Daudar Gora Book 1 page 33


 *_33_*



.........Ƙarfe takwas da rabi dai-dai agogon ƙasar ɗaya daga cikin amintattun Hadiman dake gyara ɗakunan barcin na Tajwar ta iso cikin faɗuwar gaba hanunta ɗauke da akwati da aka kawo yanzun nan daga sashen Malikat Haseenat matsayin kayan da Iffah zatai amfani da shi. Zuciyarta har wani zallo take na fargabar abinda take da tabbacin

tozali da shi kamar yanda sukayi a baya ga sauran Zawjata-almilk da suka shuɗe. Ta tura ƙofar cikin sanɗa tana mai ambaton sallama da rawar harshe badan tana tunanin samun amsa ba. Ganin Iffah kwance a saman gado, lulluɓe da lallausan bargo baisa taji ƙwarin gwiwa ba. Tai yunƙurin ajiye akwatin hanunta, cak ta tsaya dukkanin idanunta na fitowa waje dan firgici ko sumar tsaye sakamakon juyi da Iffah tai alamar gyara kwanciya. Akwatin ta saki ƙasa ta shiga jan jikinta dake ɓari baya-baya harta dangane da ƙofa gab.....

     Iffah dake ƙoƙarin gyara bargo idanunta rufe ta buɗesu da sauri saboda jin ƙarar bigewar hadimar. Da mamakin jinta kamar a gado ya sata shashshafa hannunta. (Tabbas gadonne) ta ayyana a zuciyarta tana sake buɗe idanunta da ƙyau tana mai yunƙurin tashi zaune. Tuni hadimar nan ta sake firgicewa, da lalube ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fita a guje.  Kallon ƙofar Iffah tayi, sai dai hadimar ta gama ficewa bayanta kawai ta ɗan gani kaɗan da wulgawar mayafinta. da sauri ta yaye bargon da bata san ya akai yazo jikinta ba. Ta dire ƙasa mamakin duniya na cigaba da dabaibaye ta. “Wacece wadda ta fita? Mi tazo yi? Wai ta yaya ma na dawo saman gadon nan bayan a ƙasa na kwanta?”. Ta shiga jerama kanta tambayoyin da bata san inda zata samu amsarsu ba. Sai kuma ta ɗan kamo rigar jikinta ta kai hancinta. “Ya ALLAH, da gaske fa wannan mayataccen ƙamshin a jikina ne?”. Ta sake faɗa a fili tana sake shinshinar rigar......


       A ɓangaren jama'ar masarauta dake a zaman jigum-jigum kam fitar hadimar nan ya isar da saƙon Zawjata-almilk na raye. Da farko duk wanda zancen yaje kunensa ɗaukewar numfashi na wucin gadi ne ke riskarsa, sai kuma rashin gaskatawa a zahiri ya biyo baya. Hatta da Malikat Bushirat da Daneen Ammarah yanayi da ruɗanin jin hakan bai tsallakesu ba suma. A kusan tare suka ɗauka wayoyinsu domin neman Iffah ko zasu samu jin gaskiyar zance. Cikin Sa'a kuwa ta Daneen Ammarah ta fara shiga....


      Iffah na zaune har yanzu cikin ɗaurewar kai akan wanda ya maidata saman gado da wulƙawar fitar wadda bata sani ba wayarta ta katseta. Numfashi taja ta fesar da ɗan ƙarfi tana kai hannu akan wayar. *_Mamy_* ta gani rubuce ɓaro-ɓaro. Ganin zata katse tai ƙarfin halin ɗagawa ta kai kunne tana faɗin, “Assalamu alaikum. Amincin UBANGIJI da rahamar sa su yalwatu a gareki Mamy barka da safiya”.

      A matuƙar razani da motsuwar zuciya Daneen Ammarah taja numfashin dake neman ƙwace mata. “Ibnati!”. Ta ambata cikin son tabbatarwa.

     “Na'am Mamy”.

Iffah ta amsa kanta tsaye babu alamar irin fargabar dake harshen Daneen Ammarah ɗin a tattare da ita. Dan ita wanda ya ɗauketa daga ƙasa ya maida saman gado da fitar macen data ganine kawai damuwarta a yanzu. Daneen Ammarah da taji al'amarin tamkar a mafarki ta lumshe ido hawaye na silalo mata saman ƙyakykywar fuskarta a hankali. Ƙasa takai durƙushe tana mai godema UBANGIJI ta hayar kai goshinta ƙasa tai sujjadar shukur...


        Iffah da mamaki ta cigaba da ambaton “Hallo Mamy! Mamy kina jina kuwa?”. Shiru babu alamar za'a amsa. Yanke wayar tai da yunƙurin sake kira a zatonta matsalar network ce sai ga kiran Malikat Bushirat ya shigo shima. Ɗan jimm tai tana kallon wayar, sai kuma ta ɗaga takai kunne da sallama nan ma. Malikat Bushirat da idanunta ke cikowa da ƙwalla sakamakon jin muryar Iffah tar-tar a kunenta ta kai zaune tana ambaton sunan ALLAH. Iffah na son tambaya tana jin nauyi, sai kawai tai shiru tana sauraren kalmomin godiya ga ALLAH da Malikat Bushirat ɗin ke ambata daga can.

      (Ya rabbi! Wai mike faruwa ne haka?) Ta ayyana a zuciyarta da al'ajabi. Knocking ƙofa da akai ta hanyar danna alerm a dai-dai lokacin ya katse tunanin nata. Ta kai dubanta ga kofar babu alamar zata tanka har aka sake danna alerm ɗin sannan tai ƙarfin halin amsawa da bada umarnin shigowa tana gyara mayafin data yanama kanta.. Hadimar ɗazun ce dai ta shigo ɗauke da ƙaramin tray mai ɗauke da butar shayi. Kanta a ƙasa ta ajiye a inda ya dace tana mai zubewa ƙasa durkushe. “Amincin ALLAH da tsahon rai mai albarka su kasance tare da Zawjata-almilk Barka da safiya”.

      Iffah da ke kallonta ta amsa cikin motsa lips ɗinta kaɗan. Sabo da hakan yasa hadimar bata damu da rashin amsawar Iffah ba. Cikin sake rissinar da kai tace, “Ya Zawjata-almilk yanzu lokacin wankanki ne, bayan nan karin kummalo na jiranki tare da Shugabana”.

           Yanzu ɗin ma kamar Iffah bazata amsa ba sai kuma ta jinjina kanta. “Kije abinki zan fito”.

   “Umarninki shine abin jirana. Amma a gafarceni zan haɗa ruwan”.

      “Kije abinki zan yi komai da kaina”.

   Babu yanda hafimar ta iya dole ta miƙe domin bin umarni shine kawai huruminsu. Da kallo iffah ta bita abubuwa masu yawan gaske na son fara mata kutse a ƙwaƙwalwa da zuciya. Ƙwarin gwiwar da take bama kanta akan turesu ya sata miƙewa ta nufin toilet tana mai ambaton addu'ai a bakinta saboda tuna abinda taci karo da shi a daren jiya a toilet ɗin. 

     Ko'ina tsaf, kuma cikin ƙamshi irin na daren jiya. Sai da ta ƙarema komai kallo fiye da jiya kafin ta ɗage kafaɗa irin na koma miye ta shirya masa. Tsabagen rigima da wuce wuri ko tsageranci za'ace ta haɗa ruwanta mai ɗumi da zuba duk wani nau'in turaren wanka da aka jera domin Shahan-shan ta shige cikin kwamin wankan tai luf. Sai da taji ko'ina nata ya miƙe yanda take buƙata sannan ta fita a ruwan domin fara wanka...


      Tsaf ta kammala shirinta cikin doguwar rigar material sky blue da akaima ɗinkin daya fidda ainahin halittarta tamkar ƴar tsanar roba. Rigar ta zauna mata ɗas, siririn mayafin da aka haɗa rigar da shi ta naɗa tamkar yanda larabawa keyi, ta ɗakko after dress shara-shara mai kamar alƙyabba ta ɗora a sama kalar blue sosai. Ta ɗanji babu daɗi na rashin turarurrukanta tare da ita, dan ko waɗan nan kayan ganinsu kawai tai, cikin ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa a zahiri ta dinga kwasar turarrukan da taci karo da su a ɗakin cikin wani ƙyaƙykyawan glass dake kusa da mirror ta dinga zazzagama jikinta har sai da ta gamsu ƙarfin kamshin zai kai duk inda mai rai ke numfashi a sashen sannan ta haƙura. Idanunta ƙyam a mirrorn ta saki ƙayataccen murmushi da kanne ido ɗaya a fili ta furta “Irin wannan haɗuwa haka autar Ummu”. Tai salute ɗin kanta....


         Sautin ƙarar takun takalman ƙafarta da mayataccen ƙamshin tiraren da shi kaɗai aka sani da shi ya sashi tsayawa cak daga ƙoƙarin kai hannu a abincin da aka gama haɗawa gabansa. Fararen idanunsa tar-tar tamkar madara ya ɗago ya sauke a kanta. Hakama hadiman dake a tsaye ta gefe da gefensa kawunansu a ƙasa cikin yanayin mutuwar tsaye data rikesu suka zube ƙasa kan gwiyawunsu illahirin jikkunansu na ƙyarma akan dalilai guda biyu. Na farko ganin tabbatar da wadda suka gama fidda rai da jiran tsammanin ganin an shigo fidda gawarta tamkar Zawjata-almilk na baya dai na raye ɗin kamar yanda Hadimar ta gano. Na biyu ƙamshin turaren jikinta da ga mutum ɗaya tak ake iya jinsa a duk faɗin ƙasar ruman ma bawai a daular ruman ba...

     Tamkar Iffah bata fahimci halin da suke a ciki ba ta ƙaraso cikin katafaren falon batare data dubi ko ɗaya a cikinsu ba balle mai gayya mai aikin. Cikin sauri ɗaya daga cikin hadiman ya miƙe ya gyara mata kujera, zaune ta kai tana mai dubansa  a karo na farko. Tuni shi kuma ya maida kansa ga abinda yake yi tamkar bai san da zuwan tan ba. Ta taɓe baki da juya idanunta ta maida ga hadimar dake ƙoƙarin fara haɗa mata abincin. Nunin abinda take buƙata tai mata da ɗan yatsa. Hadimar na kammalawa ta koma cikin ƴan uwanta ta tsaya itama kanta a rirrine.

       Gaba ɗaya jinta take a takure, kwarjininsa ya cika ko'ina a falon. Cikin dakewa da kaucewa gizago sa ta ɗan ɗago ta ɗan saci kallonsa da nufin gaishesa idanunta suka shige cikin nasa da ya ɗago da nufin kallon nata...

     “Who are you?”

   Ya fara faɗa cikin basarwa yana kaɗa idanusa da har yanzu ke cikin nata tamkar bashi yay maganar ba. Badan a idanunta tausasan lips ɗinsa suka motsa wajen ambaton wacece itan ba zata iya gaddamar hakan. Kaifin idanunsa sun neman sage duk wani ƙwarin gwiwarta. Ƙoƙarin fara sassauta nata idanun tai yunƙurin yi cikin ƙanƙance su sannu a hankali. Shima sai ya kankance nasa kamar yanda takeyi, fuskarsa na sake tsukewa babu alamar sassauci tattare da ita. Nata ta fisga da ƙarfi ta lumshe su, sai kuma ta buɗe a kansa tana mai sake tsuke tata fuskar itama, bazata iya jure salon nasa ba dake neman ƙone ƙudirinta, dan haka ta kauda kanta gefe babu alamar zata bashi amsar da yay yunƙurin ji daga garetan..

      “Barka da safiya”.

   Ta faɗa a ƙoƙarinta na basar da tambayarsa ta farko.

     Bai motsa ba, babu alamar kuma zai amsa ta. Hakan sai ya sake sukar zuciyarta harta ɗan saci kallonsa, da sauri ta kauda idanunta, dan da gaske fuskarsa ruguza mata lissafi take, da gasken gaske shi ƙyaƙyƙyawa ne, irin ƙyawun dako a cikin ƙasar tasu ake yabawa da shi, koda yake batai mamakin hakan ba, dan Malikat Bushirat ba'a magana, duk da girma ya fara zuwa gareta tsantsar ƙyawunta a bayyane yake. Hakama Malikat Haseena dake matsayin kakarsa data haifi babansa tunda ita dai bataga baban nasaba ko'a hoto har yanzun, amma zubin Malikat Haseena dana Daneen Ammarah ya tabbatar mata shima ɗin dai zai kasance ƙyaƙyƙywan ne......

        “What is your goal in life?”. 

  Kalmomi guda shida suka katse mata tunani a bazata. Ta kallesa tana ƙoƙarin danne mamakinta kan waɗan nan tambayoyi da yake faman yanko mata kai tsaye. Ganin yanda ya zuba mata ƙasaitattun idanunsa masu firgita mara gaskiya ta janye nata tana yamutse fuska. (Damarki ce wannan) wata zuciya ta ayyana mata. Cike da gamsuwa ta sake kauda kai gefe dan har yanzu tanajin kaifin idanunsa a kanta. “Ni ban kasance kowa ba sai talakar dake a ƙarƙashin mulkinka ranka ya daɗe. Abinda nake son cimmawa kuwa a rayuwata irin abinda shugaba ke fatan cimmawa ga talakawan ƙasarsa ta hanyar mulkarsu da fuska biyu ne”.

      Yanda tai maganar kanta tsaye babu ko ɗar ya sashi jin mamakinta. (Tabbas wannan abar ba mutum bace) zuciyarsa ta tabbatar masa. A zahiri sai ya ɗauke kansa cike da basarwa. Shiru babu alamar zai sake tankawa har Iffah tama fidda rai ta cigaba da tsakurar abincinta kamar yanda yakeyi shima. 

      “Wasa da rayuwarki kuskurene ga ƙarfin halinki, ƙin kasancewar ki tarihi a wannan safiyar bashi ke tabbatar miki nasarar tsallakewa ba”.

      A yanzun kam zantukansa sun zama masu matuƙar tasiri a fitarsu da saurarensu gareta, jin bazata iya dannewa ba ta amsa batare data ɗago ta kallesa ba,

     “Hakane shugabana, sai dai fa _Fate is some thing undeniable”_ 

         Ya basar babu alamar yanzu ma zai amsa, shayin sa ya kai baki cike da ƙasaita. Itama sai bata sake cewa komai ba ta cigaba da cin abincin tana mai kallonsa ta gefen ido, sannu-sannu tabi sautin motsa plate ɗin gabansa da kallo har kan lallausan farar fatan hanunsa masu ɗauke da tsaftatattun fararen dogayen farce, baya tai ƙoƙarin jan jikinta batare data yarda idanunta sun wuce kallon hanun nasa ba. Yanda ya basar da ita ɗin kuma sai yay matuƙar sukar zuciyarta, dan bata buƙatar tattaunawar tasu ta tsaya iya haka. Amma sai bata yarda fuskarta ta nunaba. Sai ma mamakin ƙasaita da tsantsar izzar wannan bawa da zuciyarta ke faman yi. A wani ɓangaren ita kanta dakewa kawai take, amma kwarjininsa da gizago na firgita ta matuƙa. Tana ƙara tsarkake sunan ALLAH akan yarda da jinin mulki gaskiya ne. Duk da ta shigo daular ruman da wani ƙudiri a ranta hakan bazai hanata girmamashi ba, koda ace tayima yunƙurin hakan kwarjinsa bazai bata damar yin saɓanin girmamawar da kowa ke masan ba. So take taji tsanarsa a ranta kamar yanda takeji kafin ganin wannan fuskar matsayin shi amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai. Numfashi taja a hankali ta fesar a ƙasan maƙoshinta.

         “Kokawa da ƙaddara a fuskar iyawa na nufin faɗuwa! Kinga ko what you get is, what you have?”.

      Ya faɗa cikin katse mata tunani dai-dai yana ɗagowa.......✍️


     “Fareedatu kibar danginmu su tsinkayi yini da kwana cikin sallama, Banda taro dutsen zuma inake ina kace nace da dodon may...🥱🏇”.


No comments

Powered by Blogger.