Daudar Gora Book 2 page 26

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (26)

.........“Idan nace banji ciwo akan kuskurenki ba ƙarya zan miki. Amma tunda kin fahimta da kanki shike nan komai ya wuce. Akan abinda ya faru kuwa bazan hanaki jin zafi ba, dan kinyi abinda kowacce uwa zata iya yi har ni kai na. Sai dai kuma ni bazanyi haka kamar yanda ke ki kayi ɗin ba, saboda wasu dalilai nawa, wanda bai zama lallai ke a

gareki su zama dalilan ba. Amma zan baku shawara matsayina na uwa. K shugaba ce, sannan kuma uwa. Shi shugaba an sanshi da haƙuri ne, kauda kai, jarumta, haɗiyewa komai ɗaci, shugaba kowa nashi ne, baya kuma taɓa kallon gudan jininsa kawai a matsayin ɗa sai ya haɗa da wanda ma bai haifa ba. Eh munji yarinyar tayi kuskure ƙwarai da gaske, kuskure kuma mafi girma da bai kamata ace an yafe mata cikin sauki ko sassauta mata ba. Sai dai a matsayinmu na wanda suka san ahalin da suke ciki ya kamata muyi wani nazari, sannan mu haɗiye dukkan zafin da muke ji koda ace yana ƙonamu. Domin ta hanyar wannan haɗiyewar ne kawai zamu iya sanin ainahin gaskiya. Ga duk mai hankali idan zai nutsu a shekarun yarinyar nan masu ƙaranci kai tsaye zai zamto aikin data aikata ba nata bane, anyi amfani da ita ne kawai domin samun cikar buri. Iffah yarinya ce da bata iya ɓoye abu, sannan akwai ƙuruciya a cikin al'amurran ta. Idan har ainahin mai wancan aiken zaiyi amfani da duk wannan yanayin nata, mu mezai hana bazamuyi amfani da fahimtar ta ba wajen gano koma wanene ta cikin sauƙi. Bushirat sam ban san lokacin da kika lalace haka ba, sai dai na fahimci a yanzu kina samun wasu ƴan kazagine da ke amfani da damuwarki wajen ingizaki. Bazance ki rabu da su ba, sai dai zan baki shawarar nutsuwar fahimtar manufofin su akan tunzurakin. Lokaci yayi da zaki farka, inba haka ba zakiyi nadama a gaɓar da nadamar bazata amfanar da ke komai ba face dana sani”

     Ba ƙaramin shiga jikinta kalaman Malikat Haseenat ɗin sukai ba. Sun ratsata matuƙa, ta kuma hankaltu da abinda take son nusasheta cikin hikima. Cike da girmamawa ta jinjina kanta, muryarta a raunane ta ce, “Nagode Mammah, nagode da kika farkar dani wannan nannauyan barcin da ya ɗaukeni. Kiyi haƙuri da duk abubuwan da suka faru, Insha ALLAHU kuma zaki sameni mai canjawa”.

     “ALLAH ya tabbatar da hakan”.

Malikat Haseenat ta faɗa. A tare Daneen Ammarah da Malikat Bushirat suka amsa da Amin. Da haka wajen yay ɗan shiru, sai zuwa can kuma Malikat Bushirat ta sake nisawa. “Mammah sai kuma abu na biyu, duk da fadakarwarki ta farko ni dai ta janye min komai dake raina”.

         “Ki faɗi ko miye dan a yanzu mu duk wata hanyar mafita abin nemanmu ce”.

     Kai Malikat Bushirat ta jinjina, kafin ta cigaba da magana kanta a ƙasa. “Dama Jasrah ce ɗazun ta sameni akan batun......” tsaf ta zayyane mata komai a to z batare data rage ba. Hatta da zuwan Tajwar Eshaan ɗin na bazata da ƙin cewa komai da yay akan zancen. Ta ɗaura da faɗin, “Tun kafin tazo da wannan zancen ni dama inada burin hakan, sai dai bana nufin tirsasa masa. Amma dai yanzu ina son naji ta bakinki kema”.

      Wani ɗan murmushin manyance Malikat Haseenat tayi idanunta akan Malikat Bushirat ɗin. Sai kuma ta kauda kanta kamar bazatace komai ba. Kusan minti ɗaya sannan ta nisa da sake kallonta. “Hakan tunani ne mai ƙyau, sai dai ina son ku tuna abinda ya faru last ɗin nan. Mun sake rasa ɗaya a cikin matansa, ɗayar kuma saboda firgita ta tsinta kanta a halin ciwo da dole sai da muka maidata ga iyayenta. Yarinyar nan dai Iffah da aketa ɗauki ba daɗi a kanta itace ta gagara, gagarar tata kuma na mana ishara da tabbacin zarginmu, dan yarinyar tana zagaye da kariyar UBANGIJI ne, da kuma kwananta bai ƙare ba. Shiyyasa aketa bin wasu hanyoyi amma duk da haka ba'aci nasara ba. Idan munada wayo a wannan gaɓar hakan na nufin ita ɗin ba abinda zamu banzatar bace, Insha ALLAHU itace wadda ta dace da zama Zawjata-almilk da taɓata ga maƙiyanmu wani babban yaƙine da idan suka ce zasu ci gaba to kwanakinsun nan 99 da ake faɗa na ɓarawo na gab da cika”.

      A tare Daneen Ammarah da Malikat Bushirat suka kalleta, itako ta gyaɗa musu kai cike da tabbatarwa...


      ★... 


Kallon juna suma hadiman dake lafe cikin fulawoyin garden ɗin sukai dai-dai da na su Daneen Ammarah. Sai kuma suka miƙe cikin sanɗar da baza'a gansu ba zasu bar wajen. Daneen Ammarah ce ta ɗan shiga waige-waige, dan itakam ALLAH ya bata ƙarfin ji. Jin tabbas kamar fa motsin mutum ya sata miƙewa da ɗan hanzari, inda take jin motsin ta nufa. Da wani irin rawar jiki suka koma bayan wasu flowers masu duhu sosai suka lafe. Ganin babu alamar abinda take zargin ta baro wajen, sai dai zuciyarta na cigaba da tabbatar mata akwai wani bayansu a cikin garden ɗin.

         “Lafiya?”.

     Malikat Haseenat ta tambaya lokacin da Daneen Ammarah ke dawowa. Cikin nuna ƴar damuwa ta ce, “Wlhy Mammah kamar naji motsi ne. Sai dai kuma banga komai ba”.

           Magana Malikat Haseenat tai kamar zatayi, sai kuma ta haɗiye abunta. Sai ma duban Malikat Bushirat data miƙe tai da mata alamar ta zauna. Babu musu ta koma ta zauna badan taso ba. Dan itama dai zuciyarta na raya mata dole motsin da Daneen Ammarah ta ji ya kasance wani abu......


     ★★.. ZAWJATA-ALMILK ★..... 


      Harta nufi hanyar komawa ɗaki ta canja shawara, da baya ta dawo, hanyar da suka taɓa biyowa da shi randa ta samesa a can sama tare da Miran Arshaan ta nufa, haka kawai take son sake komawa wajen. Tana gab da isa ta ɗan tsaya a ƙofar da tun wancan karon taso sanin ita kuma ta miye, babu wani ko ɗar ta nufi ƙofar ta buɗe, sai taji ta buɗe babu gardama. Ƙaton Gym ne mai ɗauke da nau'i-nau'in machines na motsa jiki masu ƙayatarwa. “Uhyim” ta faɗa tana ɗan jinjina kanta da taɓe baki hannayenta duk biyu a ƙugu. Jitai har ma taji sha'awan motsa jikin, dan haka ta juya ta fita tana murmushi da faɗin, “Zan dawo gareku kuma”.

         Hadiman nan dai na wancan lokacin ta sake tararwa yau ma, cikin sauri duk suka zube suna gaisheta, yayinda na'ura ke yayata sunanta. Murmushi ta ɗan musu kawai ta wuce abinta, a ranta kam gulmar Tajwar Eshaan take dan tasan iyayinsa ne yasa aka saka wannan na'uran da in har zaka ƙetare ƙofan wajen sai ta sanar da ko kai waye ko kuma tsoro ne oho masa. 

      “Ya rabba”. Ta faɗa a hankali tana mai lumshe idanu jin yanda iskar wajen ta wani buso mata. Sai kuma ta buɗe idanun ta kaisu ga sararin samaniya da ke ta faman haɗa giza-gizai alamar haɗuwar hadari. Da alama ruwa zai iya zubowa a koda yaushe insha ALLAHU. Iffah na matuƙar son yanayin damuna, dan koba komai tayi tsalle-tsallenta a ruwa ai. Cigaba da takawa tai murmushi na ƙara yalwatuwa a fuskarta har fararen haƙoranta na bayyana. Ƙyawawan idanunta na cigaba da bin wajen da kallo daki-daki cike da shauƙi. Inda ya tsaya ranar shi da Miran Arshaan ta ƙarasa, “Woow!!” ta faɗa tana wani irin ware idanunta ganin yanda take iya ganin masarautar baki ɗaya da ga wajen. Harma wajen masarautar ana hangowa da kaikawon motsoci dana mutane ɗai-ɗai. Ai bata taɓa tunanin haka wajen yake ba, da tuni ta maidashi wajen zamanta. Ɗan yayyafi aka fara a hankali, cike da nishaɗi ta rungume hannayenta tana sakin ƙayataccen murmushin dake sake bayyana ƙyawun da ALLAH ya azurtata da shi. Kamar da wasa ruwan ya fara ƙarfi, amma bata da alamar barin wajen kamar ma farin cikinta ƙaruwa yake, dan sam murmushi yaƙi barin face ɗinta, har ta kai ta fara ware hannayenta tana ɗan juyawa idanunta a lumshe tamkar mai hajijiya. 

       Cak ta ɗauke wuta jin ta jingina da abu a yayin da take jujjuyawarta, sai kuma sassanyan ƙamshin turarensa ya shiga rige-rigen faɗawa hancinta. Sauri-sauri ta buɗe idanun tana juyowa, ganin shi ɗinne dai tsaye cikin sabuwar shiga yasa tayi kamar wadda ta ɗan firgita. Sai kuma ta haɗiye sauran murmushin fuskarta tana saukar da idanunta ƙasa saboda yanda ya tsareta da nasa idanun.

          “Baƙya tausayin kanki ko?”.

     Ya faɗa can ƙasan maƙoshi cikin sanyi sauti da ko ita ɗin ma dan suna gab da juna ne tajisa. Lips ɗinta ta ɗan shiga motsawa kamar zatai magana sai kuma ta kasa, ƙafafunta ta ɗaga da nufin barin wajen. Taku biyu ta tsaya cak tana mai rumtse idanunta jin ya riƙo hanunta. Kallon hannun nasa fari sol da ke riƙe da nata tai ta gefen ido, ga wasu dogayen farata farare tas-tas babu ɗigon datti tattare da su sai ma sheƙi da sukeyi, jitai tsigar jiki ta na wani irin tashi, a ɗan shagwaɓe ta ce, “Zanje ciki ne”.

        Maimakon ya saketa sai ya maidota a hankali ta dawo gabansa. Kallonta ya ke da ga sama har ƙasa, kallo irin na ƙurilla. Ji tai gaba ɗaya tana neman daburcewa, dan sam bata son kallo, balle ma irin nasa mai tada tsigar jiki. A hankali ya lumshe nasa yana ƙoƙarin danne murmushin da ke taso masa ya matsota ta koma jikinsa, babu yanda ta iya face lumshe nata idanun itama da ɗaura hannayenta kan ƙarfen wajen tai luf a jikin nasa tana shaƙar sassanyan ƙamshin sa da ita dai a rayuwarta shi kaɗai ta sani da shi. Nashi hannayen shima yasa a ƙarfen ya ɗaura kansa a kafaɗarta har lokacin idanunsa a lumshe yayyafin na sauka a kansu kaɗan-kaɗan, sai ya zam tana a tsakkiyarsa shi da ƙarfen..........✍️


No comments

Powered by Blogger.