Daudar Gora Book 1 page 24
24_*
..........Komai daya faru tsakanin Iffah da Hadima Banou akan idon Daneen Ammarah ne, dan itama tayi yunƙurin fitowar ne ganin Banou na tono a bayan windown Mamman sai ta hango Iffah na tahowa. Kasancewar ta ganta da rigar jikinta a ɗazun yasa kai tsaye ta ganeta. Da farko gabantane ya fara faɗuwa da tunani iri-iri, shiyyasa ta tsaya domin
ganema idanunta. Sai dai kalaman Iffah da yanayin Hadima Banou ɗin ya sata shiga ruɗanin tunani. Idan har zata auna da hankalinta matsayin babba itama Iffah taga Hadima Banou ne shiyyasa ta fito, a yanayin Banou kuma ya nuna akwai wani ɓoyayyen al'amari na rashin gaskiya tattare da ita. To amma su maiyasa a tsahon shekaru basu taɓa ganin wannan fuskar ta Banou ɗin ba? Wacece Iffah? Anya kuwa ba akwai abinda ya kamata ta sani dangane da yarinyar nan ba?......★Iffah da al'amarin wannan masarauta ya fara ruɗama tunani tana shiga ɗakin dake matsayin nata yanzu ta murza key. A jikin ƙofar ta jingina da lumshe idanunta tana sauke numfashi. Ita kanta taga ƙarfin halinta yau, dan zata iya rantsewa bata san a ina ta samo wannan jarumtar ba. Idanun ta buɗe tare da riƙe ƙugu ta karyar da kai alamar nazari. In fa har ta canka dai-dai tabbas wannan hadimar mayya ce. Dan bata manta da wani labari da Iyyani ta taɓa basu ba na mayya yar Danƙo datai zamani a kauyen jumna shekarun baya. Babu banbanci da abinda taga matar nan tayi yanzu, dan da alama kurwar wani ta laso tazo ta boye a wajen. “Bahun ubancan, eh da gaske dai ashe lamushe ƴaƴan mutane ake a masarautar nan tunda ga alama harda su bayi an barbaɗa musu muguwar tambaya. Shi baƙin babban dodon nasu nacinye mutanen gari su kuma bayi nacinye junansu a cikin gida”. Tai maganar a fili cikin ƙankance idanu na alamar tunzuruwa...
Murmushi Daneen Ammarah dake bakin ƙofa tsaye ta saki, dan nutsuwar da zuciyarta ta kasa mata ya sata biyo bayan Iffah, har ta kai hannu zatai knoking sai kuma ta fasa da tunanin inhar Iffah nada wani mugun nufi a kansu to baro can zata samu wani abun take aikatawa a yanzu. Dan haka ta ɗan kara kunenta kaɗan jikin ƙofar, cikin Sa'a kuwa ta jiyo mi Iffah ta faɗa saboda yanda tai maganar da ɗan zafi sai ta fita da ɗan karfi kaɗan. Ƙofar ta fasa bugawa ta koma ɗakinta da baya. Itama dai ƙofar tata ta sanyama key duk da tasan babu wanda zai shigo mata. Kai tsaye wadrob ɗin ta ta nufa, a cikin wani akwatin ƙarfe karami mai ƙyau ta fiddo waya bayan ta danna madannan sirri ya buɗe. Wayar ta shiga ƙoƙarin kunnawa tana mai rufo windows ɗin ɗakin nata. Sai da tai danne-danne kusan na mintuna biyu alamar text ta tura. Kira ne ya shigo, sai a ring ɗin karshe ta ɗaga, batare da jiran wani gaisuwa daga wancan ba cikin bada umarni tace,
“Daga yanzu zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu ina buƙatar sanin komai akan Zawjata-almilk ta uku. Idan nace komai yana nufin komai da komai”. Kitt ta yanke kiran tana wani irin murmushi tun kan ma ta samu amsar data bukaci sani. Wayar ta kashe gaba ɗaya ta sake maidata inda ta dakkota......
(🤔Wai su kowa da tasa manufar ne????)
*_MALIKAT BUSHIRAT_*
Zaune take hakimce kamar ko yaushe cikin kwalliya mai matukar ɗaukar idanu. Ga wani sihirtaccen ƙamshi mai ratsa zuciyar duk wani mai shaƙa na tashi. Shi kansa falon kamshinsa na musamman ne. Gefenta na dama Jasrah ce itama cikin kwalliyar, zuwanta kenan sashen sakamakon aiken data samu daga ƴar uwar tata. (Itama dai Jasrah anan cikin masarautar take aure, tana kuma auren ƙanin marigayi Tajwar Haysam ne da suke uba ɗaya. Dan kamar yanda Tajwar Haysam suke su huɗu a ɗakinsu suna kuma da ƴan uba har su kusan tara, sai dai mata sunfi yawa a ciki. Su tarannan kuma ƴaƴan mata uku ne. Mijin Jasrah shine babba a cikin ƴaƴan amaryar Tajwar Haysam da ake kira Ameera Aasfah a masarautar. Mace ce mai kirki da sanin ya kamata, jininsu kuma yay matuƙar haɗuwa da Malikat Haseena. Dan idan ka gansu bazaka taɓa ɗauka kishiyoyi bane a sanda tana raye. Yaranta biyune ita kacal, Miran Arshaan shine babba, shine kuma ɗa na takwas a wajen Tajwar Abdul-majeed, a maza kuma na uku, shine mijin Jasrah a yanzu, sai ƙanwarsa Daneen Fu'ada, a yanzu haka tana aure itama. Ƙaunar dake tsakanin Malikat Haseena da Ameera Aasfah yasa shaƙuwa sosai a tsakanin ƴaƴansu, hakan yasa Tajwar Haysam ke kallon Miran Arshaan tamkar ƙaninsa Miran Nayyar daya rasa, shine ma da kansa ya aura masa Jasrah. Wannan kenan, ALLAH yasa kun gane🥱).
“Akia kince nazo amma kin kasa cewa komai? Wani abun ya sake faruwa ne?”.
Numfashi Malikat Bushirat ta sauke a hankali tana kallon ƴar uwar tata da takema kallo tamkar first born ɗin ta. Kamar bazatai magana ba sai kuma ta nisa cike da kasaita. “Komai bai sake faruwa ba, sai dai ina gudun sake faruwar. Sanin kanki ne Jasrah ba lallai kosu waye su haƙura ba dan yarinyar nan ta kuɓuta a yanzun, sannan ma bayan ita akwai sauran yaran biyu da har yanzu fargaba ta hanamu kaisu turakar Saifulmalik. Kin san kuma rashin kai su zuwa nan da ɗan lokaci sai kinji an fara kace-nace”.
“Hakane Akia. Amma ke mikike son cewa?”.
“Zancen dai ɗaya ne shine inajin tsoro, na biyu kuma da gaske yarinyar nan ta shiga raina fiye da duk matan da aka kawo gidan nan matsayin Zawjata-almilk”.
“Wlhy nima har cikin rai yarinyar ta shiga raina. Gata da tarbiyya daga ganinta, sannan itace mafi ƙanƙanta a duk matan na Son”.
“Wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya sake jan hankalina a kanta Jasrah, shiyyasa yanzu da wani tunani yazo min nace bara nai shawara da ke. Shin kina ganin naima Mamma (Malikat Haseena) magana gobe idan ALLAH ya kaimu da Saifulmalik zaije gaisheta a kusanta shi da yarinyar nan suga juna? Sai nake ganin hakan zai canja wani babban al'amari da masu mana yankan baya ke ƙullawa. Tunda kinga dai duk matansa sai an kaisu turaka yake da damar ganinsu kamar yanda kowa yasan dokar kenan ga duk Zawjata-almilk tun ƙarnin baya”.
“Eh gaskiya kuma wannan tunani ne mai ƙyau Akia inhar Mamma zata amince ɗin. Dan Kinga muma a karan kammu wata hanya ce da zamu fuskanci wani abu akan shi kansa..”
“Wannan gaskiya ne. Dan da gaske Jasrah a yanzu har shi kansa zuciyata rawa take ga al'amarinsa, dan abinda ke faruwa dole ne kowa ya zama abin zargi har mu kammu, ke nama takaice miki zance ni kaina yanzu ban yarda da kaina ba”.
Murmushi Jasrah tai har haƙoranta na bayyana. Tace, “Kai Akia kinada abin dariya wlhy wani lokacin. To inke baki yarda da kanki ba mu kuma dawa zamu yarda kenan?. Kawai dai inaji a jikina koma minene ya kusa zuwa ƙarshe ta silar yarinyar nan tunda har ALLAH ya fara nuna musu iyakarsu suka gaza cin nasara a harin farko da suka kai mata. Yanzu dai bamu da lokaci, ki tattauna da Mamma ɗin kawai. Hukuncin data yanke sai mu karɓa kawai”.
Malikat Bushirat ta jinjina kai kaunar ƴar uwar tata na sake ratsata. Koba komai idan ta tattauna da ita takanji sanyi a ranta.......
★★.... ★.... ★★.....
“Wai nikam ɗazu ina ƙoƙarin shiga fada naga kamar motarki ta gitta, kinje wani waje ne?”.
Shayin da take ƙoƙarin zuba masa ta karasa tare da miƙa masa. Sai da ya amsa ta koma ta zauna tana mai ɗan ɗage kafaɗunta. “Kaima kasan fita ta bata wuce wajen Akia ai Abu Harith, wlhy itace fa tai min kiran gaggawa shine ka ganni na fitan. Amma lafiya kuwa har irin wannan lokacin kuna a fada?”.
“Uhm to lafiya lau za'ace, anyi baƙin bazata ne kawai ga Shahan-shan ya rigada ya shige kuma. Dole mu mukai zaman tarbarsu. Amma kiran gaggawa wata matsalar ne ta sake faruwa? Ko jikin Zawjata-almilk ɗinne dai?”.
“No akan dai wadda ake cikine. Jikinta kuma Alhamdullah, idan ma ka ganta yanzu bazakace wani abu ya faru ba. Kawai dai Akia ce ke ganin ya kamata idan Shahan-shan yaje gaida Mamma gobe idan ALLAH ya kaimu Zawjata-almilk ta ziyarcesa ko hakan zai kawo wani sauyi kan abinda har yanzu muka kasa sanin kansa”.
“Amma baƙwa ganin hakan wani ganganci ne? Sannan dokace fa Shahan-shan baya ganin matansa sai a turaka”.
“Eh muma mun duba wannan ɗin, dan haka ma bamu wani yanke shawara ba akace sai an sanarma Mamma. Amma kai ya kake gani akan hakan. Abu Harith wlhy Akia na bani tausayi matuƙa, a yanzu har takai da kanta itama zarginsa take shi yake ɓarnar nan”.
“Ya ALLAH wannan wace irin magana ce haka? Miyasa zatai irin wannan tunanin akan ɗanta. Bana jin Eshaan zai taɓa aikata makamancin hakan. Kawai dai akwai abinda yake ba daidai ba”.
“Sosai kuwa. Amma insha ALLAHU ta sanadin yarinyar nan kowa sai yaci ƙaniyarsa. Dan haka kawai nakeji a jikina ita ɗin haske ce a wannan daula. Tunda har gashi ta karya tarihin farko na azzalumai”.
“Haka muke fata, dan muma an tattauna akan hakan sosai jiya da yau a fada. Kusanma issue ɗin da ake kai kenan kawai yanzu a majalissa. Sai na kisan hadiman can”.
“To ALLAH ya dafa mana mu da ku, ya kaimu ranar da zamu ga iyakar wannan al'amari”.
“Amin my meera”.
Yay maganar da wani salon kashe ido mai cike da soyayya da kaunarta. Murmushi tayi itama tana miƙewa, “Bara na kimtsa kafin ka kammala ko”.
Kai ya gyaɗa mata idanunsa narke a kanta.. Tana juya baya ya bita da wani irin matsiyacin kallo mai ma'anoni da yawan gaske yana tsuke fuska da jan tsaki......
🤦Jasrah kamar yanda ƴar uwarki ta faɗa miki kowa ba abin yarda bane yanzu🧐.
★★.... ★★.....
Kamar yanda Malikat Bushirat suka tattauna da Jasrah batai ƙasa a gwiwa ba tana idar da sallar asuba ta fita daga sashenta cikin badda kama zuwa sashen Malikat Haseena. Kasancewar ta sanarma Daneen Ammarah tare suka nufi ɗakin Malikat Haseena ɗin. Itama tasan da zuwan Malikat Bushirat ɗin. Dan haka basu ɓata lokaci ba suka fara tattaunawa dan ta samu ta koma kafin gari yay haske. Da farko dai malikat Haseena ta kakkawo musu dokokin masarautar masu tsari dangane da haɗa Shahan-shan da Zawjata-almilk kai tsaye ba'a turakarsa ba. Sai dai bayanin da sukai mata da nusar da ita abinda suke son tabbatarwa yasa itama ta amince. Sai dai da sharaɗin komi ya biyo bayan hakan laifinsu zata gani. Cike da yaƙinin fatan karma wani abu ya faru suka amince. Dan haka tai musu sallama ta koma. Daneen Ammarah da tunaninta nada banbanci da na Malikat Bushirat akan wannan haɗuwa tai murmushi a ranta tana mai addu'ar samun nasara. Domin wannan yaƙi kamar natane ita kaɗai sakamakon itace kawai tasan ɓoyayyen sirrin daba kowa ya sani ba sai UBANGIJIN talikai. Fatanta shine komai yazam yana gangarowane ga faɗan karshe akan maƙiya koda ita zata rasa rayuwartane a yayin gumurzun...
(Daneen Ammarah kin fara bani tsoro fa🧐😞).
*_SHAHAN-SHAN_*
Yau ɗin ce dai ta kasance rana da yake zuwa gaishe da kakarsa Malikat Haseenah. Irin wannan rana kuma tana zuwane sau ɗaya a kowanne wata. Sai dai idan ita ke buƙatar ganinsa ta samesa a sashensa. Amma a kowane wata yanada ranaku biyu na ziyartar kakar tasa da mahaifiyarsa. Malikat Haseena yake fara dubawa a farkon wata, Malikat Bushirat a tsakkiyar wata. Duk da fitace ta dare da ba lallai kowa ya gansa ba ya kasance cikin shiri mai ɓoye ainahinsa, ga wani ƙamshi na isassun da suka isa na tashi tattare da shi. Takunsa da ƙarfin izzarsa ya isa tabbatar maka eh lallai Shahan-shan ne da kansa. Ƙasaita jinin jikinsa ce, kamewa da isa adonsa ce, kwarjini da nutsuwa halittarsa ce....
Duk da farkon dare ne dan kwata-kwata ƙarfe takwas ne, amma masarautar tayi tsit kowa ya nutsu a inda ya dace saboda sanin wannan rana ce da Shahan-shan ke fitowa zuwa sashen Malikat Bushirat. Babu wani Hadimi dake kai kawo sai Ghazi da masu tsaro da suka tsare ko'ina fiye da kullum. Hakama sauran jama'a in ba babba mai faɗa aji ba babu wanda keda hurumin wani kaikawo a irin wannan daren dake zuwa a wannan rana saboda fitowar Shahan-shan...........✍️
Leave a Comment