Bakar Inuwa 60

 


*_Episode. 60_*

.........*_TAURA HOUSE_

      Tunda suka baro government house a sirrance da Raudha kai tsaye Taura house suka nufo. sai dai anan ɗin ma dai babu wanda yasan da dawowar tasu kamar yanda kowa bai san da fitarsu ba. Sake dukufa Dr Hauwa tai akan Raudha har sai da ta

tabbatar komai ya daidaita. Abin tausayi har ɗinki akai mata saboda bidirin da Ramadhan yay a jikinta. Hakan ya sake kona zuciyar Bappi da Anne sai dai babu wanda ya iya cewa komai har Dr Hauwa ta kammala aikinta ta wuce.

     Barci Raudha take saboda allurar barcin da Dr Hauwa tai mata. Dan haka Bilkisu ta zauna ta zayyanema Anne komai data sani har wanda Raudha ma bata san ta sani ɗin ba. Anne harda hawaye tausayin Raudha mai tsanani na cin zuciyarta. Koba komai sune suka jefata a wannan masifar. Maybe dasun barta ta aura dai-dai da ita da duk hakan bai faruba. Sai dai kuma ƙaddara ta riga fata inji masu iya magana. Sannan kuma babu mai sawa ko hanawa daga abinda yazo a littafin ƙaddarar wani bawa koda yana kalon kansa matsayin SILA. 


*_WASHE GARI_*

  

          Raudha ta jima bata farka ba har kusan tara, koda ta farka ɗin kuma Anne fidda kunya tai ta taimaka mata sosai kodan ɗinkin da akai mata. Ga Dr Hauwa ta tabbatar musu kar ai wasa da wani motsin Raudha mai karfi saboda cikinta a ɗofane yake. Hasalima bed rest shi tafi bukata fiye da komai a yanzun.

           Tabbas abu biyu da Raudha tayi ya matukar birge Anne da Bappi. Na farko tambayar duniya sun mata akan abinda ke tsakaninta da Ramadhan ta keƙashe ƙasa ta dage akan babu komai. Tushen abinda ya faru tsakaninta da shi a jiya harya doke ta (dan duka suka danganta abun saboda alkunya da kawaici irin nasu) amma sai Raudha tace wai faɗuwa tai a toilet. Batasan su da idonsu sukaje sukaga halin da take a ciki ba. (Saboda sun ɓoye mata cewar Bilkisu ce ta kaita asibiti suma acan suka amso ta). Na uku tunda ta tashi babu wanda yaga ko ɗigon hawayenta alamar ta dake, wannan ya sakama Anne ƙwarin gwiwar cewar lokaci yayi da zatai training ɗin Raudha a bigiren da sai Gimbiya Su'adah da shaiɗanunta sunyi dana sani. Ramadhan kuwa zai matuƙar gane kuskurensa, ba ita zata hukuntashi ba Raudha ce da kanta zata hukunta shi.


Hhhhh ashe akwai sabon show😋😉🤣.


*____★____★_____★_____★_____*


           Tsahon kwanaki uku Raudha na a Taura house babu wanda ya sani sai Bilkisu da Pa da su Anne. Koda Gimbiya Su'adah taga Bilkisu bataji komai ba tunda tasan dama tana shirin dawowa gida ai. Zuwa yau baƙi sun fara isowa daga masarautar su gimbiya Su'adah. Hakama a bangaren sauran matan gidan tunda kowa zai aurar da ɗa. Daga Taura ma dai wasu sun iso sai dai maza ne.

    Babu wanda ya sake jin labarin Ramadhan babu kuma wanda ya bibiyesa, a kwanaki ukun nan ma ko a labarai sai dai kaji ance Shugaban kasa Ramadhan ya kaddamar da kaza da yawun wane. Amma shi ko sau ɗaya ba'a nunasa ba sai a yau da kowa yasan za'a tafi hutu na ƙarshen shekara da Christmas. Kuma kakakin shugaban ƙasa ya sanar a Taura house shugaban ƙasa zaiyi hutun nasa baki daya.

        Hankalin Adda Asmah ya tashi matuka, musamman data kira bokanta yace sam karta yarda. Ita da suka gama cin burin kai Aynah government house kai tsaya ya Ramadhan ɗin zai musu haka, ya tabbatar mata ajiye Aynah a Taura house bazai taɓa haifar musu ɗa mai ido ba. Garama tayi duk yanda za'ai ta gyara barnar. Zuwa dare kuma tazo tare da Aynah zai mata wankan magani na ƙarshe da shine sirrin mallakar Ramadhan da duk ma wanda zai raɓesa, zai koma baijin magana ko umarnin kowa sai nata ita kaɗai Aina'u. 

        A rikice tai kiran Number Gimbuya Su'adah. Ita kanta gimbiya Su'adah ranta ya baci dan yau bata maida hankali akan television ba balle tasan da labarin. Tana can suna tafka rigima da Pa akan kofa dinner sai sunyi har guda uku idan ance sauran an hanasu. Shi kuma yace isar da bataiba kenan.

     Ramadhan ta shiga nema, dan rabonta da shi yau kwana uku kenan tun randa ta kunna zuciyarsa akan kiran daya sanar mata su Bappi sun masa. Maimakon hankalinta ya tashi matsayinta na uwa ta nemesa sai ta share da cewar yana lafiya shiyyasa ko kuma aikin office ne ya rikesa. 

         A lokacin kwance yake yana barci, dan tunda aka baro Raudha daga gidan ya tsinta kansa a wani irin yanayi mai matukar wahalar fassara a garesa. Ya rasa mike masa daɗi mi kuma zai kama. Ransane a ɓace? Ko damuwa da halin daya jefa ƴar mutane? Kokuwa halin da ke shirin riskarsa na auren wadda shi kansa har yanzu baisan dalilin da yasa yake mata wannan mahaikacin son ba. Bisa lallabawar cos yake fita office. Sai dai baya wani jimawa yake dawowa gida. Kuma kullum ya shigo sai yaje ɗakin Raudha da mama ladi bata gajiya da gyarawa. Hatta jinin da Raudha ta zubar a wancan ranar idan bama faɗa maka akaiba bazaka sani ba. Yakanje ya kwanta a saman gadonta. Sai dai baya haɗa mintuna biyu kansa zai shiga sarawa da karfi har sai ya fito ya koma nasa.

     Kunnawar da Ginbiya Su'adah tai masa yau ma ya sakashi tashi cike da fusata. Yay azamar dafe kansa dake juya masa da karfi. Sai kuma ya mike yana kallon agogo. Ƙarfe kusan sha ɗaya na dare. Amma tsabar yanda yake jin zuciyarsa tuni ya fice cikin ɓadda kama dan bazai iya jira sai gobe da zai huce Taura house ɗin ba ma, yanda yake komai saika ɗauka ana controling nashi da remote ne, dukya birkice, baya gane komai sai abinda su gimbiya Su'adah sukace yayi. Maimakon ma ko a motane yay fitar sirrin kamar yanda yakeyi, sai kawai ya fice da ƙafa ta karamin gate da taimakon odilan ɗinsa da baida ikon hanashi yin hakan saboda akwana biyun nan sam baya gane kan shugaban ƙasa, baya son yace wani abu kuma ga wani game da hakan saboda gargaɗi da Ramadhan yaja masa mai ƙarfi akan yanda yake fitar sirri inhar ya bari wani ya sani bayan shi duk hukuncin daya zartar a kansa yay kuka da kansa kawai. Cab ya tare sai taura house.

       

        A dai-dai lokacin da Ramadhan ke nufar Taura house Adda Asmah ce da Aynah sun dawo daga gidan bokanta anyo mata wankan maganin mallaka. Sam batai tunanin haɗuwa da Ramadhan ba, shiyyasa ta yanke shawarar biyawa ta Taura House takai maganin da bokan ya bata akan gimbiya Su'ada tai turare da shi matsayin na rufa idon su Bappi akan events ɗin da suke sonyi. Sai dai a zahirin gaskiya ba hakan bane. Na rabata da Ramadhan ne baki ɗaya yanda zai koma karƙashin ikon ita Addah Asmah ɗin.

       Kusan a tare Ramadhan da su Addah Asmah suka iso Taura house. Sai dai shi ya rigasu shigowa saboda an tsaya buɗe musu gate shiko yay wuff ya shige yanda ko mai-gadi ma bai lura da shi ba. Kai tsaye falon hutawa na gimbiya Su'adah ya nufa ta baya kamar yanda ta sanar masa ya sameta a can. Ko zama baiyiba Addah Asmah da Aynah suma suka shigo kamar yanda Gimbiya Su'adah ta sanarma Adda Asmah itama ta sameta anan. Adda Asmah bata san Ramadhan zaizo taura house ba. Haka zalika gimbiya Su'adah batasan Adda Asmah na tare da Aynah ba tunda tasan dokar dake tsakanin kar Ramadhan da Aynah su haɗu sai bayan an ɗaura aure.......


*_Tofa dole na dara kafin na cigaba🤣😂🤣😂, wannan fa shine ana dara ga dare yayi🤣. Ga boka yace kar.....🤭😂bara dai kawai na tsuke bakina muga yaya wasan zai kaya to._*


      ★Wani irin ihu Adda Asmah da Ayna'u suka fasa a tare cikin tsantsar tashin hankali. Dan kuwa sallamar Aynah dake gaban Addah Asmah tayi dai-dai da ɗagowar Ramadhan saboda ƙofar falon da aka buɗe batare da yayi tunanin wani zai shigo musu ba.

      Ita kanta Gimbiya Su'adah dake ƙoƙarin kunna buner ta saka turaren hayakin magani da boka yace ta dinga sakawa a duk sanda Ramadhan yazo gareta ta saki tare da yin wani uban tsalle tana dafe ƙirji.

         “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Allahumma ajirni fi musibati.....” Ramadhan ya ambato a jere saboda suna haɗa ido da Aynah gabansa yay wani irin mummunar faɗuwar da har sai da kansa ya sara. Hannu ya kai ya dafe kan saboda yanda ihunsu ke shiga masa har tsakkiyar kwakwkwararsa. Duk da kunne sa daya toshe ihun bai fasa shiga ba. Kai bama shi ba, hatta duk wanda yake kusa da sashen gimbiya Su'adah dole ne yaji tagwayen ihun nan.

      Pa ne ya fara shigowa a kiɗime. dan kamar yanda ya saba duk dare kafin ya kwanta sai ya zagaye gidan ya tabbatar da komai normal jininsa kuma ya motsa yauma hakance ta kasance. Yana ta wajen babban gate ɗin gidan baki ɗaya yaga shigowar Ramadhan. Duk da ya rufe fuskarsa da hular jacket ɗin jikinsa da facemask hakan bai hanashi shaidashi ba. Dan babu wata ɓadda kama da Ramadhan zaiyi bai gane abinsa ba. Shiru yay ransa fal al'ajab, bai gama dawowa hayyacinsa ba kuma sai ga motar su Adda Asmah ta danno kai. hakan ya sashi kiran Anne da Bappi da Yafendo a waya yace suzo dan ALLAH. Shi kuma ya biyo bayan su Addah Asmah ɗin.

      Takan kowa Pa bebiba tsakanin Aynah da Adda Asmah data zube ƙasa kamar wadda ma ta suma. Yakai ga ɗansa dake jujjuya kansa cikin tafukan hannunsa alamar akwai abunda ke faruwa da shi. A dai-dai nan su Anne ma suka iso, suma duk kan Ramadhan ɗin sukayi hankalinsu tashe. Sai kawai sukaji ya fasa wata gigitacciyar ƙara da duk wanda ke a gidan nan ƙarya yake yace bai jita ba.

    Innalillahi kawai suke ta ambato, Pa ya riko Ramadhan dake shirin kaiwa ƙasa ya ringumesa a jikinsa. Rawa sosai jikinsa keyi kamar mazari. Hakan yasa Bappi ma tallafawa suka riƙosa. 

        “Basheer kafin attention ɗin kowa ya dawo nan ɗin mu fita da shi”.

     Shawarar Bappi Pa yabi, suka kama Ramadhan da har yanzu yake faman jujjuya kai sukai waje da shi, fitarsu kamar ƙyaftawar ido jama'ar gidan suka fara tururuwar shigowa falon a gurguje. Su kum ganin Adda Asmah kwance duk sai sukai kanta. Da wannan damar Anne da su Yafendo suka zame jikinsu suka bar falon.


         ★★

    “Ya ALLAHU miya faru? Suma yay?”.

Cewar Anne dake shigowa falon Bappi idonta akan Ramadhan da suka shimfiɗar a ƙasan carpet Pa na kokarin shafa masa ruwa. Kai kawai Bappi dake zaune kan Ramadhan ɗin a cinyarsa ya ɗaga mata. Wani nannauyan numfashi Ramadhan ya ja a fisge sai kuma ya sake riƙe kansa zai fasa ƙara Bappi ya rufe masa bakki.

      “Tabbas akwai matsala, inaga akwai lamarin azzaluman aljanun sihiri tare da shi”. Cewar Yafendo tana kuka. Da sauri Anne ta fita a ɗakin tana faɗin bara ta ɗakko alkur'ani. Bappi na kiranta tazo ta ɗakko na ɗakinsa bama taji ba harta fice. Zaune ta iske Raudha na karatun alkur'ani da alama sallar shafa'i da wutiri ta idar. Ai tama manta da batun bedrest da Raudha keyi ta kamo hanuntan.  

        “Ameenatu taso ga inda ake buƙatar karatun nan naki can.”

    Hankali tashe Raudha ta dakata, ganin Anne a firgice yasa batabi ba'asi ba ta mike kawi ta bita. Sanye take cikin dogon hijjab fari har ƙasa. Dan haka baka iya ganin komai nata sai fuska da tafukan hannu.........✍


No comments

Powered by Blogger.