Daudar Gora Book 2 page 25

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (25)

.......Kamar ko yaushe tana kishingiɗe amintacciyar hadimarta Jazaa na da ga gefenta tana yanka mata tupa. Magana take mata a hankali itako idanunta lumshe. Jazaa cikakkiyar ƴar leƙen asirinta ce a cikin gidan. Dan duk wani hadimi dake mata aiki Jazaa ya sani ba ita ba. Ita a karan kanta Jazaar ta

ɗauka tsahon shekaru uku a sanda ta fara mata aiki bata isa faɗin ainahin wacece ita ba a cikin gidan. Dan takanzo mata ne da fuskoki daban-daban kafin ta bayyana mata ainahin fuskarta. Duk da kasancewar ta ba'a cikin hadiman gidan ba, kai ita bama a masarautar take ba UWA ce ta kawo mata ita ta razana a sanda ta san wacece itan. Amma har yau da suka kwashe tsahon shekaru tare bata taɓa iya ɗaga baki ta faɗama wani wacece ta-ƙurya ba, ta dai so gwada hakan sau ɗaya taci wahala dan daina ji da magana tayi baki ɗaya ta koma kurma. Sai da tai kusan shekara a haka sannan ji da maganarta ya dawo bayan tasha doguwar barazana. Duk wanda zai shaida makirci da tsantsar rashin imani irin na ta-ƙurya to lallai itace Jazaa. Kuma a hakan ma ba komai ta sani ba itama sai abinda taso ta sani kawai.

         “Bincike na ƙara nisa kan hadimi Israr Uwargijiya ta. Dan a yanzu haka ma naga baƙuwar fuska a cikin rukunin hadiman da Israr ke aiki. Inaji a jikina kuma ɗan leƙen asirine aka turo daga jami'an gidan nan”.

     Idanunta ta buɗe a hankali kan Jazaa. Kallo take mata mai kaifi da ya sakata sake gurfane gabanta kamar mai neman gafara. Cikin isa da kaushin harshe ta furta, “Ya jima yana mana aiki, kuma kowanne an samu nasara. Sai dai a gareni sabo da kaza bazai baya hanani yankata. Zan yanke masa hukuncin da ya dace da shi, dan dama na sanar masa in har aka samu matsala hukuncin zai zama dai-dai da irin na kowa. Bazan taɓa barin wani gaɓa da zai zame min matsala ba”.

        Yawu masu kauri Jazaa ta haɗiye. Zuciyarta sai bugu take da sauri-sauri. In dai har Israr bazai tsira da ga mummunan hukuncin uwargijiyar su ba kenan itama wataran idan tai kuskure zata iya fuskantar kowane irin hukunci. Ya ALLAH wannan wace irin rayuwace ta faɗo ciki mai ban tsoro. Wai shin mi matar nan take nema a duniya bayan wanda ALLAH ya azurtata da shi tari-tari da ita kanta bata san adadinsa ba?. Tsawar data ratsa kunenta ce ta sata zabura. Mikewa tai jikinta na rawa. “A gafarceni uwargijiyata”. Ta faɗa illahirin jikinta na tsuma. Sai kuma ta fice da sauri ta ɓarauniyar hanyar da ta ke shigowa da fita in har ganawa da uwargijiyar tata ya kama.....


         Ba ƙaramin tashin hankali wannan saƙo na Jazaa yazo mata da shi ba. Gaba ɗaya sai duk wani ɗan farin ciki data tashi da shi yau ta nemesa ta rasa. Tabbas dole ne hadimi Israr ya bar duniya a yau. Dan duk rintsi ita bata barin ƙurar da zata zame mata bi baya a bayanta koda kuwa ta wacece. Israr hadiminta ne na amana, ya matuƙar sanin abubuwa a kanta da in har aka kamashi duk da bai san ainahinta ba ayyukanta da yawa zasu kwaɓe. Wani irin lumshe idanu tai da mahaukacin zuƙar iska ta fesar, kafin tabar inda taken cikin sassarfa zuwa cikin bedroom ɗin ta, dan a yau dole ne tayi aikin nan da kanta.


      ★Duk yanda Jazaa taso haɗiye mummunan furucin Uwargijiyar tasu kan Israr ta kasa hakan, gaba ɗaya ta kasa samun nutsuwa. Ba yau ta saba jagorantar ai ma Uwargijiyar su aiki ba, idan aka samu kuskure kuma a sata da hanunnta ta shayar da mutum madarar mutuwa. Amma a wannan karon sai take ji bazata iya ba. Badan komai ba sai dan sanin irin bautar da Israr yay ga ta-ƙurya kamar yanda itama tayi koma take kanyi, duk haɗarin aiki aka sakashi sai ya zartar da shi koda zai cutu, dan kawai an samu akasi a wannan karon, akasin ma ba daga garesa bane tunda ya gudanar da umarnin data bashi sai a halakar da shi. Kai itakam zata samesa ta sanar da shi gaskiya (Ki kiyayi kanki) wata zuciya ta gargaɗe ta da sauri, tare da tuna mata wacece Ta-ƙurya idan ta manta...


  Ni dai nace, “Hummm”



    ★★... MALIKAT BUSHIRAT ★....


       Kamar ko yaushe kishingiɗe take a katafaren falon nata da ya jiƙu matuƙa da nau'i-nau'in kayan more rayuwa. Yayinda hadimai uku ne ka ɗai ke tare da ita dan yau tace bata son hayaniya duk da dama basu isa yin hayaniyar ba gareta. A kallo ɗaya zaka iya fuskantar tana cikin damuwa, duk da ita ɗin ba wai mace bace mai fara'a tun fil azal. Ba komai ke mata kaikawo a rai ba sai tattaunawarsu ta ɗazun da Jasrah. Tabbas tana buƙatar yaronta ya ƙara aure, kodan ya samu nutsuwa irin ta kowane namiji irinsa. Sannan tana son yakice Iffah da ga jikinsa, dan tunda har ta iya gwada kashe mata yaro wataran zata iya cin nasara ai. Ba'a ƙaramin damuwa take da zaman yarinyar nan tare da shi ba gudun karta maimaita abinda ta fara, kallafa babu tsoro ko shakka tattare da ita take sanar da cewar ita ta bashi madarar ya sha, ta rasa gane wai Iffah mutum ce ko aljana. Ita kama bata taɓa cin karo da yarinya mai shekarunta da babu tsoro ko shakka tattare da ita ba. Taya ma zuciyarta zata iya nutsuwar barin Iffah tare da tilon ɗanta. Ita kam ta rasa ma wane irin kalar tunani ya kamata tayi. Gaskiya tana buƙatar zama da Malikat Haseenat a wannan karon, dan ita kam dai zuciyarta ta fara sakkowa da ga zafin da take ji nata. Tana buƙatar neman shawara ma akan abinda Jasrah tazo da shi, dan shi kansa Tajwar Eshaan ɗin bai ce komai ba akan batun ƙara auren da sukai masan ɗazun, harma Jasrah ta nuna jin haushin hakan duk da dai bata fito tace komai ba.....


    

        ★... MALIKAT HASEENAT ★...


    Tana zaune a keɓantaccen garden ɗinta tana tsakurar farfesun kayan ciki da ta saka hadima Banou tai mata saboda rashin daɗin baki da take fama da shi na mura da kwana biyu ke damunta ɗaya da ga cikin hadimanta tazo da saƙon neman iso da ga Malikat Bushirat. Ɗan jimmm tayi na mamaki, dan ko rabon da ko gaisheta Malikat Bushirat tazo yi a ƙalla ana neman wata kusan uku kenan, dan tun kafin faruwar rikicin da har yanzu ya gagara ƙarewa a masarautar ne. Murmushin ta ɗan saki mai sanyi da jinjina kanta cikin halin dattako. A ƙasaitance ta jinjinama hadimar kai alamar bada dama. Cikin abinda bai fi mintuna biyar ba sai ga Malikat Bushirat da Daneen Ammarah tare suna tunkaro ta. Kallo ɗaya ta musu ta ɗauke kanta, har ga ALLAH tana matuƙar ƙaunar Malikat Bushirat, tana mata so irin wanda takema ƴaƴan cikinta, bawai dan ta haifa mata jika bane, kawai dai yanda ta ɗauketa tamkar uwa yasa itama ta ke mata kallon ɗiya. Dan duk da kasancewar Malikat Ashwaq matsayin jininta Malikat Bushirat ta fiye mata ita sau dubu....

         “Barka da hutawa Mamma”.

    Daneen Ammarah ta faɗa tana kaiwa zaune kusa da ita. Kai kawai malikat Haseenat ta jinjina mata, idanunta akan Malikat Bushirat da ta kasa zama ta kasa magana kanta a risine. Murmushi tayi mai ƙayatarwa ta kauda kanta batare da tace komai ba ta maida ga Hadima Banou dake tsaye da ga gefe kanta a rissine tana bin Malikat Bushirat da kallo, dan ita kaɗai tasan wane kalar abun daɗi take hangowa.

     “Bamu waje”.

   Ta faɗa a hankali cike da ƙasaitar ta. Da sauri hadima Banou ta amsata tana wucewar yawu taf da bakinta na kwaɗayi. Kwana biyu kenan tana neman mai ƙararren kwana bata dace ba, tayi alƙawarin sai ta maida asarar kwanakin da Iffah ta satayi na hanata laƙume kowa. Ganin Banou ta ɓace Malikat Haseenat ta maida kanta ga farfesunta batare data sake duban Daneen Ammarah da Malikat Bushirat ɗin ba. Hakan da tai na nufin tana fushi ɗin dai da gaske. 

       Duk sai Malikat Bushirat kejin ta sake shiga ruɗani, duk da tasan Mammah ɗin dama zata iya yin fushin saboda mace ce da bata ɗaukar wargi, sai dai batai tsamanin kamar haka ba. A hankali ta kai zaune kan lallausan carpet ɗin da aka shimfiɗa saman korayen ciyayin wajen dake kwance luf-luf ko'a filin ƙwallon ƙafa albarka. Ƙafafunta ta tanƙwashe tana mai fuskantar ta da ƙyau, kanta a ƙasa ta riƙe kunnuwanta. “Nasan ni mai laifice ƙwarai da gaske Mammah, mai laifin data cancanci hukunci ga mahaifiya, amma ina mai neman afuwar bazan sake ba. Nima ku fahimceni ina kan gaskiya ta ne. Duk wata uwa irina zata yi abinda yafi wanda nayi a yayin da ta fahimci kota kama mai shirin halaka mata ɗa. Har yanzu inajin zafi, zafi matuƙa akan abinda ya faru, sai dai gani nazo gareki Mammah, dan ALLAH ki fahimtar dani abinda kike son na fahimta game da wannan al'amarin. Dan maybe ni nawa tunanin a wannan gaɓar ya tsuke ne waje ɗaya ta inda bana hangen komai sai laifin yarinyar nan kawai saboda ta taɓa abinda nafi so fiye da komai a wannan duniyar, Mammah wlhy zan iya fansar da numfashina akan Eshaan iya gaskiyata nake gaya miki”.

          Idanu kawai Malikat Haseenat ta zuba mata. Sai dai a cikin ranta tana ƙara jinjina kalaman ƙarshe na Malikat Bushirat ɗin. Eh tabbas itama tana son ƴaƴanta, sai dai ba makahon so ba irin wannan, a ganinta a duk lokacin da uwa zata iyama ɗanta irin wannan makahon son to bazata taɓa iya son wanin ɗanta ba kenan, bazata taɓa iya maida maraya nata ba, bazata taɓa iya dai-daita ƴaƴanta da wasu ƴaƴan masu kiranta da uwa ba kamar yanda ita a yanzu take kallonsu duk da matsayin matan ɗanta da suke. Amma sai kawai ta shanye batace komai ba tama cigaba da shan farfesunta.

        Daneen Ammarah da batace komai ba tun ɗazun ta ɗan ɗago tana kallon mahaifiyar tasu. Ta santa, ta san in tai fushi tana da wahalar tarowa, duk da kuma batace komai akam duk abinda Malikat Bushirat ɗin tayi a kwanakin nan ba ta san ranta ya ɓaci. murya ta sanyaya cike da lallashi ta ce, “Mammah kiyi haƙuri, insha ALLAH a yanzu mu masu biyayya ne ga dukkan umarninki. Ba zaki samemu a masu saɓawaba kuma”.

       Nan ma shiru kamar bazata ce komai ba, sai kuma ta ture bowl ɗin tana jan ajiyar zuciya, a nutse ta ja tissue ta goge bakinta kafin ta dubi Malikat Bushirat da kanta ke risine ita dai, dan a gaban uwa take nata mulkin dole ya zam mai risinawa........✍️


      _(🥱gskiya itama tsohuwar nan akwai hegen mulki🏃)_

No comments

Powered by Blogger.