Daudar Gora Book 2 page 39

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (39)

.......Zuwa yanzu labarin abinda ke faruwa da iyalan Miran Jasim ya gama kewaye cikin masarautar. Hasalima babu wani ka-ce-na-ce dake kai kawo sama da zancen. Musamman da ya kasance Umm Husam na ƙarƙashin kulawar likitoci har yanzu, duk da dai Alhamdullah sun sami nasarar mata ɗorin karayar data samu a cinyarta. Amma taji

mummunan ciwo a ƙashin bayanta da bama a saka ran zata iya ƙara cigaba da takawa da ƙafafunta. Malikat Haseenat ta fita dubasu a asibitin har shi Miran Jasim ɗin dan shima dai ya jigatu a hannun Husam ƙwarai da gaske. Lokacin da take fitowa bisa rakkiyar Daneen Ammarah da hadimanta amintattu irin su Banou tawagar Tajwar Eshaan ke gabato Clinic ɗin shima. Malikat Haseenat ta kafeshi da idanu na tsahon lokaci, yanda yake tafiya ɗaɗɗaya cike da ƙasaita da izza, ga wani mayataccen ƙamshinsa da tun kafin ya iso shi ya iso hancinansu. Sai dai fuskar ciɗin-ciɗin fiye da kullum alamar akwai ɓoyayyar damuwa tattare da shi. Idanu ta ɗan lumshe tana ɗan murmushi da jin tarin ƙaunarsa na sake mamaye zuciyarta. Tana ma jikan nan nata so mai ƙarfin gaske da itama bata san adadinsa ba. Zubewar Hadimanta bisa gwiwunsu ya fargar da ita isowarsa gab da su. Itama ƙasa tai da kanta alamar girmamawa garesa. Tun kusantowarsu wajen idanunsa shima na'a kanta, sai dai bashi da damar tsayawa gareta kasancewar a Shahan-shan ɗin sa ya fito ba jikanta ba. Har cikin ransa yana ƙaunar wannan baiwar, ƙauna irin wadda shi kaɗai ya barma zuciyarsa sani. 

     Sai da suka shige sannan ta dubi Daneen Ammarah tana murmushi. Itama murmushin tai mata sai dai batace komai ba suka nufi motar da suka zo Clinic ɗin a ciki.


         Fuskar nan a matuƙar tsuke cike da barazanar da ke sake fidda ainahin kwarjininsa yake duban Miran Jasim da gaba ɗaya yake jin ya ruɗe bazai iya ma haɗa ko ido da shi ba. Gaba ɗaya yaron ya sake masa wani kwarjini mai ban mamaki fiye da da. Duk da ya tako zuwa Clinic ɗin ko uffan bai furta ba sai kaifafan idanunsa da ke sakaye a gilashin nan dan ɓoye yanayinsa da ya zuba masa. Sai su Sayeed Fayzul-haq ne ke tambayar lafiyar tasa da yawun Tajwar Eshaan ɗin. Shiko ko sau ɗaya ma bai motsa lips ɗinsa ba a wajen, hasalima shi hankalinsa kamar rabi da rabi ne a tare da su nan kawai. Basu wuce tsaiwar mintuna biyar ba suka nufi ɗakin da Umm Husam take itama. Itako ganin Tajwar Eshaan da kansa yazo dubata sai ta fashe da kuka. Idanunsa ya ɗan lumshe kawai, sai Sayeed Fayzul-haq ne ke bata haƙuri. Nan ɗin ma dai basu wuce mintuna biyar ɗin ba suka fice. 

         Da ga shi sai Miran Arshaan da Sayeed Fayzul-haq suka koma sashensa, sai amintaccen hadiminsa da baya rabo da shi a koda yaushe, jami'an da ke bashi tsaro biye da su kowanne hannu ɗauke da mahaukaciyar bindiga. Tako ina hadimai zubewa suke, sai dai ransu fari tas da ganin sarkinsu duk da ba suna ganin fuskarsa bane. Amma suna jin alfaharin sun taɓa ganinsa, koba komai suna jin shauƙi da sanin fuskarsa sau ɗaya koda bazai sake buɗeta a gare su ba har abada.


         Shigarsu da ƴan mintuna shugaban jami'an tsaron ya nema iso. Kasancewar Sayeed Fayzul-haq ya san da zuwansa cike da girmamawa yake sanar da Shahan-shan tare da neman afuwar sanar masa a ƙurarran lokaci. Alama yayi ta abashi izinin shigowar kawai. Takaici ya sake kume Miran Arshaan da ke zaune shima. Ya ballama Sayeed Fayzul-haq hararar gefen ido yana ƙwafa a zuciyarsa. 

     Cikin girmamawa shugaban jami'an tsaron ya miƙa gaisuwa, amintaccensa ya amsa a madadinsa. Zaune ya kai a inda Sayeed yay masa nuni, cikin sake risinar da kai na girmamawa ya miƙa files na hannunsa guda uku. “ALLAH ya ƙarama adalin shugabanmu lafiya da nisan kwana masu albarka. Alhamdullah mun kammala binciken da mukai alƙawarin yi yanda ya kamata, sai dai muna mai neman afuwar jinkirin da aka samu bisa wasu dalilai. Wannan files ɗin na cases ɗin ne duka uku. Alhamdullah mun sami nasarar gano hadimin da ya ɗakko Zawjata-almilk daga kurku ya jefata cikin swimming pool, a yanzu haka kuma yana hanunmu dan a daren ranar litinin muka cafkesa yana shirin guduwa da ga cikin masarautar nan. Mun gano shine ta hanyar zanen yatsun hanunsa da muka samu a jikin ƙofar kurkukun daya kasance ɗaya da ga cikin shaidun mu. Ya tabbatar mana da cewar sakashi akayi sai dai shima bai san wacece ba, amma ta jima tana sakashi ayyuka masu kamanceceniya da wannan tun ba yau ba. File na biyu akan kisan Sayeed Khairul-Bashar ne....”

     Wani irin bugawa mai azabar ƙarfi ƙirjin Miran Arshaan yayi kamar zuciyarsa zata faso ta faɗo. Shugaban jami'ai da bai san yanayi ba ya cigaba da faɗin, “......shima mun gano an kashesane ta hanyar kaisa ɗakin baya da ke a can wajen tsohon kurkukun can akai masa kisan gilla. A binciken da mukai cikin ɗakin ne muka gano zobensa da ɓalin gilashin jikin eyeglasses ɗin idonsa daya fita, tare da suffar hadimin da ya dinga azabartar da shi har ya mutu a gwajin ƙwayoyin idonsa da muka bibiya. Jinkirinmu ya samo asaline ma a dalilin binciko hadimin kasancewar yana rufe fuskarsa ne a lokacin aikata laifin. Shima dai kamar wancan ya tabbatar mana sakashi akayi, sai dai shi yanada matuƙar taurin kai dan yaƙi faɗar waɗan da suka sashi, da alama kuma shi ya sansu sani na zahiri saɓanin wancan.”

       Fitsari kawai ya ragema Miran Arshaan ya saki, amma illahirin jikinsa tsuma yake yana ƙoƙarin dannewa. Shugaban jami'ai ya cigaba da faɗin, “File na uku tushen samuwar madarar da aka kai sashen Zawjata-almilk ne.....”

          (Kun mutu Arshaan) zuciyar Miran Arshaan ta faɗa cikin matsanancin tashin hankali. Da ƙyar ya iya haɗiyar busashen yawu da fisgo numfashisa da ke neman suɓucewa da ga gangar jikinsa. Shugaban jami'ai ya cigaba da faɗin, “...madarar ta fito ne da ga sashen gidajen kuduncin wannan daula, dan an ɗauke ta daga can ne zuwa sashen uwar masu gida saboda yin ɓadda kama. Dan haka suspect ɗin mu dole zai kasance a ɗaya da ga waɗan can gidajen guda shida dake a cikin file ɗin. Domin a daren ranar ɗaya daga cikin jami'an mu ya ga wani a suffar ɓadda kama ya fito ta wata ɓarauniyar hanya da muma bamu san da ita ba a gidan nan. Munbi diddigin masu bin hanyar a tsahon kwanakin nan daya tilasta jinkirinmu, mun samu mutane huɗu sai dai har yanzu bamu tabbatar da fuskokinsu ba kasancewar a shirin ɓadda kama suke fitar. Amma hakan ba matsala bane saboda hanyar tabbatar da su ɗin su waye tana a hanunmu muna kan sake tabbatarwane gudun samun kuskure. Albishir dai da zamu bayar akan shi wannan case ɗin a yanzu haka wanda ya samar da dafin macizan yana hanunmu. An kamosa ne kuma a safiyar yau”.

      A karan farko Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ya saki wani malalacin murmushi da ya nema sumar da Miran Arshaan da ke jin kamar ya rumtse ido ya gansa a sashen sa ko clinic wajen Miran Jasim ko ma wajen boka Barbushi shi ma bai san ina yafi so yaga kansa ɗin ba. Sayeed Fayzul-haq kam kansa kawai yake faman jinjinawa ransa na mamakin waɗan nan abubuwa abin kamar wani shirin film. Amintaccen hadimin Tajwar Eshaan kam abun ya masa daɗi, musamman ganin murmushi mafi tsadar gani a fuskar shugabansa adali, sannan koba komai a su kansu ma amintattun hadimansa suna fatan kowaye ɗin kodan wahalar da suka fuskanta ta kusan wata guda a kurkuku. Shi dama ya daɗe daji a ransa Zawjata-almilk bazata iya aikata abin nan ba sai da jagorancin wani sheɗanin da ya fi ƙarfinta. Dan haka kawai yake jin ƙaunarta matuƙa musamman da ya fahimci wani abu ɓoyayye da ke tare da shugabansa game da ita duk da yana ƙoƙarin ganin ya danne. Amma kuma shi a yanzu babu wanda ya kaisa sanin wanene Tajwar Eshaan, koba komai barci ne kawai ke rabasu sai ko idan ya shiga ciki ko ya yini bai fito a bedroom ba. Kuma ko'a hakan tabbas tabbas sai ya gansa a yinin sama da sau biyar. Zai iya cewar da ga matarsa a yanzu sai shi ko a mafi ƙololuwar ganin Tajwar Eshaan ɗin.

        Wani irin kirari ya shiga jeroma shugaban jami'ai, tare da jinjinar ban girma na ƙoƙarin sa da yawun Shahan-shan da bayan murmushi babu alamar zaice wani abu. Magana da ga bakin amintaccen Tajwar Eshaan tamkar kai tsaye ne da ga bakin sa, dan yana cewa ne da say ɗin sa bawai raɗin kansa ba. Sannan koba komai shima a idanunsa Tajwar Eshaan ɗin ya saki murmushin nan da zai iya rantsuwa bai fi a karo na ƙalilan kenan ya taɓa gani ba. Hakan na nufin da gaske Shahan-shan ɗin ya yaba da ƙwazon jami'an tsaron gidan koda bai furta ɗin ba.  


       Jiƙewa iya jiƙewa jikin Miran Arshaan ya gama yi da zufa. Ga wani irin hajijiya da idanunsa suka fara gani. Kaɗan ya saci duban Tajwar Eshaan da babu alamar hankalinsa a kansa yake, hakama Sayeed Fayzul-haq. Yawu ya haɗe masu kaurin da har yanajin suna kamar ɗaɗa masa maƙoshi. Da ƙyar ya iya jarumtar cigaba da zama har shugaban jami'an tsaro ya gama ya fice. Babu alamar Tajwar Eshaan zai sake cewa wani abu akan batun, hakan yasa shima Sayeed Fayzul-haq haɗiyewa ya ɗakko zancen Miran Jasim da iyalansa, sai ɗansa dake a sashen Malikat Haseenat har yanzu. Ba ƙaramin dauriyar danne tashin hankalinsa yay wajen saka musu baki ba gudun kar Tajwar Eshaan ya harbo jirginsa. Dan ya mugu-mugun sanin hatsabibancin yaron nan, babu abinda ya baro a halin ubansa sai ma finsa taurin kai da yayi. Tattaunawar ta ɗan jasu wani lokaci dan har gab da magrib sannan suka tashi..........✍️


No comments

Powered by Blogger.