓuta da ga bata amsar da bai ma san ta ina zai fara ba. Amma sai ya dake yana ƙara ɗan kauda kai gefe tsahon sakkani kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya motsa lips a hankali a gaɓar da ma ta gama fidda rai da samun amsa. 

     “Ta girma ne”. 

  Kallonsa kawai Malikat Haseenat keyi, da jinjina murɗaɗɗen hali irin nashi mai cike da shegen miskilancin tsiya. Sai kuma ta janye a hankali ta maida kan Iffah dake raira kuka a hankali. “Niger (Sweetheart)” ta kirata a hankali. Da ƙyar Iffah ta iya amsa mata murya a ɗashe. 

          “Daure ki tashi zaune muga”.

     Kwatanta tashin tai har sau biyu amma ta kasa, sai ma wani wahallen kuka da take saki saboda yanda zafi mai azaba ke ratsata. Ta shiga jujjuya kai da faɗin, “Jaddah bazan iya ba. Zafi kamar zan mutu”.

     Idanu ya lumshe a hankali. Ji yake kukanta na wani irin sukar masa zuciya. Itama kanta malikat Haseenat ɗin wani irin tausayin Iffah'r ne ke ratsata. Ita tasan ba lalaci bane ko raki kawai. Dan zuri'ar su Tajwar Eshaan ɗin fitinannun mutane ne da indai mace taje hannunsu basa iya mata ta sauƙi. Shiyyasa mafi yawansu basa iya zama da mace ɗaya, sannan suna aure da wuri gudun faɗawa halakar zina duk da akwai bijirarru a cikinsu da kan ringa aikatawar. Amma ita a karan kanta ta daɗe tana mamaki akan Tajwar Eshaan da ya nuna baya buƙatar aure tun a shekaru fara girmansa, hakama yanda ya kai har shekarun da aka masa auren fari na sata jin waswasin ko yana neman matan banza ne ko baida isasshen lafiya. Dan tasan duk wanda ya kasance jinin zuri'ar wannan daula baya iya kauda kai ga mace irin hakan da ya nuna shi.........✍️


No comments

Powered by Blogger.