Daudar Gora Book 2 page 12
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (12)
.......Iffah da ke ƙoƙarin danne kukanta ta girgiza kanta alamar a'a. Idanunsa dake mata kallon ƙasa-ƙasa ya ɗauke ya maida ga Sayeed Hanifud-Din dake riƙe da takardar tuhume-tuhumen da akema Iffah. Miƙewa Sayeed.. yayi yana mai risinawar girmamawa ga Shahan-shan. Kafin ya sake gyara tsaiwarsa ya maida kan Iffah. “Ranki ya daɗe wannan kotu mai adalci na son ji daga bakinki dangane da waɗan nan laifuka da ake zargin kin aikata su. Shin kin aikata da gaske? Ko kuwa dai abin ba haka bane......”
“Ba haka bane? Kenan ma ƙazafi mukai mata bayan da bakinta ta furt.....” Jasrah ce mai maganar rai ɓace. Sai dai muƙut ta haɗiye batare da ta ƙarasa faɗar ba sakamakon kallon da Tajwar Eshaan yay mata, dan a yanzu sarkinta ne shi ba ɗan yayarta ba. Idanun nasa ya juya kan Sayeed.. alamar ya cigaba. Sayeed ya sake rissinar da kansa da ɗan rankwafawa sannan ya sake maida hankalinsa ga Iffah.
Tayi matuƙar jarumta da ƙoƙarin danne hawayen domin hanasu cigaba da zuba. Sai dai tanajin raɗaɗinsu a ƙarƙashin zuciyarta, har hucinsu na rige-rigen fita da numfashinta. Ta sani basai Jasrah tace komai ba, su dukansu zafinta sukeji, dan dukansu taga hakan a fuskokinsu, Daneen Ammarah ce mai ɗan sassauci, bakuma tada abinda za tace a kanta itakam.....
“Kotu na sauraren Zawjata-almilk”.
Sayeed Hanifud-Din ya faɗa a girmame duk da kuwa ya haifeta. Murmushin da ya bama kowa mamaki Iffah ta saki, tare da ɗago fuskarta a karo na farko yanda zata iya duban kowa. Sai dai bata aminta ta haɗa idonta da kowan ba. Tsaiwarta ta gyara idonta na kallon sashen su Miran Jasim ƙasa-ƙasa, murmushi ta sake saki a karo na biyu dan ganin yanda duk suka shiga yanayin firgici sai mazurai suke, duk da suna ƙoƙarin dannewa kuma. (Ku kwantar da hankalinku ai ba'a zo wajen ba) ta faɗa a zuciyarta tana ɗauke kanta. A zahiri kam natsuwarta ta sake tabbatarwa tana fuskantar kotu da ƙyau. “Ni Fareedah bint Zayyan zan fara da bada haƙuri kafin cewar da kowa ke buƙata da ga baki na. Nasan ko ba'a kawoni nan an gurfanar ba na can-can-ci acema bana numfashi a dalilin taɓa rayuwar mutum mai girman iko kamar Shahan-shan. Basai na wahal da Shari'a ba tabbas nice da kaina na bashi madarar da ya sha mai ɗauke da dafin macizai....”
Babu wanda bai zaro idanu ba a mutanen falon dan mamakin ƙarfin halinta. Shiko uban gayyar da furucin nata yazo masa a bazata kafeta kawai yay da idanu zuciyarsa na matuƙar mamakin ƙarfin halin takife ɗin yarinyar...
Cikin ɗan taɓe baki Iffah ta ɗage kafaɗu tamkar bataga yanayin da duk suka shigaba ta cigaba da faɗin. “Sai dai ba bashi madarar bace ya kamata ya zama abin mamaki ga wannan kotu mai adalci, sannan kuma ba itace ya dace ta zama abin tuhuma ba ko burin ganin an hukunta nin da kowa ke faman haƙilo da kai kawo sai kace kunajin tsoron numfashina barazanace gareku. Ni inda nice ku, tushen samuwar madarar zan maida hankali sani. Amma duk da haka ina so mai girma Shugabana da ku ahalinsa ku duƙufa wajen bincikowa, ba kuma dan inajin tsoro ko shakkar hukuncin da za'a min bane. Ba kuma dan zan kasa kama sunan wani bane wajen bayyana yanda akai madarar tazo hannuna ba. Ku da kanku nake son ku gano kafin ku sami dukkan amsoshin da kuke buƙata daga gareni dan ko numfashina zai tsaya sai na fesar da su ne tun daga tushe, ku kanku masu kisan Zawjata-almilk na baya sai ku shirya ranar tonon silili na tunkaro ku in har numfashina na harbawa daga gangar jikinna. Da ga ƙarshe ina roƙon wannan kotu mai adalci data sallami amintaccen hadimin shugabana tare da masu dafa masa abinci dan basu da laifin komai, su kuma masu ganin sun binne Iffah ne su shirya akwai sauran wasan dan ko filin ba'a share ba. Dan sai sun biya fansar jinin ƴan uwana uku da na iyayena koda zasu sami nasarar shafe nawa babin a doron wannan ƙasar”.
(Fitinanniyar yarinyar nan zata sa su binne ni a tsakkiyar ƙasata) ya faɗa a zuciyarsa yana mai lumshe idanunsa da ke bin lips ɗinta da kallon ƙasa-ƙasa, murmushi da ke neman suɓuce masa ya haɗiye a zahiri acan ƙasan zuciyarsa kuwa yinsa yake. Wanda bai sani ba sai ya ɗauka idanun nasa a lumshe suke, ga fuskarsa cike da barazana mai saka ruɗani ga duk wanda zai iya dubansa saboda yanda ya ɗaureta tamau.....
Kusan kowa sai da ya ɗauke numfashi a falon. Zukatansu kam na wata irin duka kamar ganguna, kalaman Iffah basu da banbanci da saukar nakiya a tsakkiyar kasuwar da bazaka iya banbance akan kanka ta fashe ba ko makwafcinka dan tsabar ruɗani. Cikin rashin yarda da kai aka shiga kallon kallo, kowa tsoron fara tankawa yake ko yin ƙwaƙwƙwaran motsin da zargi zai iya sauka a kansa. (Kun san mai kaza a aljihu fa baya jimirin asss). Malikat Ashwaq ta ɗan juya idanunta cikin ɓacin rai zatai magana da sauri Ameera Danish-Ara ta danne mata yatsun hannu tana mai haɗiyar yawu da ƙarfi. Shiru tai ta haɗiye abinda yake shirin suɓuce mata. Hakama Malikat Bushirat duk da kalaman Iffah sun daketa da ƙayatar da ita sai take jin kamar wani makircine yarinyar ke son ƙullawa domin kufcewa hukunci. Itama yunƙurawar tai zatai magana Daneen Ammarah ta girgiza mata kai da sauri.
Sayeed Hanifud-Din da gaba ɗaya shima yay mutuwar tsaye da waɗan nan kalamai na Zawjata-almilk da babu ɗar ko shakku na tsoro a idanunta duk da raunin dake tattare da yanayinta, jiki a sanyaye ya maida dubansa ga Shahan-shan. Babu alamar zaice wani abu har tsawon wasu mintuna da tashin hankalin duk wani wanda ke a falon ke sake bayyana. Sai da ya mula dan kansa yay gyaran murya. Cike da nutsuwa da ƙasaitar data zama ado ga sanyinsa ya ɗan sake dubanta da kallon da ke tada mata tsigar jiki a duk sanda ya yinsa. (Kinfa kife fuska tunda kin ɓallo min ruwa) a zahiri kam sai ya sake gyara gilashin fuskarsa kaɗan. “A bisa baƙon al'amarin da ya shigo a wannan shari'a bisa furucin wadda ake tuhuma, zamu ɗage wannan zama har zuwa nan da kwanaki uku. Za'a sake tsaurara tsaro ga wadda ake tuhuma fiye da da. Roƙon sakin wasu bai karɓu ba. Idan kuma da mai buƙatar cewa wani abu kotu na saurarensa”.
Shiru kowa ya kasa cewa komai, da alama wasu sun tsargu da tunanin cewar tasu zata iya zama talala musamman a sanin kaifin basira da sukaima Shahan-shan ɗin nasu. Hannun da yaga an ɗaga ya bi da kallo har ya sauke idanunsa kan kakar tasa, hakama duk wanda ke'a falon kallon nata yake. Malikat Haseenat ta jinjina kanta cike da dattako bayan kotu ta bata izinin maganar data nuna bukatar yi. A ladabce tai ƙasa da idanunta. “Muna godiya da wannan adalci na adalin shugabanmu, muna kuma roƙo a bisa adalcin wannan kotu ta bamu belin wadda ake tuhuma kodan kare lafiyarta da ranta da za'a iya nema a koda yaushe a dalilin furucin ta, babu yanda za'ai masu waɗan nan laifukan da ta ankarar su koma gefe su naɗe hannun zaman jiran a bankaɗosu batare da yunƙurin cuta mata ba”.
Nanma shiru kamar bazai amsa ba, bayan shuɗewar wasu mintuna kuma sai ya motsa. “Kotu ta gamsu da roƙon, sai dai bazata iya bada belin wadda ake tuhuma ba har sai an samo wani haske koda ƙanƙani ne da ga abinda ta faɗa ɗin. Za'a iya sake nema a zama na gaba”.
Daga haka ya miƙe abinsa cike da ƙasaita yana takun nan nasa na izza da bajinta. Dole kowa yay ƙasa da kansa har sai da ya fice sannan kowa ya ɗago. Iffah da ke jin ana kallonta ta ɗan ɗago kanta, ilai kuwa idanun Miran Arshaan da Miran Jasim ta gani na kallonta kamar zasu faɗo. Wani irin shegen makirin murmushi da ya nema wantsalo zukatansu waje ta saki tana mai kanne musu ido ɗaya da musu wani irin salo da yatsunta uku ta ɗauke kanta. Dan jam'ian dake tsare da ita sun zo tafiya da ita za'a maidata kurkuku.
(Wannan ƴa ta Babiy dai to sai ta sa anyi farfesunta a daular ruman 🥲🚶)
★★★......
Har karo suke da juna yayin tafiya tsabar fita a hayyaci. Da ƙyar suka iya ƙarasa kai kansu falon Miran Jasim da ya zamar musu mahaɗar tattauna matsalolin su.
“Tabbas kasheta zanyi, da hannuna kuma zan kashe matsiyaciyar yarinyar nan a yau”.
“Da hakan mizai hana kaje kace masa kai ne kawai ka bada madarar”. Miran Jasim ya faɗa cikin tsananin ɓacin rai yana wurgama Miran Arshaan da yay maganar farko harara. Shima a harzuƙe ya dubesa. “To mi kake so muyi ko jira? Kai a tunaninka wannan yarinyar mai kama da agwagwar ƙwa-ƙwa ta ƙi bayyana sunanmu ne danta rufa asirinmu? To ka dawo hankalinka idan ma ya suɓuce maka ne. Dan tarko ta kafa mana, tarko na talala garesa da bama mu ba hatta iyayen da suka haifemu sai munyi dana sanin zuwansu wannan masarautar. Ban taɓa sanin tsagerancin ƴar iskar yarinyar nan ya kai haka ba.”
Miran Jasim ya saki murmushi yana dafa kafaɗar Miran Arshaan. “Akwai abinda ta taka ne, amma zamu sauke mata shi ta yanda ya dace. Zamu tabbatar mata da mu iyayen iyayenta ne a wannan fanin na makirci. Ina son ka kwantar da hankalinka Akhi, ba ita ba, hatta shi mai yanke hukuncin anzo gaɓar da.....hhhhhh”. Ya ƙare da ƙyalkyalewa da dariya batare da ya ƙarasa ba........✍️
Leave a Comment