Daudar Gora Book 1 page 31
*_31_*
.......Takun da baifi uku ba Kaka ya juyo ya bisa da kallo, kamar a bazata saurayin ya tsinkayi muryarsa na faɗin, “Jumna zanje”.
Yi yay tamkar bai jisa ba. Hakan yasa Kaka sake ɗaga murya amma ya cigaba da sharesa shima. Yana ƙoƙarin shiga motarsa Kaka daya biyosa a baya yace, “Haba ɗan nan baka jini bane?”.
“Sarai na jika Baba. Na fahimci ba tafiyar zakai ba, ba kuma hurimina bane tilastaka”.
A karan farko kaka ya saki murmushi. “ALLAH sarki, to ayima tsoho haƙuri ɗana”.
“Baba kamin laifin komai ba ALLAH, ai aikina ne. Dama naji kana sanarma wancan ne ni kuma hanyatace shiyyasa ma naje gareka. Zanje ƙauyen Yamanu ne dama”.
“A Alhamdullah, lallai hanyarmu ɗaya Bara na ɗakko kayana.”
Mutum biyu kawai saurayin ya ƙara ɗauka bayan kaka suka ɗauki hanya. Hakan baisa kaka ya ji wani zargi game da shi ba. Sai ma hira da suka dingayi kai kace sun san juna. Bayan sauke mutum biyun daya ɗakko har ƙofar gida ya kai Kaka. Yaji matuƙar jin daɗin wannan karamci dan haka yay masa tayin shiga ciki yasha ruwa. Saurayin ya ɗan nuna tirjewa amma Kaka ya janye ra'ayinsa a dole ya bisa suka shiga, sai dai dama a ransa hakan yake fata.
Ummu na zaune a tsakar gida ita da Iyyani, ta rame matuƙa tayi duhu irin na wanda ya shiga damuwa. Tamkar an sare gwiyawun Kaka ya ƙarasa shiga idanunsa akan Ummu data tsurama bayansa ido. Iyyani ma jiki a sanyaye ta miƙe dan tasan komai tunda kullum sai sunyi waya da Kaka. Itace tai ƙarfin halin masa sannu da zuwa. Ya amsa a sanyaye yana waiga bayansa.
“Yaro shigo mana”.
Kaka ya faɗa domin samawa Ummu nutsuwa. Da sallama saurayin ya shiga. Ummu tai ƙasa da kanta a hankali.
Bayan sun gama zama a tabarmar da Iyyani ta shimfiɗa musu saurayin ya fara gaishe da Ummu. Bata amsa ba, hakan ya sakashi shan jinin jikinsa yay shiru a sanyaye. Iyyani data sake kawo musu ruwa ce ta amsa masa da “Bata magana yaro”.
“ALLAH sarki” ya faɗa cikin sauke ajiyar zuciya ita ya gaisheta. Da kulawa ta amsa masa dukkan hankalinta a kan Kaka dake kallon Ummu tamkar ya samu television. Ummu da hawaye suka cikama ido ta miƙe a hankali, ɗaki ta shige duk suka bita da kallo. Kaka baice komai ba hakama Iyyani data zarce kitchen sai gata da kwanon abinci.......
★★... ★★★ ....★
Tamkar raƙumi da akala haka Iffah ke tafiya bisa jagorancin Malikat Haseenat. Kasancewar dare ne babu yawaitar hadimai masu hidima. Sai dai masu tsaro tako ina kai kace zasu iya kare ran wanda suke tsaye a dalilinsa daga ziyartar mutuwa. Tsirarun hadiman da suka samu nata zubewa kwasar gaisuwa, Malikat Haseenat ce kawai ke iya jinsu da ganinsu. Iffah dake ta faman sauke ajiyar zuciya da al'ajabin dukiyar dake narke a wannan gini ji take komai ya ƙwace mata. Ta kasa fasalta komai ta kasa auna komai a ma'aunin rinjayen aikin zuciya dana ƙwaƙwalwa....
“Bismillah”.
Malikat Haseenat ta katse mata ɗimuwar da take ciki ta hanyar nuna mata ɗaya daga cikin kujerun katafaren falon mai cike da abubuwan da bazasu lissafu ba. Da gaske Iffah bazata ma iya tantance yanda akai ƙafarta tazo nan ɗin ba.
Komai Malikat Haseenat batace ba, dan ta gama karance ɗimuwar dake jagorantar fitar numfashin Iffah. Amintattun Hadiman dake a falon na uku suka zube gaban Malikat Haseenat kawunansu a ƙasa. Hannu kawai ta iya ɗaga musu. Babu buƙatar sai ta faɗa abinda tazo dan shi, shugaban hadiman dake a wannan falon ya miƙe zuwa ga landline domin isar da saƙon zuwanta...
“Tsahon rai da lafiya su tabbata ga Uwa a garemu, shugaban na tsumayen isarku a falon sama”.
Shiru malikat Haseenat batace komai ba. Yayinda Iffah da zuciyarta ke luguden ke saurarensu cikin juyewar tunaninta da har yanzu bai dawo dai-dai ba. Kusan mintuna uku Malikat Haseenat taima Iffah nuni data miƙe, ita kuma ta birka wheelchair ɗinta suka shiga lifter. Mintuna biyu ne kacal suka iso da su katafaren falon da yafi kowane falo ƙawatuwa a kaf daular ma da sashen kawai ba. Iffah tai ƙoƙarin danne harbawar ƙirjinta sakamakon tozali da wanda ke zaune a falon cikin zama na ƙasaita da izzar masu mulki. Tafiya take tamkar hawainiya saboda tsabar kasala da sanyin gaɓɓai. Zuwa yanzu wannan fuskar bata aljani take fassarata ba, neman ƙarin bayani take a kanta a dalilin ganinta a waje biyu da basu da alaƙa da juna a zahirin rayuwa...
Tajwar Eshaan da ke kishingiɗe bisa ƙayataccen kujera mai kama da wani madaidaicin gado gabansa butar shayi ce da ƙaramin kofin da alamu suka nuna yasha ko zai sha, idanunsa ya janye daga kan television da yake kallo ya ɗan waigo garesu. Akan Iffah dake tafiya tamkar hawainiya ya fara saukewa, fuskarta a sakaye take, hanunta dake riƙe da rigar jikinta ne ta ƙasa kawai a bayyane. Janye wa yay ya maida ga Malikat Haseenat. Ta ɗan hararesa da salon kulawa da nuna damuwa. Idanun ya janye a sannu daga kanta itama yana sakin kasaitaccen murmushi....
Harya gama gaisawa da kakar tasa a yanda yake kishingiɗe batare da ya motsa ba Iffah na tsaye ƙyam tamkar an dasata. Malikat Haseenat ta maida kallonta gareta tare da ambatar sunanta. A dake Iffah ta amsa dan tayi alƙawari ma kanta bazata taɓa barin rauninta sake bayyana ga kowa ba a yanzun. Kafinma Malikat ta sake cewa wani abu tai ƙasa a hankali, cikin rashin ƙwarin jiki ta zube ƙasan lallausan carpet ɗin da ko jikin zomo bazai nuna masa laushi ba. Ƙamshi ko ba'a magana dan ko'anan ake shukashi iyaka kenan.
“Amincin ALLAH ya tabbata a gareka”.
Ta faɗa badan har zuciyarta abinda take son faɗar kenan ba. Sai dai kwarjininsa daya mamaye falon da duk girmansa take jinta a matse yaƙi bata damar fitar jin zafinsa dake a ƙasan zuciyarta a zahiri. Kamar a waccan ranar yau ma bai amsa ba, babu ma alamar yajita tattare da shi. Daga cikin hular alkyabbar jikinta ta cije lips ɗinta da masifar ƙarfi tamkar zata hudasu da haƙori.....
“Ai ma Zawjata-almilk rakkiya ɗakin da Tajwar zaiyi barci a yau”.
Furucin Malikat Haseenat ga hadiman dake rakuɓe gefe zube a ƙasa kawunansu rissine tun shugowarsu ya nema sarƙe numfashin Iffah da Tajwar Eshaan a lokaci guda. Babu wanda Malikat Haseenat ta kalla a cikinsu sai ɗaya daga cikin Hadiman ce da suke girki ta miƙe da rawar jiki zuwa inda Iffah take. Dole ta mike dan a furucin Malikat Haseenat babu wasa ko ɗaukar turjiya ga kowannensu....
Shiru falon babu wanda ya sake ƙwaƙwƙwaran motsi har hadimar data raka Iffah iyakar ƙofar ɗakin ta dawo Malikat Haseenat ta sallamesu. Da ga shi sai ita suka rage, dan haka ya kafeta da idanunsa. Kai Malikat Haseenat ta ɗauke gefe tamkar bata gansa ba ko fahimtar kallon.
“Anan zata zauna, sai ka zaɓi inda kake buƙatar ta kasance har tsahon sati ɗaya, dan zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu masu mata hidima zasu kasance tare da ita. Na damƙa amanarta a hannunka, ina kuma fatan ta kasance ƙarƙashin kariyar UBANGIJI. Fatan alkairi da shiga sabuwar rayuwa, tare da tayaka murnar sabon aure. Na barku cikin amincin ALLAH”.
Da alama gushewar numfashi da rikicin wannan tsohuwa ya gama daskarar da jinin Shahan-shan. Dan harta fice a falon ko gashin idonsa bai ƙyafta ba, kai kace wani butun butumine aka dasa a wajen domin tarihi.......
(🤔Tsohuwar nan kuwa na lafiya? Zata kai mana Iffah har ƙuryar Dodon Mayu🥱🤦).
★★... ★★....
Duk da dare ne gaba ɗaya masarautar ta ɗauki ɗumi bisa wannan bahagon hukunci na Malikat Haseenat. Basu da al'amarin yazoma a bazata ba, hatta Malikat Bushirat da Daneen Ammarah da Jasrah da akai zaman da su komai ya musu cak. Abinda suka sani kawai komawar Iffah sashenta, bawai kaita turakar Shahan-shan ba. Miyasa Malikat Haseenat ta canja lissafin a kan kansu suma?. Wannan itace tambayar daketa musu kaikawo su duka.
“Ni kam dai a wannan gaɓar na kasa gane komai wlhy Akia. Shin minene dalilin Mamma nayin haka? Miyasa lissafin ya canja daga yanda muka tsara gaba ɗaya?”.
Kamar malikat Bushirat bazata tanka har ta kai ta kawo kusan sau uku kafin ta dubi Jasrah mai maganar. “Kaina ya kulle Jasrah”. Ta faɗa a takaice da kaiwa zaune bakin gadon ta dafe kanta.
“Ya ALLAH! Wlhy zuciyata ta fara kai ni ga hasashen wani abu daban?”. Jasrah ta sake faɗa tana dafe nata kan itama.
★
A ɓangaren Daneen Ammarah ma dai a rikicen take. Sai dai ita nata lissafin yasha banban da nasu Malikat Haseenat. Daga ɗakin taro bedroom ɗin Malikat Haseenat ta wuce zaman jiranta. A zaman da bai wuce mintuna arba'in ba kuwa sai gata. Kallo ɗaya taimata ta ɗauke kai. Hadimar dake biye da ita ta ajiye madarar hanunta da zubewa ƙasa tana gaida Daneen Ammarah. Hannu kawai ta ɗaga mata....
“Na matuƙar gajiya, kwanciya kawai nafi buƙata”. Malikat Haseenat ta faɗa tana wulla kekenta hanyar bathroom ɗinta batare data sake kallon Daneen Ammarah ba. Da kallo ta bita cikin shakku da shan jinin jiki. Dan duk da a dunƙule tai magana tana nufin bata bukatarta a ɗakin kenan. Jiki a sanyaye ta miƙe ta fice zuciyarta na faman tsalle-tsalle...
Duk yanda taso kwanciya ta kasa hakan, fargaba da tausayin Iffah ne ke matukar ɗawainiya da ita. Har cikin zuciya bata son rasa yarinyar dan ta matuƙar shiga ranta. Soyayya take mata irin ta ƴa da uwa. Ita kanta har takanyi mamakin yanda takejin Iffah a rai matuƙa, amma tasan wannan ƙaunar daga ALLAH ne kawai. Wayar dake a hannunta ta ƙara rumtsewa, ta gwada kiran Iffah ya kai sau huɗu kenan amma tana fasawa, so take taji lafiyarta ko zata samu ƴar nutsuwa, amma wata zuciya na gargaɗarta da kalmar rashin dacewa....
★★.....
“Mi wannan tsohuwar ke nufi wai shin? Ko itace abin neman mu kamar yanda barbushi ya sanar mana?”.
Miran Arshaan yaja numfashi ya fesar, kamar bazaice komai ba sai kuma ya kafe Miran Jasim da kallo yana girgiza kai. “Wlhy kaina ya kwance Jasim Akhi. Na kasa gane komai a wannan gaɓar, abinda na sani kawai shine mutuwar yarinyar nan a wannan gaɓar tamkar mutuwar cikar birinmu ce, dan na gama ɗora dukkan hope ɗinmu a kantane. Bai kamata ta mutu a yanzu ba har sai ta ƙarasa mana aikin da muka kwashi tsahon shekaru muna ginawa”.
“Miye mafita?”.
Cewar Miran Jasim a firgice, dan zantukan Arshaan ɗin kamar sun zaburar da shi ne abinda ke gabansu. Kai tsaye Miran Arshaan yace, “Ziyartar Barbushi a wannan daren, kafin waccan sankaran matar da ban san amfaninta a tafiyarmu ba tazo ta ishemu da tsarin banza”.
“Hakan yayi mun, babu amfanin ɓata lokaci kaje kayi shiri”.
Kai Miran Arshaan ya gyaɗa masa, tare da mikewa ya fice. Da banzan kallo Miran Jasim ya bisa, cikin ƙanƙance idanu da wani shu'umin murmushi a fuskarsa “Ba matar can bace kawai abin banza a cikinmu, har da kai Arshaan, daka gama mun amfani zan kawar da kai, dan ni kaɗai nake son mulkar daular ruman batare da ɗan uba ko ɗaya ba da zai zame min abokin gaba, nasan idan har na barka kaima zaka zamemin maƙiyi dan burinka wannan kujerar ne na sani shashasha”...
(🥱Waɗan nan mutane dai to bara nayi shiru dai🤫)
*_ZAWJATA-ALMILK_*
Duk da akwai wani ɗan ɓurɓushin tsoro a ƙasan zuciyar Iffah ta matuƙar dakewa da addu'a ta shiga ɗakin bayan ta gama ƙarema bangon dogon corridor ɗin da suka biyo kallo, ta jinjina kai cikin jin matuƙar ƙuna da tausayin talakawan ƙasan ruman baki ɗaya. Tayi imanin akwai dubbunan mutane dake barci akan titi cikin yinwa da ƙishirwa da yawa. Amma abin mamaki yau ga bangon ɗakin barcin Shahan-shan yasha ado da zinari matsayin fenti, “Taya ma imani zai zauna a zuciyar mutanen nan har su ɗauka rai wani abun mai daraja?” ta faɗa a zahiri idanunta na cika da ƙwallar baƙin ciki da ƙara jin tsanar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed..........✍️
(😭Hikenan Iffahr mu an shigo ɗakin mutuwa😱🙆).
Ko miye dalilin Malikat Haseenat na kai Iffah turakar Shahan-shan kai tsaye haka? Miye dalilinta na canja abinda suka tattauna da su Malikat Bushirat? Shin ko dai malikat Haseenat ce T....😱🤫🤭?.
Yaya zata kasance tsakanin Iffah da Shahan-shan ne? Ta wani ɓangaren abinda ke kashe Zawjata-almilk kuna ganin zai ƙyale rayuwar Iffah a wannan dare kuwa?.
Gadai wasu ɓoyayyun maƙiya na sake fitowa. Irinsu Miran Arshaan (mijin Jasrah kuma ƙani ga Tajwar Haysam) da Miran Jasim (shima ƙani ga Tajwar Haysam). Shin wacece wai matar nan da suketa a ambata batare da sunanta ba?.
Hhhh tabbas yanzu ne wasan zai fara. Sai ku shirya ku sake shiri dan sai a yanzu ne muka kalmashe bakin shimfiɗar labarin dake cikin littafin DAUƊAR GORA... Wasan na asali yanzu ne filin yinsa ya kammala. Masoya sai mu antaya kawai😉🥱🏇🏇🏇🏇.
Leave a Comment