Bakar Inuwa 63-64

 


*_Episode 63-64_*



...........Ƙasa takai durƙushe cikin rawar jiki. Ta haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo. “Ya Ramadhan dan girman ALLAH kayi haƙuri, na tuba kar kayi zan iya mutuwa yau. Wlhy wajen har yanzu yana ciwo”.

       Kasa jurewa yay, sai da ƙwalla suka taru masa a ido. Matarsa ta sunna ke tsoronsa saboda yaje gareta tamkar karen farauta. Ya kusanceta tamar babu zuciya a ƙirjinsa. Maimakon abinda Raudha tai tunanin sai taga saɓanin hakan. Dan shima gabanta yakai durƙushe. Ya ɗora duka hannayensa kan nata ya riƙe. “I'm vary sorry Ameenatu ki gafarceni dan ALLAH”.

     Ya faɗa cikin wata iriyar murya mai tsananin rauni da rawa. Da sauri Raudha ta buɗe idanunta dake rufe, danjin furucinsa da sautin muryarsa. Sosai ƙirjinta ya buga ganin hawaye a fuskar mijinta. Sai ta sake fashewa da kuka tana girgiza masa kanta. “Dan ALLAH Ya Ramadhan kabar kuka”.

         Hanunsa dake cikin nata ya riko, ya jawota ta faɗa jikinsa, sai kawai suka saki kukan a tare abin tausayi. Tsahon mintuna uku suna a haka. Kafin Raudha ta ɗago tana share hawayenta tana magana. “Kaga dan ALLAH kabar kukan Abokina. Kaga nima na daina. Kuma ni ban taɓa rikekaba dama na yafe maka. Kai harma wanda zakamin a gaba na yafe maka Ya Ramadhan. Dan ALLAH ka daina kuka kar wani ya shigo, idan wani ya ganka a haka bazan yafema kaina ba”. Ta ƙare maganar tana kai hannayenta saman fuskarsa ta shiga share masa nasa hawayen.

        Murmushi yay mata, wani irin kaunarta na ratsashi. Ya riƙo hannayen nata da take share hawayensa ya sumbata. Idanunta ta lumshe a hankali, saƙonsa na ratsa mata jini da ɓargo. Ciki disashiyar muryarsa yace, “Ustazah!”.

      Idanun ta buɗe a hankali tana kallonsa. Ya kafeta da nashi dake cikin yanayin shauƙi da bege. *_“I love you!. Am serious I love you more than you can ever comprehend. Kinada muhimmanci a duniyata. Ina miki irin son da bayan mahaifiyata da Anne ban taɓa yima wata mace a duniya ba sai ke. Bazance miki ban taɓa so ba, sai dai inajin naki daban. Ga Ramadhan nan Ameenatu, Ramadhan B. Hameed Taura ya mallaka miki kansa da duk abinda yake nasa sai yanda kikai da shi, dan ALLAH karkici amana, karkiyi butulci, karkiyi amfani da wannan soyayya da dama ki cutar da shi......”_*

      Gaba ɗaya jikin Raudha rawa yakeyi, gaba daya ya kashe mata jiki, ya sakata cikin taradadadi da kaulani. Ta fashe masa da wani irin sassanyan kuka mai tsuma zuciya.

        “Nima ina sonka Ya Ramadhan, ina ƙaunarka da iya gaskiyata. Insha ALLAH bazan taɓa cutar da ko dabban Taura family ba balle kai. Har abada ko wanda zai ci amanarka bazan barsaba ma balle ni kaina. Ina fatan ko mutuwa ta ɗaukemu rana ɗaya, lokaci ɗaya, mu zama maƙwaftan juna a kabari sannan mu kasance ma'aurata a aljanna.....”

       Fuskarta ya kamo cikin tafukan hanunsa ya haɗe goshinsu, sai kuma ya manna lips nashi akan nata tare da rungumeta a jikinsa.


       Da sauri Anne da Bappi dake tsaye jikin window suna kallonsu suka ɗauke kansu. Anne tasa hannu ta share hawayen da suke saukar mata a fuska na ɗunbin tausayin waɗan nan ma'aurata. Tun fitowar Ramadhan daga falon Bappi Anne ta biyosa da shirin dakatar da shi, dan ta ɗauki aniyar saita wanashi akan Raudha. Biyota Bappi yay da hanzari shima da zummar dakatar da ita, sai dai tana ƙoƙarin gitta window ɗin ɗakin nata dake tabayan sashen Bappin ta tsinkayi roƙon da Raudha kema Ramadhan. Cak ta tsaya, a kuma dai-dai nan Bappi ma ya iso, ganin taja birki shima yaja ya kai dubansa ga abinda take kallo. Wannan yasa komai dake wakana a kan idonsu ne akuma kan kunnuwansu. Hannunta Bappi ya kama suka bar wajen.


      “I need you Please”.

Ya faɗa murya a sarƙe lokacin da yake janye lips nasa daga kan nata. kai ta shiga jujjuya masa cikin tashin hankali, har hawaye sun sake cika mata idanu. 

       “Please Ya Ramadhan forgive me wlhy akwai ciwo”.

    Da ƙyar ya iya rumtse idanunsa da suka kaɗa sukai jajur, dan tabbas bukatarta yake mai tsanani, bakuma zaiso cutar da ita ba. Amma dole ya samawa kansa mafita ba kuma a ɗakin Annensa ba, dan akwai kunya a raka baƙo ya ruga...

      “Shike nan naji, amma muje zan duba naga ɓarnar da nayi dan ALLAH”. Yay maganar a wani irin marairaicewa kamar bashi ba. Zatai magana itama ya girgiza mata kai tare da ɗora hanunsa kan lips nata alamar kartace komai. Dole tai shiru, ga tsoro ga fargaba. Haka ya kamata ya miƙar, batare daya bata damar cewa komai ba ya kama hanunta suka fito. Addu'a take a ranta ALLAH yasa babu kowa a falon, duk da tasan dai ta inda zasu ratsa ɗin ba falon da kowa ke iya shigowa bane sai iya ahalin gidan kawai. 

       Ta ɗanji sanyi da basu haɗu da kowa ba, sai dai mai aikin Anne dake ƙoƙarin shirya abincin dare a dining. Koda suka fito kam kasa tai da kanta tana gaida Ramadhan ɗin. Hannu kawai ya iya ɗaga mata suka wuce, dan yasan inhar yay magana kai tsaye za'a gane yanayin da yake ciki. Ko'ina ƙal yake a sashen nasa. Sai ma kamshi na musamman dake tashi dan Bilkisu da Basma ne sukai bautar gyaransa. Suna shigowa cikin ɗar-ɗar Raudha tace zanyi fitsari dan ALLAH. Sakar mata hannu yay kawai batare da yace komaiba. Sai ma ƙoƙarin rage babbar rigar shaddar jikinsa yake. 

      Babu wani fitsari da zatayi, tayi hakane danta kuɓutar da kanta daga garesa. Sai dai tasan hakan bamai yuwuwa bane. Amma tanada tabbacin yace zaiyi wani abu yanzu ɗinkin jikinta zai farke ne. Bayan kuma Dr Hauwa ta mata gargaɗi matuƙa akan ta kiyaye ta kuma kula sosai, shiyyasa Anne ke tsaye kanta kullum sau uku take shiga ruwan zafi. 

       Jin sautin kiran salla ya sata lumshe ido daɗi na matuƙar ratsata. ALLAH ya kawo mafita kenan. Jin kamar ana taɓa ƙofar tai saurin fara alwala. Kallonta kawai ya tsayayi sai kuma yay murmushi. 

       “Duk dai wayon Amarya Ustazah...”

     Baki ta tura gaba lokacin da take ɗagowa bayan kammala alwalar, “Toni wane wayo nayi”. Tai maganar da kauda idonta a kansa dan ya cire har ƴar cikin da ga shi sai wandon shaddar da singlet baka.

          “A'a ni minace kuma. Kefa daɗina dake fassara bawa a mizanin da bai kai ba. Ke dai jirani nai alwala kawai”.

        Gwalo ta masa batare da tunanin ya ganta ta mirror ba. Sai dai yay shiru kawai dariya na cinsa a ciki. Bayan ya kammala suka fito, shine yay musu jam'i, dan duk nasihar datai masa akan zuwa massallaci nunawa yay ai lalura ce zata hanashi. Tasan ya bijirene kawai dan son ransa. Amma badan baisan hakan ba. Bayan sun idar ta ɗauka alkur'ani zata fara karatu ya riƙe. 

        “K ALLAH inaga zare miki ido zan komayi maybe zaki fara tsorona. Mai kan kwakwa kawai”. Ya kare maganar da mangare mata kai. Fuska ta kwaɓe tana shafa wajen. “Ni gasky ban yarda ba”.

        Cikin ɗage gira yace, “Ko? To zoki rama mana”.

      Tashin kuwa tai ta bisa, yana ajiye Alkur'anin zai ɗago ta bashi mintsini mai shegen zafi a damtsen hanunsa. 

     “Kamm lalai yarinyar nan kinci abinci, ni kikama wannan muguntar?”. 

      Dariya ta ƙyalƙyale da shi tana ƙoƙarin kwasa da gudu yay tsalle ɗaya ya cafkota. Jikinta ta fara fisga tana haɗiye dariyar dake cinta amma ina tazo hannu, gaba ɗayanta ya dauka cak yay kan sofa da ita. Duk yanda take watsal-watsal da ƙafafu bai saurareta ba. Sai ma dariya da yake mata harya direta. “Rama cuta ga macuci ai ibada ne yarinya”.

         Yay maganar da kwashe hijjabinta gaba daya ya ajiye. Hannayenta dake kai masa ƙananun duka a ƙirji ya riƙe tare da kwantowa kanta, sai dai bai sakar mata nauyinsa ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ladabtar da zille-zillenta ta nutsu tana amsar saƙonsa. Sai dai acan kasan ranta a matukar tsorace take. Sai da ya tabbatar tayi laushi ya nema bin hanayar da take tsoro ta fara masa kuka da magiya. Dama ba zuwan zai ba. Amma ya tabbatar mata zai ƙyaleta idan tai masa abinda yace. Ko musu babu kuwa ta amince. Dan gwara hakan ita dai da abinda takewa tsoron.......


      Luf take shiru a jikinsa tana sauraren yanda yake sauke numfashi a hankali da sanya mata albarka. Yayinda hanunsa ke cikin sumar kanta yana faman wasa da ita duk ya birkita mata ita. Murya can kasa a ɗashe tace, “Ya Ramadhan sallar isha'i fa akeyi”.

      “Uhhm naji ai”.

Ya faɗa a shaƙe idanunsa rufe. Shiru tai bata sake cewa komai ba har kusan mintuna biyar sannan ya miƙe. Kai tsaye toilet ya shiga, hakan yasa Raudha lumshe idanu da sauke ajiyar zuciya takai hanunta saman cikinta tana shafawa. Bata san yaya zaijiba idan yasan tanada ciki, ita kanta a duk sanda ta tuna akwai ɗa mai alaka da shi tanajin tsantsar farin ciki. Badan shi shugaban kasa bane, badan shi jinin Taura family bane. Sai dai ɗunbin soyayyarta da take hangowa a cikin idanunsa. Motsin fitowarsa a bayin ya sata dawowa hayyacinta daga dogon tunanin data lula.

          Yanda ya fito yana goge sumarsa da jiki ya tabbatar mata wanka yayo, saurin ɗauke kanta tai ta maida gefe. Yay ɗan murmushi da ƙarasawa jikin Wadrobe ɗinsa domin duba kaya. “Madam tashi kiyi wanka muyi salla”.

       “Ni alwala kawai zanyi”.

Ta faɗa a shagwaɓe tana mikewa a gadon itama. Murmushi kawai yayi amma komai baiceba harta shige toilet. Sai dai kuma ashe cika bakinne kawai, dan itama dai hummm kawai............✍


No comments

Powered by Blogger.