Daudar Gora Book 1 page 23


*_23_*


........Itama ɗin dai switch up. Wasu zafafan hawaye suka silalo a kumatun ta. Ƙoƙarin sake kiran waccan number ta gwadayi knoking ƙofar da akai ya katseta. Da sauri ta yanke kiran da kashe wayar ma baki ɗaya ta ɗaga gadon ta tusasu har da takardar gaba ɗaya sannan ta sauka dan tasan bazai wuce Daneen Ammarah ba...

      “Ibnati baki barci ba kenan?”.

   Kan Iffah a ƙasa tai ɗan murmushi. “Yanzu zanyi Mamy karatu na kammala”.

    “Masha ALLAH, ya kamata ki kwanta to dare yaja, nima zuwa zanje na kwanta”.

  “To Mamy ALLAH ya tashemu lafiya”.  

        Koda Daneen Ammarah ta wuce Iffah ba kwanciyar tai ba, sake ɗakko wayar tayi ta cigaba da neman wancan layin da a yanzu ake cemata not available saɓanin switch up na ɗazun. Hakama number Malam Fawzan har yanzun. Daga ƙarshe dai barci ɓarawo gwanin iya sata ne ya saceta akan dole ta haƙura, sai da asuba ta tsinta wayar a ƙasa yashe....


        Yau dai kam ta ƙudiri niyyar fita gaida tsohuwa Malikat Haseena da kanta, tunda dai jikinta Alhamdullah hatta saɓar ma sai inda ba'a rasa bane bai gama ba. Bayan hadimar dake gyara ɗakin ta kammala ta fita key ta sama ƙofar sannan ta shiga wanka. Dan duk da tausayin hadiman da takeji a yanzu batajin zata sake yarda da waninsu. Ta fito tana tsaka da shiryawa cikin ɗaya daga kayanta na gida akai knoking. Karasa saka abayar tayi sannan taje ta buɗe, a tare suka sakarma juna murmushi, tai ƙasa da kanta tana faɗin, “Barka da safiya Mamy”.

      Daneen Ammarah takai hannu ta taɓa kanta da faɗin, “Kin tashi lafiya?”.

    “Alhamdullah”.

“Haka ake so. Ga kayanki nan na amfanin yau, mun zaɓi yin hakane saboda gudun abinda zai iya zuwa ya dawo Ibnati, amma insha ALLAH kayanki na amfani na gab da kammaluwa, saiki shirya ni zanje sashen Umm Jasrah. Ki tabbatar kinci abinci sosai yanzu zan dawo ba jimawa zanyi ba”.

     “Adawo lafiya Mamy a gaisheta”.

  “Zataji, amma ki tabbatar kin canja waɗan nan kayan”.

  Kai kawai Iffah ta jinjina mata. Amma a ranta tana mamakin minene aibun abayar tata? Tana cikin sabbin kayantama da take matuƙar ji da su. Shigowar hadimai biyu da kayayyaki ya katse mata mitar tata, sai dai batace komai ba bayan amsa musu gaisuwa. Fita ɗayar tai aka barta da wadda tafi yawan kasancewa da ita, tazo gabanta ta zube kanta a rissine. “Ya Zawjata-almilki bisa umarninki za'a shirya kayan”.

      Karo na biyu Iffah ta amsa neman izini da umarni ga hadimai a gidan. “Ba yanzu ba, zaki mun rakkiya ga Mamma ne, ki jirani a waje”.

    “Umarninki shi nake zaman jira ya Zawjata-almilki”.

    Hadimar na fita ta taka inda kayan suke tana dubawa. Tunda ta samu lafiya kullum da safe za'a kawo mata kaya kala uku, washe gari za'a kwashesu koda daya kawai ta saka a sake ajiye mata wasu. Da farko ta ɗauka ko haka tsarin masarautar yake. Sai a yau bayanin Daneen Ammarah yasa ta fahimci ita akema hakan saboda tsaro. Waɗanda ranta yafi kwantawa da su ta dauka ta saka. Ta koyi ƙyau sosai musamman da suka kasance bakake da adon stones masu sheƙi da ɗaukar idanu. Ga farar fatarta data koma ja ƙaɗan saboda saɓar datai tamkar ta larabawa ta sake fitowa. Ɓoyayyun turarenta na wajen Kaka ta ɗakko ta saka, wani irin ƙamshi mai daɗi da saka zuciya nutsuwa ya fara ratsa ɗakin...


    Sosai murmushi ya bayyana a fuskar tsohuwa Malikat Haseena saboda ganin Iffah akan kafafunta, takuma ji daɗin wannan ziyarar bazata data kawo mata duk da kuwa suna a sashe ɗaya ne. Iffah data kai zaune gefenta bisa tattausar dardumar da aka ƙawata falon da shi ta risinar da kai tana gaisheta da tambayarta yaya jiki?.

     “Alhamdullahi ƴar albarka. Yaya naki jikin?”. Malikat Haseena ta amsa da kulawa har yanzu murmushi ƙawace da fuskarta. 

  “Naji sauƙi ai Mamma” (kamar yanda taji Daneen Ammarah na kiranta.

        “To Alhamdullah ALLAH ya ƙara kiyaye gaba”.

   Da amin duk hadiman wajen suka amsa. Malikat Haseena sallamar duk Hadiman tayi, tare da bada umarnin a shirya mata breakfast da Iffah. Hakan ya bama hadiman mamaki sosai, dan duk wanda Malikat Haseena zata buƙaci zaman cin abinci da shi ba karamin mai sa'a bane ba. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa aka kammala shirya komai, ita dai Iffah na kallon ikon ALLAH da tsagwaron mulki wajen wannan tsohuwa. A ranta kam tunani take shin wai idan haka matan suke waishi babban dodon nasu yaya za'a gansa kenan?. Bisa umarnin Malikat Haseena Iffah ta mike suka nufi wajen da aka shirya abincin. Zamansu dai-dai da shigowar amintacciyar hadimar Malikat ɗin ɗauke da wani ƙaramin kwano...

     Shigar ƙamshin turaren Iffah hancin Hadima Banou ya saka jikinta fara tsuma. Hanunta na ɗan rawa ta sunkiya zata ajiye kwanon suka haɗa ido da Iffah. Zabura tayi da sauri ta miƙe kanta a sunkuye. Iffah ma dake jin jikinta na wani irin yamutsawa ta sake kallonta da kyau, haka kawai matar batai mata ba, gata wata irin doguwar mace gandaƙaiƙai kamar namiji babu wani fasalin mata tattare da ita... Malikat Haseena da rawar jikin Hadimar ya bata mamaki itama ta tsura mata idanu. Sai dai mulki da kasaita baisa ta tanka ba. Hadima Banou dake jin kamar ta zura a guje saboda yanda take jin jikinta ta zube ƙasa, cikin rawar hannu ta fara yunƙurin haɗama Malikat Haseena abinci.. Iffah dake mata kallon nazari ta dakatar da ita. “Kinga jeki kawai”.

    Ai kafin ma ta rufe baki tuni ta mike zaram kamar wadda ke akan wuta. Iffah da gaba ɗaya abin ya gama ɗaure kanta ta fara haɗama Malikat Haseena abincin da kanta. Itako Malikat Haseena komai bata kawo a ranta ba game da yanayin Amintacciyar hadimar tata, saboda takan ganta a wasu yanayi daya fima hakan, dan haka ta jima da sakata a jerin masu aljanu...


      Hadima Banou na fita a falon ta sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya da kai hannu ta yarce gumin dayay sharkaf a goshinta kamar wadda ta tiƙi surfen gero. Gaba ɗaya manyan idanunta masu saka tsigar jikin mutane tashi sunyi jazur. Gefe ta koma ta zauna a ranta tana fatan ALLAH yasa har Iffah ta tafi Malikat Haseena bazata nemeta ba. A ganinta ma tai zamanta anan koda an nemetan ai sai an ganta. Wannan shawarar data yankema ranta ya sata cigaba da zama a wajen har lokacin jikinta bai gama komawa dai-dai ba....


       Gaba ɗaya Iffah kasa sakewa taci abincin tai saboda kunya, ganin haka cikin hikima Malikat Haseena ta cigaba da ɗan jan ta da hira domin jan ra'ayinta, itako tana amsa mata a kunyace da tsakurar abincin. Suna a haka Daneen Ammarah ta shigo, itama dai ta nuna jin daɗinta na ganin Iffah ɗin tare da jin kaunarrta har cikin rai. Zama tai itama aka ɗora cin abincin da ita suna yar hira jefe-jefi da Malikat Haseena. Iffahn dai nata saurare kawai, sai kuma murmushi. Rabin hankalinta kam nacan wajen tunanin hadima banou da yanayin ta....

        

           ★★.... ★..  ★★....


    Kamar yanda Barrister yayma su kaka alƙawari ya samo Ibrahim Askari ta hanyar mutumin nan da suka fara zuwa wajensa. Fuskarsa cike da murmushi yake dubansu, dan tun yana can ya sanarma Abu Zainab su haɗu a office. Sai gashi kafin ya iso ma su har sun iso. Ko cikakkiyar gaisuwa basuyi ba ya fara musu bayani.

     “Alhamdulh an samo Ibrahim Askari, ya kuma bani cikakken adireshin Dawood ɗin, hasalima yace shiyya sayar masa da gidan daya koma ɗin. Ga adireshin gidan ya bani”.

        Sosai farin ciki ya bayyana a fuskar Kaka. Ya dinga jerama Barrister addu'a da fatan alkairi. Shima dai Abu Zainab yayi masa godiya, tare da ɗorawa da faɗin, “Barrister yanzu mune zamuje can ɗin? Kokuwa kai ne?”.

       “Mu duka babu wanda zai je Zakariyya”.

   Kallonsa sukai su duka, ya jinjina musu kansa da buɗe wani littafi a gefensa ya yago takarda, ɗan rubutu yay da sake ɗagowa ya dubesu. “Kamar yanda na faɗa muku mu duka babu wanda zaije. Domin ita Shari'a takanzo saɓanin hankali. Sannan bamu san nasu shiri ba, zasu iya amfani da duk wani yunkurinmu a yanzu. Dan haka nayi abinda ya dace bayan barina wajen Ibrahim Askari. Akwai wani babban police dana sani kai tsaye naje garesa, nakumayi sa'asar samunsa. Nayi magana dashi da rokonsa ya bincika mana inda zamu iya samun su, Alhamdullah kuma ya amsa, yanzu haka kiransa nake jira kamar yanda yaymin alkawarin kafin cikar awa ɗaya”.

      Anan ɗin ma dai farin ciki ne a fuskokin su Kaka, sai faman sauke ajiyar zuciya sukeyi.....


         ★... ★★.... ★....


  Zamu iya cewa gaba ɗaya yinin yau Iffah ta kare shine a neman number Malaminta Fawzan da abokinsa Ajmaal. Amma abin mamaki har yamma amsa ɗaya ce layukansu not available. Gaba ɗaya tayi firingai-firingai na damuwa, duk yanda take ƙoƙarin ɓoyewa da danne hawayenta sai da suka zubo bayan ta idar da salla. Bakomai yasata shiga damuwar akan son samunsu ba sai rashin samun number Babiy da Hanash da batai ba suma. Tana son jin wani abu game da ahalinta, dan yawan faduwar gaban da take da mummunan mafarki yasa tanaji a jikinta akwai matsala. Tama rasa wane tunani zatayi, har text message ta turama Malam Fawzan akan ya taimaketa ya duba mata iyayenta amma shiru kakeji, bama tada tabbacin ya gani ko bai gani ba. Kuka taci sosai a wajen kafin ta mike tana share hawaye bisa shawarar zuciyarta. Wayar ta sake ɗauka ta sake tura sakon data turama Malam Fawzan a layin Ajmaal abokin nasa. Tana fatan ɗaya daga cikinsu yaga saƙon koda bata samu sauran biyan bukatarta ba. Jikin window ta koma ta tsaya tana mai shaƙar iskar dake busowa mai daɗi, kamar ance kalla gefe ta hango Hadima Banou can jikin filawoyin saitin ɗakin Malikat Haseena tsugunne kamar tana tona rami, sai faman waige-waige take alamar rashin gaskiya. Da farko tsura mata idanu Iffah tai, sai kuma ta zabura bisa umarnin zuciyarta. Sai da ta tabbatar wani baiga sanda ta fito a dakinta ba sannan ta fice, kasancewar ta naɗe har fuskarta da ɗan kwalin abayar jikinta yasa babu wanda ya ganeta, balle abayar jikin nata ɗaya daga cikin natane na gida data canja bayan barowarta wajen Malikat Haseena. Da ƙyar ta gane hanyar dazata ɓulla bayan, dai-dai Hadima Banou na ƙoƙarin maida kasar data tone alamar harta saka abinda zata saka. Sauri-sauri takeyi harta kammala, ta ɗago da nufin barin wajen taja ta tsaya a kiɗime ganin mutum tsaye a bayanta. Amma kasancewar ta mai shegen tsurin ido sai ta dake a zahiri tana kallon Iffah da har yanzu bata janye mayafin data yane har fuskar ba....

     “K! Ubanwa ya kawoki nan?”.

Ta faɗa da zaton cikin hadimai ne irinta. A hankali iffah ta karasa takowa gabanta, tare da janye mayafin ta saka idanunta cikin nata jajaye marasa ƙyan gani. Sosai hadima banou ta rikice har rawar jikinta ya bayyana. Iffah ta janye idanunta daga kanta ta maida akan ramin,

     “Mi kika binne?”.

“Ranki ya daɗe babu komai, w... W... Wani magani ne kawai da nake son yin amfani da shi.....”

     “.....Shine kika shuka shi anan cikin rashin gaskiya? Wacece ke? Mi kike kullawa”.

    Tambayoyin sunma Banou yawa da tsauri wajen bada amsa, a take ta sake gigicewa duk da tana ƙoƙarin ƙirƙirar jarumtar dole. Wuceta Iffah tai zuwa wajen ramin, ta tsugunna da daukar iccen datai tonan da shi ta shiga sake tone kasar da Bismillah. Firrr wani abu kamar tsintsuwa ya fito a ramin yay sama. Iffah ta mike da sauri ta bisa da kallo harya bace. Juyawa tai da sauri inda Banou take, dai-dai ko tayi shirin silalewa tabar wajen ta dakatar da ita.

     Ƙasa tai da kanta jikinta na matukar rawa, Iffah ta kare mata kallo sama da kasa na wasu sakkani, sai kuma ta girgiza kai. “Wani asirinne haka bizne tsuntsuwa da ranta saboda son zuciya? Ko wani ya sakaki biznewar saboda ya isa? Kokuwa ke ɗin kina a cikin jinsin Mayu ne? Dan a cikin ukun nan dana lissafa dole ne a samu ɗaya tattare da ke tsohuwa”.

     Kuka Banou ta fashe da shi gwuyawunta a ƙasa. “Ranki ya daɗe ban fahimci abinda kike nufi ba, nifa magani na shuka ki yarda dani”.

         “Uhhm wato magani kika shuka, tsohuwa kalleni da kyau ki ganni banyi kama da wanda akema rufa ido ba, amma zan baki lokaci kije, zan nemeki a lokacin daya dace. Idan kika hangi gudu baki da wajen iya ɓoye min, idan cutar dani ne zagaye nake da kariyar UBANGIJINA, idan yunkurin salwantar da rayuwarkine idona biye yake dake tako ina. Shawara ya rage gamai shiga rijiya”.

      Da wani irin mummunan kallo hadima banou tabi bayanta da shi, ta cije baki da rumtse jajayen idanunta da karfi.........✍️


      🤔 Wannan ƴa ta Babiy ƙarfin halinta da tarar aradu sun mata yawa. Dole dai sai ta kai kanta inda za'a lamushete oh ni Balki😜.

     

No comments

Powered by Blogger.