Daudar Gora Book 2 page 43


 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (43)



........Murmushi ya saki yana mai lumshe rinannun idanunsa. Lumshesu yay a hankali yana cije lips ɗinsa, yayinda wani abu mai sanyi ke saukar masa tun daga saman kai har yatsar ƙafar sa. Tabbas shi yasan juriyarsa tazo maƙura, maƙurar da in har bai samarwa kansa abinda yake so ba akwai babbar matsala, matsala irin wadda doctor ɗinsa ya sanar masa a ƙasar Cuba shekaru huɗu kenan da suka shuɗe

. A hankali ya buɗe fitinannun idanunsa a kanta ya sake lumshewa tare da kaiwa kwance kusa da ita shima. Idanun ya sake buɗewa tare da kamo hanunta cikin nasa, cirota yay daga cikin filos ɗin da take ƙara cusa kanta ya maidata jikinsa ya rungume ya na wani irin tsuma. Cikin disashiyar muryarsa da ke ƙara sarƙewa ya shiga faɗi a kunnenta “Kin yarda ke ce sirrin Eshaan bin Haysam Abdul-majeed Aliy Qutb? Tabbas kece, ki yarda kece Fhareedah bint Zayyan. Lokaci yayi da kowama zai yarda kece sirrin Eshaan, dole su tabbatar, dole ne na sakasu su tabbatar”. Ya ƙare maganar da ɗago fuskarta saitin tashi da tai jazur abinka da fari. Hawaye take sosai tana ƙara rumtse idanunta, itama tata fuskar duk ta birkice, jikinta kuwa rawa yake sosai har yana iya jin yanda bugun zuciyarta ke harbawa da azabar gudu. Dan yau tayi gamo, gamo mai tsananin saka ɗimuwa da tsayawar bugun zuciya musamman ga irinta.

        “Open your eyes my Sohaa. Please Open”. Ya faɗa cikin muryarsa da ke ƙara komawa can ƙasan maƙoshi yana ɗan bubbuga fuskarta. Maimakon buɗe idanun da ya buƙata sai kawai ta sakar masa kuka tana girgiza masa kai alamar bazata iya ba. Wani irin lallausan murmushi ya saki a wahalce da har take iya jin sautinsa cikin kunenta. Ya sake kusanta fuskokinsu dab-dab har hancinansu na gugar juna. A hankali ya sake matso da ita jikinsa yana shafa kanta da ɗan bubbuga bayanta yana hura mata iskar bakinsa cikin kunne alamar lallashi. Sannu-sannu ta fara sassauta rawar jikinta tana haɗiye hawayen da takeyi, sai kuma ta koma sauke ajiyar zuciya da sake yin luff a jikinsa kamar wata ƴar mage. Sai da ya tabbatar nutsuwar da yake buƙata gareta ta dawo jikinta sannan ya ɗan ɗago yana kallon fuskarta da tai shaɓe-shaɓe da hawaye. Dariya ta bashi ganin duk bakin tsiwar nan da baya mutuwa tun kan aje ko'ina har ya mutu yau murus. Cikin ƙoƙarin son danne dariyar ya furta, “Na ƙyale ki?” acan ƙasan maƙoshi.

    Da sauri ta ɗaga masa kai tana taɓe fuska zata sake sakin kuka.

      “No bana son kuka”.

   Saurin haɗiyewa tai tana jinjina masa kai.

            “Open your eyes muyi magana, in ba hakaba babu batun haƙuri”.

       Mar-mar ta farayi da idanun kamar zata buɗe amma kuma ta kasa, da ƙyar ta motsa lips ɗinta da ke rawa tana sake takwaf-takwaf da fuska. “Ka saka kaya to dan ALLAH”. 

    Murmushi yayi, tare da riko hanunta ya ɗaura a saman lallausan duvet ɗin gadon ya ce. “Lulluɓeni to”. Da ƙyar ta iya riƙo bargon saboda yanda hanunta ke rawa, ganin yanda take yi ɗin ya taimaka mata suka janyo a tare. 

      Cikin ƙara ƙasa da muryarsa ya ce, “Tom buɗe”.

    Ta jima tana kokawa da kanta kafin tai ƙundinbalar buɗewar ta saukesu kan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa da gaba ɗaya ya canja mata kamanni kamar ba Shahan-shan ba. Da sauri tai ƙoƙarin sake maidasu zata rufe ya girgiza mata kansa. Bata rufe ba sai dai taƙi yarda ta sake kallonsa. Yatsun hanunsa ya saka cikin nata yana murmushin nan nasa na iya lips, yana shaƙar numfashinta da busa mata nasa tana shaƙa itama.

        “Miyasa baki so mu zama abu ɗaya?”. Kanta ta girgiza masa alamar bata sani ba. “Magana nake so”.

      “Ba komai”. 

   Ta faɗa cikin muryarta da ke a matuƙar ɗashe dan gaba ɗaya wani irin kalar tsoronsa take ji. 

          “Dole akwai dalili, gashi ni kuma na kai matsayar da bazan iya amsar uzirinki ba balle tunanin zan dakata. Sai dai zan miki alkawarin kasancewa da ke ina mai lallashinki daga nan har lokacin da hawayenki zasu daina kwaranya Niazmina. K ba MATATA bace kawai RAYUWATACE, ke RAYUWATA ce ki riƙe wannan ki faɗama duniya da ƙarfin iko”. Ya nisa a hankali yana ɗan kai hannu saman goshinsa ya murza alamar ya gaji da maganar dauriya kawai yake. “Bazan so tilastaki ba, ba kuma zan iya barinki ba. Am so sorry zan baki sirrina da ban taɓa koda kwatanta bama wata ba a duniya, sirrina da nake ɓoyewa a tsahon rayuwar hankalina gaba ɗaya, sirrina da nake faman adanawa domin ke dana ɗauka tsahon rayuwar hankalina ina addu'ar samuwarki da ƙyawawan suffofi matar ƙwarai. ALLAH ya tsare miki ni ne domin wannan ranar Fhareedah, kamar yanda kema nake ji a jikina ya killacemin ke domin ni kaɗai, mijinki bai taɓa koda kwatanta aikata Zina ba, wata mace daba muharramarsa ba bata taɓa raɓarsa ba, mijinki ya jure wahalar ƙishin yini da tsahon dare domin ya kasance naki ke kaɗai, ke kaɗai ɗin da nake fatan ki zama ke kaɗai har ƙarshen numfashina, ki yarda zan baki wannan sirrin domin *KECE SIRRINA* Fhareedah bint Zayyan...”

        Kalamansa masu tasiri ne ga rauninta, ita bamai jayayya bace mai saurin sallamawa ce. Ita bamai taurin kai bace mai saurin karɓa ce. Ita ba mai saurin ƙaryatawa bace tana da rinjayen gaskatawa musamman ga mutum mai daraja irinsa da ƙarfin iko. Bata da zaɓin da ya wuce shigewa cikin jikinsa ta sake masa siririn kuka mara sauti da tasirinsa yafi amsa kuwwar baradan mayaƙa dubu bisa dubu a katafaren filin gumurzin yaƙi na ƙarƙashin daular mulkinsa.

         “Karka cutar da ni”.

     Ta faɗa tana mai ƙara ƙanƙamesa cike da sallamawa baki ɗayanta. Hannu biyu ya amsheta cikin tsumar jiki ya ƙara matsota ya rungumeta jikinsa da ƙyau, “Eshaan ba mai cutarwa bane ga maƙiyansa ma balle ke da ke ce rayuwarsa my Farishta (My Angle)”.

         “Na baka amanar rayuwata, na baka tukuycin hidimata domin ALLAH da girman hidimtawarka gareni da zuri'ata”.

     “Ni shugabane, bama kowane rai kariya a cikin ƙasata dolene gareni balle zuri'arki Niger. Ba ahalinki kawai ba, ko ƙasar gidanku idan wani yace zai damƙa da cutarwa baza'a sake jin labarinsa ba a duniya sai dai wani ba shi ba”. Ya faɗa yana ƙoƙarin rabata da duk abinda yay masa shamaki da ainahinta. Tai ƙoƙarin kanƙamesa amma yaƙi bata damar hakan, ga lips ɗinta ya riƙe cikin nasa alamar baya buƙatar sake jin komai da ga gareta kuma. Daga haka dukkan labarin ya canja kansa. Canjawa mai girman da girmansa ya wuce fassara da baki ko rubutu. Abinda kawai na sani shine Iffah ta zama Eshaan, Eshaan ya zama Iffah a wata gaɓa mai wahalar hasashe ga duk masu iya zama ƙololuwa a hasashen. Da gaske itace ɗin sirrinsa, sirrinsa da ke matsayin sirri mafi girma a duk cikin zagayen sirrikansa....


      ★★..... ★.....


   Duk yanda doctor ya so fahimtar da Miran Jasim da ya matsa a sallamesa ya ƙi saurarensa, akan dole ya sallamesa a daren. Motar asibiti ta kaisa har ƙofar sashensa. Duk ruɗewa matansa sukai da ganinsa, sai dai ko kallon inda suke baiyi ba ya shige ɗakin shi. A falonsa ya samu Miran Arshaan na faman kaiwa da komowa. Bai yi mamaki ba dan yasan shegen ruɗewa irin na Miran Arshaan ɗin, shi sam bai iya controlling tashin hankali ba ta siyasa a wani lokutan. caraf kawai yaji Miran Arshaan ɗin ya cafki hannunsa ya nufi bedroom ɗin sa da shi abinda bai taɓa faruwa ba. 

      “Anya kana lafiya kuwa Arshaan?”. Ya tambaya yana dafe wuyansa da ke masa zafi ko magana yayi, cikin gatse Miran Arshaan ya ce, “Haukacewa nai”. Dai-dai da shigarsu ɗakin. Miran Jasim ya fisge hannunsa yana mai dalla masa harara, “Ai na fahimci hakan tun ɗazun, nikam ka ajiye wannan shirmen naka kamun bayanin da zan fahimceka kasan ban cika son hauka ba fa”. Wata irin shegiyar dariya Miran Arshaan ya kwashe da ita yana nuna Miran Jasim, “Idan hauka nake kaima wlhy yanzu zaka fara Jasim.......” tiryan-tiryan ya kwashe komai ya sanar masa. Ashe kam haukan Miran Arshaan ɗin ƙarami ne da gaske. Dan take Miran Jasim ya rikice yana rantsuwar lasar takobi akan sai ya datse numfashin Tajwar Eshaan da Iffah kafin su su tona musu asiri.

        “Wannan duk bashi ne mafitarmu ba in faɗa maka, neman barbushi a wannan daren shine. Sai dai kuma akwai matsala, dan a haƙe wancan matsiyacin yake da son ganin wanda zai fita a daren nan. Shawara ɗaya gareni muyi fitar rana kuma a daban-daban”.

       Miran Jasim ya gamsu da hakan, anan suka tsaida maganar Miran Arshaan ya wuce. Sai dai a wannan daren kam babu wanda ya rintsa a cikinsu. Dan hatta Jasrah kasa gane kan Miran Arshaan tayi gaba ɗaya.....


       ★★.. TA-KURYA ★....


     A wani irin matsanancin firgici ta farka da ga mummunan mafarkin da ya nema zama sanadin bugawar zuciyarta cikin barcin jiran uwa da ya figeta. Sai kuma ta zabura dan farkawar tata dai-dai da dirowar UWA kamar wadda aka jeho. A gaban uwa ta zube babu alamar tana cikin hayyacinta, “Uwa ki tabbatar min mafarki nake, kice min ba Saiful-malik ɗina ba, kar kicemin tabbatacce al'amari na gani......”

        “Tabbatace ne, tabbas tabbatacce ne. Taci nasara, taci nasara ta-ƙurya taci nasara a kanki Ajlaan ya sallama mata. Ƴar shilar kanari ta zama mai nasara saman nasararki, ya bata sirrinsa fiye da girman kowane sirrinsa da wani ya sani a duniya, kin karya mana alƙawari da sakacinki. Dukkanin wahalarki ta baya ta rusa. Kina cikin matsala. Ke ce a matsala Ta-ƙurya, dan mu ba'a karya mana alƙawari ta-ƙurya, ba'a saɓa mana alƙawari, domin mu sharaɗinmu baya tashi hhahaha!!!!!.....”.

     Rawa jikin Malikat Bushirat yake kamar mazari, ga zufa tai mata wani irin mahaukacin sharkaf a jiki. Idanunta kam duhu-duhu take gani a cikinsu, tun tana iya jin furucin Uwa a kusa da ita har ya fara nesa-nesa, a cikin mintuna biyu tai rufff tare da yin baya yarafff ta zube alamar babu rai.......✍️


        _Tofa abin na gaske ne. 😱🏃🏃🏇🏇🚴🚵🚲🛵🏍️🚙🚗🛻🚐🚚🚛🚜🏎️🚒🚑🚓🚕🛺🚌🚈🚝🚅🚄🚂🚃🚋🚎🚞🚊🚉🚍🚔🚘🚖🚆🚢🛳️🛥️🚤⛴️⛵🛶🚟🚠🚡🚁🛸🚀✈️🛫🛬🛩️Wanda duk wanda ya shirya yazo mu ware kawai😷😷🙆🙆_


No comments

Powered by Blogger.