Bakar Inuwa 7
*_Episode 7_*
...........*_BINGO CITY_*
Kasancewar tafiyar dare da sukayi a tasha suka ƙarasa kwana, sai da safe suka fito domin shiga cikin garin Bingo. Duk da Asabe a tsorace take, hakan bai hanata tarar motar taxi suka shigaba. Kai tsaye anguwar data san su hajiyar birni na zaune a yanzu suka nufa. Sai dai har cikin rai tana tsoron
haɗuwa da Gwaggon nata. Tana kuma tausayin ƴaƴanta akan tarbar da zasu samu ga mahaifiyar tata da sauran ƴan uwanta. Amma sai ta danne dan kar ta tada hankalin ƴaƴan nata da sukai zugum-zugum musamman Raudha.Tun a farkon shigowa layin sukai tambayar gidan Hajiyan Birni (sunan da asabe tasan ake kiran Gwaggo a ko ina). Sananniyace a anguwar kodan katafaren shagonta na abinci da duk kewayan babu kamarsa a yanzu. Dan takai manya-manyan masu kuɗi da sanannun mutane ke zuwa wajen cin abinci da shan giya wajenta. Ta iya abinci kala-kala na ƙawa, gashi tana tsaftacewa. Ta samu kuɗi matuƙa shiyyasa ma ta baro geto ta dawo wannan anguwar da zama kodan customers nata ƴan ƙarya da sanannu wanda basa buƙatar shiga kowane waje.
Basu Raudha ba, hatta da Asabe mamakin ganin ƙaton wajen kuma lafiyayye take, itadai tasan Gwaggo bata da ƙarfin gina irin wannan wajen da sunan gidan abincinta. Kodai watace mai irin sunan Gwaggo itama......
“Mommy fitsari nakeji”.
Yasmin ta katse ma Asabe tunaninta. Numfashi taja da ƙarfi tana ɗan waige-waige ko zataga inda Yasmin ɗin zata tsugunna. “Kinga jeki bayan dustbin ɗin can kiyi”.
Da sauri Raudha ta ɗan girgizama Asabe kai tana riƙo hannun Yasmin dake ƙoƙarin tsillawa da gudu. “A'a Mommy bai dace ba. Itafa mace ce, ya zata duƙa a titi yin fitsari? Mizai hana mu tambaya kodan guje mata ɗaukan wani cutan”.
Fatisa ta ballama Raudha harara tana yamutse fuska, “Raudha bazaki bar dai iyayi ba a rayuwarki? Miye idan tayi fitsari a can, duka shekarun Yasmin ɗin nawa a duniya da har za'a kirata mace”.
Kafin wani ya sake magana wata matashiyar budurwa sanye cikin wando baƙi da t-shirt pink alamun Uniform ɗin wajen kenan ta fito a cikin wajen cin abincin, cikin gurɓatacciyar hausanta tana faɗin, “Kai lafiya kuwa? Nan ba wajen tsayawa bane ba ku ƙara gaba”.
Fati zata fara magana cikin hasala Asabe ta dakatar da ita. “Yi haƙuri ƴammata ba haka nan muka tsayaba muma, muna neman wata ne anan ɗin?”.
“Wata kuma?”
“Eh wata muke nema Hajiyar Birni. An kuma tabbatar mana tana anan wajen”.
Wani kallon banza budurwar ta sake musu sama da ƙasa. “Tabbas sunan mai wajen nan kenan. Sai dai ku kuma sam bakuyi kala da masu alaƙa da ita ba, da har zaku nemi ganinta haka kai tsaye”.
Asabe da ƙwalla ya cikoma idanu tace, “Hakane yarinya. amma ki taimakemu ki sanar mata Asabe ce da ga Hutawa”.
Kamar budurwarnan bazata motsaba tanata musu kallon banza. Sai kuma taja guntun tsaki. A yatsine ta ce, “Kunga kuɗan koma daga can”.
Nan ma Fati zatai magana Asabe ta hanata. Sai da budurwar ta juya ciki Asabe ta dubesu. “Dan ALLAH ku kwantar da hankalinku bana son wata fitina. Idan munga ba ita bace gaba zamuyi ai. Maida zance ga kowa ba namu bane a yanzu”.
Badan hakan ya musu daɗi ba suka ɗaga mata kai alamar to.......
*★★★**★★**★★*
Kasancewar yau rana ce ta aiki kowanne ofishin gwamnati zaka samu ma'aikaci harma dana wanda ba gwamnatin ba ma'abota ayyuka a cikinsu. Baka ganin komai sai kaiwa da komowar ma'aikata a dukan ma'aikatu.
Sai dai a mafi yawan ma'aikatun gwamnati kamar yanda kowa ya sani ƴan siyasa ne mafi rinjaye a cikin yankin ofisoshin da suka shafi gwamnati. Kamar dai a yankin gidan gwamnati na babban birnin ƙasar NAYA (Bingo). Yawaitar ƴan siyasa a wajen yana da alaƙa da zaman taron meeting da shugaban ƙasa yayi har kusan sau biyu a safiyar ta yau saboda gabatowar watannin zaɓe da muka shiga shekarar ƙarshe na saukar duk wani mai mulki da ya ƙulla hawa biyu akan karagarsa.
A yanda alama ta nuna taron baima wasu daɗi ba. Dan lokacin tashi ma baiyiba shugaban ƙasa ya fita a wajen taro na biyu da aka zauna da wasu manyan dattijan jam'iyyar masu faɗa aji da mafi yawansu suka kasance masu sakawa da hanawa na wannan jam'iyya ne. Sai dai kuma bayan fitar shugaban ƙasa daga wajen taron da kamar mintuna goma sha biyar labari ya shigo kunnensu ya sake zama na musamman da ƙasaitaccen dattijon mai arziƙin nan kuma tsohon alƙali da kowa yakejin sunansa a ƙasar dama wajen ƙasar, har zamu iya cewa a yanzu ya zama tamkar wani shugaba dan ko masu mulkin babu abinda zasu layance masa na gwagwarmayar rayuwa da sanin muhimmancin talaka.
Kamar yanda basu fasa cigaba da ƙananun magana irin wadda akasan ƴan siyasa da itaba, haka ma shugaban ƙasa bai fasa ganawar sirrinsa da *_Alhaji Hameed Harith Taura_* ba.
Kallo ɗaya zakaima ƙyaƙyƙyawar fuskar dattijo Alhaji Hameed Taura dake ɗauke da ƙasaitaccen murmushin manya ka fahimci ɗunbin kamala da dattako tattare da shi. Yana zaune cikin luntsumemiyar kujerar da ke a ƙayataccen katafaren falon hutawa na shugaban ƙasa mai zaman mutum uku (three sitter). Zama ne irin na ƙasaita da dattijan taka, yana sanye cikin ɗanyar farar shadda harda malun-malun da suka ƙawatu da aikin surfani na maƙudan kuɗi. Ƙyaƙyƙyawane, duk da tsufa na farin gashi yama fuskar tasa shinge. Sai dai maimakon ya ɓata ta sai ya sake ƙawatata da kamala. Gefensa kaɗan shugaban ƙasa ne zaune shima cikin tasa ƙasaitar irin ta masu mulki. ba zasu iya zama shekaru ɗaya ba, sai dai yanayin jiki yasa Shugaban ƙasa yafi Alhaji Hameed ƙiba. Amma kuma kasantuwarsu cikin jin daɗi ya zaftare kaso mafi yawa na tsufan nasu gamai kallo.
Shugaban ƙasa dake magana cikin tsantsar damuwa ya sake gyara zamansa fuskarsa na nuna tsantsar damuwa da taraddadi. Cikin harshen turanci yake cigaba da faɗin, “Alhaji Hameed a wannan gaɓar da gaske nake bana buƙatar mulkin nan yabar hannunmu, dan na tabbatar maƙiyanmu na amsa tamkar mun bada sandunan rusa dukan tanadinmu ne a zahiri. Kai shaidane akan faɗi tashin da mukaitayi na ganin nayi shekaru goma bisa mulkin nan kafin yau. Miyasa bazaka amsa shawarata ba na fitowa takara kaima. Dan ni kai kaɗai idanuna ke iya hangomin zaka kawo kujerarnan a yanzun....”
Alhaji Haneed dake kallon shugaban ƙasa fuska ɗauke da murmushi na dattijantaka ya ɗan muskuta. Shima cikin harshen turancin ya fara magana da sigar rashin muhimmancin maganar ta shugaban ƙasa da rangwamen tasirinta a garesa. “Your Excellency badan a bakinka zancen nan ya fitoba dana kirasa da tarin wauta ƙwarai da gaske. Karka bari daɗin mulki ya kasa barinka ka dinga hango cewar ni Abdul-Hameed zan iya. Excellency ni sam bani da sha'awar mulki a ƙasarnan sam. Na zuri'ata da harkokin kasuwancina ma ya isheni gayya da takura. Sanin kankane dan na huta na tattara ayyukana na damƙa a hannun yarona tsahon shekaru goma kenan, iyakata a yanzu na taimaka masa da abinda bazan takura ba da ga gida. Ka ajiye maganata a gefe muyi mai muhimmanci. Kaine ka tilastani shiga siyasa saboda wasu abubuwa da muke iya hangowa zamu gyara koda bata hanyar mulki ba. Amma daka nuna sha'awar zakayi mulkin kai sai na baka goyon baya nima saboda nasan zaka iya. Kuma Alhmdllhi kayi ɗin an yaba. Ni yanzu inada shawara guda ɗaya zuwa biyu Excellency. Mizai hana mu duba a cikin yaran nan dake biye da kai ƙafa da ƙafa mu ɗora mai nagarta akan hanyar da mukeso, mu tallafa masa da taimakon UBANGIJI idan ya amince sai ya bashi mulkin tamkar yanda ya baka...”
Wani numfashi mai ƙarfi daya dakatar da Alhaji Hameed a magana Shugaban ƙasa yaja, cikin jin ɗaci da sukar da kalaman Alhaji Hameed ke masa a zuciya, ya haɗiye abinda ya tokare masa maƙoshi da ƙyar yana ƙaƙaro murmushi a saman fuskarsa. “Am sorry to say bana katseka bane ba Alhaji Hameed. Maganarkace tazo dai-dai gaɓar dataimin daɗi matuƙa. Harma a dalilinta wani tunani ya faɗomin a rai nima.”
“Masha ALLAH, wane irin tunanine?”.
Alhaji Hameed ya faɗa cike da yardar daya bama shugaban ƙasa matsayinsa na amini garesa shekaru aru-aru.
Shugaban ƙasa dake jin tamkar ya sokama Alhaji Hameed wuƙa ya sake ƙawata fuskarsa da murmushi. “Na yarda mu sami wani da muke ganin zai ɗora aikinsa bisa namu ɗin, sai dai a duk yaran dake tare da ni ɗin ban hango wannan nagartar ga kowa ba sai ga ɗanmu....”
Cike da mamaki Alhaji Hameed yace, “Ɗanmu kuma excellency!?”.
“Yes ɗanmu Alhaji Hameed. Basheer shi kaɗaine zai iya mana yanda mukeso batare da ya rusamu ba. Zamu tallata Basheer kuma inaji a jikina zai zama mai nasara insha ALLAH”.
(Dariya) karo na farko Alhaji Hameed yay dariya mai faɗi har haƙoransa na bayyana sosai. “Excellency baka rabo da wasa kai sam a rayuwarka. Banda ma dai iskar ac na busaka ta yaya kake tunanin Basheer zai iya siyasa harma takaisa ga mulki?. Idan ka manta bara na tuna maka. Bazan iya sakacin da Basheer zai ajiye harkokinmu ya dawo harkar siyasa ba, dan haka mubarma maganarnan Please, dan nasan bashi da interest akan hakan shi kansa....”
“Saboda ni ban isa da Basheer ba kenan Alhaji Hameed?”.
“Kash! Banso kai wannan zancen ba sam excellency, kaima ka sani kai ɗin mai iya zartar da hukuncine akan dukkan zuri'a ta. Sai dai kai baka hango ni abinda nake hangowa a wannan gaɓar. Dan haka ka sake shawara badai wannan ba”.
A take ɓacin rai ya gauraye fuskar shugaban ƙasa. Dan kuwa wannan itace dama ta ƙarshe da suke da ita akan Alhaji Hameed ɗin a wannan karon ma kamar yanda suke gani. Sun ɗauka tsahon shekaru suna shiryama Alhaji Hameed Taura tuggu iri daban-daban, amma yana tsallakewa, sai dai a wannan karon sun ɗauka alwashin bazasu taɓa bari damarsu ta suɓuce musu ba. Dole ne Alhaji Hameed ya amince da buƙatarsu ko yana so ko baya so......
Miƙewar da yay cikin fushi ya saka Alhaji Hameed riƙosa da hanzari. “Wai badai fushi kayi ba?”.
Cikin pretending shugaban ƙasa ya sake tsuke fuska yana son ƙwace jikinsa. “Mizaisa raina ya ɓaci tunda ka nunamin ban isa da jininka ba. Niko kaga komi ka zartar akan yarana ko tari bazanyiba balle ma na nuna maka inada alaƙa da sawarka ko hanawarka a kansu”.
Murmushi Alhaji Hameed yay yana girgiza kansa. “To naji zauna muyi magana. Dan nima ba ina nufin baka isa baneba. kawai dai akwai ƙurar da nake hangowa da tasowarta na dai-dai da guguwar da babu abinda zai iya tareta yayinda ta keto tsakkiyar birnin Bingo dama NAYA baki ɗaya”.
“Wannan hausan naka yayi girma da yawa ban fahimci komai ba”.
“Zaka fahimta ai”. Cewar Alhaji Hameed Harith Taura yana dariya.......
★★★*****★★★
Rai ɓace dattijuwar tsohuwar ta fito sanye cikin kaya na alfarma. Leshi ne daya amsa sunansa leshi mai tsadar gaske irin na jama'ar wannan yanki (masu hannu da shuni). Sai dai tana buɗe baki zatayi magana idanunta suka sauka akan su Asabe dake tsaye gefe har yanzu cikin alamun gajiya da buƙatar hutu. Turus ta ɗanyi a tsaye, sai dai fuskarta ta shanye tsoro da mamakinta. Asabe da jikinta keɗan rawa tun fitowar mahaifiyar tata ta fara takowa a hankali zuwa gareta hawaye na ƙoƙarin cika mata ido. Batun yanzu ba tasan mahaifiyar tasu ƴar gayu ce, sannan takowace hanya bi take domin neman kuɗi, tun ƙuruciya burinta tara manyan kuɗi ne, sai dai kota fara tarawar sukan rushe ne. Amma a bin mamaki a yau sai gata cikin yanayin da mai kallo kawai ya isa shaida lallai ta tara ɗin.....
“Wacece ke! Da ga ina kuma?!”.
Muryar Hajiyar birni ta katse tunanin Asabe da bata san ma ta iso gareta ba. A firgice ta ɗaga kai ta dubi mahaifiyar tasu hawayen da take maƙalewa na sakko mata a guje.
“Dan ALLAH Gwaggo kiyi haƙuri, nasan ni mai laifice a gareki....”
Baki Hajiyar birni taɗan taɓe kamar zata juya. Da sauri Asabe ta riƙo hannunta tana sake fashewa da kuka. Sanin halin Asabe da abinda zata iya yasa Hajiyar Birni juyowa a tsawace tace, “Sakarmin hannu. Danni tuni nama fiddaki a cikin ƴaƴana. Na barma Dauda dandi dan na kula ya fini kima da mutunci a idonki ai.”
“Wlhy baiko kamo yatsan ƙafarkiba Gwaggo. Na tuba nabi ALLAH na biki dan ALLAH kimin rai. Kece komaina gwaggo, dan ALLAH ki tausayamin ni da yarana dan ke kaɗaice dolenmu sai ƴan uwana”.
Kamar hajiyar birni zata sake cewa wani abu sai kuma ta fasa saboda sanin a inda take, yanzu ko gab ma'aikata suke da fitowa cin abinci, bata fatan abinda zai ɓata mata rai. Gaba tai tanama matashiyar budurwar ɗazun magana da ido tai shigewarta ciki tabar Asabe nan tsugunne da su Raudha dake a tsaye cirko-cirko ransu a dagule matuƙa, duk da sun fahimci hamshaƙiyar matar data fito Gwaggo ce mahaifiyar Mommynsu. Dan rabonsu da ita tun suna ƙanana sosai.
★
Gida ne matsakaici mai rangwamen girma da ƙyawu budurwar nan ta kawosu. Wadda alama ta nuna umarnin hajiyar birni tabi. Basu sami kowaba a gidan, sai dai a kallo guda zaka fahimci mazauna cikinsa ya wuce mutum ɗaya kacal. Duk da budurwar tasan lokacin azumine hakan bai hanata ajiye musu abincin data taho da shi ba daga restaurant ɗin. Daga haka ta juya inda ta fito.
Asabe data fahimci nanne gidan mahaifiyar tasu saita bama yaran nata umarnin tashi su fara gyara jikinsu, musamman ma Raudha dake a yanayin buƙatar hakan matuƙa. Duk basuyi musun hakan ba, dan dama sunada buƙata suma.
Ɗaya bayan ɗaya suka dinga wanka a toilet ɗin dake a tsakar gidan bayan Raudha ta tsaftace sa, suna kammalawa Yasmin tai zaman cin abinci, Raudha ma ta ɗan tsakura tasha magani ta kwanta. Ganin Asabe ma ta kwanta Fatisa da Fatima suka faki idanunta sukacinye sauran abincin da Yasmin ta rage. A taƙaice dai suka karya azumin dake a bakunansu. Suma kwanciyar sukai suna sauke ajiyar zuciyoyi najin nutsuwar abincin da sukaci.....
Leave a Comment