Daudar Gora Book 2 page 31

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (31)

..........Abune da bai taɓa faruwa ba a tsakaninsu, a tsahon shekarun da suka kwashe tare na aure talatin da ɗaya cif. Cikin ido take dubansa da wani irin kallo mai gigita zuciya “Jasim tsahon shekaru talatin da ɗaya kenan nake zaune a ƙarƙashin mulkin mallakarka. Nayi juriyar nayi kawaicin

amma na fahimci kai ɗin gafalalle ne da baya gane komai a rayuwarsa sai son zuciyarsa. A da dai na haƙurce maka na shanye, amma a yanzu zan tabbatar maka dai-dai nake da kai asararre kawai da ya girma bai san ya girma ba!”. Ta yarfar da hannunsa gefe da wulla masa wani irin mugun kallo ta juya zata fice. Wata irin zabura yay da ga sumar wucin gadin mamakinta daya riskesa, ya wani shaƙo wuyan rigarta ta baya ya fizgita jikinsa na rawa. Kiyyyyy rigar ta shiga kecewa, hakan yasata yin gaba. Tsabar shi cikakken mugune yasa ƙafa ya taɗeta.  Mummunar buguwar da ta sakata ƙwalla wahalalliyar ƙara tai a ƙasan wajen. Cikin rufewar idanu yasa ƙafar ya taka mata gadon baya sai ga ƙashi na bada sauti.

        A guje suka dinga rige-rigen shigowa dan ƙarar tata ta matuƙar ratsa kunnuwansu. Basu kaɗai ba hatta da hadiman dake musu hidima a sashen babu wanda zai ce baiji ƙarar baiwar ALLAHr nan ba. Ganinsu baisa ya dakata da dukanta ba. Cikin wata iriyar fusata babban ɗansa da itace mahaifiyarsa Husam yay wani irin kukan kura ya hankaɗashi baya sai da ya daki bango. Baiyi wata-wata ba kuma ya damƙi wuyan rigarsa ya shaƙeshi dan shima yaron tsageran kanshi ne. Kaf halin Miran Jasim ɗin ya kwaso, sai dai duk da haka yana bala'i bala'in son mahaifinsa. Ya jima da ciwon dukanta da mahaifinsa keyi duk da bata taɓa fitowa fili ta sanar masa ba. Tun yana yaro ko shatin yatsu ya gani a fuskarta ya tabbaya sai tace bakomai ko bigewa tayi. Sai bayan ya girama ne ya fahimci mahaifinsa ne ke marinta kamar yanda suma sauran matansa biyu ba tsira sukai ba. 

         Rawa jikin sauran matan nasa ya shigayi, sun rasa ma wa zasu bama ɗauki, shi da Husam ya shaƙe ko Buhaysah da ke kwance tana madoɗowar azaba. Gwara kansa da bango da Husam yayi yana ƙaraji ya sa matan yin kansa da sauri suna kuka da roƙon Husam ɗin ya sakesa. Amma ina yaron nan ƙara gwara kan Miran Jasim yake yana kai masa naushi kamar ba mahaifinsa ba. Ga wani irin ƙarajin ɓacin rai yanayi mai haɗe da kuka.

      Sukam al'amarin nan yafi ƙarfinsu, hankali tashe suka shiga neman number Miran Arshaan amma ba'a daga ba. Har kira uku babu alamar za'a amsa dole suka maida akalar kiran ga Daneen Ammarah domin ta sanar da Mammah da Sayeed Fayzul-haq kasancewar sun san yana ɗan jin shakkarsu, dan daga Malikat Haseenat ɗin har Sayeed Fayzul-haq ɗin basa ɗaukar raini ko wasa a garesu dama masarautar kowa yasan haka.

     Wayar ta riski Sayeed ne lokacin da yake fitowa daga sashen Tajwar Eshaan bayan masa rakkiya daga sallar la'asar da suka idar. Itama Daneen Ammarah lokacin tana ƙoƙarin tashi da ga abin salla. Hankali tashe duk suka nufi sashen Miran Jasim ɗin har da Malikat Haseenat ɗin da aka saka a mota, dai-dai da shima Miran Arshaan ya nufi can dan shima yayi mamakin rashin ganinsa wajen tattaunawar da akayi duk da yasan dai ransa a ɓace yake matuƙa. Dan tun jin Tajwar Eshaan bai fito fada ba da safe ransu ke'a jagule. Yanzu kuma a wannan zaman ashe ma akansu ne akayisa duk da dai shi Tajwar Eshaan ɗin bai fito fili ya ambaci suna ba, amma duk da wannan sanin da yay akan Miran Jasim ɗin ya zaɓi yimasa zamba cikin aminci dan a ganinsa lokaci yayi da shima zai dakata da ga rakkiyar Miran Jasim ɗin ya fara yaƙin kansa...


         Da ƙayar aka ɓanɓare Husam da ga shaƙar da yay ma Miran Jasim, yaraf ya zube ƙasa hannunsa kan maƙoshinsa yana kakari. Idanunsa sunyi ruƙu-ruƙu tsabar yanda yaji shaƙar nan, ga kansa daya fashe saboda ƙuma masan daya dinga yi sai jini yake yi. A gefe ga Buhaysah da ke kukan wahala Husam ya je ya rungumeta yana kuka da alama dai yaji mata ciwo a baya koma ya karya ta ne oho. Malikat Haseenat da ta ɗan girgiza kanta da duban Sayeed. A matuƙar ruɗe Sayeed Fayzul-haq ya jinjina mata kai. Waya ya ciro yay kiran clinic ya bada umarnin a kawo ambulance ƙofar sashen Miran Jasim ɗin.....


        A gaggauce aka miƙa Miran Jasim da Buhaysah asibiti. Husam kuma Malikat Haseenat tasa Daneen Ammarah su wuce da shi sashenta, yaron sai kuka yake mai matuƙar cin rai da zai baka tausayi, dan duk wanda ya kalla mahaifiyarsa yasan akwai babbar matsala a bayan nan nata da mahaifinsa ya taka 

      Jigum-jigum sauran matansa da yara suka zauna. Kowa ka gani cikin damuwa. Dan wannan abun kunya ne da in har ya fita koda a cikin masarautar ne bazasu taɓa jin daɗi ba. Mijinsu mugu ne, dan ba yau ya fara kai hannunsa kansu ba, sai dai in ka cire Tajwar Haysam da Malikat Haseenat da mahaifiyarsa Ameera Banafsha kafin ta mutu babu wanda yasan hakan. Ko ƴayansu Husam ɗinne kawai ya sani sai mai bi masa Faida data zama babbar budurwa, inda ma ALLAH ya bata miji da tuni tai aure. Koda yake ba mijin ta rasa ba, taƙi sauraren samarin ne saboda mutuwar son Tajwar Eshaan da takeyi tun dawowarsa ƙasar ruman. Hatta da mutuwar matansa bai taɓa saka Faida jin zata iya daina son sa ba. Randa ya bayyana fuskarsa ba ƙaramin hauka tayi ba, duk da kuwa itama ɗin ƙyaƙyƙyawa ce sosai, sai dai shi kuma baima san tanayi ba..


      Abinda suke gudun dai kam sai da ya faru, dan tuni hadiman sashen nasu suka fara zare jiki kai gulma ga iyayen gidansu. Dan wannan al'adace ta masarautar. Mafi yawan hadiman kowane sashe zaka samesu ƴan leƙen asirin ɓangarori daban-daban ne, duk da iyayen gidansu kanji a ransu akwai ƴan leƙen asirin bazasu iya banbance su ko fitowa suce ga su ba balle su fiddasu a masu hidimar tasu. Hakan yasa dole kowa ya haƙura da kasancewa cikin taka tsantsan kawai. Fitar wannan magana kuma sai tai dai-dai da wadda ta fara yawo na sakama Tajwar Eshaan kayan tsafi a kujerar zamansa da maganar Miran Arshaan da kai tsaye aka fara fassarata da cewar da Miran Jasim ɗin yake. ga kuma abinda ya aikata yanzu na sake tabbatar da maganar Miran Arshaan ɗin akwai ƙamshin gaskiya kenan.....


       

    ★★.... ★....


       Iffah kam da bata san mike faruwa ba rabonta da ganin Tajwar Eshaan tunda ya bar sashen ɗazun da azhar. Duk da dai itama barcinta ta sha bayan idar da sallar azhar ɗin. A makare ma tai sallar la'asar. Kaɗan ta tsakuri abincin da aka kawo mata har ɗaki. Sanin babu mai hawowa floor ɗin na ƙarshe sai shi da amintaccensa yasa ta ɗauka wayar da ya faɗa da card ɗin data gani ta fito katafaren falon da wani irin ƙamshi mai masifar daɗi ke tashi. Shiru babu kowa hatta da television a kashe suke, dan girman falon yasa kusan tv uku ne. Itama kallon bawani ya ɗaɗarata da ƙasa bane, barta dai da son bibiyar labarai saboda yanda take matuƙar ƙaunar aikin jarida. Shine burinta, kuma Insha ALLAHU sai ta cika shi in har ta cigaba da numfashi a doron duniya. Cikin ɗaya daga lafiyayyun kujerun ta shige tana mai bin haɗaɗɗen falon da kallo kamar yau ne ta fara shigarsa. Komai na ciki ka kalla kasan an narka dukiya mai ban mamaki, ya fita tsaf kamar ba'a duniyar mutane ake ba (😂to dama irin wanga falo kam ai sai duniyar novel🤣 lols). Baki ta ɗan taɓe tana ƙunƙunin da ita ta barma kanta sani, daga haka takai kwance ta fara sarrafa wayar domin yin online shopping ɗin da ya umarce ta, dan bata son takurama Mamy kunyarta ta ke ji, akan abin nan daya faru tana jin nauyin haɗuwa da mutane biyu, Malikat Haseenat da Daneen Ammarah, saboda yanda ta shayar da jininsu guba amma su goyon baya da son bata kariya ne burinsu, wannan al'amari na bata mamaki da ƙara sakata a kunyar gudun haduwa da su. 

     Wasu kayan motsa jiki ne kalar pink sukai matuƙar fara ɗaukar hankalinta, ta shiga sakin murmushi tana yaba kayan a zuciyarta. Sai dai kuma ganin kuɗin da aka rubuta na sayensu ya sata zaro idanu waje. Sai kuma ta ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa tana ƙunƙuni wai ai dai kuɗin ma nasu ne su talakawan RUMAN, garama ta ci musu. Da wannan shawarar zuciyar tata ta dinga jidar kaya masu ƙyau da tsada tana ƴar dariyar muguntar yau sai tama asusun nasa wawason taron dangi zai gane ita Iffah bata wasan yara bace. (Ni dai nace hummmm 😂)

        Ganin magrib ta gabato ga ɗan sanyi-sanyi na ratsata ya tadata a falon ta koma ɗaki. Shigewarta babu jimawa ya shigo shi kuma da ga wajen hawan doki. Ɗan waige-waige ya shigayi a falon saboda jin ƙamshin turarenta. Ganin dai babu alamar mutum ma ya sashi fesar da numfashi cike da basarwa ya nufi ciki. Bai jima ba sosai ya sake fitowa cikin shirin tafiya masallaci. A kallo ɗaya da zakai mai zaka fahimci wanka kawai yayi ya fito. Sake ficewa yay gabatar da sallar magrib.....


      ★★.....


     Kamar yanda labarin abinda ke faruwa yaje kunnen kowa a masarautar haka itama ya isa nata kunnen. Dai-dai amintacciyar hadimarta na sanar mata Jasrah ta shigo a rikice. Malikat Bushirat da gaba ɗaya hankalinta yay masifar tashi jin wai an samu kayan sihiri a karagar mulkin Shahan-shan tabi Jasrah da ke shigowa itama a masifar tashin hankalin da kallo. Tsawa Jasrah ta dakama Hadimar, cikin rawar jiki ta tashi ta fice. 

        Kafin ma hadimar ta gama ficewa ta fara magana a masifar tashin hankali hawaye na zubo mata. “Akia akwai matsala wlhy, ni dai wannan masifa ta isheni, kar mutanen nan suyi galabar halaka mana Eshaan. Kiga fa da ga wannan musiba sai wannan, ni wlhy gara ya sauka ya bar musu mulkin nan da dai mu rasa shi, dan ALLAH ki kirashi muji a wane hali yake, zuciyata ta kasa nutsuwa duk da Abu Harith ya sanar min bai zauna ba”.

         Cikin sake shiga tashin hankali Malikat Bushirat da ke sauke numfashi da ɗaɗɗaya idanunta a lumshe ta girgiza kanta, sai kuma ta buɗe idanun nata da ke jajur. Ita duk wannan surutun bashi take buƙata ba, yaronta take son gani, so take ta gansa da idanunta ta tabbatar da lafiyarsa ƙalau sannan koma miye da ke a ranta sai ta fitar. Dan wlhy a wannan gaɓar taci matuƙar alwashin in har wani abu ya sami ɗanta kamar wancan karon du da bai bar duniya ba azabar daya ɗan ɗana fansarta shine ran kowane shege. Duk kuma wanda yay yunƙurin shiga mata hanci koda Malikat Haseenat ce zata fyato ta. Ta shirya tsaf a wannan karon koda za'a babbakama DAULAR RUMAN gaba ɗaya wuta sai ta ƙwatoma ɗanta hakkinsa ga duk wani mai hannu a kan abinda ya faru bama Iffah kawai ba.........✍️

     

       _Tofa ran manya ya kai ƙololuwa a ɓaci🧐._

No comments

Powered by Blogger.