Bakon Lamari 17

 


*BAƘON LAMARI...!*🌹

     { Eternal love }


           *NA*

*AUTAR MANYA*


ADABI WRITTER'S ASSOCIATION


                     *17*


Tun da ta fito ya zuba mata idanu ta cikin motar yana kallonta Goyon yayi mata kyau sai dai ba zaka ce nata bane zaka ɗauka ƴar wani ta goya.

Gajiya yayi dan kanshi ya haska saitin ta da fitilar Motar yana mai danna mata Horn mai ƙarfi.

Idanunta ya haske mata dan haka ta sanya hannu tana karewa Harta ƙaraso gaban motar Gabanta ya faɗi Lokacin datai idanu Huɗu da Ahmad acikin motar Ba ƙaramin kyau yayi mata ba.

Da ƙyar ta kame kanta tana Kiran sunan Allah acikin zuciyarta haka ta Buɗe Ƙofar motar ta shiga ta zauna bakinta ɗauke da sallama.


Amaimakon yayi mata magana sai ma Zira hannun shi dayayi ya Kunce Goyon Iman ya ɗorata saman Cinyar shi yana mai satar Kallon lallan dayay mata jaa sosai a hannunta.


Haka ya tashi Motar batare daya Ce mata ƙala ba.

Itama batai masa magana ba taja bakinta tai shuru wani Fitsarin tsoro ne ya kamata Lokacin data ga  ya karya kwanar Shiga jambulo third gate bata gama Tantance komai ba har saida tagan shi yana zuba Horn a bakin gidan da sukai ta zarya da Sabuwa mai kai ƴan aiki Ta cika da mamakin yadda taga masu gadi na rawar Jiki wajan Buɗe masa Gate Ɗin gidan zare Idanu tai tana tasbihi ga Allah lallai Wannan gida ya tsaru kamar ba'a wannan ƙasa tamu ba.


Parking yayi a parking space na gidan yana ciro wayar shi ya shiga kiran Zainab wadda duk ranta ya gama ɓaci da yadda Ahmad ya shanyata kowa yana wajan Event ɗin ita kaɗai da ango ake jira sai waya ake mata har ta gaji da ɗaga wayar mutane.

"Ina parking space Ki fito"

Daga haka ya katse wayar yana mai jingina da Jikin kujerar.

Zainab sai da taja lokaci mai tsayi kafin ta fito ita kaɗai jal sabida tana Gudun wata taga angon nata a ƙawayenta yasa tace Musu suyi gaba zasu zo ita dashi.

Da yake akwai haske a wajan wannan ya bawa Amatullah damar ƙarewa zainab kallo wadda take tafe kamar wata ɗawisu taci gayu bana wasa ba wanda nan da nan Amatullah taji ta raina kanta.

A hankali ta ɗora hannunta saman Iman dake Cinyar shi ta ɗauke ta tana ƙoƙarin fita daga Cikin Motar.

"Ina kuma zaki?"

Taji tambayar tashi akan ta tun kafin takai ga fita.

"Zan koma gidan baya ne Yayah Naga Antyn tawa zata shiga nan"

Ta faɗa Muryarta na rawa.

"Koma ki zauna malama"

Bata bi ta kan maganar shiba ta ja ƙofar ta Fita ta koma gidan baya ta zauna tana faman zaro idanu waje.


Ƙamshin turaren Zainab ya cika Motar wadda take ta faman masa ƙorafi akan ya jima bai zo ɗaukarta ba.

Sai wani langwaɓe masa take tana faman zuba masa shagwaɓa bai kulata ba yaja Motar a sukwane suka bar Gidan.


Amatullah ta saki bakin mamakin muskilancin sa au matar daze aura ma haka take fama dashi tunda ta shigo take magana yayi mata banza.


Kukan Iman ne ya sanya zainab ta farga akwai Mutum a motar da sauri ta juyo ta dubi Amatullah wadda suka haɗa idanu da ita.

"Dee wannan wace a bayan motar ka?"

Jin tambayar yayi kamar rainin wayo idan ya bata amsa ya zama Bin Umarni dan haka yayi mata banza.

Itama Kuma Amatullah haka kawai taji ta kasa gaida zainab Sannan ta kasa rarrashin Iman dake ta kuka harda ƙwarewa.


Wani Burki yaja.

ƙeeeeeee.

Kana ya juyo rai a ɓace ya dube ta.

"Idan ba zaki bata Nonon ba fitar Min daga mota shasha sha kawai wadda bata san ina ke mata ciwo ba"


Tsintar kanta tayi da sakin Kuka kuma taƙi bawa Iman Nonon sai ma ƙoƙarin Buɗe Motar da take yi zata fitan kamar yadda yace haka kawai taji zuciyar na mata Ƙunci ji take tana jin haushin kowa.


"Indan kika buɗe saina karya Miki hannun ki"

Ya faɗa yana ƙoƙarin tada Motar Zainab wadda suka Kulle mata kai da mamaki tabi wannan da kallo tabi wannan da kallo haka ta koma.


Ai ina ko sauraran shi batai ba Ta ɓalle Motar ta fice a zuciye tayi hanyar Titi zata tsallaka.

Da wani irin sauri ya Ɓalle nashi ɓarin yabi ta.

Kafin yaje har tai Nisa a ɗaya ɓarin.

"Amatu ke Amatu ina zaki da daren nan baki da hankali ne?"

Ya faɗa yana binta da sauri.


Ina kafin yaje harta sha wata kwana wadda sai da ya haɗa da Gudu kafin ya cimmata.

Yana zuwa Gabanta ya saka hannu ya wanke ta da wani irin Mari wanda sai da taga wuta  a gigice ta saki Ƴar a ƙasa tana mai zubewa Itama a ƙasan tai zaman Bori tana Zunduma Ihu!

"Mai nayi maka zaka mare ni Ina ruwanka dani"

Ta faɗi maganar kamar bata hayyacin ta.

Tashin hankali cewar Ahmad Cikin zuciyar shi kafin ya ɗaga Iman yana cewa.

"Dan baki da tunani ina zaki je anan wajan ina kika sani danna gaya Miki magana shine zaki fushi saboda Kinga ina shiga Hurumin ki"

A zafafe itama ta ɗago tana cewa.

"To ka dena shiga hurumina mana kaga idan zan Mutu zan rayu tunda uwata ma ta juyan baya na rayu waye zai Juyan baya na Mutu ka tafi ka barni na rayu da ƴata Wallahi duniya zan shiga na gaji nagaji da wannan bala"in kowa baya sona na rasa gatana"

Ta faɗi tana kwanciya a ƙasan wajan.


Ya haɗa Gumi ya share to duka mai ya kawo wannan abu?

A hankali ya ɗagota ya Sanyata ajikinsa ya Rungumeta wanda ya bawa Kukan nata damar tsayawa.


"Ya isa muje Gida mutattauna Ni ban tsane kiba Amatu Kiyi haƙuri In marin danai Miki ne Ga fuskata nan ki rama"

Ya faɗa Muryar shi tana sauyawa.


Tsintar kanta tai dajin wata Irin faɗuwar gaba.

Zuciyarta tana ce mata Amatullah Hakan fa haramun ne yakamata ki sanar dashi da auren Ki ya daina raɓarki.

A hankali ta zare Jikinta anasa tai gaba tabar shi a baya haka ya bita kamar raƙumi da akala Har suka je Motar sai dai abin mamaki babu zainab babu dalilinta acikin Motar wadda tuni zakara ya bata sa'a ta bar motar.


Haka ya lallaɓata ta shiga Ciki ta zauna yaja Motar ya nufi Gida sai dai zuciyarta babu daɗi na yadda Tai masa rashin Kunya a ɗazu.


Koda suka je Gidan ma tana amsar Iman tai cikin ɗaki har washe gari ranar juma'a wunin ɗaki tai haka kawai take Jin faɗuwar Gaba na ziyartar Kirjinta.


Daga Gidansu zainab Kuwa haka akai shagali ba amarya ba ango Sai dai koda Hajiya mahaifiyar zainab ta koma gida tai mamakin yadda taga zainab ta hargitsa Komai na ɗakinta tana ta kuka duk ta birkice.

Nan da nan hankalin mahaifanta ya tashi sunyi tambayar Duniya ta gaya musu meke damunta taƙi sai da Ƙyar ta iya furtawa mahaifinta cewa.


"Dady na fasa auren Ahmad koda shi kaɗai ne yay saura a mazan Duniya saboda ina zargin sa dayi wa wata yarinya ciki dan Jiya abin da nagani ya ɗagan hankali da ita fa yazo har nan ya tafi dani wajan Event sai dai a hanya data Turje haka ya barni a mota ya bita agaskiya Dady ni na fasa auren shi kawai"

Ta faɗa tana kuka sosai.

"A,a Ƴar Dady ya kamata ki soma Bincike kafin ki zartar da Hukunci akan shi Gudun Yin dana sani"

Cewar mahaifiyarta.

Ta ɗago da idanunta da sukai jajir sabida Kuka tace wa Hajiya.

"Dama nina kawo maku shi nace Ina son shi to yanzu na fasa in kuma Kuka yarda kuka auren shi to zaku rasani, Yarinya ƙarama ya samu ƴar talakawa ya ɗirka mata Ciki Ƙila ma dadiro ya mayar da ita gashi nan Jaririyar kamar su ɗaya"

Duk yadda Iyayen zainab suka so ta basu damar Bincike taƙi haka dady ya fita da ɓacin ran yadda tasa zai abun Kunya wato magana Biyu.

Da tsananin nauyin abin da zai cewa Iyayen Ahmad ya kwana har ranar ɗaurin aure ya kasa Tunkarar wani dan ya gaya musu cewar Ƴarsu tace ta haƙura.


Yau ta kama Asabar Ranar ɗaurin auren Ahmad da Zainab Tun safe Yake kwance a ɗaki ya kasa wanka abokan shi na ta masa waya akan ya shirya ya kasa kataɓus Babu abin da yake So ya gani kamar Amatu kwana ɗayan dayayi bai ganta ba ji yake kamar ya shekara Gashi kuma ya fahimci kamar haushin sa take Ji ta kulle kanta Ko falon mama bata fitowa tana ɗaki ita da ƴarta Haka dai ya Miƙe yana Jin duk babu daɗi ajikinsa wanka yayi tare da sanya Farar shadda ƙal sabuwa wadda tai masa Matiƙar kyau ya fesa turare ya ɗauki wayar shi ya fita.


Adaidai wannan Lokaci itama Amatullah tai wankanta ita da Iman Mama ce ta aiketa sashin su kawu dan ta amso robobin rabon abinci kamar ance ta ɗaga kanta ta hangi Imran Tsaye shida Ummah a bakin ƙofar sashin su sai dai daga gani magana suke mai mahimmanci gabanta yay wani Irin faɗuwa tana Ƙoƙarin juyawa domin ta Koma  Sashin mama

Ummah ta nuno ta wa Imran wanda yay wani Irin tsalle ya damƙo hannunta yana lashe bakin sa.


"Yau zaki zama nama na yau Ishirwar dana jima ina Ji zan kawar tabbas ayau duk Nacin ki sai nai yadda naga dama dake wuce Mota mu tafi Gida kwaɗayayyar Uwarki ta sallamamin Ke"

Ya faɗa lokacin da yake jan hannunta tana Doke shi.

Yana ƙarasawa gaban Ummah yay raurau da idanunsa tare da cewa Ummah.

"Kinga ni dai yadda take Doken hannu ko? ummah ke kina kallon kamar bana son mai da ita ne a,a wannan abubuwan da take Min  shine yake fusatani"

Ya faɗa cikin kirsa da iya haɗa sharri Umma ta sanya Hannu ta doke Amatullah tare da ce mata.

"Shegiya mai ƙashin tsiya Kinsan Allah yau sai kin bishi ba zaki kuma kwanar Min agida ba daman zuba Muku idanu nai"

Amatullah Kuka take tana tirjewa tana cewa.

"Ummah ki bari na gaya Miki waye Imran dan Allah kada ki turani inda zaki nadamar Kukan da ba hawaye"

Sai dai Ina ummah idanunta ya rufe sai ma ƙara Danƙara mata baƙar maganar da take tare da aibata ta.


Ganin tana ɓata masa Lokaci ne yasa ya Soma janta ta ƙarfin tsiya.


Ahmad dake amsa wayar Alhaji wanda yace ya same su a babban masallacin layin wanda zasu haɗu ashiga Mota a tafi wajan ɗaurin aure da sauri ya mayar da wayar Idanunshi har wani hazo yake ɗauka Lokacin daya ga Wani ƙato najan Amatuh tana kuka.

Da sauri ya ƙaraso wajan Imran wanda har ya kusan Kai Amatu Bakin gate.

Wani mari ya Zuba wa Imran kafin ya juyo ya kuma bashi Wani.

"Uban wa ya baka damar Taɓata har zaka shigo gidan mutane kana janta dan kai ɗan akuya ne"

"Nice nan na bashi wannan dama nida na kawo ta Duniya"

Cewar Ummah data ƙaraso wajan cikin masifa

A fusace Ahmad ya Juyo wajan ummah yana cewa.

"Ke kam ba uwa bace wallahi Na rasa wace Irin mace ce......."

"Yaya Ummah fa mahaifiyata ce dan Allah kada kai faɗa da ita"

Amatu ta faɗa tana kuka.


Dariya Ummah ta kwashe da ita kana ta Dubi Imran.

"Mai kake Jira da bazaka tafi da matarka ba ka tsaya wani ƙaton banza na baka doka da order'

Imran na Ƙoƙarin kama Amatu Ahmad ya kuma kai masa duka kana yace.

"Wannan ta haramta agare ka har abada ba matarka bace zan yi nisa da ita zan ɓatar da ita daga Duniyarku yadda daga kai har Uwar tata zakuyi rashin ta na har abada babu wanda Amatu ta dace dashi kamar Ni nina san wace ita nina raini abata nina san ciwon ta da mutuncin ta da darajarta kuma sai na tafi da amatu tafiya ta har abada Kai kuma ka jirani haɗina da kai babu alkairi ke kuma sai kinyi Kukan nadamar wannan kwaɗayin naki a lokacin da Kika buɗi idanu babu Amatuhhhhh"

Ahmad na kawai nan ya Finciki Amatu yay waje da ita bai damu da mutanan dake kallon su ba ya cillata a mota ita da Iman sannan yaja Motar da Gudun tsiya yabar Unguwar.


Duk yadda Alhaji yaso kamewa abun ya gagara Lokacin daya ji Kiran Alhaji idiris wanda ke bashi haƙuri akan fasa auren Zainab da AHMAD wanda sai da Suka bari mutane suka haɗu sannan za'a kira waya ace sun janye Alhaji ya yarfe Gumin da yake tsatstsafo mashi kawu ya Dubi Baffa Baffa ya dubi liman suka ɗan zanta Irin  na sirri kafin Masallacin yay shuru Liman ya ɗauki lasafika.


"An daka ta da tafiya Gidan su waccan amarya sai dai za'a ɗaura auren da Ƴar uwar shi kamar yadda iyayen shi suka Umarta jama'a a saurara An Ɗaura AUREN AHMAD ALI MAKAMA DA AMARYAR SHI..............wadda Alhaji Ali makama shine ya zama waliyin Amarya Malam Yusuf makama ya zama waliyin ango tare da Cikakken sadaki naira dubu Ɗari lakadan ba ajalan ba shedu ku shaida aure ya ɗauru da ikon ALLAH"

Nan da nan masallaci ya ɗauki surutai wanda sam surutun ya hana jin wacece Amaryar AHMAD ɗin.


Adai dai wannan Lokacin Kuma Ahmad ke sheƙa gudun Halaka da Amatu wadda take ta kuka kamar ranta zai fita.

A hankali ta ɗago ta kalle shi tausayin sa ya kamata Ita ma kuma tausayin kanta ya kamata sabida maganar da zata faɗa masa daidai take da wargaza dukkan kwanciyar hankalinsu.


"Yayah Imran bai sake ni ba wallahi da auren shi akai na yayah"

Da wani irin sauri ya juyo Da idanun shi masu aman wuta.

"Amatuh Kin cucen mai yasa baki gayan ba! Amatu kin cuci kanki a karo na Biyu wannan shine zai zama na ƙarshe! Macuciya azzaluma mayaudariya, Kin wa kanki Kin cuci kanki zan barki da Mijinki Yayi duk yadda yaso dake Tunda ke shasha sha ce wawiya marar tunani ya zama Dole Ki koma gidan Jiya!"


Ya faɗi maganar yana mai sakin kan Motar, a gigice Amatullah ta saki Iman tayi kanshi ta cakumo shi ta faɗa Jikinshi tana mai rungume shi sosai Cikin kuka ta Furta masa YAYA AHMAD..............

*LAST FREE PAGE*

Wannan shine ƙar shen shafin kyauta.

*Akwai tarin abubuwa agaba wanda sai wanda ya Biya kuɗi ne zaiji su*

*TIRƘASHI INA MAFITAR AHMAD AMATU YAYA CAKWAKIYAR TASU ZATA KASANCE NA WANNAN BAƘON LAMARI DAYA KUTSO...?*

*DA WA AKA ƊAURA AUREN AHMAD*?

*SHIN YAYA MAFITAR AMEERAH DA UWARTA*?

*YAYA ZAINAB ZATA TSINCI KANTA A GABA*

*WANI SAKA MAKO UMMAH ZATA GIRBA ITA DA IMRAN*?

*WAI WACE DANGANTA KAR CE A TSAKANIN AMATUH DA AHMAD ADA*?

*INA TARIHIN LABARIN WAIWAYE ADON TAFIYA*?"

*YAYA AHMAD ZAI JI IDAN YASAN AN FASA AUREN SHI DA ZAINAB AN ƊAURA DA WATA....?*

To bamu ji komai ba har yanzu akan wannan Labarin shin mene ma BAƘON LAMARIN? Soyayya Yaudara makirci kirsa munafurci duka suna ƙunshe Cikin wannan labari zaka more da Jin daɗi idan ka Biya domin akwai tarin abubuwan da bamu bayyana suba a free page's  ba maza hanzarta Biyan naka Kafin ai babu kai/ke.

Ƙofar Biya na nan a buɗe.

*BAƘON LAMARI! littafin kuɗi ne 500 naira zuwa  wannan asusun bankin 0078174806 Sterling bank,  idan kuma kati ne mtn card na 500 hoton sa za'a ɗauka a turo,shaidar biya 09022260850*


*Wannan karon ba zan sai da Baƙon lamari complt ga kowa ba domin na riga da na sayar da labarin ga wata kafa jira kawai suke na gama posting na basu kayan su dan haka duk mai son karantawa ya saya tun yanzu da nake posting inna gama ya zama complt ba zan sayar da shi ba Nagode*

No comments

Powered by Blogger.