Daudar Gora Book 1 page 4
*_4_*
_______________
.........Iffah tayi mamaki da kaka ya bari salin alin tabi Hanash washe gari, duk da Iyyani taso borewa ita. Amma wasu lafuza daga cuɗaɗɗun kalamansa ya sata yin shiru ta bisu da addu'a. Kaka yayma Iffah gargaɗi matuƙa akan abubuwan daya bata, ya kuma tabbatar mata ko guda ɗaya taƙiyi zaiji hakan a jikinsa.
A hankali ta murza awarwarayen hannunta da shine ya sakamata, ta sake lumshe idanunta da sakin ajiyar zuciya. Haka kawai takejin awarwarayen da girma da kuma banbanci da irin wanda take sakawa a baya domin kwalliya, ko miye dalili oho.
Daga Ummu har Babiy a tsorace suke kallon Iffah da Hanash da suka shigo. Hanash ya girgiza musu kansa cikin sauri yana faɗin, “Wlhy ba laifina bane Babiy. Itace ta bore akan saita biyoni, kaka kuma ya bata goyon baya. Dan a cewarsa _(Babu wani nisa dake bada tazarar gujema ƙaddara. A wani ajin jarabawar data biyoka ma gara kai ka tunkareta. Dan ba kowane kogo bane ke zama kogo ga ma'abocin gudun ceton rai)._ Babiy na kasa fassarawa, akoda yaushe cirkuɗaɗɗun kalamai daga bakin Kaka masu tsaurine da wahalar fahimta. Dan ALLAH idan kun sani ku fassara mana”.
Maimakon amsa daga Babiy baya sukaga yayi tamkar zai faɗi, sai dai cikin sa'a ya dafe gini tare da dafe kansa alamar hajijiya. Ummu ma ƙasa takai zaune jikinta na rawa, hakan sai ya ƙara firgitasu. Da sauri duk sukai kansu suna mai tambayarsu suna lafiya kuwa?. Da kai kawai suka amsa musu, Babiy harda ƙoƙarin ƙaƙaro murmushi. Cikin son kwantar musu da hankali yake kallonsu. “Kunga karku sakama zukatanku wata damuwa, ba maganar Baba bace ba, kawai dai bana jin daɗine kwana biyun nan dama”.
Jimm sukai alamar tunani, sai dai kuma babu damar yin musu ko ƙin aminta da cewar tasa. Hanash ya taimaka masa suka koma cikin runfa, Iffah kuma tana riƙe da Ummu..
★★★
Washe gari batare da sun sani ba Babiy yay sammakon yin tafiya zuwa ƙauyen Jumna. Ya samu tarba daga surukan nasa ko ta girmamawa....
Ƙyaƙyƙyawan tsohon da Tattarowar fatarsa ta tsufa bai hana bayyanar ƙyawun cikar halittarsa ba ya sake kallon dattijon gabansa a karo na babu adadadi. Murmushi ya saki a karon farko, cikin karyar da kai da ƙanƙan da idanu ya kai hannu bisa kafaɗar dattijon. Numfashi yaja kakkaura da juyowa alamar dawowa hayyaci. Ya maida kansa ƙasa ya sunkiyar saboda girmamawa ta surukuta dake a tsakaninsu na tsahon shekaru.
“Humm Muhammadu Zayyanu!”.
Tsohon ya kira sunan tamkar mai sake bita a ranar da aka raɗa ga mai shi. Ɗago idanu ya sakeyi a karo na biyu sai kuma ya risinar tare da amsawa da “Na'am Baba”.
“Tun isowarka magana nake gani shimfiɗe a fuskarka amma bakinka ya kasa furtawa, ko wani abu ya sami Hanash da ƴar uwarsa ne a hanyarsu ta komawa gida jiya?”.
“A'a baba ko ɗaya, lafiya lau sukaje cikin ƙoshin lafiya kuma, sai dai.....”
Sai kuma yay shiru ya kasa ƙarasawa. Kaka dake kallonsa yay ɗan murmushi, “Sai dai baku so komawar Iffah ba ko?”.
“Hakane baba. Domin kuwa babu abinda ya canja a daular Ruman, muna jin tsoron rasata itama kamar ƴan uwanta, duk da bamu da tabbacin zasu sake waiwayrnmu, sai dai kalamanka sun sakamu a ruɗani har muka kasa rumtse idanu a daren jiya domin yin barc......”
“Hana ido barci bashi ke nufin damar iya sauya abinda bakai ka rubuta ba. Muhammadu Zayyanu! Da ace ƙaddararmu a hannayenmu take da kaf mutane bazasu zana zaman duniya ba a littafinsu musamman idan sun san koda daɗin busawar iskar dake cikin aljanna ce. Karka damu kanka da sanin sirrin cikin dutsen da ko'a kallo abin firgitarwa ne. Mumini yakan kasance mai azumtar yini daga UBANGIJI, ya kuma sallaci duhun dare daga UBANGIJI domin yaye damuwa ko samuwar nutsuwa a duniyarsa. Gaibu daga ALLAH take, zahirin da yaso mu sani kawai yake iya nuna mana ta isharar rayuwa ko canjawar tunanin zuciyo
yi”.
Nannauyan numfashi yaja ya fesar tare da jinjina kai, bawai kwanciyar hankalin da yazo nema ya samu ba, sai dai rashin zaɓi ko bakin zaren kamawa ya sashi fahimtar tsohon na masa nuni da shiru ne kawai a zubama sarautar ALLAH ido dan shine kawai gagara misali.....
_________________
★Kwanaki biyu kenan da dawowar Iffah gida, inda dawowar tata ta zame mata tamkar wani famin ciwo a jikinta. Dan a kullum takanyi hawaye sama da sau babu adadi akan rashin ƴan uwanta guda biyu. Komai ta kalla nasu yakan dawo mata da jiyansune mai cike da farin ciki da babu tunanin yankewa. Duk halin da take a ciki Ummu da Babiy na hankalce da ita, tausayi take basu matuƙa, wani lokacin Ummu har hawaye takan share itama.
Yau ma tamkar kullum tun bayan dawowarta tai shirin makaranta ta fice badan hankalin su Ummu ya kwanta ba. Kawai dai dan ta dagene akan komawar. Sun bartane ko komawar zaisa ta sake samun nutsuwa da farin cikin da ko'a fuskarta yanzu baka hangosa. Sanye take cikin skirt golden yellow da t-shirt fara da suka kasance Uniform ɗinsu, sai hijjab fari ƙarami shima ta ɗora niƙab ta yanda ƙwayar idanunta kawai ake iya gani. Bayanta goye da school bag. A nutse take tafiya kanta a ƙasa tamkar bata son taka ƙasar har ta iso bakin titi, tsayuwar da batafi ta mintuna uku ba ta samu abin hawa kamar sauran ɗalibai daketa ɓillowa a kowane kusurwa. Makarantarsu babbar makarantace mai ɗauke da ɗalibai masu hazaƙa, domin kuwa an tattarosu ne daga mabanbanta makarantu aka kawo nan saboda hazaƙarsu. Kowa bata kulaba ta shige aji tai zamanta, saɓanin da da kowa yasan Iffah mai tsiwa da surutu, gata ba'a kadata a himma. Kauɗinta yasa mafi yawan malamai saninta ga kuma ƙoƙari. Amma tunda ta dawo yanzu ta canjama kowa, magana ma saita zo har a tashi batai da wani ba. Kamar yanda malaman sukai mata uziri haka ɗaliban ma sukai mata, dan kowa yasan tana cikin yanayin da uzirin kawai tafi buƙata.
Duk wanda ya shigo yakan miƙa mata hannu su gaisa, itama babu musu take miƙawa tare da amsa sallamar da sukai mata. A haka har duk ɗaliban ajin suka kammala shigowa malamin farko ya shigo musu. Da farko ta nutsu wajen fara fahimtar darasin da yake musu, a hankali kuma tunaninta ya fara janyewa zuwa ga abinda taketa faman shiryawa da zuciyarta a kwanakin nan har malamin ya kammala ya fita babu abinda ta ɗauka. Haka na bayansa suka cigaba da shigowa basu darasi daban-daban, wani hankalinta na kai wani harya fita babu abinda zatace ta saurara. Ana tashi tana a ɗalibai sahun farko da suka fara fitowa, jitai kawai tana sha'awar yin tattaki da ƙafafunta yau, dan haka bata tsaya neman abun hawa ba ta miƙo titi da ƙafa ta fara tafiya kamar wasu tsirarun ɗalibai irinta da gidajensu ke kusa da makarantar. Tafiya tayi mai nisa sosai batare da nuna alamun gajiyawa ba, harta kusa isowa roundabout ɗin daya raba hanyar gidansu da ainahin titin hanyar masarauta daular ruman. Daga roundabout ɗin ana iya hango ƙaton tambarin ƙosashen zaki da akayisa da gold na tambarin Masarauta. Iffah taja wani kakkauran tsaki da ɗauke kanta zuciyarta na mata zafi. Harta kusa tsallakawa ta hango wata tsohuwa dake riƙe da wani yaro da Uniform a jikinsa da alama titin take so su tsallaka amma sunata inda-inda. Karan farko murmushi ya suɓuce mata ganin yanda yaron ke jan hanun tsohuwar sai sun tafi kamar zasu tsallaka saita fisgo yaron su dawo baya tana masifa. Sallama tai musu, tsohuwar ta amsa mata. Ta gaisheta da girmamawa tare da faɗin, “Ammi kuna so ku tsalla ne?”.
Amsawa tsohuwar tai da “Eh Ibnati ”.
Iffah ta sake murmusawa daga cikin niƙab ɗinta, kafin takai hannu ta riƙo na tsohuwar dake riƙe da yaron ita kuma. Suna gab da kaiwa tsakkiya yaron ya fisge hanunsa ya koma baya da gudu yana faɗin yabar abunsa a baya. Tsohuwar zata fisge itama tana masifa da kiran yaron ya dawo Iffah ta riƙeta gam suka karasa tsallakawa. “Ammi yi haƙuri barsa naje zan sake tsallako miki da shi. Rufe bakin Iffah yay dai-dai da taka wani bahagon birkin daya bada sautin ƙuuuuuu!!!. Sai sautin fitar ƙara mai razanarwa ta biyo bayansa.
Wani irin zabura Iffah tai na juyowa dan ƙarar har tsakkiyar kanta ta jita. Ai batama san sanda ta yaye niƙab ɗin fuskarta ba da waro manyan ƙyawawan idanunta waje gaba ɗaya ba tana mai ambaton sunan ALLAH ganin yaron nan tsaye cak a tsakkiyar titi hancin wata mota gab da shi allamar kaɗan ya hana ayi ɗanyen aiki. Kusan a tare suka isa kansa ita da tsohuwar data fashe da kuka da ƙwala kiran sunan yaron a matuƙar firgice.
Iffah da jikinta ke ɓari ta riƙo yaron jikinta tana duddubashi da sauke ajiyar zuciya a jajjere, ganin babu ko ƙwarzane a jikin nasa. Saurin sakin yaron tai ga tsohuwar tasha gaban motar ranta a ɓace ganin mai motar ko fitowa baiyiba ya ɗan leƙone kawai, ganin baima yaron komaiba ya maida kansa yanama ƙoƙarin barin wajen. A fusace ta buɗe murfin, ba saurayin daya kasance drivern motar ba hatta wanda ke gefensa hankalinsa akan lap-top dake saman cinyarsa sai da ya ɗago suka zuba mata idanu. Gaba ɗayansu ta haɗa ta dallama harara da manyan idanunta masu matuƙar haske tamkar madara.
“Kai malam baka san darajar mutane bane?....” Zazzaƙar muryarta mai taushi da nutsuwa a cikinta ta daki kunnuwansu cikin faɗa babu ko ɗigon tsoro a tare da ita. Batare data damu da yanda suka zuba mata ido ba ta murguɗa musu bakinta da sake dalla musu harara ta cigaba da masifarta, “Ka kusan bige yaro amma tsabar kanka ba'a daidai yake ba shine koka fito kaga yaya yake ma saboda ku masu kuɗin nan ɗaukar talaka kuke baida banbanci da titin da kuke gurza tayoyin banzayen motocinku da kuka saya da kuɗinmu”.
“Kai!”.
Drivern ya faɗa da maɗaukakin mamaki Iffah.
Harara ta sake dalla masa da zira hannunta ta zare key ɗin motar daya riga ya kashe tun ɓuɗe musu murfin da tayi.
“K! K! Dalla bani key kajimun fitsararriyar yarinya kinga mun taɓashi ne?”.
“Anƙi a bakun, wlhy duk sai kun fito kun dubashi kun bama kakarsa haƙuri zan baku key ɗin nan, inba hakaba sai dai mu kwana anan.”
Hannu saurayin ya kai da nufin warto key ɗin taja baya, sai dai duk da haka saida yaɗan taɓa skirt ɗinta kaɗan. Cikin matsanancin ɓacin rai ta jinjina yatsarta a kan fuskar matashin tamkar zata tsone masa ido. “Idan hanunka ya sake gigin taɓa koda hijjab ɗin jikina ne sai na karyashi, Sannan koda Shahanshan ne yay wannan aikin bai isa barin wajen nan ba balle kai shashasha driver”.
“K!!”.
Na gefensa ya faɗa cikin matuƙar waro idanu. A karan farko wanda ke hakimce zaune a sit ɗin bayansu lap-top a cinyarsa da tarin takardu a gefe da gefensa ya ɗago ƙyawawan idanunsa dake tattare da matsananciyar gajiya da ƙosawa yana yamutsa fuska. Baya ganin yarinyar, sai dai duk abinda take faɗa raɗam a kunensa zazzaƙar muryarta ke sauka. Baiko kalla yaran nasa ba ya sauke Lap-top ɗin dake cinyar tasa tare da kai hannu ya buɗe murfin. A tare suka zabura, sai dai kafin suyi wani yunƙuri harya fita a motar. Dolo suka fito suma da sauri...........✍
Leave a Comment