Daudar Gora Book 2 page 33

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (33)




........Ruwan da ke ajiye kan table ɗin cikin jug ya ɗauka ya tsiyaya, cike da kulawa ya miƙa mata yana lumshe idanu da buɗewa. Kai ta girgiza masa zatai magana, shima ya girgiza masa nata alamar kartace komai. Ya ce, “please Ammie”. 

      Ruwan ta amsa, kurɓa biyu tai masa ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya, ta sake yunƙurowa zatai magana ya sake girgiza mata kai dai. “Please Ammie slow dawn ki faɗa min mike faruwa?”.

          “So nake ka saketa kawai, ka janye garkuwar da ka bata, na sani dama Saiful-malik yarinyar nan bazata taɓa barinka ba. Amma Mammah da kai da Ammarah duk kuka gagara fahimtata, to gashi tun ba'aje ko'ina ba ta sake aikatawa. Yanzu badan ALLAH ya sa shi Sayeed Fayzul-haq ɗin ya lura ba wani zancen ake ba wannan ba, bazan iya jure rasaka ba a duniya wlhy Eshaan, dan haka ni kawai ka saketa na gaji haka bazan iya ba..”

          “Wlhy Ammie ban aikata abinda kike zargina da shi ba”.

      A tare duk suka dubi inda maganar ke fitowa, Iffah ce tsaye kanta a ƙasa, amma duk da haka ana iya hango yanda fuskarta tai jage-jage da hawaye. Abinka da fara tai jajir musamman ma kan hancinta. Wani irin mugun kallo Malikat Bushirat ke jifanta da shi, sai kuma ta miƙe cike da takun izza ta nufeta. Ji kake tauuuu!! Ta ɗauke fuskar Iffah da mari lafiyayyu haggu da dama. “K! Har kinyi isar da ina magana da ɗana ki kasance a wajen? Wacece k!? Ƴar uban waye k!?”.

        Idanunsa ya rumtse da sauri jikinsa na wani irin yamutsawa, amma a zahiri zaune yake a dake yanda ta barsa ko kallonsu ma bayayi. Malikat Bushirat ta shaƙo Iffah da ko gezau batai a tsayen da take ba saboda taurin zuciya, duk da kuwa marin ya matuƙar ratsata dan zata iya rantsuwa ba'a taɓa mata mari mai azaba irin wannan ba. Yanda ta shaƙontanne yasa fuskarta ɗagowa, da wani irin gudu jini ya shiga fitowa a hancinta yana sauka har kan hannun Malikat Bushirat, hawayen fuskarta kuwa tsaf sun ɗauke, sai wani irin mugun jaa da idanun sukayi mai ban tsoro.

        Malikat Bushirat da idanunta suka riga suka rufe ta ƙare matse wuyan Iffah duk da ganin jinin tana zazzaro manyan idanunta da itama suka kaɗa sukai ja.. “Yau zan kasheki na kashe banza wofi, sai naga ubanda ya tsaya miki da har kike tunanin idanunki sunyi tsaurin halakamin yaro...”

     Wani irin kakarin azaba Iffah ta shigayi, ga idanunta sun fara juyewa, jinin hancinta ko sake gudu yake dan a tsinke yake (haɓo). Amma tsabar ƙarfin hali bakin bai mutu ba, jajayen idanunta da ke neman wulƙicewa ta zuba cikin na Malikat Bushirat tana sakin wani murmushin wahala. “A tunaninki kasheni ne zai canja komai? To kinyi kus...ku...ren fa... fahimtar hakan Ammie, dan masu san kashe ɗakin zagaye su...suke da ke. Idan kin kasheni ki ma... maciji kika kashe baki sare kanshi ba, ki rubuta ki ajiya ko gangar jikina ta daina numfashi sai ruhina ya dawo wannan masarautar ɗaukar fansar ruhin ƴan uwana......”

         Wani irin yarfar da ita Malikat Bushirat da jikinta ke rawa yayi, dan wani irin guguwar bala'i ta hango a cikin idanun Iffah masu matuƙar gigitarwa tamkar ba ainahin idanun yarinyar ba. Akan jikinsa Iffah ta faɗa, dan yarfar da ita da Malikat Bushirat tayi dai-dai da mikewarsa dama, sai dai kalaman Ammien sa da shaƙar da tai mata kawai suka shiga kunensa da idanunsa, baiji komai na da ga abinda Iffah ta faɗa ba ita. Hankalinsa ne yay bala'in tashi da ganin jinin da ke fita a hancin Iffah, yay saurin tarota jikinsa ganin jiri na neman zubar da ita. Sake harzuƙowa Malikat Bushirat tayi. “Please Ammie, Please! Please” ya faɗa da wata irin raunananniyar murya mai sage duk wani kuzarin mutum. 

       Idanunta da suka gama juyewa gaba ɗaya ta watsa masa, tana mai nuna shi da ɗan yatsa a kausashe. “Na baka nanda awa ashirin da huɗu in bakabi umarnina ba zakasha mamaki Eshaan”. Fuuuu ta nufi Alevator batare da jiran amsarsa ba ta shige....

     

     Hankalin Tajwar Eshaan gaba ɗaya sai ya rabu biyu. Furucin Amminen sa ga kuma jinin da ke zuba da ga hancin Iffah. Tsabar yanda ya rikice sai ya shiga laluben waya. Hannunsa Iffah da ke ƙoƙarin ganin jinin ya tsagaita ta riƙe dan ba yau ta fara haɓo ba. Kanta ta shiga girgiza masa tana magana da ƙyar dan ta shaƙu a wuyantan nan. “Karka kira kowa Sultan Please. Haɓo ne kawai ka samun ruwa a kaina in munyi sa'a zai tsaya”.

       Kansa ya jinjina mata kawai, dan duk da ruɗanin da yake a ciki babu abinda ya canja a nutsuwarsa da ƙasaitar nan. Wanda ma zai iya ganinsa a haka sai ya iya ɗauka ai baima wani damu ba. Ɗagata yay cak cikin hannayensa yana tafiya cikin takun nan nasa step by step babu wani gargada ko garaje a ciki. Ɗakin da suka fito ya koma da ita. Kai tsaye cikin haɗaɗɗen toilet ɗin ɗakin ya kaita, faɗa masa duk yanda Ummu ke mata idan tana haɓo tayi, cikin sa'a kuwa sai gashi ya tsaya. Sai dai ba ita ba hatta shima kayansa jinin duk ya ɗan taɓa, nashi ma sai yafi bayyana kasancewarsu masu haske. Dole ya cire rigar dan jini na ɗaya daga cikin abinda bai son gani, yanzu hakan ma tsigar jikinsa sai tashi take yi, dakewarsa ce kawai ta ɓoye hakan a zahiri. Gama cire rigar dai-dai da ɗagowar Iffah da ke son ce masa thanks you. Cikin sauri ta maida idanunta ƙasa ƙirjinta na wani irin harbawa, dan babu komai a cikin rigar, da ya ciren sai ya zam da ga shi sai dogon wandon pyjamas ɗin kawai ya rage. Koda wasa bata taɓa sanin mutumin nan haka yake a murɗe ba kamar wani ɗan wasan danbe ba, ita fa duk tsiwar nan tata haka kawai duk wani mai irin suffar nan tsoronsa ma takeji, shiyyasa bata kallon wristiling koda wasan wasa.

          Shiko da tun sanda ta maida kai ta duƙar ya fahimci inda ta dosa hanyar fita ya nufa, sai da ya je gab da ƙofa a maganar nan tasa kamar ta dole ƙasa-ƙasa ya furta “kiyi wanka” ya ƙarasa ficewa. Ta jima zaune maganar kiyi wankan na juya mata a rai, tana da buƙatar wankan, amma tana jin kunyar yinsa saboda sanin bata da kaya a nan. To amma tunda shine ya ce tayi tasan maybe ya ɗauka mata kamar wancan ranakun. Da wannan tunanin ta gamsu da yin wankan. Sai da kuma ta kammala ta duba babu bathrobe duk sai towels a bathroom ɗin. Kamar zatai kuka ganin duk basu da wani girma, da ga ƙarshe ta samu ɗan babba da ya kai mata gwiwa da ƙyar.

       Kamar mai shirin yin sata haka ta fito da sanɗa, ta saki wata wawuyar ajiyar zuciya ganin babu kowa a ɗakin, da ɗan hanzarinta ta ƙaraso cikin ɗakin tana dube-duben koya ajiye mata kayan, ganin dai babun tai ƙwalƙwal da idanu kamar zatai kuka. Zuciyarta na raya mata ta koma ɗakin da kayanta suke, ɗan ɗagowa tai  firgigit dan jin motsi da tai har towel ɗin na neman suɓuce mata saboda tun asali ita fa bata iya ɗaure towel da ƙyau ba sai Arfa ta mata, shiyyasa tafi son babban towel da zata iya cikuyewa a hanunta ta riƙe.

      Cak ya tsaya sakamakon saukar idanunsa kan wani damɓareren tabon tawadar ALLAH a bayanta dake fari sol a ta ɓangaren kafaɗar damanta. Iffah da duk ta rikice da ganinsa tuni ta ɗane gadonsa taja lallausan duvet ɗin sa ta cikuykuye jikinta dake mazarin rawa. Babu abinda ta tsana kamar namiji ya gammata jikinta. Musamman ma shi da takema kallon wani abu da ban. Gwanin naku tuni ya basar da haɗiye komai kamar ma bai san da zamanta a ɗakin ba. Sai ma ƙarasa takowa da yay jikin gadon ya ajiye mata kayan da ke hannunsa ya kai zaune shima ya bata baya. Idanunsa ya rumtse zuciyarsa na wani irin harbawa da ganin ƙyaƙyƙyawar surarta da tabon nan na tawadar ALLAH da ke a bayanta. Buƙatar son sake gani yake dan tabbatar da abinda zuciyarsa ke cusa masa yana ƙaryatawa. Sai dai yasan haka gatsau gareta bazai yuwu ba, dan haka sai kawai yama miƙe ya fice a ɗakin domin bata damar shiryawa.


      Tsahon mintuna goma sha biyar ya ɗauka kafin ya sake dawowa ɗakin. Ta saka kayan sai dai tana zaune a kan gadon ta cusa kanta cikin ƙafafunta komai da ya faru na dawo mata tamkar mafarki. Dan tsantsar tsanarta data hango cikin idanun Malikat Bushirat yaƙi barin ranta sam. Tasan zata iya ganin fiyema da haka saboda abinda ta aikatama tilon ɗanta amma sai zuciyarta ke tabbatar mata akwai dai.... 

       Motsin shigowarsa ta sata katse tunanin sai dai bata ɗago ba. Kallo ɗaya yay mata a cikin kayan nasa da sukai mata burum-burum duk da t-shirt ce fara da wando 3quater ya ɗauke kai. Bayan minti ɗaya da wasu ƴan sakkani taji motsin zamansa kusa da ita. Ɗagowa tai tana ƙoƙarin haɗiye hawayenta, dan wani kewar iyayenta da yan uwanta takeji. Shayin da ya ajiye a ɗan coffee table ɗin gaban gadon ya tura mata batare da ya ce komai ba. Ƙyakyƙyawan kofin ta bi da kallo, sai taji shayin ya burgeta dan tunda ta shigo ɗazun dama ƙamshin ya cika mata hanci. Ɗan ɗagowa tai, sai ko suka haɗa ido, ƙif-ƙif ta farayi da nata kamar zata sake sakar masa wani kukan da take ƙoƙarin haɗiyewa. 

       “What?”.

   Ya faɗa ƙasa-ƙasa shanyayyun idanunsa na bin hawayen fuskar tata da kallo. Sake ƙwaɓe fuskar tayi a hankali ta furta, “Kai ne ai”.

     “Nai miye?”. 

  Ya tambaya cikin ɗan waro idanunsa waje.

         “Ni bana son kallo”.

     Yanda ta faɗa tana tura baki da share hawayenta ba ƙaramin tunzurashi yay ba. Amma sai ya kanne yana ƙara ƙanƙance idanun nasa a kanta da motsa lips ɗinsa kaɗan yana binta da shegen kallon nan nasa. Sai kuma ya ɗan laɓe baki a fisge ya furta, “Sadakina na kalla ai”.

         Furucin nasa yazo mata a bazata, dakatawa tai daga ƙoƙarin kai kofin shayin bakinta ta dubesa da sauri domin tabbatar da shi ɗinne ya faɗa ko wani aljani. Bayan ita da shi ɗin dai babu wani a ɗakin, sannan kuma ya ƙi ɗauke idanun nasa da ga kanta, sai ma sake narkesu yake da wani salon kallo mai saka tsigar jiki tashi kamar mai jiran cewarta..........✍️


No comments

Powered by Blogger.