Daudar Gora Book 1 page 45

 


*_45_*

     ........Daneen Ammarah dake tunanin yanayin ma Iffah tashin hankaline kawai sai ta shiga rarrashinta. Dole Iffah ta cigaba da pretending da matsawa a sallameta taji sauƙi. Daneen Ammarah na rakata sashen ta wuce dan jikin Malikat Haseena ma dai babu daɗi sam. Dama Daneen Ammarah ɗin ta zauna

da Iffah ne domin saka ido kar wani ya cuta mata itama. Hakan yama Iffah daɗi, dan ya bata damar nutsuwa a kallon videon data ɗauka ɗazun. Sosai tai zooming gawar Zawjata-almilk tana kai bin jikinta ta inda yake a waje daki-daki. Wata irin zabura tai ganin abinda take ma ɗin kuwa a saitin wuyan gawar ta gefen kunenta na haggu. Wato alamar ɗigon sarin maciji har biyu. Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un take ambata wata irin zufan na keto mata, dan kuwa tabbas zancen mutumin can ya zama gaskiya. Amma duk da haka tana buƙatar sake tabbatar wa. Cikin rawar da jikinta ke mata ta shiga laluben number ɗin Sir Fawzan. Bugu ɗaya kuwa ya amsa kasancewar dama a jirace yake da kiran, dan ya nemeta amma bai samu ba. Yaci kuka har ya godema ALLAH dan zatonsa ma ita suka rasa. Cikin rawar murya ya ambaci sunanta duk da yaji muryarta. Amsawa tai da kuka, bata jira cewarsa ba tace, “Sir kaji tsoron ALLAH ka sanarmin gaskiya akan iyayena. Na rokeka karka ɓoyemun komai”. Zufa ce ta shiga karyo masa tako ina, dan baiyi tunanin jin wannan tambayar bazatanba a bakinta. 

     Shirunsa ya sake tada hankalin Iffah, ta cigaba da masa magiyar da dole ya faɗa mata gaskiyar data buƙata. “Tabbas na ɓoye miki Iffah, amma tun bayan barinki gida baifi da kwanaki ba aka rasa ɗan uwanki da Babiy sakamakon......”

    Ya zayyane mata labari tiryan-tiryan kamar yanda ya bincika. Babu kuma banbanci da abinda ta gani a wancan video ɗin na farko. Ya kare da faɗin, “Wlhy har yanzu akan binciken inda aka kaisu ake amma babu labarinsu. Nima kuma a yanzu haka ina yin nawa ta ƙarƙashin ƙasa amma har yanzu ban samu wani bakin zaren ba....”

     Kukan data fashe masa da shi ne ya katsesa daga jawabin nasa. “Ba zaku gansu ba, ba zamu ƙara ganinsu ba, sun rabani da su kamar yanda suka rabamu da ƴan uwana. Wlhy nima sai na kasheshi kamar yanda ya kashesu. Na rantse bazan barsa ba, bazan taɓa barinsa ba. Yanda ya halakasu da macijin tsafi sai na halakashi da dafin maciji na gaskiya. Shima sai ya ɗanɗa......” kuka ya sarƙeta ta kasa cigaba da magana...

      Cikin tashin hankali daga can Sir Fawzan ke faɗin, “Iffah ban gane ba. Dan ALLAH ki daina kuka kimun bayani, kaina ya kulle dan ALLAH kiyi shiru kinji, wlhy na miki alkawarin taimaka miki akan koma minene, koda kuwa nima zan rasa rayuwata ne.....”.

    “Babu wannan lokacin sir, bani da shi. Kai dai kawai ina zan samu dafin maciji mai haɗarin gaske?”. 

   “Ya ALLAHU! dan ALLAH ki faɗamin mike faruwa? a yanda zan fahimceki”.

       “Idan bazaka samamin abinda nake buƙata ba na Barka lafiya”. 

    Yana hello-hello bata sauraresa ba ta yanke wayar, koda ya sake kira bata ɗauka ba, da taga zai dameta ma sai ta jefa shi a black list. Kaikawo ta cigaba dayi a ɗakin tana kuka. Komai ya cakuɗe mata, zuciyarta ta gama ƙeƙashewa da bushewa. Ta sallama duk wani ɗan sauran rangwamenta. Abinda kawai idonta da zuciyarta ke gani gawa huɗu ta ahalinta kwance duk a dalilin mutum ɗaya tak, lokaci yayi da zatai abinda ya kawota itama dan bai cancanci cigaba da rayuwa ba mutumin nan sam, tayi alkawarin tare zasu mutu, amma sai ta kasheshi ta kuma bayyanama duniya wanene shi.

      Yanda taci kuka ta fita hayyacinta dole ta bama duk wani tausayi, da ƙyar ta iya zaman rubuta komai da ya rage, ta tattare ga Ajmaal, a ganinta ta gama tattare dukan abinda ya dace ta tattare masa. Hatta ƙudirinta na kawar da Shahan-shan ta hanyar dafin maciji bata ɓoye masa ba. Ta kwashe videos ɗin dake wayar zuwa wayarta ta turama Ajmaal ɗin, takumayi gajeren video da kalaman masu girgiza zuciya har biyu. Ɗaya na Ummu da su Kaka ta roƙa ya bamawa, ɗaya kuma na al'ummar ƙasar ruman ne baki ɗaya. Shima tai masa godiya da fatan alheri da nasara har ƙarshen rayuwa.......


  

        ★★..... BARRISTER ★★..... 


      Barrister dake jin kamar ya ƙwaɗa wayar da ƙasa ya rumtseta a hannunsa da masifar ƙarfi, a karo na farko wasu zafafan hawaye suke silalo masa. Jarumar zuciyarsa zugasa take kada ya yarda ya amince koda zai rasa rayuwarsa, yayinda wani ɓangaren kuma ke haska masa iyalansa da yafi so fiye da komai a duniya a halin yanzun. Wannan shine tashin hankalin mafi ƙololuwar girma daya taɓa cin karo da shi a rayuwarsa....


        Washe gari da safe wujiga-wujiga ya wayi gari, amma hakan bai saka ko gezau ga mutanen ba. Sai ma duk wani details daya shafi case ɗin da suka dire masa. Mamaki da tsoronsu ya sake mamayesa ganin duk wani abinda ke hannunsa ne. Kuma ya adanasu ne a mabanbanta wajeje. Akwai wanda a gidansa suke, akwai wanda a office suke, akwai na mota ma. Amma abin mamaki gasu duk a gabansa sun tattaro sun kawo masa. Tabbas ya sadaƙar, dan mutanen nan hatsabibaine na innanaha. In har zasu iya hakan a kankanin lokaci bayaji idan ya bijire musu iyalansa zasu tsira kuwa....

      “Barrister baka da lokacin dogon tunani, ka shirya dan a yau oga ke son ka tattaro masa duk bayanin da yake buƙata a wajen mutanen can. Ciki har da sanin su wanene ainahin masu aikin, da inda suka ɓoye Abu Hanash da ɗansa”.

    Karan farko Barrister ya dubeshi a razane, har ƙoƙarin taune harshe yake wajen faɗin, “Kana nufin dama baku bane ke riƙe da su Abu Hanash ɗin...?”

          Saurayin yay ɗan waige-waige alamar baya son wani yaji, cikin raɗa-raɗa yace, “Bamu bane Barrister. Muma kuɓutar da su muke son yi har ma da kai kanka. Sai dai ban san miyasa oga bai son ka sani ba ya zaɓi baka aikin a kife”.

    Ba ƙaramin zabura Barrister yay ba jikinsa har rawa yake ya matsa gab da saurayin. “Dan ALLAH kada ka yaudareni ka faɗa min gaskiya”.

    Da sauri saurayin ke masa nuni da yay ƙasa da murya kar wani yaji, “Barrister wlhy kaji na rantse maka abinda na faɗa maka shine gaskiya. Na kuma sanar maka ne saboda ka bani tausayi. Amma iyalanka kansu suna zagaye da tsaro ta yanda wani bazai taɓa iya samun damar cutar da su ba, kai kanka kusan sati uku fa muna tare da kai batare daka sani ba. Oga ba azzalumi bane ba, amma ban san miyasa bai son kasan taimakonku zaiyi ba. ya kamata kaima ai ka gane hakan tun farko musamman aikin daya baka ɗin, taya wanda zai cutar da kai zai kuɓutar da kai?, taya wanda zai cutar da kai zai ɗauraka akan hanyar abinda kake nema ya baka bakin zarensa haka cikin sauƙi?”.

     “Hakane wlhy ɗan uwa hakane. Kaina ne ya kulle a ruɗani nake gaba ɗaya. Nagode nagode yanzu kam ka bani ƙwarin gwiwa, insha ALLAHU kuma sai na bada mamaki. Dan a wannan gaɓar sai su Abu Hanash sun fita da izinin UBANGIJI, zan kuma gano koma wanene da hannu a kan ɓoyesu”.

       “ALLAH ya baka nasara. Ni bara naje kar wani ya fahimci ina anan har yanzu”.

   Kai kawai Barrister ya ɗaga masa yana murmushi. Wannan tattaunawa ce ta bama Barrister duk wani ƙarfi da sabuwar himma na musamman, a yanzu kama baka iya ganin komai sai murmushi tare da shi, lokacin da aka kawo masa abincin rana ya buƙaci takarda da abin rubutu. Takardu aka kawo masa bama takarda ba, hakan ko ya masa daɗi, dan ya kwashe sauran wannan yinin da dare wajen tsara duk abinda ya dace. Washe gari har ya fisu zumuɗin son fita ma, sauran da basu san miya faru ba canjawar Barrister ɗin taita basu mamaki.....


     ★★... KAUYEN JUMNA ★★....


    Tun kammala bayanin Abu Zainab ga su Kaka jikkunansu duk yay sanyi, Ummu ma hawaye takeyi, Barrister shine hope ɗin su a yanzu bayan UBANGIJI masanin abinda ke fili da ɓoye. Gashi a dalilinsu an rasashi. Idan har aka cutar da shi ta dalilinsu bazasu yafema kawunansu ba.

         Kaka dai jinjina kai kawai yake amma komai ya kasa cewa, sai Iyyani ce cikin ƙarfin hali da sharar ƙwalla ta dubi Abu Zainab da damuwa ke shimfiɗe a fuskarsa. “Zakariyya kuyi haƙuri dan ALLAH, mun jefa rayuwarku a haɗari, ya ALLAH ka bayyana Abdullahi da gaggawa”.

    Ɗan murmushin yaƙe Abu Zainab yayi, cikin danne abinda ke masa kaikawo yace, “A'a mama ai mutum baya taɓa wuce ƙaddararsa, kuma har yanzu bamu tabbatar ba ko akan wannan case ɗin bane muka rasa shin, dan Barrister da kike ganinsa nan shima hatsabibin kansa ne, gaskiyarsa da tsayuwa akan ganin tabbatar da ita yasa yanada maƙiya da yawa akan cases daban-daban hatta a cikin abokan aikinsa ma. Kinga kuwa zama ta iya yiwuwa ba'akan wannan ɗin bane.....”

      “Dole ya zama akan wannan ne”

Kaka ya faɗa cikin katse Abu Zainab. Duk kallonsu suka maida a kansa. Ya jinjina kai batare da ya kallesu ba. “Ban san gaibu ba, amma inaji a jikina akan su Muhammad Zayyanu ne, sai dai kuma tabbas koma a ina yake har yanzu yana raye insha ALLAHU. Inajin wannan ƙwarin gwiwar ne a zuciyata”.

       Ba ƙaramin mamaki kalaman kakan suka basu ba, sai dai kowa ya gagara cewa komai sun dai zuba masa ido. Kusan mintuna biyu gidan shiru kafin kaka ya miƙe, babu jimawa ya dawo da jakka a hanunsa. Su dai duk suna kallonsa kawai. Takardar daya zaro ya miƙama Abu Zainab. “Ungo duba wannan”.

     Da sauri Abu Zainab ya amsa ya fara karantawa. Bakinsa cike da magana ya ɗago yana duban kaka da ke kallonsa. “Baba wannan kuma fa?”.

    Murmushi Kaka yayi da kauda kansa kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya ɗan taɓe baki da fara basu labarin yanda duk a kai a randa zai dawo. Ya ɗora da faɗin, “Saurayin daya kawoni gidan nan zuciyata ta bani ba haka nan ya kawoni ba....”

        “Amma baba shine ka amince harma da nuna masa gida?”.

    Kaka yay ƴar dariyarsu ta manya. “Zakariyya kenan, to idan baka iya kama ɓarawo ba ai shi sai ya kamaka. Ka ganni nan barni kawai inda ka ganni. Idan na nuna nasan yanada manufa a kaina tun farko kamar yanda naso nuna masa a tasha ai bazan san sirrin zuciyarsa ba. Amma dana bashi dama fa? Yanzu a tafin hannuna yake, kuma jirace nake da zuwansa dan na tabbatar zai dawo, na masa talalar da tabbas sai ya dawo da izinin UBANGIJI”.

         Abu Zainab kam a yau Kaka ya fara bashi tsoro. Sai dai ya danne bai yarda ya nuna ba. Kaka ma ya fahimci haka amma ya kanne, sai jakkar ya tura ma Abu Zainab yana faɗin, “Wannan sune kuɗin dake tare da takardar”.

    Nan ma dai da mamaki Abu Zainab ke kallon kuɗin, kuɗine masu yawa sabbi ƙal sai ƙamshi suke na sabunta. “Baba waɗan nan mutanen kuwa anya....”

         Kaka yay murmushi mai bayyana haƙora. Sai kuma ya ɗan kalli sashen da Ummu ke zaune. Tuni ta tashi batare da sun farga ba har Iyyani..........✍️


No comments

Powered by Blogger.