Daudar Gora Book 2 page 30
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (30)
..........“Ƙoƙarin kare kai bashi zai fidda kowanne mu ba, duk da bazai yiwu ace dukanmu anan ne muka aikata ɗin ba, sai dai dole duk ma wanda ya aikata a cikinmun yake dai. Shin wace irin rayuwa ce muke son ta cigaba da yaɗuwa a wannan zuri'ar tamu
ne bayan kasancewar mu jini ɗaya?. Shin mi muke nema wanda UBANGIJI baiyi mana shi ba? Mi muke buƙata da ga siffofin shugaba na gari da ALLAH bai azurta bawan ALLAHn nan da shi ba da a kullum muke son nuna bore da hukuncin ALLAH? Ni na rasa gane mi duk mai ƙoƙarin assasa fitine-finen nan ke buƙata ba ko san zuwa. Shin mulkin yake so ne? Ko kuwa rayuwar wannan bawan ALLAH da'a kullum alkairinsa ke zagaye da mu..” takaici ya saka hawaye ziraro masa. Handkherciff yasa ya share tare da sake dubansu ya cigaba da faɗin, “Shike nan babu mai hana koma waye yin yanda ya ke so, sai dai ya sani a duk randa yazo hanunmu wlhy ko shi waye a cikinmu sai yayi dana sani da nadamar kasancewarsa cikin zuri'ar mu. Sannan tarihi zai masa tanadin da bazai taɓa goge sunansa ba a matsayin azzalumi mai fuska biyu a cikin zuri'ar mu. Wannan faɗan ba nashi bane namu ne, dan mu nan da mu akeyi ba da shi ba, dan haka duk wanda ya shirya bismillah muma mun shirya”.A zahirance duk nuna goyon baya a kan maganarsa sukai, sai dai a ransu ji suke kamar su shaƙo wuyan Sayeed Tasadduq-Husain ɗin. Yasan da hakan, shiyyasa ko kallo babu wanda ya ishesa a cikinsu, ya kuma ci dubu sai ceto. Miran Arshaan da gaba ɗaya ya ke jin kamar ya danne Sayeed Tasadduq-Husain a wajen ya masa yankan rago ya taushi zuciyarsa da ƙyar, dan wannan wata dama ce a garesa, rashin ganin Miran Jasim a wajen yay masa da ɗi, dan haka ya miƙe cike da dakewa da tsan-tsar iya makirci shima ya fuskancesu ya zuba kausasan kalamai, da ga ƙarshe ya rufe da faɗin, “In ma tsoro da kunya sun hana duk ma wanda ya aikata ɗin zuwa nan batare da mun farga ba to na tabbata akwai mabiyansa da irinsa anan ɗin, sai su isar da saƙonmu na tabbatar da duk randa mutum yazo hanunmu sai ya yabama aya zaƙinta a wannan masarauta kamar yanda Sayeed Tasadduq-Husain ya faɗa”.
Kalamansa kam tabbas sun saka wasu fara hasaso abinda yake son dama ai hasashen, sai dai babu wanda ya furta a zahirance aka cigaba da tattaunawa.
Ya ɗauka tsahon lokaci da su a falon suna tattaunawar, dan suna fitowa da ga zaman ma masallaci suka zarce sallar la'asar. Bayan an idar ya koma sashensa. Bai nema Iffah ba yanzun kam. Dan yana buƙatar ɗan hutawa saboda yau zai ɗanyi fitar dare ta sirri zuwa cikin gari. Sai dai koda ya shiga ɗakin ma sai yaji baida buƙatar kwanciyar saboda ransa a matuƙar ɓace ya ke har yanzun. Tashi yay ya canja kayansa cikin wasu fararen wando da riga tas na kamfanin *Nike* da sukai masa matuƙar ƙyau duk da ya sane badan kwalliya ba. Takalma ya ɗaura a ƙafarsa baƙaƙe ya ɗauka p-cap a hannu ya fito cikin takun nan nasa mai tabbatar da shi ɗinne dai ko da ga nesa. Cikin sauri amintaccensa ya miƙe ƙansa rissine, ba sai yace masa ga abinda yake buƙata ba, kai tsaye ya fahimci inda suka dosa. Kafin ya ƙaraso gareshi yay saurin ɗaga waya yay kiran sarkin barga. Ana ɗagawa yay saurin bashi umarnin shirya dokin amana da kowa ya san in ba shi ba Shahan-shan ɗin baya hawan kowanne doki a gidan. Wayar ya katse dan dai-dai da isowar Tajwar Eshaan ɗin, ganin ya nufi elevator batare da ko kallon inda yake yayi ba shima ya zabura. Cikin sauri ya danna floor 1 bayan ƙofar ta maida kanta ta zuge.
Suna fitowa da ga lift ɗin ɓoyayyar hanyar da zata fiddasu batare da ko hadiman ƙasan sungansu ba ya nufa, amintaccensa biye da shi. A wani ƙaton fili suka fito, an gyara wajen da wani irin farin yashi mai matuƙar ɗaukar idon mai kallo da birgewa. Kasancewar ruwan saman da aka sha sai wajen ya sake bada wani yanayi mai matuƙar daɗi ga sassanyar iskar da bishiyoyin da aka ƙawata wajen na dabino na bayarwa. Da ga ɗan nesa da su Sarkin barga ke riƙe da ƙyaƙyƙyawan farin dokin da shi da kansa ya raɗa ma abinsa suna da ƙyautar ALLAH. Kamar yanda ɗabi'ar dokin take suna fitowa yay wata irin haniniya da girgiza kai kace ƙamshin Tajwar Eshaan ɗin yake ji ya shaida kasancewar sa a waje. Da wani irin gudun bajinta ya nufosu, yana isowa gabansa yay wata irin ƙwafutar ƙasa yay girgiza da haniniya, har gashin saman kansa zuwa wuya na wani tarwatsewa da haɗe kansa waje guda. A hankali Tajwar Eshaan ya lumshe idanunsa yana sakin sassanyan murmushi da mutane kan jima basu gani tare da shi ba sannan ya kai hannu ya shafi fuskar dokin yana masa magana ƙasa-ƙasa da ko Sarkin barga da amintaccen hadiminsa dake tsaye gefe kawuna a risine basa iya jinsa. Cikin wani irin salon da ke tabbatar da ƙwarewarsa a iya sarrafa dokin ya damƙi linzamin sa cikin action mai matuƙar ɗaukar hankali da bajinta ya ɗane saman sa. Cikin tabbatar da ƙwarewar da dokin ya samu a hanunsa yay wata irin haniniya da ƙwafutar ƙasa ya ɗiba hanya tamkar a filin polo. Rere suka fara ɗan gaske da sauran dokunan huɗu da aka sakakarma linzami batare da kowa a kansu ba. Duk wanda ya ga yanda yake sarrafa dokin basai an faɗaba ya san shi ɗin ƙwarren ɗan wasan polo ne kuma jarumin gaske. Dan cikin ƙanƙanin lokaci yay ma sauran dokunan da babu kowa ɗin fintinkau, har ya sake dawowa ya koma sannan su suka iso. Kaida gani kasan yana nishaɗi da wasan matuƙa. Sosai su sarkin barga ke murmushi da jinjina jarumta irin ta gwarzon Sarkin nasu. Ko'a cikin dubu shi ɗin na dabanne da kai tsaye za'a nuna a shaida. Dan suna da tabbacin da a lokacin yaƙi ne yazo babu abinda zai hana ya zama babban jarumin da tararsa a filin daga abin tsoro ne. Ya ɗauka tsahon lokaci yana wasan dokin har sai da yaji ya gamsu jininsa ya tashi fiye ma da yanda yake buƙata sannan yaja linzamin dokin ya dire bisa ƙasa cike da bajinta yana sauke numfashi ɗaya-ɗaya. Da sauri amintaccensa ya matsa garesa hannunsa ɗauke da ƙyaƙyƙyawan tray mai ɗauke da gorar ruwa da glass cup. Goran ruwan ya ɗauka batare da ya haɗa da cup ɗin ba, ya ɓalle murfin ya kai bakinsa. Yasha kusan fin rabi sannan ya juyo ya juye sauran akan fuskar dokin nasa yana ɗan murmushi. Haniniya dokin yayi mai nuni da isharar jin daɗin kasancewarsa da adalin ubangidan nasa. Shima sai ya kai hannu ya share masa ruwan yana murmushi. Ƙaramin towel Sarkin barga ya miƙo masa da sauri, bai musaba ya amsa ya goge hannunsa da wuyansa sannan ya kai shi ga fuskar dokin shima ya share masa ruwan da ƙyau. Yanda yake ma dokin da kansa dolene ka tabbatar akwai matuƙar shaƙuwa a tsakaninsu mai birgewa da ƙayatarwa. (Ko dabba ma ta san me bata kulawa da nuna ƙauna kenan☺️😘)
★★...... ★.... ★...
Karo na biyu kenan da ta sake dawowa ɗakin ta samesa yana kai kawo rai a ɓace. So take taji miye damuwarsa, sai dai tana matuƙar shakkar hakan. Dan mijin nasu wani irin bahagon mutum ne da sam baida daɗin zama. Su dake tare da shine kuma kawai suka san hakan. Amma ga al'ummar masarautar kowa yabonsa yake, shiyyasa a lokuta da yawa idan suka kai ƙararsa ga Shahan-shan tun ma zamanin Tajwar Haysam sai kiga ana ganin laifinsu na gajen haƙuri da rashin godiyar UBANGIJI.
Hayaƙin Shishar da ya bulbule ɗakin da shi ta ɗan saka hannu ta kore, dan shi kansa ma da ƙyar take iya hangosa. Ƙundunbalar shiga tayi dan so take ta sanar masa kiran da aka aiko ana masa da ga Shahan-shan, amma tsoro takeji ganin yanayin da yake ciki. Muryarta na ɗan rawa ta risina da ga tsakkiyar ɗakin tana shaƙar hayaƙin madadin iska da ƙyar. “Barka da wannan lokaci Abu Husam”.
Cak ya tsaya da ga zuƙar Shishar, yay wani masifar bulbulo hayaƙin bakinsa da ya sake turniƙe ɗakin zuciyarsa na wani irin kumburowa da takaicin wace ƴar ƙunar baƙin waken ce a matan nasa data manta da dokarsa. Sai da hayaƙin ya lafa sannan ya iya ganinta da ƙyau, e ai ya sani sai ita ɗin, dan babu mai yawan shiga masa hanci kamarta. Tsawa ya daka mata yana miƙewa a fusace. “Buhaysah! Ban ce bana buƙatar ganin wani a sashe na ba da ga nan har sai idan nine na nema mutum?!!”.
A ɗan firgice ta zabura baya, sai kuma ta shiga girgiza masa kai jikinta na ƙyarma. “Hakane, amma Ka gafarce ni Abu Husam, wlhy bada son raina na karya maka doka ba. Saƙone da ga Shahan-shan ana buƙatar ganinka. Naga kada kai laifi ne shiyyas....”
“Tasss!!”
Kakejin saukar wani lafiyayyen mari akan ƙyaƙyƙyawar fuskar ta. Dan mace ce zankaɗeɗiyar gaske dirarriya. Duk da shekaru sunja gareta ƙyawunta a bayyane yake gata ƴar gayu. Ba yau ta saba shan mari a wajensa ba, amma sai na yau ɗin yay mata ciwo fiye da ko yaushe. A hankali ta ɗaga jajayen idanunta ta kallesa, fuskarta na nuna alamar ɓacin rai, abune kuma da bai taɓa gani da ga gareta ba.
“Abu Husam minene laifina anan da har na cancanci mari dan ALLAH?”..
“Ƙari kike buƙata kenan?”. Ya faɗa a zafafe da sake yunƙurowa zai sauke mata wani duk da jin wani shakkarta a yau ɗin da yaji ta shigesa.. Abin mamaki da firgici ga Miran Jasim, sai ga Buhaysah kam ta riƙe hannunsa caraf.........✍️
Leave a Comment