Daudar Gora Book 2 page 38

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (38)

........Da wani irin zazzaɓi mai masifar zafi da ƙullewar ciki ya fito da ga bayin, amma kasancewar sa jarumin jarumai ya shanye komai yana cigaba da ƙoƙarin shanye wanda ma ke taso masa sabo. Babu kowa a ɗakin da alama Iffah ta gudu, dan rigarta da ya cire ce kawai yashe a ƙasa, sai dai babu after dress ɗin da alama ita ta saka ta fice. Samun kansa yay da ɗan sakin wani miskilin murmushi yana cije lips ɗinsa da azabar ƙarfi.

Duk yanda yake son dannewa hakan ya gagara, dan wannan shine karo na farko da ya iya nisan kiwo da mace kamar haka. Hakan na nufin ya tsokaloma kansa abinda ya fi ƙarfin jarumtarsa, dan yanda cikinsa ke cigaba da ƙullewa har numfashinsa ya ɗan fara fisga lokaci zuwa lokaci. Duk da sanyin da ya fara ji na ratsa shi bai iya ya canja bathrobe ɗin jikinsa ba ga sumarsa ma jiƙe take da ruwa ya kai kan gado da ƙyar ya zauna, zufa yake ga jikinsa na tsuma abun kamar wani tsafi. Addu'ar da duk tazo bakinsa ya fara ambato da damƙo fillon data runguma ɗazun ya matse cikin hannunsa da azabar ƙarfin da ke bayyana asalin gwarzantakarsa. Wannan ranar yake gudu, wannan ranar ya ɗauka tsahon shekaru yana kaucemawa. Amma duk da haka sai da ta zo masa a gaɓar da bai shirya amsarta ba. Gaɓar da bai shirya fuskantarta ba. Gaɓar da bai shirya komai na yanda zai fara gudanar da ita ba. “Ya arrahaman”. Ya furta a hankali komai na masa kaikawo cikin gizo. Ya tabbatar idan har aka cigaba a haka to tabbas yau aiki zai buɗe, dan babu shakka kwaɓarsace zatai ruwa. Da ƙyar ya iya miƙewa, maganin da ya jima da daina sha ya shiga nema a inda ya tabbatar ya killacesa, da ƙyar ya samosa dan yayi nisa kasancewar ya daɗe da kauda idanunsa a shansa saboda abinda ka iya zuwa ya dawo kamar yanda doctor ya sanar masa har yay sanadin ajiyewar. Kwalin ya buɗe ya ciro, sai dai a mamakinsa babu komai a ciki sai kwafsan ashe ya shanyesa ma a wancan lokacin, bashi da zaɓin daya wuce sakin kwalin a wajen ya kai kwance yana jan bargo jikinsa dan rawar sanyinsa ƙaruwa yake yi, ga wani irin sarawa da kansa kemasa. Da gaske abubuwa sun masa matuƙar yawa, har ma yakan rasa wane irin tunani zaiyi. Ammien sa da sharaɗinta? Ko Iffah da abubuwan ban tsoronta? Ko Uncle's na sa da son zuciyarsu? Ko matsalolin talakawarsa da dogaransu kan jiran adalcinsa a koda yaushe? Ko.... Ko.... Ko.... Ɗin sun masa yawa, yawan da matsalar dake tattare da shi a yanzu kamar tana son nuna fin ƙarfinsu. Dan ya jima da fahimtar kansa, amma ya zama mayaƙi na gaske akan kansa da kare mutuncinsa da ga taɓa ƴar kowa. Babban fatansa a koda yaushe ALLAH ya bashi ikon riƙe kansa har zuwa ga halalinsa da zai iya bama sirrinsa, sirrin da yake fata bayan matar aurensa kar wani mahaluki ya taɓa koda kwatanta sani insha ALLAH. yana ganin ko yaƙi ko yaso lokacin yayi, sai dai lokacin yazo da wasu abubuwa masu nauyin gaske. nauyin da ya rasa ma ina ya kamata ya fara kamawa......


       ★A ɓangaren Iffah data sulale ta gudu tun bayan shigarsa bayi duk yanda tayi domin ganin ƙamshinsa ya bar jikinta hakan ya gagara. Tayi wanka, ta shafa nau'in turarruka daban-daban sai dai ƙamshin jikinsan na nan daram a cikin hancinta da yaƙi bata damar jin kowane ƙamshi bayan shi. Kamar wadda aka zarema lakar jiki tai sakwat a jikin bango tana lumshe idanu. Ita kanta bata san ainahin mima take ji a kansa ba, abinda kawai ta sani komai kawai ya ƙwace mata, bata da wani ƙarfi a zuciya da jikinta a halin yanzun, abinda ya farun kuma yay mata tsaiwar sojan badakare a ƙahon zuciya babu alamar zai motsa. Hanunnta ta kai ta shafi lips ɗinta, sai kuma tai saurin janye yatsun biyu tana mai girgiza kanta kamar wadda akema magana a kunne. Buɗe idanun nata tai cikin sauri ta sake nufar inda turarrukan suke, ɗaya bayan ɗaya ta dinga binsu tana shafama jikinta, ita dai a dole sai ta daina jin wancan ƙamshi. Abin dariya abin tausai harta gama ƙamshin na nan dai bata daina jinsa a cikin hancin nata ba duk da yanda ɗakin yay wani masifar haukacewa da ƙamshin data baza har ana jinsa waje. Miya rage kawai ta saki kuka ta huta, sai ko tai takwaf-takwaf da fuska kamar zata fashe...

         Haka taita kai kawonta a ɗakin har mai gyarawa yazo gyara da sanar mata an gama shirya break fast. Da gaske yunwar take ji, amma bazata fita su haɗu da shi ba, dan haka ta bada umarnin kawo mata nan tana mazurai a karo na farko. Cikin ƙanƙanin lokaci aka cika umarnin nata kuwa....


      ★★.... ★....


       A can fada tun kusan awa ɗaya baya ake tsammanin fitowarsa, amma shiru kakeji. Hakan abune da ba faruwa yake ba. Tajwar Eshaan mutum ne da baya saɓa alƙawari. In har yace zaiyi abu to zai yisan komai girman ƙalubale da zai iya fuskanta a yayin yinsa kuwa. Hakama in har yace bazai yiba tofa ko kai waye bazaiyi ɗin ba. Kaifi ɗaya ne shi, mai faɗa da cikawa. Mai gaskiya da son tabbatar da ita a mulkinsa, waɗan nan halayensa ne dake matuƙar sake ƙawatashi da kwarzantashi ga al'ummar sa a bayyane. 

         “Anya kuwa lafiya yau?”.

    Miran Arshaan daya matsu da ganin fitowar Tajwar Eshaan ɗin ya taso zuwa inda Sayeed Fayzul-haq ke tsaye ya faɗa cike da nuna damuwa. Kai Sayeed Fayzul-haq ɗin ya jinjina masa shima da ƴar damuwar a fuskarsa. “Banajin matsala ce insha ALLAH. Dan ban daɗe da ganawa da shi ba, sai dai kasan mutum mai iyali...” ya ƙare maganar da wani ɗan murmushin su na manya. Kamar Miran Arshaan ya sokama Sayeed Fayzul-haq wuƙa a ƙirji yaji, dan haka kawai maganar iyalin na Tajwar Eshaan ta soki ransa, murmushi Sayeed Fayzul-haq ya ɗanyi yana kauda kai kamar bashi ya takalosa ba, dama kuma ya fadane da biyu.... 


     ★★..... ★....


     Shikam mai gayya da aikin har akai sallar azhar bai gama samun kansa yanda ya kamata ba, dan haka yay sallarsa a ɗaki cikin ƙarfin hali. Rashin fitowarsa salla ya sa su Sayeed Fayzul-haq suka tabbatar da akwai dalili mai ƙarfi daya hana shi fitowar kam tabbas. Ya cigaba da son ganin ya dawo normal, hakan bata samu ba sai kusan gab da la'asar da ya sake komawa Gym ya maida kansa busy, dan wani irin mahaukacin work out yayi, kafin ya fito sharɓan da zufa idanun nan babu alamar rahama yau kam an tsokalo maza. Tsaf yay shiri cikin ɗan sauran ƙarfin da ke jikinsa, dan gaba ɗaya jinsa yake sai a hankali. Haka dai ya daure ya fito domin zuwa massalaci. 

        Iffah dake sharce ruwan alwala da tayo a fuskarta da wani irin sauri ta buɗe idanunta jin an buɗe ƙofar. Ido huɗu sukai da shi, da wani shegen sauri ta maida nata idanun ta rumtse da juyama ƙofar baya, cikin salon nasa na basarwa da shegen miskilanci da ƙasaitar nan tasa shima sai ya ɗauke kai tamkar bai ganta ba. Ta bayanta ya raɓa ya wuce, wasu takardu da ya ajiye ya ɗauka a kan study table ɗin ɗakin ya sake zuwa zai gittata. Tsaye take har yanzu idanunta a rufen ita a dole bata son su haɗa ido. Ƙirjin Iffah bugawa ya dingayi da sauri-sauri jinsa a kusa da ita, idanun ta buɗe kaɗan dan son tabbatarwa. Shi ɗinne dai a gabanta ya zuba mata idanunsa da ke cikin eyeglasses masu ɗan duhu. (Wayyo ni ALLAH) ta ambata a zuciyarta tana maida idanun ta rumtse a daburce ta ce “Barka da rana”. 

      Idanunsa dake a wani irin yanayin da ya tilasta mishi saka gilashin ya ɗan lumshe yana sake buɗewa a kanta. Cikin dakewar muryarsa dake ɗan shaƙe fiye da koda yaushe data sani kamar wanda akaima tilas acan ƙasan maƙoshi ya furta, “After Isha ki sameni”. Idanunta ta buɗe a firgice, sai dai shi tuni ma har yayi gaba abinsa. Dai-dai yana ƙoƙarin ficewa taji kamar ta fasa kuka, amma sai ta haɗiyesa tana ƙoƙarin aro jarumta. A hankali ta furta, “Zanje na ga Ammie to kafin sannan Please”.

    Cak ya dakata sai dai bai juyo ba har na wasu sakkani. Kin san dai kina a ƙarƙashin umarnin shari'a ne ko?”.

         Kanta ta jinjina kamar yana kallonta, kafin ta ce, “Eh na sani, alfarma kawai nake nema. Jiya ranta ya ɓaci, matsayinta na mahaifiyata bai kamata na kwanta cikin nutsuwa ba tana fushi da ni. Ina son naje gareta domin neman afuwa”.

    Gaba ɗaya jijiyoyin jikinsa ne suka ƙarasa saki, wani sanyi na ratsa masa tun daga kan yatsun ƙafa har tsakkiyar kansa. A sannu ya waiwayo ya zuba mata idanunsa. Kallo yake mata irin na kin mamaye komai da komai ɗin nan, a zahiri kam baka isa tantance komai bai tattare da shi, dan fuskar na'a yanda taken nan tsuke tamau. “Ki jira ni”. 

      Ya faɗa kai tsaye dai-dai yana ficewa. Numfashi ta sauke a hankali da yin ɗan baya kamar maijin jiri ta manne da bango, mamaki takeyi, mamakin kanta da komai ma, ta wani gefen kuma ta fara tsoron abubuwan da ke neman cigaba da wajabta kansu a ƙarƙashin mafarkinta, toso ture wannan amma zuciyarta nata ingizata akai, abu mafi ɗaure kai kamar yanda tai mafarkin ta tambayesa zuwan a mafarkin a zahirin amsar da ya bata acan ne anan ma, mi hakan ke nufi? Tayaya ma kanta zai cigaba da ɗauka, gaba ɗaya sai kewar iyayenta ta sake dawo mata sabuwa a zuciya, ta shiga jan ajiyar zuciya hawaye na ciko mata idanu. Iska ta ƙara fesarwa ta buɗe idanunta tana sakin murmushi, murmushi mai ciwo da ita kaɗai ta barma kanta sani sai ALLAH. Sai kuma ta taɓe baki kaɗan da tuno furucinsa. _Wai ta sameshi, to ta sameshi kamar ya? Itakam wace ƙaddara ce ma ta sata amincewa auren mutumin nan? Jibafa yanda yake wani ɗacin rai da ɗa duniya bashi ya gama murje mata lips da jikinta ɗazun ba, halan ma wai ya manta tsiyar da ya aikata ne. (Ko zaki tambayosa) zuciyarta ta ayyana mata. Zabura tai cikin masifa da tsiwa kamar zuciyar tata mutum ce, sai dai kuma batace komai ba aka dai cuna bakin gaba. (😂Gwara dai kiyi shirun ta gidana)........✍️


No comments

Powered by Blogger.