Bakar Inuwa 6


 *_Episode 6_*



...........Da ga Asabe har ƴaƴanta hankalinsu a matuƙar tashe yake. Hakama Baba Nafi, duk da Asabe kishiyace a gareta aurota da akai a gidan ba ƙaramin alkairi ya zame musu ba ta wani ɓangaren. Dan koba komai Asabe kansaka Malam ɗan-azumi ya sauke

haƙƙoƙin su dake kansa koda baiyi niyyar hakan ba. Dan kafin ya aurota sai ya gadama yakeyi, ya gwammaci yaje yay caca ko neman mata. Sannan duk jarabarnan tata da wahala kaga tana faɗa da kishiya, wani lokacin Larai kanso suyi, amma Asabe sai taƙi kulata. Mal. Dan-azumin ne dai ita da shi kamar suna kallon hanjin juna. Hatta da sauran yaran gidan duk sun zama sukuku, musamman ma da Inna mahaifiyar malam Dauda ɗin tazo ta sake zazzaga tata masifar ga Asabe saboda Larai taje ta sanar mata ƙarya da gaskiya, duk da kuwa ba ƙaunar laran take ba. Babu wanda ya tanka mata sai larain, dan harda kawoma Innar ruwa saboda tsugudidi. Saida ta gama zazzage masifarta tsaf da gorin Asabe tabar mata gidan ɗanta sannan tabar gidan, Asabe dai na ɗaki ita da yaranta duka cikin matsananciyar damuwa. Dan har Inna tayi ta gama babu wanda ya leƙo.

       Gaba ɗaya wannan yini dai anyisa a gidan cikin rashin daɗin rai ga azumi. Idan ka cire Larai dakejin tamkar ta ciji sama dan farin ciki. Malam Dauda bai sake dawowa gidan ba sai dare bayan sallar isha'i. Tsabar jinsa yau a sama da sigari ya shigo gidan yana busawa, wayarsa mai shegen ƙara tana raira waƙar (marigayi Ali makaho)

       Galala Baba Nafi tai tana kallonsa, dan duk iskancinsa bai taɓa shigowa gidansa yana shan sigari ba tunma yanaji da ƙuruciya a iskancin. Amma abin mamaki sai gashi a yau cikin watan azumin ramadana, a kwanakin goman ƙarshe da kowa ke dagewa da ibadar ALLAH, ya shigo gidansa dake cike da ƴaƴa a wannan yanayi.

       Tsakar gida ya zauna akan rijiyarsu yana kaɗa ƙafa da kai yana zuƙar sigari da ƙwala kiran sunan Asabe tamkar zai tsaga bangon gidan. Ko tari bataiba ballantana ƴaƴanta, jin taƙi tankawar ya sakashi fara zazzaga ruwan masifa da jaddada mata ta bar masa gidansa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu baisan sake ganinta. Kuma ko Yasmin bai yarda ta ɗauka ba idan zata wuce, ta bar masa abarsa.

     Nan ma ko tari babu wanda yayi sai Larai data fito daga ɗakinta ɗauke da tire ta jero kwanika. Dan duk da bai bada kuɗin cefane ba, ba kuma aikinta ba yau kuɗinta ta saka tai girki iya ita da ƴaƴanta da shi. Wani irin washe baki yayi yana gyara zama a lokacin data kai tsugunne gabansa tana dire tray ɗin.

      “A'a! Larai na mina samu haka ne?”.

   Cikin jin daɗin sunan daya kirata da shi ta buɗe tsohuwar kular dake sama, wadda ke cike da taliya da miyar kifi, sai kunun tsamiya a kofi da ƙosai data sayo masa a ƙaramin kwano. Albarka ya shiga kwarara mata da gyara zama ko kunya babu da tunanin bashi yay cefanen ba. Baba Nafi kuwa dake kallonsu tuni zuciyarta ta harba. Dan zuwa yanzu ta fara zargin Larai akan wannan fitinar dake faruwa tsakanin mijin nasu da Asabe. Dan lallai akwai wani abu a ƙasa gaskiya.

      Cikin farin ciki Malam Dauda ya kwashi girki yana kwararama Larai kirari tamkar wani jikan maroƙa. Itako sai wangale baki take.


★★★


     Washe gari sabuwar fitina ta sake tashi tsakanin Asabe da malam ɗan-azumi. Dan ya tabbatar mata sai ta bar masa gida a yau. Kuma bazata tafi masa da yaransa ko'ina ba. Ta bashi haƙuri sosai tana kuka amma yaƙi saurarenta, saima yi yake tamkar tana zugashi. Dan gaba ɗaya ya sake birkicewa, har mamakinsa mutane keyi musamman yanda aka san yana bala'in son Asabe, ba kuma yaune karon farko da suke irin wannan fitinarba a cikin anguwar, harma wadda tafi haka sunayi kuma su shirya. Ana tsaka da hakan kuma sai ga Inna yau ma. Komai sake rincaɓewa yayi har maƙwafta da suka taru domin bashi haƙuri akan ya maida Asabe kodan ƴaƴansa sai da ta shafesu. Dan Inna tas ta zagesu ta sake saka malam ɗan-azumi ƙarama Asaben saki ɗaya daya saura a tsakaninsu wanda ya mantama yayisa tun shekarun baya.

      Wannan abu yayima su Fatisa zafi matuƙa. Dan haka suka shiga haɗa kayansu masu muhimmanci dana mahaifiyarsu. Cikin ɓacin rai Fatima taje ta jawo hannun Raudha da Asabe dake gurfane suna basa haƙuri, dan itama Asaben ta zama tamkar ba itaba yau duk masifarnan babu ita. 

      “Mommy dan girman ALLAH in har ba Abbanmu ne autan maza ba a duniya ki barsa kizo mu wuce tunda kema kina da dangi ba'a bola ya tsintoki ba, dan ALLAH idan ya tashi ya auri Innar dake zugashi ɗin...”

      “K! fitsararriya!!”.

Inna ta faɗa a tsawace. Ko kallonta Fatima batayiba taja hannun Raudha da Asabe suka nufi ɗaki. 


      Abinda Fatiman tayi ya sake hargitse gidan, Malam Dan-azumi da kansa ya shiga har cikin ɗaki ya fisgo Asabe ya kaita har ƙofar gida yana faɗin tabar masa gidansa, baya son ganinta ya tsaneta. Cikar da ƙofar gidan ta sakeyi ne yasa harsu Raudha suka fito da kaya malam Dan-azumi da Inna basu lura ba. Hakama Baba Nafi. Larai kuwa sarai ta gansu dan tana gefe tanata kwasar dariyarta.

      Mota ƙarama suka fara samu da zata kaisu har jihar Bina shata, kafin wata makwafciyarsu da suke ƙawance da Asaben taje ta kamo hannunta ta kawota har wajen motar, dan itace ta hana su Fatisa komawa wajen gudun kar Malam Dan-azumi ya gansu ya hanasu bin Asaben. Itako bata fatan Asabe ta tafi tabar ƴaƴanta, gara duk rintsi ta tafi da abinta kafin abun yay sauƙi, dan da gani kasan malam dauda baya cikin hankalinsa sam. Tafiyar Asabe yasa akaɗan samu sauƙin hayaniyar. Sai mutane daketa yima Malam Dan-azumi ɗin ALLAH wadai da koran Asaben da yayi batare da wani ƙwaƙwƙwaran laifi ba, dan koda aka tambayesa ya rasa mi zaice tayi masa sai babbotan borin kunya yakeyi shida Inna da dama kowa yasan batan ƙaunar Asabe dama duk surukan nata sai baba nafi kawai, ita kanta wani lokacin baba Nafin baji da dadi take hannun innar ba. Na Larai da Asabe yafi zafi ne kawai dai dan ta kasa tanƙwara Malam Dauda ɗinne ya sakesu dole ta haƙura. Yanzu ko data samu dama shiyyasa tai tsayuwar daka wajen ganin ƙarshen Asaben da take kallo matsayin wani miki ga ɗan nata....



       ★A Bina su Asabe suka yada zango gidan yayarta Halima da take aure anan. Sai dai kuma sunyi rashin sa'a bata nan wai tana jihar Loss kusan wata guda kenan ita da ƴaƴanta duka da mijinta. Sam Asabe bataso haka ba. Dan bata buƙatar zuwa babban birinin ƙasar Bingo dasu Fatisa wajen Gwaggo (Mahaifiyarsu hajiyar birni). Saboda ta tabbata idon hajiyar birni idon su Raudha to akwai matsala.

      Cikin damuwa da sanyin murya Raudha ta kalli Asabe da sauran ƴan uwanta da duk suka jigata saboda azumi, ita kanta daba azumin takeba a jigace take dan babu abinda taci tun jiya da rana sai ruwa. Hawayen dake a idanunta ta share da faɗin, “Mommy nikam a ganina mizai hana mu wuce Bingo wajen su Gwaggo direct mana. Babu amfanin wani raɓe-raɓe a gareki damu a yanzu. Na tabbata Gwaggo ta canja zuwa yanzu, sannan zata amsheki hannu biyu tunda daman zamanki da Abbanmu ne bata so.”

       Shiru asabe batace komaiba. Tasan maganar Raudha gaskiyane, sai dai tana fargabar zuwa dasu Bingo su lalace kuma. Su Fatisa basa jin magana tabbas, amma rashin jinsu bai kai inda masu karatu ke hasashe ba, sai dai ta tabbatar kusantasu da hajiyar birni a yanzu komai zai iya faruwa, saboda masifar son kuɗinta. Suma ƴaƴanta ta ɗorasu a hanyar banza dan kawai ta samu kuɗi, balle su kuma jikoki gasu kuma yaranta dukansu masha ALLAH, ba duk namiji zai kalla ya iya kauda kai ba......

      “Mommy gaskiyafa Raudha ta faɗa wlhy, gara kawai mu tafi Bingo ɗin”.

    Fatima ta faɗa cikin katse tunanin Asabe. 

      Numfashi asaben taja mai nauyi, “Banƙi ta taku ba, sai dai nima akwai abinda nake lissafawa. Amma kuma banida wata mafita saita tafiya Bingo ɗin a yanzu. Matsalar kawai dai itace bamu da isassun kuɗin motar da zasu kaimu ne mu duka”.

        “Akwai kuɗi Mommy”.

  A tare duk suka dubi Raudha datai maganar cikin mamaki. Cikin rashin damuwa da kallon da suke matan ta zaro kuɗi a cikin zani sabbi ƙal ƴan ɗari biyu ta miƙama Asabe. “Mommy jiya mutumin nan da yazo dubani a asibiti ya bani su. Nayi niyyar bakine dama idan munzo gida danki fara sana'a. Amma yanzu na tabbatar insha ALLAH zasu kaimu duk inda zamuje ko?”.

       Hawaye ne suka ciko idon asabe. Dan bata taɓa tunanin Raudha haka ba. Ganin yanda take musu nuni dasu gyara yasa take tunanin sam Raudha bata ƙaunarta matsayin mahaifiya. Ashe ba haka bane ba. “ALLAH yayi muku albarka, ya kare min ku”.

    Ta faɗa gawaye na silalo mata na nadamar sakaci da tasoyi akan tarbiyyar ƴaƴanta saboda ruɗin shaiɗan da son zuciya. Hannu Yasmin dake jikinta tasa ta share mata hawayen. “Mommy ki daina kuka, banason naga kina kuka kamar irin na Aunty R”.

      Asabe ta rungume Yasmin tana murmushi da share sauran hawayen. “Na bari auta, itama bazata sake yin kukaba insha ALLAHU. Da ga yau zan tsaya akanku da inganta tarbiyyarku da muku addu'ar miji nagari ba irin mahaifinku ba da ni.”

     Ba Raudha da ɗabi'ar iyayensu ke damunta a rai ba, hatta su Fatisa yau duk sai jikinsu yay sanyi ƙalau. Bayan asabe ta kira ƙawarta dake hutuwa sukai magana sai suka ɗunguma tasha duk da yamma tayi liƙis. Basu damuba dan tafiyar daren ma sai tafi musu kwanciyar hankali. Anan tasha sukasha ruwa dayin sallar magriba. Kafin motarsu ta tashi zuwa birnin Bingo. (Babban birnin ƙasar NAYA kenan. Dan yanzu hajiyar birni tana nan da zama ta baro jihar loss).


★★★


         Ko bayan tafiyar Asabe Malam Dan-azumi bai farga da rashin su Raudha a gidan ba har yamma. Dan bayan lafawar komai sai zuciyarsa kuma ta sake shiga ƙuntata fiye da farko. Rasa mike masa daɗi yayi dan haka yabi Inna data jashi zuwa can asalin gidansu na gado. Barci ya kwanta yayi sosai dan har gab da magrib sannan ya tashi. Sai da ya fara shiga massallaci yay ramuwar sallar azhar da la'asar sannan yay zaman jiran magrib zuciyarsa duk babu daɗi. Koda aka idar da sallar magriba yau bai zauna shan kunun sadaka ba yayo gida fagan-fagan tamkar zai kifa ƙasa dan sauri. Da akuyar Larai dake bakin kwata ya fara bal. ta saki wani marayan kuka daya saka duk jama'ar fitowa daga ɗakunansu.

      “Malam lafiya kuwa?”.

Larai ta faɗa tana hararsa da nufar akuyarta dake kwance ta kasa tashi dan azaba. Bai tanka mataba, sai nufar ɗakin da yara ke kwana yayi ya leƙa, duk da kuwa duk sauran yaran gidan sun fito suma. Cikin sauri ya afka ɗakin ya hau leƙe-leƙe duk da babu wani lungu da zai iya ɓoye mutum a ciki. A zabure ya sake yo waje, nan ma bai kula sauran yaran dake masa barka da shan ruwaba ya nufi ɗakin Asabe dake garƙame da ƙwaɗo.

       Wata muguwar ashariya ya lailayo ya dire yana duban Baba Nafi. “Ina yarana?”.

     Duk da sarai tasan su Raudha yake nufi sai ta haɗe rai itama. A ɗan zafafe tace, “Gasu nan tsaitsaye ai”.

        “Mtsoww! Su Raudha nake nufi!!”.

     Yanda yay maganar a tsawace ya saka kowa zabura banda Larai data laɓe baki tana hura hanci. Cikin jin zafin yanda ya nuna damuwa da rashin ganin ƴaƴan na Asabe ta ce, “Tunda ka kori uwarsu mi zasu zauna kuma su mana anan muma. Kaima kasan sun bita”.

      Wata muguwar shaƙa ya kaima Larai ido a rufe, ya maƙureta jikin bango, “Ubanwa yace ta tafimini da ƴaƴa kuna gani kuka barta!!?”.

      Cikin fisge-fisgen azaba Larai ta turesa tana kakarin shaƙa. Kafinma wani yay magana ya nufi hanyar fita ƙofar gida da sauri.


      Kai tsaye gidan Malam Gambo amininsa ya nufa. Cikin sa'a kuwa yaci karo da shi a ƙofar gidansa. Ko sallama babu ya zube a tabarmar da Malam Gambo yake kai yana huci. 

      Malam Gambo dake dubansa yana murmushin ƙeta yace, “Mutumina lafiya dai ko? Badai Asaben bace ta sake dawowa kuma?”.

      Harara ya zuba masa yana sake ƙwaɓe fuska. “Gambo gaba ɗaya shawararka ruguzani take nemanyi ba gyarani ba. Kai kace naima Asabe saki ɗaya zakasa ta dawo gidanka da zama har sai na gama hidimar auren Raudha da Alhaji Maude na jiƙu da kuɗi sannan na dawo da ita, amma har akaci aka tsire banma ganka a wajen ba. Gashi daga ƙarshe tama sace su Raudhan ta wuce da su”.

       M. Gambo dake gimtse dariya yay ƙoƙarin dai-daita kansa da ƙyar. Cikin nuna ɓacin ran ƙarya ya miƙe zaune sosai. “Ya zakace banzo ba M. Dauda. Idonkane kai dai kawai ya rufe har bakaga sanda naketa ƙoƙarin ganin na saka Inna ta huce bata sakaka yin saki ukun nan ba.....”

       Cikin ƙosawa M. Dan-azumi ya katse M. Gambo.

      “Ni wannan duk bashi bane damuwata a yanzu M. Gambo. Babbar matsalata ta tafimin da yara. Shirina duk ya zama na banza kenan?”.

       “Kwantar da hankalinka bai zamaba M. Dauda. Ai mugu shine yasan makwantar mugu. Badai kasan inda ka auro Asabe ba?”.

        “Ya kake min wannan banzar tambayar. Idan ban sani ba daga sama akaimin wahayinta!”.

     “ALLAH ya baka haƙuri ba haka nake nufi ba. Abinda nake nufi tunda kasan gidansu a loss mizai hana muyi shiri muje mu amso ƴaƴanmu”.

      “Kai bazai yuwuba. Mahaifiyarta da ƴan uwanta jarababbune na bugawa a filin idi. Gashi basa ƙaunata ko kaɗan. Wannan ne yasa naje wajen malam na tsandu yay mata wani kafi da bata sake zuwa loss ba tun Yasmin na shekara uku. Yanzu ma uwar tata tabar Loss tana birinin Bingo....”

       “A lallai likafa taci gaba, Bingo? to basai mu satosu ba kawai. Ai shiyyasa na faɗa maka mugu shine yasan makwantar mugu ai”.

       Karan farko M. Dan-azumi ya saki murmushi dan gamsuwa da maganar M. Gambo. “Eh to kazo da magana mai ƙyau kuwa. Inko hakane dole na tsara wani abu a wannan gaɓar ma kodan na samu ƴan kuɗaɗe hanun Alhaji Maude Dallatu.”

       “A wlhy ina bayanka M. Dauda. Tatsi ka more rabonka ɗan takarar ɗan-majalisa ba wasa bane. Kaga idan ALLAH ya taimakemu akai auren nan kuma yaci ɗin nan aimu mun haye wlhy. Kakarmu ta yanke saƙa rabajau zaka ganmu mutumina. Surukan ɗan-majalisa fa kenan, kai wlhy ƙilama ai maka Ministan kuɗi kona man fetur ni kuma kwamishina...”

      “Minister kuma? Kai fa M. Gambo wani zubin kamar haka-haka kake. Minista ba shugaban ƙasa keyi ba?...”

      “Af wlhy na shafa'a ne Dauda. Kasan maijin yunwa ko goruba aka bashi gani yake abinci ce”.

        “Kai dai ka sani, ni kaga tafiyata shawararka ta faɗa. Zanje na ɓata daren yau wajen shirin yanda komai zai tafi har tafiyarmu Bingo ɗin ma”.

    “Af to babu damuwa sai na jika. Amma sai bayan salla ko? Tunda naga kwana shida sallar ta rage kacal”.

        “Ko gobe ta kama nidai tafiya zanyi na amso ƴaƴana”.

    M. Dauda ya faɗa yana barin wajen.  Shaƙiyyar dariya M. Gambo ya saki yana kaiwa kishingiɗe. “M. Dauda kenan inka san wata ai baka san wataba. Badai ni ka raba da Ladi dandi ba muna tsaka da more duniyata. To kai gashi na rabaka da Asaben da kake ji da ita kuma zan koma ta bayan gida na aureta kai dai kaini gidan nasu kaga ikon ALLAH. Dan ba wani dawo da yaranka zai kaini ba hhhhhh”...........✍



🤔Tofa, Larai ko M. gambo?. ALLAH dai ka tsaremu da abokai masu fiska biyu😥.


No comments

Powered by Blogger.