Daudar Gora Book 1 page 20
*_20_*
........Abu Moosa dake sonyin magana ya dafe ƙirjinsa da numfashi ke kokawar kufcewa, tari ne ya suɓuce masa sai ga jini. Hankalin Babiy da Ummu ya tashi, amma Hanash ko'a jikinsa. Da ƙyar tarin ya lafa, Babiy dake riƙe da shi yace, “Kayi haƙuri muje asibiti, aman jini fa kake yi”. Murmushi yay mai ciwo da kaɗa ma Babiy kansa da ƙyar. “Abu Hanash zuwa asibiti bazai canja komai ba, dan gubar da aka shayar da ni bata da makari a ko'ina sai a wajensu.”
“Ya ALLAH! Guba kuma?” “Wannan shine hukuncin daya dace da masu irin halina ai karka damu, kai dai kawai ka saurareni zan gaya maka ta hanyar da zaka kuɓutar da yarinyarka, ina fatan hakan ya zamar min aikin alkairin dazan samu sassauci a kabarina”. Babiy zai yi magana ya dakatar da shi. “Ka saurareni kawa Ab.....” ya kasa ƙarasawa saboda sabon tarin daya sake sarƙesa. Sosai Babiy ya rikice ya shiga ƙwala kiran Hanash duk da yana a kusa da shi. Hanash dake jin tamkar yasa wuƙa ya ƙarasa numfashin wanan shegen tsoho ya amsa da ƙyar.
“Kaga kamashi maza muje asibiti”. “K...k...karku wahal da kan.. Ku. ka saurareni kawai”.
Abu Moosa ya tari numfashinsu da ƙyar yana dafe ƙircinsa da tari ke yunƙurowa. Babiy ya buɗe baki zai yi magana cikin taresa shima sai kawai sukaga yarab alamar rai yayi halinsa. Salati suka ɗauka a tare, wanda yay dai-dai da shigowar jami'an tsaro dake na ƴan sanda a ƙasar, bayansu wata mata ce ke rusar kuka... “Ranka ya daɗe dama na faɗa muku, na faɗa muku mutumin nan baya ƙaunar mijina, yanzu kun gani da idonku gashi nan ya kashe mini shi, dama kullum yana faɗa min neman rayuwarsa yake yi, ashe dai shine ɗin zai zama ajalinsa.....” ta zube ƙasa tana cigaba da kuka harda kururuwa.......
Hankali tashe su Babiy ke kallon wannan mata da jami'an tsaron, ba shigowarce ta tada hankalinsu ba da farko, dan tunaninsu ya basu duk wanda ya bama Abu Moosa guba shine yasa suka biyo sa. Furicin wannan mata da kai tsaye Babiy ya gane matar Abu Moosa ce ya firgitar dasu. Cikin ƙarfin hali Babiy yace, “Yallaɓai taya daga taimako kuma zan zama mai kisa? Abu Moosa abokina ne tun ƙuruciya kowa ya sani, ban kashesa a da da muke tare ba sai yanzu da a ƙalla nama kai shekara biyar kenan ban sakashi a idona ba sai yanzu dana gansa ayam cikin gidana babu zato.....”
“......Shiyyasa akaga gawarsa a cikin gidanka yanzu daka samu damar ganin nasa ko?”. Jami'in ya tari numfashin Babiy da sauri yana wani makirin murmushin ƙeta...
“Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairin minha” Babiy ya faɗa a zahiri gumi na karyo masa. Duban jami'in yay zaiyi magana matar ta taresa tana cigaba da kukanta mai cike da bori.... “Ƙarya yake wlhy yallaɓai, shekaran jiya jiyan nan sai da yaje har gidanmu ya faffaɗa masa magana mara daɗi da tabbatar masa shine ajalinsa, idan ya ƙaryata ai munada shaidar hakan”.
Hanash da zuciyarsa tazo ta tokare maƙoshi a hasale yayo kan matar, wata shegiyar shaƙa yakai mata saiga idanunta tamkar zasu fito waje. “K! baƙar matsiyaciya, dan kawai anga gawar mutum a waje sai ya tabbatar masu wajen suka kashe shi!!”. Idanuta ta rumtse da ƙarfi jikinta na ɓari, ta fara kakarin azaba dan da gaske ta shaƙu. Tuni jami'an tsaron duk sukai kansu da ƙoƙarin ɓanɓare hanun Hanash a wuyanta amma sun kasa. Ummu kuka ta sanya, yayinda Babiy keta kiran sunan Hanash da faɗin ya saketa amma sam babu alamar yana ma jinsa. Da ƙyar aka iya ɓanɓare Hanash, ta zube gefe tana sauke nunfashi da ƙyar hanunta riƙe da wuyanta. Sai da suka bata ruwan da suka fita suka ɗakko a mota da sauri tasha ta samu dai-daiton numfashi.
Cike da gadara ogan tawagar ya bama yaransa umarnin kama Babiy da Hanash. Sosai Ummu ke kuka da roƙonsu amma babu wanda ya saurareta, har ƙofar gidansu daya cika da mutane tun isowar jami'an tsaron ta biyosu amma kamarma basu san tanayi ba. Haka aka saka Babiy da Hanash a mota, sai gawar Abu Moosa a Ambulance da sukazo da ita (Alamar akwai dai lauje cikin naɗi kenan. Inba hakaba miye na zuwa da Ambulance ɗin?🤔).
Matan anguwar ne suka rufu kan Ummu data yanke jiki ta faɗi bayan wucewar motocin. Amma koda suka zuba mata ruwa bata farfaɗo ba. Hankalinsu ne ya sake tashi, makwafcinsu ya bada umarnin a sakata a motarsa a kaita asibiti. Da taimakon matan aka sakata a mota, matarsa da wata mata dake anguwar itama mijinta ya rasu suka shiga. Sai lokacinne mutane suka samu bakin magana. Wasu na nuna tausayawa ga wannan ahali, wasu na jin farin ciki badan sun taɓa musu komaiba, sai dan kawai dalilin hassada na rashin dalili.
A asibiti kam har an amshesu za'a fara dubata sai sukaga Doctor ɗin ya dakata sakamakon kiran wayarsa da akayi. Kansa ya girgiza musu ya nufi barin ɗakin yana sanar musu yanada uziri. Hankali tashe makwafcin nan nasu da ake kira Abu Zainab ya shiga roƙonsa amma bai sauraresu ba. Sun fara neman taikon Nurses suma sai zuƙewa suke saboda gargaɗin da Doctor yay musu. Al'amarin kamar wasa anƙi taɓa Ummu, dole suka ɗauketa suka bar asibitin zuwa wani, sai dai acan ɗin ma har an amshesu aka koresu. Basu gajiyaba suna kuka suka nufi privet ko acan za'a dace tunda aikin kuɗine. Anan sun amsheta, amma sun sara musu maƙudan kuɗaɗe kafin su taɓata, acewarsu dokarsu kenan. Matar nan da mijinta ya rasu ta fashe da kuka tana girgiza kai. “Suma basa son su amshemu ne kawai, shiyyasa suke mana kora da hali. Inba kora da hali ba ai banajin Abu Hanash ya mallaki koda kwatar waɗan nan kuɗaɗen da suka ambata inba dai kaddararsa zai saida ba”.
“Hakane Umm Yazeed maganarki nakan gaskiya, kuma tabbas na fara ji a jikina akwai lauje cikin naɗi a wannan lamarin, da alama hanasu amsarmu akeyi”. Abu Zainab ya faɗa ransa a ɓace.
Matar Abu Zainab dake share hawayen itama ta ce, “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Wannan wace irin masiface haka? Mi bayin ALLAH nan suka tarema wani da zafi haka?”.
“Sanin gaibu sai ALLAH, inaga inada mafita ɗaya, mu ɗauketa mu maidata gida sai a sanar da ƴan uwansu ko? Tunda mudai munyi iya ƙoƙarin mu...”
“Da hakan kukai tun farko da baku wahal da kanku ba”. Wata murya ta faɗa a bayansu. Da sauri suka juya su duka, sai dai bayan mutumin kawai suka iya gani. Da gudu Abu Zainab ya bisa, amma kafin yaƙarasa garesan harya shige mota sai ƙura ya bulesa da shi.......
(🤔????)
*_MASARAUTA_*
Babban ɗaki na musamman aka warema Iffah a sashen Malikat Haseena. Tare da amintattun hadimai biyar da zasu dinga mata hidima. Sai Ghazi biyar suma da zasu dinga bata tsaro duk da dama sashen zagaye yake da masu tsaron, amma an ware biyar ɗinne na musamman domin kula da duk wani motsin shiga da fitar mutane da zai shafi Iffah. Hakan ya sake saka Malikat Bushirat a farin ciki matuƙa. Yayinda sabanin haka ya bayyana a fuskokin munafukai, sai dai wasu sunyi jarumtar dannewa baƙin cikin nacin zukatansu tamkar wutar daji. Malikat Haseena data zartar da hukuncin batama nuna tasan sunai ba. Ita kuwa Daneen Ammarah damar nutsuwar nazartarsu ta samu ɗaya bayan ɗaya dalilin wani ɓoyayyen al'amari dake ajiye a zuciyarta tsahon shekaru.
Daneen Ammarah ta kasance ɗaya daga cikin ƴaƴan Malikat Haseena da Tajwar Abdul-majeed Ibn Aliy. Su huɗu suka haifa. Tajwar Haysam shine babba, (sarkin daya shuɗe kuma mahaifin sarkin yanzun). Sai Daneen Waheeda tana auren wani babban sarki a yankin larabawa. Sai Daneen Ammarah, itama tayi aure sai dai auren bai jimaba sakamakon wani ɓoyayyen al'amari dake tattare da ita, wannan ne sanadin dawowarta gida take zaune kusan shekara goma sha tara kenan bata kuma sake wani auren ba. Ƴar uwarta da mahaifiyarsu Malikat Haseena da marigayi Tajwar Haysam da mahaifinsu daya bar duniya da tabon damuwar ƙaddarar ɗiyar tasa ne kawai sukasan wannan sirrin, al'amarin ya sameta tun tana ƙarama dan bata wuce shekara 14 ba, shiyyasa ta jima batayi aure ba, bayan ta samu tai auren kuma bata jimaba suka rabu da mijin dan auren baifi wata takwas ba ma. Manyan masarauta sunta ƙananan magana akan hakan da fassara al'amarin na Daneen Ammarah ta siga daban-daban amma su Malikat Haseena sukai biris dasu. Sai auta Miran Nayyar nada shekara bakwai ALLAH yay masa rasuwa.
Bazamuce Iffah tayi garau ba kam a wannan yini. Dan har yanzu ko idanunta bata iya ɗagawa ta kalla kowa. Sai dai daidaituwar fitar numfashinta ya saka nutsuwa a zuciyar kowa. Koba komai dai an samu sassauci ai. Daneen Ammarah itace da kanta ta gogema Iffah jiki ta canja mata kaya, itace kuma da kanta tai zaman bata abinci daya kasance mai ruwa-ruwa. Daga haka aka ƙara bata magungunan da duk suka dace da gyara mata kwanciya a lafiyayyen gadon da yaji shimfiɗu na alfarma. Wani irin barcine mai daɗi yay awon gaba da ita, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi. Daneen Ammarah dake kallonta cike da tausayawa da jin wani ɓoyayyen al'amari akan yarinyar ta sauke numfashi ahankali da mata addu'ar samun lafiya da fatan ya zama kaffara a gareta.......
★★.... ★.... ★★.....
Duk wani nau'in kiranye ga uwa ta yisa tun lokacin da labarin abinda ya faru da yarinyar can sakamakon saka riga ya risketa, tabbas sune suka bada riga, amma abinda ya faru da yarinyar bashine ya kamata ya faru ba akan rigar, dan shirinsu sam bashi da alaƙa da halin da take a ciki yanzun. Hakan na nufin kenan bayansu akwai wasu masu shiri akan yarinyar kenan?. In dai har hakane kuwa to su ɗin su wanene? Minene tasu manufar kuma?.
Wannan amsar take buƙatar ji a wajen Uwa, sai dai har zuwa duhun dare babu alamar zata ziyarce ta. Tun zuciyarta na raya mata ta jira har ta fara jin ita taje gareta mana kawai. Amma tuna zuwa ga Uwa babban al'amari ne mai wahalar yiwuwa gareta yasa ta kasa iya cigaba da tabuka komai har dare ya cigaba da tsalawa masarautar ta ɗauki shiru tamkar babu wani mahaluki mai sauran numfashi. Ta cigaba da kaikawo a cikin wannan shiru, tare da ƙara gwada dabaru kala-kala na kiranye ga Uwa. Dai-dai lokacin da take sarewa, gaɓɓanta ke nuna gajiyawa mummunan sautin dariyar Uwa mara daɗin saurare a kunnuwa ta fara mata kaikawo tamkar tana yawo cikin iska. Ƙasa ta zube akan gwuyawunta tana mai jan nannauyan numfashi dajin sanyi a ranta. Tarwai Uwa ta bayyana a gabanta, akan kujerar baƙin karfenta mai adon gwal sanye cikin jajayen kaya kamar koyaushe. Mummunar fuskarta a matuƙar tsuke take babu alamar itace ta gama dariyar dataita amsa kuwa a mintocin da suka shuɗe.....
“Barka da isowa Uwa mai share kukan masu kuka. Uwa ina cikin matuƙar ruɗani, dan aikinmu yasha banban da wanda ya bayyana ga ƴar shilar suda. Kamar yanda na riski yinin jiya a cikin ruɗani, haka na kasance a duhun dare batare da na rintsa ba, na kuma sake wayar gari da ƙishirwar ganinki a yinin yau har zuwa iyanzu da daren ke ƙoƙarin zama dare biyu da faruwar komai?. Shin kuskuren daga garemu ne? Kokuwa kece kika canja aikin ya koma hakan? Ko akwai wasu masu irin shirinmu ne a wannan daula batare da mun san dasu ba? Minene manufarsu su? Wane buri kuma suke da shirin cimmawa?. Uwa ki taimakeni nasan wannan amsoshi in ba hakaba zuciyata na gab da tarwatsewa ne”.
“Bazan gaji da tuna miki akwai ƙalubale zagaye da cikar matakin aykinki na biyu ba, kuma wannan ƴar shila na tare da kaddarar ƙalubalenne, sai dai na miki alkawarin tsayuwar daka akan hana faruwar nasarar da zatazo in har bataki bace ba. Tabbas aikin ba namu bane, kuma rigar da aka kai mata ta sanya ba tamu bace itama. Na gano hakane a daren jiya bayan mutuwar waɗan can hadiman da kuma samun lafiyar ƴar shilar.. Hakane ya sani duƙufa bincike tuƙuru domin gano daga ina matsalar take?, wanene ya shirya aikin laɓewa bayan namu? Har yaci nasarar kuɓutar da ita da tarkon makircin sa cikin sauƙi haka?......”
“Uwa kin gano kenan?”. Ta-kurya ta tari numfashinta cike da zalamar son jin amsa........✍️
Leave a Comment