Daudar Gora Book 2 page 22

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (22)

........Komai ya ƙara kwaɓema ta-ƙurya, ta rasa wace hanya ya kamata tabi dan ganin wannan aure ya ƙullu tsakanin Shahan-shan da yarinyar da sai a yau ta saka amintaccen bawanta bincike a kanta. A ɗan gefen ga jami'an gidan sun mugun duƙufa domin gano wanda yay tsaurin idon ɗaukar Zawjata-

almilk daga kurkuku zuwa cikin pool har da kashe jami'an dake tsaronta. Da zafi-zafi suke aiki a wannan yini dan Tajwar Eshaan ya basu kwana biyu ne kacal. Sunko duƙufan matuƙa, domin umarnin mai gayya mai aiki ba abin wasa bane a garesu.

      Tasan amintaccen hadimin nata shi a karan kansa bai san ita ɗin wacece ba, dan bayan muryar da take masa magana da ita a duk sanda zata sakashi aiki babu abinda ya sani tattare da ita kuma. To ko muryar ma ai bada tata ta ainahi take masa maganar ba. Sai dai duk da wannan tsaron data tabbatar tana da shi bata kasa jin wani ɓurɓushin damuwa ba a ƙasan ranta game da tsananta binciken. Ga Uwa tai mata alƙawarin bazata taimaketa da komai ba a wannan gaɓar, acewarta shine hukuncinta. Ta tsani yarinyar nan, tsana irin wanda batajin ta taɓa yima wani mahaluki irinta a rayuwa. Bata taɓa fuskantar tangarɗa a aikinta ba sai da yarinyar ta shigo rayuwarta. Matsala bata taɓa shiga a aikinta ba sai da yarinyar ta shigo masarautar. Tabi hanyoyi da yawa domin ganin bayanta amma ko gezau. Ta rasa wane kalar shegen taurin kai yarinyar ke da shi. Ita zuciyarta ta fara bata ma anya yarinyar ba shugabar wata ƙungiyar asiri bace mai zaman kanta? Dan abubuwan da ke faruwa a kanta sun fara bata tsoro. Sai dai taci alwashin kota halin ƙaƙa ne sai ta shafe babin rayuwar yarinyar da kaf zuri'arta a duniya nan bada jimawa ba. Wannan alkawarin ta ne......


    (Ni dai nace hummmm).


    ★★.... ★★....


        Fuska cike da murmushi yake duban kayan surkullen da boka Barbushi ya basu. Cikin ƴar dariya-dariya ya dubi Miran Arshaan da shima a kallo ɗaya zaka fahimci nasa nishaɗin. “Idan ya isa shi hatsabibi ne a wannan karon ya tsallake mana, ai idan yasan wata bai san wata ba damu yake labarin da ga shi har ƴar iskar yarinyar tashi”.

    Ƴar dariyar shima Miran Arshaan ɗin yayi, cike da nishaɗi ya ce, “Sai dai uwarsa Bushirat kuwa ta haifi wani amma ba madadinsa ba. Tunda taƙamarsa taurin rai sai mu bisa ta hanyar da zai laushi ta dolen dole da ƙaniyarsa. Shegen yaro kamar jinin aljanu da ga shi har ƴar ƙaniyar yarinyar”.

           “Kona ifiritai ne wannan karon dai tasu ta ƙare. Dan haka a daren nan na yau zamu saka komai a inda ya dace kamar yanda Barbushi ya bada umarni. Dan ubansu badai sunƙi mutuwa ta sauƙi ba, to ga rayuwar yayita sai dai a cikin ƙunci da baƙin ciki da ga shi har duk wani mai iya jin zai bashi kariyar.”

    Dariya suka sheƙe da ita har da tafawa kamar wasu abokai. Kafin su miƙe cikin ɓadda kamar da suka gama shiryawa suka nufi fada yanda boka Barbushi ya basu umarni.....

  

             ★★... ★★....


      Kamar yanda ta saba farkawa akan lokaci domin gudanar da sallar asubahi yau ma bata makara ba. Sai dai saɓanin ko yaushe yau a firgice ta farka. Da sauri-sauri ta ke karanto addu'ar tashi da ga barci tana faman waige-waige a ɗakin mummunan mafarkin da tai a daren jiya da ya sake maimaita kansa gareta yanzu na sake dawo mata. Sosai take jin zuciyarta na tsitstsinkewa, dole taja jikinta ta maƙure kanta a fuskar gadon tana mai naɗe jikinta da son riƙe rawar da yake yi bakinta na ambaton sunan ALLAH kamar yanda kaka ya horeta da daina ihu a duk sanda tai mafarki makamantan hakan saɓanin da da take ihun. Ta ɗauka tsahon mintuna shida kafin ta ɗan samu nutsuwa. Sai ajiyar zuciya da take faman saki a jajjere. Da alama ita ɗaya ta kwana a ɗakin batare da tasan sanda ya fice ba. Hanunta ta kai saman goshinta da zuwa yanzu Alhamdullah babu matsanancin ciwon kan nan data kwanta da shi. Sai ma ɗan sanyi-sanyi da damshin zufar data haɗa ya haddasa mata. Janyewa ta sake yi tana mai lumshe idanunta, haka kawai take jinta wata daban a yau kamar ba Iffahn Babiy da Ummu ba. Ko miye dalilin jin hakan bata sani ba. Kabbara salla da aka farayi ya sata miƙewa zumbur tana ture komai gefe. Gaba ɗaya jikinta babu ƙarfi, ga mafarkin da tai ya sake nunar mata da gaɓɓan jikin baki ɗaya. Haka dai ta ɗan watsa ruwa mai ɗumi ko zai saki sannan tayo alwala ta fito. Bayan ta gabatar da salla maimakon ta koma ta kwanta sai tai zaman karatun Alkur'ani ko zata samu nauyin da zuciyarta ta mata na kwana biyu ya ɗan rage...


       ★ Saɓanin ita shi ko rintsawar ma baiyi ba gaba ɗaya. Dan tun bayan barowarsa ɗakin da take yana zaune ne gaban laptop yana aikin da shi ya barma kansa sani. Har kusan uku yana zaune kafin ya tattara ya ajiye ya ɗauro alwala. Bai tashi a sallayar ba sai lokacin asubahi da zai wuce masallaci. A maimakon Gym da ya saba shiga ko yin wasan takobi a wasu ranakun sai ya nufi sashen Malikat Bushirat ta sirrintacciyar ƙofar dake kaisa sashen batare da kowa ya gansa ba idan yaso hakan. Jin nutsatstsiyar muryarsa nayin sallama a can ƙasan maƙoshi Jasrah da Malikat Bushirat suka dubi juna a yanayin mamaki. Cikin rashin aminta da abinda suka jin Malikat Bushirat ta bada umarnin shigowa. A maimakonsa shi ɗinne kuwa. Shi kam baiyi wani mamakin ganinsu taren ba duk da a yanzu aka idar da salla, dan yasan ɗunbin shaƙuwar dake tsakaninsu ta dabance. Maimakon zama a cikin kujera a hankali ya kai zaune kusa da Malikat Bushirat dake zaune kan sallaya har yanzun. Dan tana idar da salla Jasrah ta shigo mata. Gab-gab da ita yake zaune yana mai tanƙwashe ƙafafunsa tare da ɗaura kansa a kafaɗarta. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana lumshe idanunsa.

       Malikat Bushirat da ke kallonsa cike da tausayawa sanin in har ta gansa a yanayin nan yana cikin damuwa ta kai hanunta kan tattausar sumarsa yalwatacciya ta shafa a hankali. Nan ma ajiyar zuciyar ya ɗan ƙara saukewa. Kafin ya motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta “Barka da asuba ya Ammie-na”.

       “Ka tashi lafiya Saiful-malik”.

  Ta amsashi da kulawa tana sake tura yatsunta cikin sumar kansa a hankali. Kai kawai ya ɗan gyaɗa mata, sai kuma batare da ya dubi Jasrah da ke kallonsa ba ya ce, “Aunt good morning”. Murmushi ta saki jin yau kuma ita ake gaidawa. Itama ta amsashi da kulawa tana tasowa da ga inda take ta dawo ta ɗayan gefen Malikat Bushirat suka sakata tsakkiya ita da shi. Idanunsa ya ɗan buɗe kaɗan ya mata hararar wasa, a zahiri kam babu alamar ko murmushi a fuskarsa. Cikin fisgo maganar tasa da kamar an masa tilas yace, “Ammie kice ta tafi ta barni, ita kullum tana nane da ke tai auren ma baki huta ba”. Wani sassanyan murmushi Malikat Bushirat ta saki, dan yanda yay ɗin sai ya tuna mata da ƙuruciyarsa lokacin idan sunje dubashi harda Jasrah. Yata mita kenan Jasrah ta tafi tunda ita tana ganinta kullum har sai mahaifinsa ya shiga lallashinsa yake haƙura. Ita kanta Jasrah sai komai yake dawo mata, fuska ɗauke da murmushi tace, “Nikam babu inda zanje, sai dai kai ka koma inda ka fito ka barni da mamata”. Fuska ya ɗan kauda gefe yana sake tsuketa, amma baice komai ba. Ita kuma Jasrah ta cigaba da ɗan tsokanarsa kamar yanda takeyi a baya Malikat Bushirat na karesa tana musu dariya. Shi dai da ya fara takalo wasan bai sake ce musu ko kanzil ba.

        Bayan wasu ƴan mintuna Malikat Bushirat taci serious tana maida dukkan hankalinta kansa. Murya cike da kulawa ta ce, “Baka da lafiya ne?”. Kai ya juya mata alamar a'a. Sai kuma ya motsa lips ɗinsa kaɗan ya furta “Ina missing ɗinki ne my first luv”. Ji tai wani daɗi na ratsata, kanta na sake kumbura da alfaharin kasancewarta mahaifiya ga wannan ƙasaitaccen bajimin ƙyaƙyƙyawan sarkin. Ta sake shafa fuskarsa da kulawa matuƙa. “ALLAH yay maka albarka, ya cigaba da kulamin da kai da baka kariya”.

       “Amin”.

    Ya furta a saman lips, Jasrah kam a zahiri tana murmushi. Idanunsa ya maida kan Jasrah, fuskarsa babu alamar wasa ya furta “Mi kikeyi anan da safen nan kika bar mijinki?”.

      Murmushi ta masa ganin a serious yay maganar babu wasa a ciki. Tana ɗan wasa da yatsunta dan bazata iya kallonsa ba tai maganar dake bakinta duk da a shekaru itace sama da shi, sai dai ALLAH ya kwace girman ya bashi matsayinsa na namiji kuma sarkinta, a hankali ta ce, “Maganace mai muhimmanci ta kawoni”. Ta ƙare maganar tana ɗan ɗagowa ta dubi Malikat Bushirat. Shima kallonsa ya maida ga Ammien tasa. Malikat Bushirat ta sauke sassanyar ajiyar zuciya tana ɗan shafa kansa, “Magana ce muhimmiya Jasrah tazo da ita a kanka Saiful-malik”.

       Kaifafan idanunsa ya ɗan tsura ma Jasrahn ganin yaƙi yarda ta kallesa ya janye su ya sake maidawa ga Ammien sa. “Wani abu ya faru ne?”.

          Kai Malikat Bushirat ta girgiza masa, “Komai bai faruba, na baya ne dai da suka faru musamman akan abinda yarinyar nan ta aikata. Ba kowa ne zai fahimci irin abin da naji ba a lokacin da na fahimci zan iya rasa tilon ɗan dana mallaka a duniya. Amma sai na danne zuciyata wajen maida hankali na maka addu'ar samun lafiya fiye da ɗaukar mataki. Bani da jayayya akan hukuncinka, sai dai ƴar uwata tazo da shawarar dana gamsu da ita nima”........✍️


No comments

Powered by Blogger.