Daudar Gora Book 2 page 21

 


𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (21)

........Har ya kammala shirin barcinsa zai kwanta zuciyarsa taƙi bashi haɗin kan hakan. Fuska ya ɗan yamutse kai kace bashi da ra'ayin abinda zuciyar tasa ke so. Sai dai a kallo ɗaya zaka fahimci tsabar miskilanci ke cinsa da ƙasaitar mulki. Cike da izzar dake bayyana takunsa a matsayinsa ya nufi ɗakin.

A hankali ya tura ƙofan ya shiga bakinsa da sallama ƙasa-ƙasa. Kallon mamaki yake mata ganinta naɗe a cikin bargo, ga alamar ɗan rawa-rawa da jikinta ke mata da yake gani. Hannu ya kai ya ɗan janye bargon daga saman fuskarta. Aiko ta wani zabura, caraf ta damƙe hannunsa idanunta rufe ruf da alamar tana cikin mayen barcin dai bakinta na motsi cikin faɗa-faɗa take faɗin abinda baya ji. 

    (Fitinatu har a cikin barcin ma ba'a kadata) ya faɗa a zuciyarsa yana lumshe ido da riƙota ganin da gaske fa faɗan take ga zafin hanunta dake kan nasa na ratsa fatar shi. Jikinta rawa yake sosai, dan mafarkin da tai ya matuƙar firgitata, ta daɗe batai irin mafarkan nan ba. Da farko mamakin yanda take ɗinne ya shiga, sai dai ganin abinfa na gaske ne sai hankalinsa ya tashi. Amma bazaka taɓa tantancewa ba a face ɗin sa. Kaɗan ya girgizata muryarsa a ƙasan maƙoshi ya furta “K!”.

     Ina batama san yanai ba, sai ƙoƙarin fisge jikinta da take kamar dai yanayin da takan shiga a duk lokacin da tai irin mafarkan. Jikinsa ya jawota sosai yana ɗan bubbuga fuskarta kaɗan-kaɗan, sai kuma ya sake faɗin, “Open your eyes. Iffah k!”.

       Karan farko daya taɓa ambatar sunanta, duk da bata a hayyacinta sai da taji fitar sautin sunan. Buɗe idanun tai a hankali jikinta na ɗan tsuma ta sauke a kansa, sai kuma taja nannauyan numfashi tana ɗan ƙara warosu domin tabbatar da shi ɗinne a zahiri ko har yanzu a mafarkin ne dai. A hankali ya mannata da ƙirjinsa ya rungume. Wani ajiyar zuciya ta sake ja mai ƴar shashshekar data saka tsigar jikinsa tashi. Sai kuma ta maida idanunta ta lumshe sannu a hankali ganin yanda ya tsareta da kaifafan nasa idanun. Lafewa tai a jikin nasa kamar wata mage, dan kanta ciwo yake matuƙa. Ba ƙaramin dauriya yay ba na zamanta jikinsa har tsahon mintuna uku, cikin son danne yanayin da ke neman halaka shi ya buɗe idanunsa da suka canja kala akan ƙyaƙyƙyawar fuskarta. Wani irin kallo yake binta da shi tun daga fuskarta har zuwa ƙafafunta, gaba ɗayanta naɗe take a jikinsa. Yanda ta naɗe ɗin ya bama abayarta mai sanyi damar lafewa a jikin nata ya fidda mata suranta da ƙyau. A kasalance ya lumshe idanunsa yana kauda kansa jin numfashinsa na wata rawa-rawa. Ga ɗumin jikinta na matuƙar ratsa nasa jikin.

        “What happend?”.

    Ya faɗa a cikin kunenta da wata irin shaƙaƙƙiyar murya da bata taɓa ji da ga garesa ba, gata acan ƙasan maƙoshi matuƙa. Yanda sautin ya ratsa kunenta har cikin ɓargonta da ƙwaƙwalwar ta ya sata rumtse idanunta da masifar ƙarfi tana wani ƙanƙamesa. Ihu kawai ya rage ya sakar mata ko zata gane a wane riski ta jefashi, amma sai ya danne cike da jarumta ya furzar da boyayyan huci. Cikin sigar tambaya ya sake faɗin, “Uhhuyim?”.

    Nan ma kamar bazata amsa ba sai kuma ta nisa tana sauke ajiyar zuciya. Kanta ta ɗan girgiza a hankali ta ce, “Mafarki”.

         “Mafarki?”.

   Ya maimaita akan lips ɗinsa yana ƙoƙarin saka idanunsa cikin nata kasancewar ta ɗago da ga jikin nasa. Kanta ta gyaɗa masa tana ɗan kauda idonta, dan tun abinda ya faru ɗazu a tsakaninsu sai ta tsinci kanta da jin matsananciyar kunyarsa. Yanzun ma dan kawai tana a firgice ne. Kamar zai ƙara magana sai kuma ya share, murya a shaƙe mai tabbatar da ya gaji da magana ya motsa lips ɗinsa a nutse kamar a fisge, “Kinyi salla?”.

      Kanta ta ke girgiza masa batare da ta yarda ta kallesan ba yanzu ma. Komai bai sake cewa ba ya miƙe kawai, kamar wanda ke'a yanayin sanyi jiki ya nufi hanyar bathroom. Da kallo ta bisa ƙasa-ƙasa, mummunan mafarkin da tayi a kansa na dawo mata. (Mafarki ba gaskiya ba ne) zuciyarta ta ayyana mata, hakan ya sata sauke ajiyar zuciya ta zame ta kwanta jin sanyi na ratsa mata gaɓoɓi. Bai wani jima sosai ba ya fito, bargon data rufa ya kama ya yaye, tai saurin riƙowa tana ɓata fuska da turo masa baki. “Ni dai sanyi nake ji”. Ido kawai ya tsirama lips ɗin nata batare da ya iya cewa komai ba, kafin ya ranƙwafa a kanta slowly ya ɗauke ta cak ɗinta cikin hannayensa. Ba ƙaramin waro masa manyan idanunta tai ba. Ya ɗan harareta yana kauda nasa. Itama kauda natan tai tana kumbura bakin gaba sosai.

     (Stubborn girl) ya faɗa a ransa, a zahiri kam fuskar ya sake tsukewa da kyau kai kace da ɗa duniya bai san miye murmushi ba. Yana direta yay fitowansa abinsa. Binsa tai da kallo, abubuwa masu yawa na mata yawo a zuciya game da shi....


     Da ƙyar ta iya bin bango ta fito bayan idar da alwalar, yana zaune a cikin kujerar idonsa kan television ɗin ɗakin. Kaɗan ya ɗaga idanunsa ya kalleta ta ƙasa-ƙasa. Duk da yaga yanda take layi tsabar baƙin hali da ƙasaitar mulki ya hanashi tashi ya sake taimaka mata. Harta ƙaraso inda ya shimfiɗa sallayar kamar bai ma san da fitowarta ba. Kallonsa ta sata ta kauda kanta, sai kuma hakan da yay mata ya ƙona mata rai. Cikin jin haushi-haushinsa ta ɗan ƙarfafa kanta, gyalen daya ajiye mata ta ɗauka ta naɗa a kanta, kasancewar abayar jikinta babu ta inda ta tawaya ta kabbara sallarta cike da nutsuwar da ke tabbatar da ta samu wadataccen ilimin addini. Shi kansa yanda take sallar a nutsu duk da wani lokacin jiri kanyi kamar zai kadata sai yaji wata nutsuwa ta ratsashi. Wani kimar iyayenta da sake ganin darajarsu na mamaye sa. A zahiri kam bama zaka taɓa ɗauka hankalinsa a kanta yake ba. Fuskar nan tai ciɗin-ciɗin ko ɗan yankar kanun mutane sai haka😏.

        Tana idarwa ta zame a wajen ta kwanta hanunta dafe da kanta dake matsanancin sara mata, zuwa can kamar wadda aka zabura ta miƙe zumbur hanunta a baki, sai kuma ta nufi bathroom da ɗan gudu-gudu alamar amai. 

      “OMG!”.

  Ya faɗa a hankali ƙasan maƙoshinsa jin tana kakarin amai. Bai motsa ba duk da yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri, kusan mintuna biyu da wasu sakanni sai gata ta sake fitowa tana layi. Ga hawaye shaɓe-shaɓe a fuskar gwanin ban tausayi. Yanzu kam miƙewa yay da ƙyar ya nufeta, kamar jira dai-dai yana isowa gab da ita tai wani luuuu zatai baya ya tareta cikin zafin nama ta faɗo cikin hannunsa..

         A hankali ta dinga jan ajiyar zuciya jin bata faɗin ba. Sai dai ta kasa buɗe idanunta da ke rufe ruf duk da tanajin alamun nasa kamar na binta da kallo. Kallon nata kuwa yake cike da kasala, sai kuma ya ɗan lumshe nasa idanun shima yana sake rungumota da ƙyau har yana jin saukar numfashinta a jikinsa. Yanda nunfashinta ke saukar masa a jiki sai yake jin tamkar shima hajijiyar na neman kwasarsa, gudun kar ai abin kunya ya ɗagata cak ya ajiye a saman gadon. Kafin ya zauna a kusa da ita yana mai tsura mata fararen idanunsa. Sun kai kusan mintuna biyu a haka, kafin ya katse shirun ɗakin ta hanyar motsa lips ɗinsa a hankali ya furta,

        “What again?”.

    Kanta ta nuna masa da gyar ta furta. “Kaina kamar zai fashe”. Sai ga hawaye sharr. Ita kanta bata san miyasa take jin karaya ba a gabansa ko ma shagwaɓa ne oho. Idanunsa ya zuba mata kawai yana bin hawayen da ke bin ƙyaƙyƙyawar fuskarta da gudu-gudu da kallo. Haka kawai sai yaji murmushi na suɓuce masa. Kansa ya kauda gefe yay murmushin sannan ya ɗan sake matsawa kusa da kan nata sosai. Numfashi ta ɗan ja a sanyaye jin saukar lallausan tafin hannunsa saman goshinta. Shi kansa yanda zafin kan ya ratsa hanun nasa sai da ya ɗan lumshe ido. Murya can ƙasan maƙoshi ya ce, “Ta nan ne?”. Kanta ta ɗan jinjina masa, sai kuma ta ɗaura nata hannun saman nasa ta ɗan matsar zuwa gefen kunenta idanunta na sake kawo ƙwalla ta ce, “Harda nan da ma duka”. A yanda tai maganar cikin shagwaɓa kamar wata ƴar baby yaji tsigar jikinsa na wani yamutsawa. Amma jarumin naku sai yay ƙoƙarin basarwa har da yamutsa fuska kaɗan ya furta, “K raguwa ne ko? Just ciwon kai ki ke ma kuka?”. Kamar ya tunzurata ta sake turo masa baki da son ture hannunsa da ke kanta. Ko gezau, dan haka tai yunƙurin juyawa. Nan ma sai da ya nema sakin murmushi amma ya fuske. Cikin wata murya da mai lura zai iya fahimtar shauƙin da yanayin da suke cikin ke bashi ya ɗan matso da jikinsa gab-gab da nata yana faɗin, “Kin cika ragwantaka ne ai. Na miki addu'a?”. Kamar zata sakar masa kuka ta ɗaga kan dan da gaske kan na mata ciwo ne sosai.

         Shiru bai sake magana ba ya kamota, kan nata ya ɗaura saman jikinsa. Sannan ya sake maida hanunsa saman goshin yana ɗan murza mata sannu a hankali yana mata addu'an. Idanun ta dinga lumshewa sannu-sannu itama, batare data farga ba barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Bai daina addu'an da murza mata goshin ba, sai ma wani mayataccen kallo da yake mata idanunsa a shanye. Ya kwashe tsahon lokacin da bai fargaba a wajen zaune, dan tun kan da zafi har ya fara hucewa. Inda wani yace masa hakan zata faru tsakaninsa da wata ɗiya mace zai ƙaryata. Sai dai shi lissafin ƙaddara bai damu da wanda zai lissafa maka ba komai taka tsantsan ɗin ka akan nisanta kai ga abu.........✍️


No comments

Powered by Blogger.