Daudar Gora Book 1 page 43

 


*_43_*


..........Yau kwanaki huɗu kenan da rashin ganin Sayyid Khairul-Bashar, kwana shidda kuma cur da kai Iffah sashen Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed. Sosai masarautar a harmutse take, yayinda ƙananun magana da rikice-rikice ke neman tashi a dalilin fitar zantukan da Sayeed Khairul-Bashar ɗin yayi kan Tajwar Eshaan a daren da za'a rasashi.

Nan fa kowa ya shiga yima al'amarin fashin baƙi da ga ɓangaren masu faɗa ajin gidan, wanda kai tsaye kusan mafi yawansu sun karkata zarginsu ne da kalaman da Tajwar Eshaan yayi shi kuma..


      Duk abinda ke faruwa sarai yana isa kunensa, sai dai abin mamaki yayi biris kamar yanda ya saba. Yayinda shirun nasa ke ƙara wutar al'amarin matuƙa a tsakanin ahalin gidan baki ɗaya. Rashin daɗin maganganun da ke neman kawo bore ga mulkin Shahan-shan ɗin kai tsaye ne ya tada hankalin Malikat Bushirat matuƙa ta nema ganawa da ɗan nata, dan tun ana yi iya su ahali har abu ya zagaye masarauta yana neman fara fita waje.

       Bayan mintinan da basu gaza talatin ba amsa daga Tajwar Eshaan ta dawo ga Malikat Bushirat cewar baya buƙatar ganawa da kowa. Ranta ya matuƙar ɓaci da wannan amsa, dan take ta kori dukkan hadimanta ta shiga Safa da marwa. Tasan kota kirashi bazai ɗaga ba, kuma tunda yace bai buƙatar ganawa da kowan ta san halinsa har zuciya baya bukatar hakan. A kaikawon nata Iffah ta faɗo mata a rai, babu ɓata lokaci a karo na biyu ta bukaci ganinta duk da kuwa sune sukai mata katanga da sake baro sashen Tajwar Eshaan tun a waccan fitar acewarsu har sai ta cika kwanakin bakwai ciff.

        Iffah na zaune a ƴar barandar da takan sha iska da nazarin littattafan data maida hankali saƙon na Malikat Bushirat ya risketa, ta ɗanji mamaki, amma sai ta shanye a ranta kawai, dan tun washe garin kwananta na biyu Malikat Haseenat ta kirata a waya da kanta ta sanar mata karta sake cewa zata baro sashen Tajwar ɗin har sai kwanakin bakwai sun cika. Haƙuri ta bada bisa kuskurenta, daga ranar kuma ta haƙura duk da a takure take matuƙa da zaman, ganin ranta zaita ɓaci ma a banza sai ta maida hankalinta ga nazarin littattafan nan data ɗibo a books room, ko shi Tajwar Eshaan ɗin ma sai ta ƙulla wasan ɓuya da shi, dan tun faruwar tashin bomb ɗin nan ta riƙesa a rai, sai kuma maganar ɓatan Sayeed Khairul-Bashar da a yanzu aketa dangantashi da shi ya ƙara tabbatar mata da shi mutumin banza ne.... 

       Cikin ƙanƙanin lokaci ta kimtsa, ta saka kamshin data maida nata ta ƙarfi da yaji. Tana fitowa daga sashen ta samu hadimanta na jiranta. Gaisuwarsu ta amsa a yau kam da kulawa, kafin ta shiga motar da zasuje sashen Malikat Bushirat ɗin a ciki duk da bawani uban nisa bane, amma akwai tazara gaskiya. Sojan daya buɗe mata yay salute ɗinta kafin ya maida ƙofar ya rufe, da sauri suma hadiman suka shiga ɗayar motar bayanta.

      A tafiyar da bata gaza mintuna biyar zuwa bakwai ba suka iso, anan ɗin ma dai buɗe mata akai, yayinda hadimai ke faman zubewa ƙasa bisa gwiyawunsu. Hannu kawai Iffah ke ɗaga musu da sakewa. Tausayinsu da sake jin zafin wannan mulkin iko na kasarsu a ranta. Tun a falo na farko tabar hadimanta, inda amintacciyar hadimar Malikat Bushirat ta karasa mata iso har inda take.

      “Barka da yamma Mah-mah”.

Iffah ta faɗa cikin girmamawa ga Malikat Bushirat dake hakimce fuska babu walwala. Hannu kawai ta ɗaga mata, daga haka falon yayi shiru. Sai da ta gama shan kamshinta kafin ta tashi zaune da ƙyau idonta akan Iffah da ta rissinar da kai .

    “Ibnati kin san miyasa na kiraki?”.

“A'a Mah-mah”.

Iffah ta amsata da sauri. Cikin ɗacin murya Malikat Bushirat ta cigaba da faɗin, “Akan mijinki ne, nasan duk abinda ke faruwa a Masarautar nan kin sani kema”.

          “Hakane Mah-mah, amma sai nake ganin kamar ba haka bane, kawai dai wasu ne ke son ɓata masa suna”.

       Har cikin rai kamalan Iffah sun saka Malikat Bushirat jin sanyi a rai, sai zuciyarta na rawa dan zuwa yanzu al'amarin ɗan nata da gaske tsoro yake bata. Yayinda ita ko Iffah ta faɗi hakanne da manufar wayon da ALLAH ya bata domin son fahimtar abinda take son sani.

        Malikat Bushirat ta katse mata tunani da faɗin, “Hakan zai iya zama gaskiya, sai dai bazamu saki jiki ba dan da gaske al'amarin mijinki na bani tsoro. A yanzu haka na bukaci ganinsa amma shi yace bai buƙatar ganin kowa”.

     Da mamaki Iffah ta ɗan ɗago ta dubeta, a ranta kam jinjina rashin mutuncin sa take, a tunaninta ai ko kowa bai tsiraba mahaifiyarsa ta tsira.  “Mah-mah kuma shi ɗinne ya faɗa?”. 

    A karan farko Malikat Bushirat tai murmushin takaici. “Kar kiji ko tantama akan hakan Ibnati. Dan duk yanda kike tunaninsa ya wuce nan ɗin. A yanzu dai tunda ya nuna bai buƙatar ganin kowan bazai gani ɗin ba. Shiyyasa na kiraki nan dan kimin wani taimako na haɗani da shi ta waya”.

         Yawu Iffah ta haɗiye muƙut, dan itama dai a karan kanta kwanaki huɗu kenan bata sanyashi a ido ba. Tayaya kuma zata haɗasu a waya. To wanda ma ya nuna kai tsaye bazai haɗu da ita matsayin mahaifiyarsa ba ita kuma ƴar karere taya zatai hakan?. Amma bara ta amsa mata kawai, dan koba komai itama tana buƙatar jin gaskiyar lamarin ai.......


        ★★.......


   Har lokacin kwanciya barci Iffah bata samu wata makamar riƙewa na tunkarar Tajwar Eshaan ba. Hasalima bata da tabbacin a inda zata samesa. Tambayar hadimai kuma tamkar gazawace a gareta matsayinta na Zawjata-almilk. Kusan ƙarfe ɗayan dare tana tsaka da kai kawonta da faman jan tsaki saƙo ya shigo wayarta. Kamar zata share sai kuma ta ɗauka dan koba komai kullum a cikin tsumayen ji daga su Babiy take. Mamaki ya sata buɗe saƙon da hanzari ganin Malikat Bushirat.

      _Ina alfahari da kasancewar ki tare da gudan jinina Ibnati. ALLAH yay miki albarka, yanda kika zama sanadin yaye damuwata kema ALLAH ya yaye miki taki yanzu na gama waya da shi_.

     “What!!”.

Iffah ta faɗa cikin ɗan zabura tana sakin wayar akan carpet. To mi hakan ke nufi? Ita da batama gansa ba taya har yay kiran mahaifiyar tasa da har ta gamsu itace sanadi. “Anya mutumin nan kuwa ba ifiritin aljani bane?”. Ta faɗa a zahiri tana waige-waige a ɗakin da tunanin ko dai akwai camara, to inma camara ɗin ce itada sukai magana a sashen Malikat Bushirat ma ta ina camara ɗin zatai tasiri kenan...


       Har waye war gari babu nutsuwata tattare da Iffah akan wannan al'amarin, dan ko barcin kirki batayi ba sam. Sai dai tuna a'a yau zata bar sashen ya saka mata ɗan jin sassauci ka ɗan a zuciyarta. Tana ko idar da sallar asubahi ta taattara kayanta waje guda tsaf tana jiran gari ya ƙara haske ta kama gabanta duk da kuwa wata zuciyar na bata shawarar take akan zuwa Tajwar Eshaan wai ko zata fahimci wata gaskiya saɓanin wadda zuciyarta ke tabbatar mata. Amma dai ta dake dan tana buƙatar damar keɓance kanta ko zata samu nutsuwa.

        A bisa al'adar masarautar kamar yanda ake kai Zawjata-almilk turakar Shahan-shan haka ake zuwa a ɗakkota cikin tattali da giramamawa tare da manyan ƙyaututtuka a randa ta cika kwanaki bakwai cif. Kowa ya ɗauka tunda an kai Iffah ba bisa ƙa'ida ba baza'ai wannan al'ada ba gareta musamman yanda tama karya doka a kwana ɗaya ta fito. Ga kuma a yanda masarautar take harmutse kwana biyun nan. Amma sai Malikat Haseena ta bama kowa mamaki ta hanyar haɗa komai na al'ada da akeyi, tare da mukulllin zabgegiyar mota ƙirar zamani da masu hidima har guda goma, da tarin turarurruka na musamman, Daneen Ammarah da tsaffin dake da hurumin gudanar da al'adar a masarautar suka yima sashen Tajwar Eshaan tsinke cikin busar sarewa mai tabbatar da isar da saƙon manufar al'amarin.


      Tofa wannan fa shine an tsokalo tsuliyar dodo. Dan kuma masu rajin faɗa aji tuni sun sake buɗe shafin caccakar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed da kakar tasa Malikat Haseena kan basu damu da ɓatan Sayeed Khairul-Bashar ba. Ko kuma ma dai sun san komai ɗin da gaske. Wannan al'ada ta sake saka jikin Iffah mutuwa da shiga ɗunbin mamaki na gaske, har aka maidata sashinta babu alamar tana cikin cikakken tunaninta ma. Bin dai kowa take da ido tamkar gunkiyar da aka ƙirƙira domin tarihi...


     ★Ashe duk wan can ƙarami ne a abin mamaki da Malikat Haseena ta tanada a yau ɗin. Dan ƙarfe tara na dare da kanta kamar yanda tayi akan Iffah ta sake jagorantar rakiyar ɗaya cikin biyun Zawjata-almilk dake gidan tun kafin zuwan Iffah. Duk da bata haɗu da Tajwar Eshaan ba yau bata dawo da ita ba kuma dan acewarta zai ma gaji ne itama ya kulata idan ya gama zaman kulle kansa a ɗakin kamar yanda zukatansu ke basu sakamakon sanin hakan al'adarsa ce a duk sanda ransa ke ɓace.

       A wannan gaɓar kam kowa ya saki jiki waccan matsalar ta shuɗe tunda ga Iffah tai kwanakinta lafiya ta fito. Maimakon shiga fargabar rasata itama sai kowa ya ɓige da ƙananun magana akan rashin dacewar hakan. Yau ɗin ma dai malikat Haseenat tayi kunnen uwar shegu da su, yayinda Malikat Bushirat da Daneen Ammarah suka shiga halin mamaki da hukuncin na Malikat Haseenat a karo na biyu saɓanin dukkan shirye-shiryen su. A wannan karon kam sun yanke ƙuirin tun kararta suji ba'asi, sai dai sun barma safiya komai....


       ★★


     Surutai akan ɗimuwar da aka wayi gari da shi a masarautar ne ya farkar da Iffah dake fashin salla ɗan barcin daya figeta, dama da ƙyar ta yisa sakamakon kwana da tai neman Sir Fawzan da Sir Ajmaal a waya amma bata samesu a online ba hakama a kira. Sai abinda ta karanta da yay matuƙar tada hankalinta a ɗaya daga cikin littafan da take nazarta akan Tajwar Eshaan. “Tabbas babu lafiya” ta faɗa a zahiri tana miƙewa zumbur. Har ta nufi ƙofa ta dawo da sauri, toilet ta shiga a gurguje ta watsa ruwa ta fito. Sama-sama ta kimtsa jikinta ta fito. Hadiman ta da alamun sanyin jiki ya bayyana a agaresu suka dinga zubewa gaisheta. Maimakon amsa ta jefa musu tambayar da ruɗani ya bayyana kansa a cikin idanunsu da jikkunansu lokaci ɗaya.

      “Mike faruwa a masarautar nan? Da alama babu lafiya?”.

    Duk sun rikice babu alamar wani zai amsa mata. Sai kaɗuwa suke kamar masu jin sanyi. Halin da take ciki ya assasa mata jin zafin hakan ta daka musu tsawa. Sake firgicewa sukai, sai dai wajibi ne a gare su bin umarninta, dan haka cikin ƙarfin hali wadda ke matsayin amintatta a gareta ta sanar mata cewar an wayi gari da rashin Zawjata-almilk ne ta farko da jiya ta kwana turakar Shahan-shan sai Sayeed Khairul-Bashar shima da aka samu gawarsa a wani ɗaki cikin masarautar. Iffah da bata san da hakan ba ta ƙame ƙam alamar sumar tsaye ta wucin gadi ce ta risketa. Sai kuma hajijiya ta fara juya mata falon da hadiman, a hankali duhu ya dinga lulluɓe idanunta data kafa musu tabbacin bata cikin hayyacinta..........✍️

 

No comments

Powered by Blogger.