Daudar Gora Book 2 page 23

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (23)

.......Kansa dake a kafaɗarta ya ɗago a hankali jin yanda take maganar a serious, sai dai baice komai ba. Itama batare data kallesa ba ta cigaba da faɗin, “A nawa ra'ayin ka rabu da yarinyar nan, sai dai bazan tirsasaka kan hakan ba zan jira har lokacin da za'a yanke mata hukunci bisa abinda ta aikata. Amma kamar yanda Jasrah ta faɗa ya kamata ka ƙara aure. Ina son ka samu farin ciki kaima kamar kowane namiji mai irin shekarunka.

Ina son naga zuri'arka Eshaan. Na kuma shirya fito-na-fito da duk mai son daƙile waɗan nan zaren farin cikin namu ta hanyar kashe yaran da basu ji ba basu gani ba dan kawai kasancewarsu matanka. Nima a wannan karon na shirya, na shirya tarar kowa Eshaan...”

    Kuka mai tsuma zuciya ya sarƙe ta. Har cikin ransa yake jin kukan nata, sai dai babu alamar zaice wani abu. Jasrah da itama ke hawayen ta miƙe a hankali zuwa gabansa, zama tai ta kamo hanunsa cikin nata cike da kulawa ta kira sunansa. Ɗagowa yay a hankali ya zuba mata idanunsa da baka isa gane yanayin da yake ciki ba koda a cikinsu. Hawayen da ke cigaba da zubo mata ta share tana ɗan kauda idanunta zuwa ƙasa, dan kaifin nasa sun mata yawa. “Kayi haƙuri ka fahimcemu Abni, muna tsananin jin zafin abubuwan da ke faruwa da gaba ɗaya sun ta'allaka da kai ne matsayinka na shugaba sama da kowa na ƙasar nan. Lokaci yayi da zamu tashi yin fito na fito da kowa a wannan gaɓar. Ba zai yiwu mu cigaba da zuba ido ba kuma. Kafin yau mun tattara hope ɗin mu gaba ɗaya kan yarinyar nan, amma daga ƙarshe itama tai shirin halaka ka ma. Shiyyasa nai tunanin ya kamata a nema maka wata matar dan nasan kai dai baka da wannan lokacin, mu kuma Insha ALLAHU zamuyi duk shirin da ya dace don ganin mun kamo bakin zaren. Fatanmu mu dai kawai amincewar ka, dan wannan al'amarin baya buƙatar cigaba da zuba idanu kuma”.

        Uffan bashi da alamar cewa, bai kuma canja da ga kallon da yake musu ba a zahiri. Suma sai duk sukai shiru, dan sun san halinsa sarai....


      ★★....


      Bayan barowarsa daga sashen Malikat Bushirat ƙayataccen Gym ɗinsa mai ɗauke da nau'ikan machines na zamani ya nufa. Tuni hadimai masu tsaron wajen suka zube kan gwiyawunsu suna miƙa gaisuwa. Idanunsa kawai ya lumshe yay shigewarsa batare da yako kallesu ba. Da alama dai yau ƴan mulki ne bisa kai da miskilancin, ko kuwa maganar da yay da su Ammien tasa ne ke tsikarar masa rai oho dai. Sosai Gym ɗin ya ƙayatu ga mai kallo, dan hatta kaya motsa jikin an musu wadrube ne na musamman gasu nan iri-iri. Tattausar jallabiyar jikinsa ya cire ya ajiye, sannan ya fiddo set ɗaya na kayan ya ɗauka dogon wandon kawai ya saka. Sosai mutum ne buɗaɗɗe da baka gane hakan kai tsaye idan baya cikin riga. Cikin zafi-zafin da ke nuna kamar yana cikin fushi ya fara sarrafa machine ɗin gudun idanunsa a rufe ruf. Ya kwashe tsawon lokaci yanayi dan sai da yay sharkaf da zufa kafin ya kashe ya koma wajen ɗaga ƙananan ƙarfe irin na riƙewa a hannun nan ko kana daga zaune zaka ɗaga, duk da dai a zahiri kallon kitse akema rogo suna da matuƙar nauyi. Nan ma kusan mintuna goma sha biyar ya ajiye ya koma ɗaga ainahin ƙarfe daga kwance rigingine. Haka ya dinga caccanjawa har ya shafe tsahon awa biyu da wasu mintuna a ciki. Kafin yaja rigar wandon ya saka tare da ɗaukar goran ruwa ya kwankwaɗa yana sauke numfashi, dan shi ɗaya ke zuwa nan kawai bayan hadiman dake tsaren wajen. Ko amintaccen hadiminsa baya zuwa da shi.

        Kamar yanda aka saba ya samu shayinsa na ƙa'ida a ɗakin da ya kwana, dan masu aikin girka abincinsa sun cigaba da aikinsu tare da amintacen hadiminsa. Zaman shan shayin yay yana mai shaƙar daddaɗan kamshin da ɗakin keyi na gyaran da ya sha harya kammala. Da ga haka ya nufi bayi tsaftace jikinsa. Ya kwashe lokaci mai tsayi anan ma kafin ya fito ya shige inda kayansa suke domin shiryawa.


       Masha ALLAH na ambata lokacin da yake fitowa cikin wata irin shiga ta alfarma. Ga wani ni'imtaccen ƙamshi na musamman da ya sake gauraye ɗakin cikin ƙanƙanin lokaci. Dubansa ya kai ga agogon ɗakin yana ɗan ɓata fuska. Yana da buƙatar zuwa ya duba yaya ta kwana. Ga shi kuma ya makara, dan yanada shari'ar da zai gudanar a fada yau. Batare da ya yanke hukuncin abinda ya dace yay ba ya fito cike da takun nan nasa na izza da ƙasaita tamkar mai tafiya a saman iska tsabar yanda yake wani ɗaga ƙafafun da sauke su a nutse. Fuskar nan tsam babu alamar yama san minene yaran murmushi. Har ya nufi hanyar da zata sada shi kai tsaye da falo ya ɗan dakata, gajeren tsaki ya ja da juyowa sannu a hankali ya doshi ɗakin da Iffah ta kwana.

        Ƙamshinsa da sautin takun sawayensa da ke alamta isowarsa waje ya sata ɗan ɗago idanunta ta zubama ƙofar, sai kuma ta kauda da sauri ta cigaba da tsamar dabinon da aka zuba cikin zuma a wani ɗan farin bowl da ke a cinyarta. Kamar yanda yay sallamarsa ciki-ciki haka itama ta amsa masa can ƙasan maƙoshi batare da ta motsa da ga yanda take ba har ya iso tsakkiyar ɗakin.

    “Barka da safiya”.

Ta faɗa kanta tsaye batare da ta ɗago ta kallesa ba, duk da kuwa tana matuƙar buƙatar hakan amma ta kwaɓi kanta. Maimakon amsa gaisuwar da tai masa sai ya jeho mata tambaya a bazata yana wani shanye idanunsa da ke binta da kallon ƙurilla.

          “Kina jin wani ciwon ne a yanzu?”.

     Idanunta ta ɗago sannu a hankali ta zubasu a kansa karo na farko. Gabanta yay wata irin mummunar faɗuwa ganin exactly kayan da tai mafarki da shi dai sune a jikinsa daren jiya da asubahin yau ne dai abin kamar wani almara. Sai dai kwarjinsa da wata barazanar cikar haiba ta cika mata idanun. Babu shiri ta maida nata ta rissinar zuciyarta na wani irin bugawa da sauri-sauri. Amma a zahiri ta wani sake tsuke fuskar ne kamar yanda tashi ke'a tsuke. Kanta ta girgiza masa maimakon amsa masa da baki.

     Sosai fitinar yarinyar nan ke bashi mamaki, a fuska bazaka taɓa tunanin halayyarta ba, dan tanada suffar mutane masu sanyin hali da rashin son yawan magana ma, sai dai inta buɗe baki ko kanari albarka ya kada ita. Rigimarta ta musamman ce sama da duk ta wani rigimamme da ya sani a tsayin rayuwarsa. Lips ɗinsa ya ɗan laɓe cike da sake tsuke fuska magana can ƙasan maƙoshi a fisge ya furta, “Akwai phone a side drawer, zaki iya magana da Mammy game da abubuwan buƙatarki, idan kuma zaki online shopping ne da kanki fine. Da akwai card tare da ita” ya ƙare maganar yana ɗan matsawa ga table ɗin dake ɗauke da takardun da bata san na minene ba ya ɗauka pen. Ɗan rubutu yay a takarda ya tako har gabanta ya ajiye batare da ya sake cewa komai ba ya juya zai bar ɗakin.

      “Jazakallahu khairan”.

    Ta faɗa a hankali, lumshe idanu yay batare da yace komai ba ya cigaba da tafiyarsa. Kamar wadda aka tsikara ta miƙe zumbur. Kaɗan ya rage tai tuntuɓe da lallausan carpet ɗin gaban gadon ALLAH dai ya bata sa'ar tsallakewa ta cimmasa. Yana ƙoƙarin ɗaura hannunsa kan handle ɗin ƙofar sai ganinta yay a gabansa kamar wata aljana. Mar-mar ta ɗan yi da idanunta tana motsa pink lips ɗinta a marairaice. “Indai fita ta wuce iya nan sashenka ka haƙura kar kayi Pleaseee”.

       Idanunsa ya tsura mata da wani irin kallo da ta kasa bama fassara, dole ta risinar da nata tana ɗan wasa da bazar veil ɗin abayar jikinta da tai mata matuƙar ƙyau kasancewar blue black. Itama dai tashi tai kawai ta ganta bata san daga ina ba, amma tasan dai shine ya ajiye kamar yanda ya ajiye mata jiya. Idanun ya sauke a hankali kan hanun nata fari tas da babu wani datti a ƙunbunan suma. Kamar bazai ce komai ba sai kuma ya sake maida idanunsa kan fuskarta a fisge ya furta, “Akan wane dalili?”.

      Baki ta ɗan turo kaɗan, ta ce, “Kawai”.

          “Kawai?”.

      Ya maimaita a sigar tambaya da wata irin muryar jinjina wautar ta. Kallonta ya cigaba da yi cike da nazari.. Tsintar kanta tai da jin ƙafafunta na rawa, dan idanunsa kaifafa da ya tsareta da su ji take suna sagar da ɗan sauran ƙwarin gwiwar tata. A hankali ta motsa da nufin barin wajen ya tareta da hannunsa. A marairaice ta ɗago tana dubansa kamar zata fasa kuka, sai kuma ta sake maida idanun ta risinar tana ɗan ƙara tura baki dan yaƙi daina kallon nata..

       Idanun ya ɗan lumshe da sake buɗewa a kanta, a wata irin ƙaramar muryar da inba kusa da su kake bazaka taɓa sanin yana magana ba ya ce, “Kin san a gaban wa kike kuwa?”.......✍️



     _😂Da alama ta manta Shahan-shan, sai ka tuna mata fa🏃🏃🏃🥱._


No comments

Powered by Blogger.