Daudar Gora Book 2 page 13


 𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (13)

..........Cikin kallon kai mahaukaci ne Miran Arshaan yaja guntun tsaki. “Na kwantar da hankali fa kace? A gaɓar da nake hango cikar 99days ɗina kake tunanin kwanciyar hankali a gareni. Jasim kanka kawai ka sani a hatsabibanci, dan haka kar kai sakaci da ɗan hakkin da ka raina, dan shike zama RAINA KAMA KAGA GAYYA. Da ganin idon wannan tsinanmiyar yarinyar kai ka san akwai abinda ta taka. Nama fara zargin shegen yaron nan ba yana tare da ita bane kuwa?”.

         Kalaman Miran Arshaan sun sanyaya jikin Miran Jasim da alama, dama can ƙarfin haline kawai. Yaja numfashi mai nauyi yana jinjina kansa. “Hakane Arshaan, amma ina son ka fahimta kasheta ma kai tsaye ba abune mai sauƙi ba. Dan bazasu taɓa iya sakaci da bata kariya ba kamar yanda munafukan tsohuwar can ta ambata. Damar da ke garemu kawai a yanzu shine komawa wajen Barbushi. Shine ya kamata ya mana wannan aikin”.

     Jiki a saɓule Miran Arshaan ya jinjina masa kai shima alamar gamsuwa.....


★★★.......


         Duk yanda yake yaƙi da murmushin a karo na babu adadi ya gagara nasarar dakatar da shi bayyana a kan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. Akan dole dai ya sakeshi tare da lumshe idanunsa. “Fitinanniya”. Ya faɗa a hankali da sake nutsa kansa cikin lallausar kujerar da yake zaune. 

        *_(Kai malam baka san darajar mutane bane?....)_* Kalaman da suka zama na farko a haɗuwar farkon da bazai taɓa iya mantawa ba domin rubutattu ne a sashen da baya goge muhimman abubuwa suka dawo masa kamar yanzu take furtasu. *_(Ka kusan bige yaro amma tsabar kanka ba'a dai-dai yake ba shine koka fito kaga yaya yake ma saboda ku masu kuɗin nan ɗaukar talaka kuke baida banbanci da titin da kuke gurza tayoyin banzayen motocinku da kuka saya da kuɗinmu”). (“Anƙi a bakun, wlhy duk sai kun fito kun dubashi kun bama kakarsa haƙuri zan baku key ɗin nan, inba hakaba sai dai mu kwana anan.”)._* 

      “Zaki iya”. 

    Ya faɗa a hankali da ƙara sakin ɗan wani murmushin da kauda fuska kai kace bayan shi akwai wani a ɗakin. Ƙoƙarin ture komai yake sai dai hakan kamar da wahala dan komai kokawar sake maimaita kansa yake tamkar a yau ne ranar ke faruwa (Idan hanunka ya sake gigin taɓa koda hijjab ɗin jikina ne sai na karyashi, Sannan koda Shahan-shan ne yay wannan aikin bai isa barin wajen nan ba balle kai shashasha driver”) (“Daga yau ko daga nesa kuka hangoni to ku canja hanya koda a jirgi kuke kuwa”). Idanunsa ya lumshe da kai hannu ya shafi tattausar baƙar sumar kansa. Sai kuma ya miƙe cike da ƙasaita yana mai ɗan sakin murmushin gefen baki da faɗin, “Drama queen”. 


       (☺️Da alama su Shanshani an shiga lambun fulawoyi🥱🚶)

         


        ★★...... ★....


  “Mammah wlhy yarinyar nan ta fara bani tsoro nikam”. Daneen Ammarah ta faɗa da alamar tsoron da gaske a kan fuskarta. Murmushi Malikat Haseenat tayi har haƙoranta na bayyana. Sai kuma ta dubi Daneen Ammarah ɗin da ƙyau cikin ido. “Banda abin Ammarah minene abin tsoron anan to?...”

        “Mammah akwai wlhy, ki dubi fa furucin da yarinyar nan keyi, ni gaba ɗaya komai ma neman ƙwacemin yakeyi. Ga shi tun ɗazu nake neman sister (Daneen Waheeda. Ƴar uwarta dake aure a yankin larabawa) amma wayan yaƙi shiga.”

      Sosai Malikat Haseenat ta tsareta da idanu, sai kuma ta ɗan muskuta kamar mai son bada gargaɗi “Badai sanar mata zakiyi ba? Kirki ma fara wannan gamgancin, kin san dai halinta ko, fitinanniya ce ta gaske. Bata haɗa al'amarin duk wani jininta da kowa ba. Kuma kin san yanda ta nuna adawarta akan auran yarinyar nan da janta da mukai jikinmu tun farko saboda ƙin bata haɗin kai taƙi zuwa ko dubashi duk da labarin abinda ya samesa babu inda bai karaɗe ba”.

         A sanyaye Daneen Ammarah ta jinjina kanta. “Hakane kuma Mamma, kiyi haƙuri wlhy abinne duk ya ɗaure mun kai. Ita waccan (Malikat Bushirat) da zamu iya tattaunawa kuma an riga an birkita al'amarin ta da zuga gaba ɗaya. Amma gaskiya furucin yarinyar nan ya matuƙar gigitani. Mita sani haka akan abinda kowa bai sani ba? Ta yaya ma ta sani ɗin bayan bata da alaƙa da wannan masarautar a lokacin da abubuwan ke faruwa. Anya kuwa Iffah ba aljana bace Mamma”.

        Dariya sosai Malikat Haseenat keyi, sai da tai mai isarta ta tsagaita tana mai duban Daneen Ammarah da tai kasaƙe tana kallonta. “Babu wani aljana Ammarah. Mutumce kamar kowa. Kuma duk abinda kike tunanin ta sani ɗin a ɗan zaman nan nata ta fahimceshi. Ni kaina na san yarinyar hatsabibiya ce, sannan akwai wani ɓoyayyen al'amari tattare da ita mai girman gaske da ita kanta bana tunanin tasan akwaishi tare da ita”.

       “Mamma kema fa kin fara bani tsoro”.

    “To ko nima na zama aljanar?”. Malikat Haseenat ta faɗa cike da zolaya tana murmushi.

          “Wayyo Mamma ni dai bance ba kar kisa jikanki ya tsireni a tsakkiyar masarautar sa. Kinga tafiyata”.

    Da kallo kawai Malikat Haseenat ta bita tana murmushi. Tana matuƙar ƙaunar ɗiyar tata da tausayinta. Ammarah itace ɗiya mafi soyuwa a ranta. Dan ta haɗa abubuwa da yawa da ƴan uwanta basu da shi. Ga kuma ƙaddarar da ta sameta wadda har yanzu sun kasa fahimtar tushenta, duk da dai zuciyarsu na karkata musu wani abu daya shuɗe a rayuwarsu mara daɗin tunawa. Taja siririn tsaki da kauda al'amarin a ranta cike da ƙunar zuciya......


    ★★.....


   Dariya take sosai mai haɗe da kuka. Dariyar na zuwa mata ne a dalilin tuno fuskokin Miran Jasim da Miran Arshaan a ɗazun, harma da na waɗanda bata san dalilin razanar tasu ba game da furucin nata. Kuka kuwa tana yinsa ne da sanin ko mi zatayi a yanzu ta dai riga ta rasa ahalinta, rasawa ta har abada. Sai dai koba komai tana jinta sakayau a yau, kai koda ace su Miran Jasim sun halakata a wannan daren bazatai baƙin ciki ba. Dan wannan ruɗanin da ta saka a zukatan manyan masu faɗa ajin masarautar zai zama rikici ne na har abada da zai cigaba da hanasu farin ciki. Sannan zai fargar da al'ummar ƙasar ruman son sanin wanene Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed da banbance abinda suke son sanin gaskiyarsa. Shima zai sakashi ya maganantu ga al'ummar tasa ko da babu haka a cikin kundin tsarin mulkin nasa. Zai saka tsoro kuma ga masu kashe masa matan da zai sake iya aura anan gaba. Ta jefa tsuntsu biyu da dutse ɗaya kenan, kuma harga ALLAH ta sako zance masu kashe masa mata ne badan tasan komai akan hakan ba, sai dai zuciyarta na zargin su Miran Jasim ɗin ma anan, dan tunda suka iya shirya kashe Tajwar Eshaan ɗin lallai zasu iya halaka matansa dan su goga masa baƙin fenti ko wani dalilinsu da ban. “Na barku da wannan a halin daular ruman”.

   Ta faɗa tana sake ƙyalƙyalewa da dariya a karo na babu adadi tun maidota ɗakin kurkukun. Masifaffen kamshin da ya daki hancinta da kai saƙo cikin ƙwaƙwalwarta kai tsaye ya sata haɗiye dariyar. Shiru tai zuciyarta dake ƙoƙarin ƙaryata ƙwaƙwalwar tata na kaikawo da sauri-sauri. Tabbas alamar tsayuwar mutum take ji a ɗakin, sai dai yaushe ya shigo? Ta ina kuma? Shine abu mafi ban mamaki. Cikin ƙoƙarin son kauda abinda brain ɗin ta ke son tabbatar mata duk da zuciyarta na ƙaryata wa ta ɗago kanta data tura cikin cinyoyi. Zabura ta ɗanyi idanunta na sake fitowa waje, sai kuma ta shiga waige-waige. Shi ɗinne dai a zaune, zama irin na ƙasaita da iko a cikin sabon ɗakin nata na kurku da aka canja mata a yau. Ga wani kwarjini da cikar haiba zagaye da ƙyaƙykyawar fuskarsa dake bayyana shekarunsa. Ko maƙiyinsa ya kallesa yasan ya iya tsara ado, adon da koda a ƙaramar sutura yayisa sai ya nuna kansa....

       Ƙafarsa dake kan ɗaya ya sauke, hakan ya sakata dawowa hayyacinta tai saurin kauda kanta tana cure fuska waje guda ita a dole ba kallonsa take ba. Shima cikin nasa salon basarwar ya kauda nasa idanun dake mata kallon ƙasa-ƙasa yana mai miƙewa gaba ɗayansa. Hannayensa biyu duka ya zuba aljihu tare da yin ɗan taku ɗaya zuwa biyu tamkar namijin tantabarar da ke son birge matarsa, sai kuma ya juyo a sannu gareta ya sake sauke kaifafan idanun nasa a kanta. Cikin yanayin son lumshesu da sake buɗewa ya motsa lips ɗinsa cikin sautin ƙasan maƙoshi ya furta, “Wacece ke? Mi kike buƙata? Waya turoki a gareni ko ga ahalina? Dukiya? Mulki? Ko yin suna?”.

      Tabbas kalamansa sun mata zafi, sai dai kwarjininsa da wata kima da take kallonsa da shi a cikin idanunta sun hanata koda motsi. Shiru kusan na minti ɗaya taƙi ta tanka, sai can kamar wadda aka zaburar taja nannauyan numfashi da sake suƙe fuska tana mai fisgo jarumtarta a zahirance ta saki sassanyan murmushi. Da ƙyar ta iya riƙe rauninta wajen bashi amsa tana mai haɗiye murmushin. “Ni ba kowa bace. Bana buƙatar komai ga wani na sai UBANGIJI na. Farin cikin dunƙulallen ahalina zinare ko lu'u-lu'u da duk dukiyar da ƙasar ruman ke taƙama da ita bazai iya sayensa ba. Mulki baya cikin lissafina dan bai taɓa ko birge ni ba. Da suna nake buƙata akwai hanyar da tafi wannan da zan bi nayi duniya ta sanni ba ƙasata ba kawai ta ruman. Ni na turo kaina domin rama cuta ga macuci koda ace ya kasance k.....” Sai kuma ta haɗiye tana mai kauda kanta da ga kallon da yake mata. Jin babu alamar zai daina kallon nata ya sata sake juyowa garesa fuskarta a tsuke kamar yanda tasa take. Suɓul ɗan ƙarfin gwiwar da take da ya suɓuce kamar yanda takejin saurin kuzarinta na ida sabulewa da ga gangar jikinta shima. Idanu ta zuba masa a karo na biyu tamkar wata gaula ko shasha. A yanda take kallonsa da ƙamewarta ya sakashi cigaba da zuba mata idanun shima, sai dai duk da kallon nata ke ɗaukar wata siga da ban, shi tayar masa da tsigar jiki yake a sigar da shi tashi zuciyar ke amsa. Cikin son kauda abinda ke son masa kutsen ya fara takawa sannu-sannu kamar mai sanɗa har zuwa gabanta..

       Ta tafi kam, tafiyar da mai kallo zai iya kira suman zaune dan tsayuwarsa gab da ita baisa ta motsa ba. Sannu a hankali ya tokare hannunsa ga ƙarfen ɗan gadon da ke a ɗakin, tare da rissinowa gareta fuskarsu gab-gab da juna ya zuƙa numfashinta ya fesa mata nasa da ya maidota hayyacinta, tsinin hancinsa kan nata tamkar zai haɗe lips ɗinsu da ya dai-daita, ƙyawawan idanunsa da suka ɗan canja launinsu tare da shanyewa kamar mai jin barci ƙyam akan nata da wani irin sassanyan kallo data kasa fassarawa.

        “Ko giwa ta faɗi tafi ƙarfin wawaso. Kina da kauɗi! Gaki da hayaƙi. Kar ki kaini bango na aikata abinda zuciyata ke raya min faaaa..”.........✍️




     _🙄😏Mufa a daina shige mana ba wannan ya kawomu daular ruman ba, dan duk abun mutum sai mun masa hukunci ehe😌🚶. (Dangin Iffah'r mu koya kukace🥱)_


No comments

Powered by Blogger.