Daudar Gora Book 1 page 12


 *_12_*

.........Kalaman Iffah sun zama mafi ƙololuwar zama famin gyambo a zukatan Ummu da Babiy harma da Hanash. Sun zanu da zanen da zuciya ta killace koda tunasu zai zama mai raɗaɗi a cikinta. Sun karɓa domin karɓar ta zama tilas a garesu saboda rashin murya da ƙarfin iko da suka rasa a hannayensu. Sun cigaba da kuka saboda kukan shine kawai mafita a garesu. A haka kwanaki suka cigaba da tafiya da raunin zukatansu har zuwan ranar juma'ar da masu ƙarfin iko suka tsaida matsayin ranar ɗaurin auren ƴarsu. Bayyana ko misalta kasancewar wannan dare da wayewarsa ma ɓata lokacine game da halin da ahalin malam Zayyan suka tsinci kawunansu. Babu wani alamomin biki daga ɓangarensu sai ma zaman makoki. Dan bayan Iyyani da Kaka da wasu dattijai da basu gaza biyar ba a cikin zuri'arsu babu wanda ya halacci wannan makahon aure hatta da maƙwaftansu. Bisa tilastawar Kaka Babiy da Hanash sukai shirin halartar massallaci yin sallar juma'a da riskar abinda zuciyoyi ke tsananin ƙuna a kansa. Sun tafi sun bar Ummu da Iyyani da tazo itama a yanayi mai ban tausayi. Amarya Iffah kam idanunta ma babu wanda ya gani a wannan safiya abinci ma Iyyani ta bita da shi har ɗaki....


           *_TAFARU TA ƘARE_*


     Bayan gushewar wasu awanni, masu tafiya da ƙarfin bugun zuciya busa irin ta sarakai da tashin tambura ya karaɗe cikin birnin Daular Ruman dake cike da manyan baƙi tako ina. Dan kuwa sarakuna goma cif na ƙasar Ruman duk sun halarta duk da suma akwai raɗaɗin rasa ƴaƴayensu a zukatansu har yanzu. Koda yake wasu a ciki sun bada ne da kwaɗayi na burin zamowar ƴaƴan nasu zama matan Shahanshan, suna ganin hakan wani ɗaukaka ce a garesu da samun wasu damammaki......


      Iffah dake kwance a ɗaki zuciyarta a bushe, idanunta dake zubda hawaye a ɗazun a soye ta jiyo bayanin ɗaura aurenta da Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-Majieed daga bakin su Kaka. Wani irin dimmm taji a cikin kunnuwanta tamkar ɗaukewar wutar lantarki daga tashar gidan redio, ta koma ita ba wadda ta suma ba, ba kuma wadda ke a raye ba tsabar tsintar kai a wani hali. Ta jima a haka kafin ta dawo hankalinta kwakwalwata ta fara tantance abinda taji ɗin. Kenan abinda ya faru da yan uwanta a wasu watanni da suka shuɗe itama shine ya faru da ita yau? Itama zata mutu mutuwar rashin gata da ƴanci a hanun azzalumin mai mulkin Ruman da jama'ar cikinta. Daga yau za'a koma ƙirga mintuna da daƙiƙun mutuwarta da suka rage mata, daga yau tayi bankwana da Ummu, da Babiy, da Hanash Akhi da su Kaka. Anya kuwa zata iya? Anya kuwa sadaukarwar nan ta dace da rubutattun burukanta? Anya kuwa zata iya jurewa? Kai ina bazai yuwu ba. (Mizai hanasa yuwuwa? Bayan zakije inda ko kuwwa kikai babu maijin muryarki?) wata zuciya acan gefe ta ayyana mata. A karo na farko hawaye masu zafi da raɗaɗi suka silalo bisa kumatunta da gudu. “Dole ma na jure, jurewa irin wadda a duk faɗin duniya labarina zai karaɗesa a lokacin dana hukunta Tajwar Eshaan ibn Haysam ibn Abdul-majeed”. Ta faɗa cike da ƙwarin gwiwa na tabbatar da burin mai ɗaukar fansa.

      Batare data goge hawayen dake cigaba da rige-rigen zubo mata ba ta sauka a gadon tana tangaɗin jiri. Wayar data maida ta ajiye da ƙudirin ta daina amfani da ita ta lalubo, haɗata tai ta kunna, sai dai tai ɗan jimm namai nazari kafin ta fara rubuta saƙo. Minti biyu bayan turawa kira ya shigo. Numfashi ta fesar, sai kuma ta saki murmushin takaici jin abinda aka faɗa daga can. 

     “Sir bamu da lokacin tattauna wannan a yanzu”.

   “Na sani Fareedah, sai dai inajin matuƙar tsoro, tsoro irin wanda ko'a ido aka kalla an san tsoro ne. Nasan na rasaki na har abada a yanzu”.

      Murmushin takaici ya suɓuce ma fuskarta, sai dai ta hana hawayen da suka ciko mata ido zubowa. “Wannan shine tsoron dana gudar maka fuskanta tun farko dama duk jama'ar Ruman. Amma bazan gajiya ba, plan A dama yaƙin sunƙuru ne, plan B mafi haɗari amma da yaƙinin nasara”.

          “Ta yaya Fareedah? Kin san kuwa waye Shahanshan? Kin san minene girman ikonsa?.....”

   “Na sani mana tunda nima a ƙasar aka haifeni. Sannan na zama cikin ahalin da sukafi ɗanɗana ɗacin girman ikon nasa da zalunci. Karka damu da haɗari sir, taimako ɗaya zakamun a wannan plan ɗin wanda babu wani abu da zai shafeka da iznin ALLAH”.

       “Amma Fareed....”

  “Please sir”.

Kakkauran numfashi yaja ya fesar cike da ƙarfin halin son danne rauninsa a gareta. 

          “Okay ina jinki”.

    “Ka bani number abokinka”.

“Fareedah mi kuma ya rage?”.

        “Abubuwa masu yawa da amfani, hasalima yanzu ne za'a fara wasan na gaskiya”.

    “Karki taurin kai”.

“Na jima da zama mai busashiyar zuciya”.

        “Ki fahimceni”.

    “Ko kaina ma bana iya fahimta sir”.

“Bana son na rasaki Fareedah”.

“Iyayena sun jima da haƙurin rasa ni, kamar yanda na jima da sadaukar da kaina”.

     “Miyasa kike da taurin kai Fareedah”.

  “Shine izzata, ƙarfin gwiwa ta wajen tunkarar maƙiyi na”.

Wani irin cije lips yayi daga can, hawayen da tun randa labarin auren wadda ya fara so yake kuma kan so yazo masa da wanda yafi ƙarfinsa suke kwaranya ya kasa sharesu suka shiga rige-rigen zubowa daga idanunsa, yasan ta ƙare kuma, abinda ya rage kawai ƙyautatama masoyiyarsa koda hakan zai kasance sadaukarwa ta ƙarshe da zaiyi a rayuwarsa. 

         “Na barki lafiya, ki kasance cikin aminci da kariyar UBANGIJI”. Ya faɗa harshensa a sarƙe da yanke wayar a lokaci guda.

       Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga gudu a fuskar Iffah, bata san tana son Sir Fawzan ba sai a yanzu. A yanzun da kowa zai iya kiransa ƙurarren lokaci a rayuwarta. Zata cigaba da masa fatan alkairin samun madadinta koma wadda ta fita, jin kamar motsin ana tunkaro ɗakin yasata saurin kwanciya taja bargo har saman kanta....

     

     ★★........


         “Muhammad Zayyan!”.

   Kaka ya kira Babiy tamkar yana gabansa cikin matsanancin damuwa da firgici na zahiri dake kan fuskarsa. Ɗago kansa dake sunkuye yay a hankali shima tamkar yana a gaban Kakan. Hakan ya bayyana jajayen idanunsa da damuwa ta rinar. Sun rabu ne tun a wajen ɗaurin aure basu dawo nan gidan ba suka wuce Jumna. 

   “Na'am Baba”.

  “Kayi haƙuri. Karku zama masu baƙin ciki kai da matarka. Ku zama masu juriya da karɓar ƙaddara rubutacciya daga UBANGIJI. Nasan akwai raɗaɗi, nima kuma makamancin irinsa nakeji a ƙirjina. Sai dai bazan gaji da faɗa maka *_Kibiyar ajali sulke baya tareta sai ta gitta ba_* kamar yanda babu wata duster data isa goge abinda alƙalamin ƙaddara ya rubuta. Mu mun wuce yanzu, dan mungama namu ku ya rage kuyi naku mu barma UBANGIJI sauran, dan dama duka nasa ne. Iyyani itace zata shiryata kafin isowarsu ɗaukarta, nau'in turaren da yake a cikin gidanka kawai nake buƙatar fitar ƙamshinsa daga jikinta. Ta kuma sha iya adadin madara datake gidanka kawai daga yanzun har zuwa wayewar gari. Ta kwana a ɗakin daba shi aka ajiyeta ba. Karta karɓa daga wanda zuciyarta tai rawa a kansa. Ta zama ƴar kallo a takun farko, ta zama kurma a shigar farko, ta zama mai rauni a tawagar farko, tasa a ranta kariyar UBANGIJI na tare da ita. Na barku lafiya”.

        Ummu ta juya ta kalla Babiy dake riƙe da wayar a hannu tamkar dasashen gunkin da akai ado dashi domin tunawa a tarihi. “Lafiya kuwa? Baba ma baida wata mafita ko? Shiyyasa yaƙi dawowa tanan ya wuce gida?”.

    Idanu ya cigaba da tsura mata tsahon wasu sakanni harta fara kuka, ya ciza leɓensa na ƙasa yana mai haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi. Gefenta ya kai zaune, tamkar mai bitar karatu ya shiga maimaita kalaman baba a zahiri _“Iyyani za ta shiryata kafin isowarsu ɗaukarta, nau'in turaren da yake a cikin gidanka kawai nake buƙatar fitar ƙamshinsa daga jikinta. Ta kuma sha iya adadin madara datake gidank.......”_

     Kallonsa Ummu tai da share hawayenta a lokaci guda, cikin rashin fahimta tace, “Mi kake son faɗa?”.

   Kansa shima ya girgiza mata. “Ba dagani bane ba, Baba ne. Amma na kasa fahimtar komai Jamaima. Ko ke kin fahimta?”.

            Har zatace a'a sai kuma tai ɗan jimm idanunta masu girma da su Iffah suka gada a kansa. Itama maimaita kalaman tayi kamar yanda ya faɗa har sau uku, “Idanfa har na fahimta, Baba yana nufin _Iyyani ta shirya Iffah da kanata, idan sunzo da wani turare karmu bari tai amfani da shi, sannan ko taje can an bata wani abu kar taci......, Kaga kenan daga nan mu saka mata turaren, sannan mu bata abinci taci cikinta ya cika. Mu kuma......”

        Numfashi ya ja daga hancinsa a hankali ya saukar a ƙirjinsa, itama ta sauke numfashin mai haɗe da zubar hawaye sakamakon dakatar da ita da yay da hannu alamar ya fahimta ba sai ta ƙarasa ba. duk da bawai nauyin da zuciyarsa tayi ya ragu bane, ya dai samu sassauci daga kalaman Baba duk da basu san manufarsuba kai tsaye. Sai dai bin umarninsa a garesu tilas ne.......


      ★ Tsaf Iyyani ta shirya Iffah dake faman zubda hawaye har yanzu cikin shiga ta alfarma kamar yanda Kaka ya bada umarni. Wata haɗaɗɗiyar riga ce da akanga irinta kawai a jikin hamshaƙan matan gidan sarauta na ƙasar ruman mai kama da alƙyabba da ita kanta Iyyani bata taɓa sanin a kwaita a gidansu ba Kaka ya kawo yace a saka mata. Duk da shirine bana daɗin rai ba tayi ƙyau matuƙa. Ga wasu nau'in sirrika na ƙamshi na tashi daga jikinta har suna hawa kai. Tsaff Ummu da kanta ta shirya mata wasu abubuwa masu muhimmanci nata duk da sun san zama ne na taƙaitaccen lokaci ga ƴar tasu mace tilo data rage yanzu. Daga Babiy har Ummu zama sukai suna mata nasiha, nasihar kuma gaba ɗayanta tafi ƙarfine akan addu'a, ta kula da addininta, azkar, karatun alkur'ani kar tai sakaci da su. Babiy da kansa ya ɗakko wayar Fariha ya bata yace ta ɓoye kozasuna rinƙa jinta, baima san ta Arfa ma na hanunta ba. Isowar jama'ar daular ruman ta katse zaman nasu. Inda mayan matan da suka shigo gidan tare da rakkiyar tawagar hadimai suka buƙaci a basu amarya da ruwa mai ɗumi su shiryata. Kan Babiy a ƙasa ya basu amsa da

     “A shirye take domin cika umarninku”.

    Sosai mamaki ya bayyana a fuskokinsu dajin kalaman Babiy da kuma fitowar Iffah da Iyyani ta riƙo suka fito. Baki ɗaya daga cikinsu ta buɗe zatai magana wata ta girgiza mata kai alamar kartace komai. Badan taso ba tai shiru, sai dai ta juya ta fita tana mai danna wayar hanunta da alama wani take ƙoƙarin kira. 

     Babiy da kansa ya kama hanun Iffah tare da akwatin kayanta ƙarami har ƙofar gida gaban motar da aka tabbatar masa itace ta ɗaukar amarya.. Da gayya Iffah tai gaba zata kifa suna gab da fita a soron kamar tayi tuntuɓe da rigar jikinta dake jan ƙasa. Da sauri hadimai mazan dake tare da su sukai mata runfa da bayansu dan kar wanda yaganta, dan kofar gidan dama cike yake da jama'a, cikin sauri ta gefenta mai sanye da baƙar abaya harda niƙaf tai ƙoƙarin yin kamar zata tarota suka duƙe tare, a hankali ta ɗan ɗago suka haɗa ido, matar dake ƙoƙarin taimaka mata ɗin tai saurin kautar da nata da sukai jajur tare da ɗaukar littafin da Iffah ta saki ƙasa yayin da take kaiwa sunkuye. Miƙewa matar tai, itama Iffah ta ɗauka envelope ɗin da matar ta saki ƙasa dai-dai Babiy na ɗagota. Da baya-baya Sir Fawzan da yay  ɓaddabamin shigar mata cikin baƙar abaya da niƙab kamar hadiman masarauta ya dinga jan jikinsa cikin mutane ƴan kallo har ya sulale gaba ɗaya a wajen.....


         *_DAULAR RUMAN_*

    

    Wannan ne karo na farko da Iffah ta shigo cikin masarautar daular Ruman. Duk da a cikin mota suke kuma har yanzu hawaye basu daina zirara daga idaniyarta zuwa fiskarta ba hakan bai hanata tsarkake sunan UBANGIJI ba, yayin da motocin da suke a ciki suka gama keta katafaren gate ɗin farko zuwa cikin masarautar mai matuƙar girma da hasashe ko kintace bazai iya bayyanawa ba kai tsaye sai al'amarin ya sake girmama zuciyata........✍


Tabɗi jan🙆🏻 Ga aure dai ya ɗauru tsakanin Tajwar Eshaan Bin Haysam Abdull-Majeed. Da Fareedah Bint Zayyan. Shin itama zata mutunne kamar sauran matansa ko zata tsira? Wacece Uwa? Wacece Ta-ƙurya? Wanene shi kansa Tajwar Eshaan da ƴan ƙasar Ruman baki ɗaya kema kallon Fir'aunan wannan ƙarnin?. Miye dalilin mutuwar matan Tajwar? Shike kashesu? Ko akwai lauje cikin naɗi a kashesun?. amsoshinku duk suna a cikakken littafin nan na DAUƊAR GORA CIKI KA SHATA, dan cakwakiyarfa yanzune ma zata fara😉🤗.


No comments

Powered by Blogger.