Bakar Inuwa 58
*_Episode 58_*
..........A hankali ta saki numfashi tare da nannauyar ajiyar zuciya ganin Bilkisu ce ba wanda take fargabar haɗuwar da shi ba ko'a hanya bare a cikin ɗaki da ga ita sai shi. Zama Bilkisu tai kusa da ita tana kai hannu a goshinta. “Aunty Lafiya kuwa kika dawo da w....”
Maganar tata ta maƙale jin jikin Raudha da zafi. “Ya salam baki da lafiya yauma ko? Dan ALLAH ki yarda muje ko cikin clinic ɗin gidan nanne inma bazamu je wajan Mommyn Jabeer ɗin ba. Aunty wai zaki cigaba da cutar da kankine akan Yaya Ramadhan ne? Kin hana na faɗama kosu Anne halin da kuke ciki, ni kaina ɓoyemin abubuwa da yawa kikeyi wlhy. Harga ALLAH nidai na gaji da shurun nan da kika dabaibayeni da haɗani da ALLAH akan nayi”.
Murmushi Raudha tayi tana haɗiye hawayen dake son zubo mata. Ta tashi zaune cike da ƙarfin hali ta kamo hanun Bilkisu cikin nata. “Aunty B kiyi haƙuri dan ALLAH, ban hanaki gayama su Anne bane sai dan yanda kike kallon matsalar ba haka take ba. Aiki ne kawai yay masa yawa, sannan ni babu wani abu na rashin daɗi dake tsakanina da shi, kawai dan ba zaman gidan yake kamar da ba saboda ayyuka yasa kike ganin akwai matsalane. Kinga babu dalilin kai ƙara akan laifin da babu shi aunty. Nasan kina ganin kamar auren nan nasane cutarwa a gareni shiyyasa. Dan ALLAH kibar damuwa ALLAH ni banajin komai akan hakan duk da nasan dole ne naji kishi matsayina na matarsa. Amma karki manta Aunty ALLAH ya bashi damar yayi huɗu, a addinance ma da biyu aka fara, sannan uku, sannan huɗu. Sannan a yanayin da Ya Ramadhan ke ciki dama ya kamata ace yanada mace mai ilimi da zata jagoranci wasu abubuwa na mulkinsa bawai irina da iyakata secondary ba kuma mai ƙarancin shekaru. Karki manta aunty yanzufa nake shekara ta shatara kawai a duniya, koba komai kuwa Aynah nada kusan ashirin da tara ko talatin da ɗaya ko fin hakan ma, sannan tayi ilimi mai zurfi daga ƙasar NAYA har wajenta. Tako ina ta cancanci zama matarsa koda nauyin al'umma dake a kansa”.
“Humm Raudha sam ban gamsu da wannan bayanin naki ba. Babu ruwan hankali da ƙarancin shekaru, hakama babu ruwan sanin yakamata da ilimi. Mutane nawane a zamanin da basuyi ilimin boko ba amma sunada basirar tsara abinda ko professor na yanzu bai iya tsarawa ba. Kai har a wannan zamanin akwai wanda basuyi ilimin boko ba amma wlhy idan sukai miki wani abun sai kinsha mamaki. Hakama shekaru, shekaru baga kowa suke taka rawar hankali ba ga mai su. Zakiga mutum da shekarun manya amma idan yana tafka miki baranɓarama ke kyace ɗan goma sha ne. Kuma kiga karamin yaro na gyara masa. So ni a tawa mahangar banga ta inda Aynah zata taimaki Brother ba wlhy. Ƴar uwatace ita kuma jinina, amma bazan ɓoye miki cewar inaji a raina akwai manufa acinkin wannan al'amarin ba Raudha. kuma insha ALLAH bazan gajiyaba wajen ganin na daƙile hakan sai dai in ƙaddararsa ce zama da ita”.
Tana gama faɗa ta mike ta fita hawaye na sakko mata a fuska. Da kallo kawai Raudha ta bita sai itama ta fashe da kuka. Sai da tayi mai isarta sannan ta mike ta shiga toilet ta wanko fuskarta....
(ALLAH ka bamu ikon cinye jarabawa a duk yanda tazo mana🙏🏻😭).
*______________★_____________*
A ɓangaren su Gimbiya Su'adah kuwa shirin biki suke na ƴaƴan gata, dan a wannan gaɓar ko auren Lubnah da Bilkisu bata bama muhimmanci ba kamar na Ramadhan da Ayna'u. Babu abinda zuciyarta ke raya mata sai cewar zata haɗa cikar birinta da maido ɗanta ƙarƙashin umarninta ta kuma rabashi da wadda ta zame mata ƙayar kifi a maƙoshi badan ta taɓa mata wani laifi ba ko kuskure.
Hatta da Ramadhan yanzu wani gata take masa na fitar hankali ita da su fulani da uwar gayya Addah Asmah. Baya iya jera sati baizo gidan ba a sace. Takai yanzu ko sashen su Anne baya shiga sai dai suji labarin yazo a bakin Basma. Hatta yin waya ya rage dasu, komansa gimbiya Su'adah. Ko abu ya shige masa akan harkar mulki maimakon kiran Bappi da yakeyi ko Anne a da sai ya kira Gimbiya Su'adah yanzun. A mafi yawan lokuta shawarar tata bata haifar da ɗa mai ido a garesa. Dan kuwa dai gadarace kawai da son nuna isa take ɗorasa akai, ALLAH ne kawai ke taimakonsa da in yay maganar da Cos sai yay saurin faɗama Bappi shi kuma ya gyara, wani lokacin idan Bappi ya kirasa yace kar ai kaza ɗin nan kaza ya kamata ayi har haushi yakeji, ya dinga ƙunkuni kenan yana cika yana batsewar fushi. Idan kaga haƙoransa a waje yanzu to tare yake da su gimbiya Su'adah. Aynah kam kamar yanda bokan Adda Asmah ya faɗa mata a ɓoyeta kar Ramadhan ya ganta har sai an kaita gidan gwamnati haka akai, sai suka fake da cewar gyaran jiki ake mata, amma a zahiri umarnin boka suke bi, dan ya tabbatar musu inhar Ramadhan yay ido huɗu da Aynah kafin aure duk wani sihirin jikinsa sai ya warware.
Game da Raudha kuwa a yanzu basu da lokacinta, dan su tunaninsu sun gama da shafinta lokacin komawarta gidansu kawai suke jira. Shiyyasa ko bibiyar lamarinta basa waniyi gaba ɗayansu.
Mutane har yanzu basu farga da halin da Ramadhan ɗin ke ciki ba, sai dai yanayinsa na kullum fuska a cunkushe yanzu kansa wasu yin kananun magana. Ƴan adawa kuma suka samu na suka a garesa da sake dawo da furicin nan na mai girman kai garesa.
Pa da duk abinda ake a gidan ya saka ido badan baya cikin damuwa da halin da ɗansa yake a ciki ba. Ya barine kawai azo gaɓar da gimbiya Su'adah zata gane kurenta. Sai dai a yanzu bita da ƙullin daya shirya musu akan shirin da suke gagarumi na auren ne. Dan ko events an haɗa yakai kala goma, sanin Taura family ba'a wannan almabazaranci sai suka fake da cewar duk a gidansu amarya aka ɗauki komai. Lokacin da gimbiya Su'adah tazoma Pa da zancen dariya sosai abin ya bashi. Amma sai ya gimtse kayarsa yace ALLAH ya bada sa'a.
Daɗine ya kama gimbiya Su'adah, dan gani take yanzu fa kamar ta fara samun kan Pa ɗin a dalilin turaren da Adda Asmah ta kawo mata tace tai amfani da shi a duk sanda zataje gareta. Dukan wata bukatarta sai ya amsa babu musu sai ma shakkarta da zai dingayi. Murmushi tai tana ficewa cike da tafiyar takama. A ranta kuwa sakama Addah Asmah albarka take da yaba mata. Dan ta tabbatar wannan turare shike taimaka mata wajen hawa kan Pa ɗin yanzu a yanda takeso. Amma da tasan bata isaba indai wannan uban kafiyar ne da taurin kai.
Bayan ficewarta nannauyan numfashi ya sauke da girgiza kansa, sai kuma ya saki murmushi tausayin ɗansa na ƙara ratsa masa zuciya. Mikewa yay ya fice sashen mahaifansa. Acan ya samu har su Yafendo suna hirarsu cike da farin ciki kamar yanda suka saba.
Bappi dake shan fura ya ɗan tsura masa idanu cike da nazarin ɗan nasa. Sai kuma ya ɗauke kansa. Ita kanta Anne idanun nata a kansa suke, dan tun shigowarsa ta fahimci akwai damuwa tattare da shi. Bayan ya gaishesu Inna ke faɗin, “Bashari lafiya kuwa na ganka kamar mai damuwa?”.
Ɗan murmushi yay mata yana furzar da huci. Sai kuma ya gyara zamansa sosai yana fuskantarsu. “Lafiya lau Inna, kawai nazo nayi magana da ku ne in ba damuwa”.
Yafendo tace, “Faɗi kanka tsaye Bashari mike faruwa?”.
Jin Anne da Bappi basuce komai ba ya sashi dubansu, sai dai yanda suka maida hankalinsu garesa suma ya sashi sauke ajiyar zuya. “Ba komai bane dama akan Ramadhan ne da wannan auren nasa.”
“Ba mun wuce wannan babin ba mi kuma ya faru?”.
Bappi ya faɗa yana kallonsa fuska a tsuke.
“Kayi haƙuri Bappah, bawai na dawo da hanun agogo baya baneba. Kawai ina son muyi wani abune dan ALLAH saboda wani nazari dana zauna nayi.” batare da ya jira cewarsa ba ya cigaba da faɗin. “Ni da ku duk munsan waye Ramadhan da kuma kammu, amma jama'ar gari da Ramadhan ke mulka har yanzu basu gama sanin waye shi ba. Auren Ramadhan da yarinyar nan Ameenatu dududu watanni na bakwai muke a ciki yanzu, ko shekara bamuyiba. Aurene da yasha soke-soke da kace nace a idanun mutane da bakunansu dalilin tazarar da su suke hange da mu babu ita a zukatanmu. Shin ya kuke tunani idan akace yanzu an fiddo maganar ƙara auren Ramadhan wa duniya, kuma da ɗiya irinsa mai irin matsayinsa kuma ƴar uwarsa sannan mai dukkan kishiyar abinda akai cece kuce Ameenatu bata da shi a baya?. Dama ance munyi haɗin auren Ameenatune da Ramadhan saboda mu gyara masa siyasarsa ace yana son talaka gashi harya auri ɗiyar cikinsu. To yanzu wannan auren nasa da har yanzu bamu gama sanin kansaba ake masa shiri na tashin hankali bama tunanin cikkakkiyar amsace ga ƴan ƙasa da abokan hamayya?. Ba ina fargar damu bane dan tunanin kar Ramadhan ya rasa kujera a zaɓe nagaba. Ina fargar damune domun kare mutuncin kammu dana Ameenatu yarinyar kirki da batajiba bata ganiba, hakama ina kare kunyar da zamu daurama bayin ALLAH da suka goya da bayanmu suka kuma tabbatar da tsarkake abinda mukayin badan sakamakon mu a hanunsu yake ba, sai dan bana son mu cire hope ɗin mutane akan mulkin Ramadhan. A yanzu Su'adah tazomin da wannan invitation card ɗin” ya ajiye iv ɗin gaban Bappi. “Bappah ka dubafa ka gani, events kusan goma ne anan aka shirya wanda ake fatan duniya ta gani ta shaida za'ama Ramadhan auren gata bama ƙasar NAYA kaɗai ba. Bayan kuma mu a wannan gidan duk bama hakan tun auren ƴaƴanmu na farko, sannan ko'a yanzun ma bawai shine kaɗai auren da za'a ɗaura ɗin ba”.
Tsitt falon yay bayan Pa yayi shiru. Sai dai tsananin ɓacin rai ya bayyana ga fiskokinsu bayan duk sun ga katin da tarin bidi'oin dake a ciki. Anne da idanunta suka fara cika da ƙwalla tace, “Anya kuwa Ramadhan ma yana cikin hayyacinsa? Bana son zargi sam a rayuwata ballema dana san dai Su'adah mahaifiyarsa ce babu yanda za'ai ta cutar da shi....”
Murmushi Pa yayi, cikin kunar rai yace, “Idan ita bata cutar da shi ba ai anyi amfani da ita da son zuciyarta an cutar da shi Anne. Bara yau na fito na sanar muku gaskiyar lamari akwai sihiri tattare da Ramadhan, sam abinda yakeyi ba'a cikin hankalinsa yakeba..”
Salllami falon ya ɗauka da sautin kukan su Yafendo. Yayinda Bappi ya tsurama ɗan nasa ido duk da shima ya jima yana wannan zargin. Pa yaja numfashi mai cike da takaici. “Karku wani damu kanku ni hakan yamun daɗi ai, maybe a dalilinsa Su'adah zata dawo cikin hankalinta tasan abinda ke mata ciwo. Na jima da fahimtar hakan amma bana son kowa ya nemawa Ramadhan magani dan ALLAH har sai anzo gaɓar daya dace...”
Da sauri Inna ta katse Pa, “Baka da hankali Bashari. Taya za'abar yaro a baƙar inuwar sihiri? Kenanfa kusan duk abinda yakeyi baima san yanai ba! Kai nifa ina mamakin canjawar yaron nan lokaci guda. Har takai yanzu zaizo gidan nan amma bamu sani ba. Barinsa cikin wannan tashin hankalin ai matsalane, sai ya iya shafar mulkin da yake kai ko kai baka san hakaba”.
Karon farko Bappi ya saki murmushi, cikin takaici yace, “Sadiya kenan wannan na nawa kuma. Badan ALLAH ya bashi chief of staffs na ƙwarai mai amana da tsoron ALLAH ba ai da tuni halin da Ramadhan ke ciki ya bayyana a cikin mulkin nasa. ALLAH dai ya ƙyauta. Ni yanzu inaga kai Basheer faɗi dalilinka muji, idan mai yuwuwane saimu riƙe. Idan bazai yuwuba a sake shawara”.
Kai Pa ya jinjina masa. “Bappi abinda yasa na roƙeku kar'a nema masa magani saboda dalilai uku ne zuwa biyu. Na farko ina son Su'adah ta gane kuskurenta akan Ameenatu, na biyu ina son ta gane wacece ƴar uwarta Asma'u. Na ƙarahen da bakinta nake son ta bayyana dana saninta a kansa. Dan haka ina roƙonku yin wannan aure a sirrance. A ɗaurashi a sirrance iya wakilansa da wakilan yarinyar. Akuma hana kowanne biki da suka shirya da an ɗaura aure ya dauka matarsa su wuce kawai, sauran dokokina a kansa sai bayan ɗaurin auren ne”.
Shiru falon yayi kowa na nazari, bayan shuɗewar wasu mintuna Bappi ya fara jinjina kansa alamar gamsuwa. “Kamar hakan duk yayi gaskiya. Sai dai Jannatu mi kuke gani ku?”.
Anne dake ta danne kukan dake taso mata ta haɗiye da ƙyar. “Dattijo hukuncinka ai namune. ALLAH yasa haka shine mafi alkairi”.
Da amin duk suka amsa. Daga haka suka cigaba da tattauna abinda ya dace............✍
Leave a Comment