Bakar Inuwa 57




*_Episode 57_*



..........“Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un aunty Raudha jini kuma?”. Bilkisu data shigo ɗakin a birkice ta faɗa tana ƙarawo gareta. Kamata tai suka nufi toilet, ta haɗa ruwa mai ɗumi ta taimaka mata ta wanke fuskar da hanunta, jinin dai bai tsaya ba. Sai dai sun tare da

tissue. A bakin gado ta zaunar da ita, ta ɗakko first aid box ta shiga ƙoƙarin tsaida jinin, da ƙyar aka rufe wajen da audiga da bange. Ita dai Raudha babu abinda take sai sakin ajiyar zuciya.

      “Aunty Raudha wai garin yaya? Ina Yaya kuma?”.

   Komai Raudha kasa cemata tai, sai hawaye take sharewa kawai. Hankalin bilkisu ya ƙara tashi, sai dai ta barta bata sake maganaba. Tana niyar mikewa ta maida first aid box ɗin ma'ajiyarsa ta lura da kumbirin hanun Raudha kuma. Gaba ɗaya saita sake ruɗewa ta kamo hanun tana kallo. “Ya ALLAHU, nan ma ai ciwon kikaji Aunty! Kinga bara na kira Yaya da mama ladi dan ta iya gyaran ƙashi”.

       Ita dai Raudha komai batace ba, babu jimawa suka dawo da mama ladi, bilkisu ta sake fita. Duk da ta fahimci akwai matsala ƙofar Ramadhan ta dingama knocking a ɗarare. Shiru babu ko motsi, sai ta ɗan tura ƙofar ta leƙa. Gabanta ne yay masifar faɗuwa hango Yayan nasu zaune akan tum-tum ya dafe kansa. Babu shiri ta shigo ɗakin da sassarfa. Muryarta har rawa yake ta durƙusa gabansa “Yayanmu dan ALLAH mike faruwa ne? Aunty Raudha taji ciwo sosai wlhy har a hanunta mi'akai mata”.

        Da ƙyar ya samu damar fisgo kalmar innalillahi... A cikin zuciya. Ya ɗago jajayen idanunsa ya zuba kan Bilkisu datai matuƙar razana. Dan rabon da su gansa a irin wannan yanayin tun rasuwar su Haseenah. Baya taɗan ja jikinta na rawa. Shima sai ya cije lips sinsa da ɗago hanunsa ya kalla. Sai kuma ya dafe kansa dake matuƙar juya masa. Kusan minti ɗaya ya sake ɗagowa ya dubi Bilkisu da gaba ɗaya ta gama tsorata. Cikin yanayin damuwa yace, “Ina Ameenatun?”.

       “Tana ɗakinta Yaya, nabar Mama ladi zatai mata gyara a hanunta dan harya kumbura, ga goshinta ya fashe da ƙyar na iya tsaida jini....”

      Ai bama ta ƙarasa ba ya miƙe hankali tashe. Sai dai hakan bai hana bayyanar nutsuwarsa ba. Fita yay Bilkisu tabi bayansa. Kai tsaye ɗakin Raudha ya nufa, sai dai yana ɗaura hanunsa bisa handle ɗin ƙofar ya dafe kansa da yay masifar sara masa. Da sauri ya shiga girgiza kansa yana ja da baya. Barin wajen yay ya sake komawa hanyar ɗakinsa. Bilkisu ta bisa da sauri tana kiransa. Wata razananniyar tsawa data sakata jan birki ya daka mata, yay shigewarsa ya bugo ƙofar da ƙarfi har Bilkisu na zabura.

          Kuka Bilkisu ta fashe da shi. dan kuwa ta fahimci lallai akwai matsala, sai da tayi mai isarta ta koma ɗakin Raudha. Ta jiƙe sharkaf da zufa kamar ba ac a ɗin saboda gyaran da mama ladi tai mata. Mama ladi dake naɗe mata hanun da bandage ta dubi Bilkisu. “Taji ciwo sosai, dan gocewar ƙashi ta samu. Garin yay hakan?”.

        Kafin Bilkisu ta bada amsa cikin share hawaye Raudha tace, “A toilet ne na zame”.

      Sannu Mama ladi ta shiga jera mata. Bilkisu dai wani irin tausayin Raudha ɗinne ya lulluɓeta. Dan ta tabbatar daga yayansu aka samu matsalar musamman da taga shatin yatsu a fuskar Raudha alamar marinta akai. Magani ta sha ta kwanta bayan tayi sallar magrib da isha'i, babu jimawa kuwa barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Bakajin komai sai ajiyar zuciyarta.

        Tagumi Bilkisu tai zuciyarta nata kaikawo. tama rasa ina zata kama akan wannan al'amari. Kusan tara na dare sai ga kiran Basma ya shigo mata. Da farko kamar bazata ɗaga ba sai kuma ta daure ta ɗaga wayar na gab da tsinkewa. Wani irin dummm kunen Bilkisu yayi jin abinda Basma ta faɗa. Muryarta har rawa take wajen maimaita “Basma shi Yaya Ramadhan ɗin da kansa yace zai auri Aynah?”.

      Daga can Basma tace, “Wlhy kuwa Aunty B. A gabana Maah tai waya da shi yanzun nan sai farin ciki take tana saka masa albarka. Ni nama rasa wanda zan tunkara da wannan abun al'ajab shine fa na kiraki naji ko wani abu ya faru anan”.

     “Nan dai babu abinda ya faru, sai dai yana ɗakinsa. Amma dai wannan lamari da ɗaure kai. Basma anya Adda Asmah bata fara cin galaba akan Maah ba?”.

        “Aunty Kamar ya?”.

Saurin dafe kai Bilkisu tai jin zata saki layi. Ta manta ita kaɗai taji abinda Adda Asmah ta taɓa faɗa akan Mahaifiyarsu kwanakin baya sanda ake tsaka da rikicin auren Yayansu da Raudha. Kuma bata taɓa nuna ta saniba ko taɓa faɗama wani. Sai dai tana kallonta da abun kuma tun daga ranar taji bata sonta duk da yayar Maah ce. Hasalima tafi shiri da ita fiye da kowa a ƴaƴan gidansu, dan ita takan iya zuwa ta kwana gidansu Aynah ɗin ma ba kamar su Basma ba. 

           


★★★_____★_____★★★


         Tabbas abubuwa sun kwaɓe a tsakanin Raudha da shugaban ƙasa Ramadhan. Ita gaba ɗaya tsoron haduwarsu ma takeyi, yayinda shi yasha gwada zuwa gareta da zaran ya iso kofar ɗakin sai yaji wani irin mugun tsanarta mai ban mamaki, dole yake juyawa ya fasa. Babu abinda Raudha keyi sai kuka, sai dai duk da haka tana ƙoƙarin zuwa makaranta. Bilkisu tayi-tayi ta faɗa mata ainahin abinda ya haɗasu taki. Takuma roƙota ALLAH akan karta sanarma su Anne. Rasa mi Bilkisu zatai tayi, sai kawai ta zubama sarautar ALLAH ido tana tayasu da addu'a.

       A cikin kwanakin da basu gaza gomaba da faruwar komai Raudha duk ta fige ta rame. Sai uban haske datai ta ƙara tsayi. Kullum babu fashi zataje ta gyara masa ɗakinsa, duk bayan kwana biyu ta wanke masa under wears ɗinsa dan tafi gane wankesu da hannu ba Worthing machine ba. Idan ta gama sai tai drying nasu a machine ɗin. Komai dare kuma sai tayi zaman gogesu bayan ta musu turare na turaren wutarta na kaya mai daɗin ƙamshi sannan ta maida ɗakinsa ta jere masa.

        Sam ya daina shigowa gidan da wuri, weekend kuwa har taci ta ƙare bai yarda sun gamu ba. Bata da aiki sai kuka da gayama UBANGIJI. Dan ta rasa wanema irin tunani zatai akan sauyawar tasa. Koda zuciyarta ta nuna mata dama sabbin halayyar daya fara mata yayine dan ya samu jikinta sai tai saurin ture tunani dayin a'uziyya. A haka suka sake cinye sati uku babu wani canji.


*_RAMADHAN_*


       A sashen Ramadhan shi kaɗai yasan tashin hankalin da yake ciki na tsananin son Ayna'u. Bashi da burin daya wuce mallakar Ayna'u matsayin matar aurensa. Kullum cikin yima su Bappi nacin akai kuɗi yake dan abun yanzu ya wuce Maah kawai har Anne da Pa da Bappi duk sun sani. Tun suna ɗaukar abun nasa wasa harya koma basu haushi. Dan ranar daya kai Pa ƙarshe akan lamarin ba karamin zagesa yay ciki da bai ba. Ya kuma masa dogon gargaɗi akan inya sake zuwa masa da batun Aynah sai ya matuƙar ɓata ransa. Dama kuma itama Maah yaja mata gargaɗi akan damunsa akai kuɗi da takeyi.

       Wannan zagi da Pa yay masa ya matuƙar ƙona masa rai, dan kuwa dai a fusace ya dawo gidan. Abin tsautsayi Raudha na ɗakinsa tana gyarawa dan yau ta fita school da wuri tama rigashi fita, shiyyasa bata gyara masa ɗakin ba sai da ta dawo tunda shi bai dawo ba. Ba karamin firgita tai da ganinsa ba, dan rabonta da shi tun randa abin nan ya faru sai dai ta gansa a tv ko hoto. Duk ya rame mata a ido yayi duhu. Wata irin tsawa ya daka mata data nema wantsalo zuciyarta ta baki. Tai nufi fita masa a ɗaki ya shaƙota ya jefa saman gado.


       Lallai Raudha ta tabbatar a baya wahalar da takesha a hanunsa ba wahala bace. Dan kuwa lallaɓata yake kuma cikin soyayya mai gusar da hankali. Amma a yau ta tabbatar da waye Ramadhan. Kuka take kamar ranta zai fita tsabar yanda ya wajiga rayuwarta. Daga ƙarshe ya korota a ɗakin. Da ƙyar ta iya kai kanta nata ɗakin, ALLAH ma ya sota Bilkisu bata gidan. Su mama ladi kuma indai ba ita ta buƙaci ganinsu ba babu mai hawo musu nan sai in zaiyi aiki. Ƙofar ta murzawa key sai dai bai rufu da ƙyau ba ta zube jikinta tana jan numfashi da ƙyar, tsabar kukan da taci har asthma ɗinta na ƙoƙarin tashi. Rarrafe ta dingayi hanunta rike da ƙirjinta, da ƙyar takai kanta jikin gado ta ɗauka inhaler ɗin akan bedside drawer. Tata ƙoƙarin ganin ta shaƙa hakan bai yuwuba, har takai numfashinta na neman fara nisa ALLAH ya kawo Bilkisu.

       ALLAH ya taimaka ƙofar data rufe bata rufu ba. Da lallai zatama iya rasa ranta a wannan lokacin. Taimakon gaggawa Bilkisu ta bata, da ƙyar numfashinta ya dai-daita. Raudha dake magana a wahale ta roƙa Bilkisu ta haɗa mata ruwa mai zafi sosai. Bilkisu batasan mike faruwa ba. A tunaninta ko duk halin tashin Asthma ɗinne data shiga da kuma gajiyar makaranta. Bayan ta haɗa mata ta fito ta taimaka mata zuwa bayin, duk da dai yanda taga Raudha na tafiya a bubbuɗe ya ɗaure mata kai matuƙa.

      Da ƙyar Raudha ta iya gyara jikinta, tai luff a cikin ruwan ɗumi tana hawaye da addu'ar ALLAH ya bata juriyar cinye wannan jarabawa. Amma tabbas zuwa yau ta fara fahimtar mijinta baya cikin hayyacinsa. Akwai abinda ke faruwa da shi da su basu sani ba. Zata tayashi da addu'a koma minene ALLAH ya yaye masa shi.

  

     Kamar wasa sai ga karamar magana ta zama babba, dan kuwa dai ciwo sosai Raudha ta kwanta washe gari ko makaranta bata iya leƙawa ba ma. Kusan kwananta uku a halin jiyya kafin ta warware ta cigaba da harkokinta. Sai dai fa a yanzu babu wanda take tsananin tsoron haduwa da shi a duniya sama da Ramadhan. Ko maganarsa taji a tv sai gabanta ya faɗi. A haka rayuwa ta sake turawa suka sake cinye sati huɗu, sati kusan na bakwai kenan da shiga halin da suke ciki. Zuwa yanzu kuma har an kai kuɗin auren Aynah saboda birkicewar da Ramadhan yay musu.

       Tuni Pa ya fahimci akwai sihiri tattare da yaronsa. Amma ya zaɓi barinsa a hakan dan yanaji a ransa dole sai Adda Asmah ta shayar da gimbiya Su'adah zumar mamaki sannan zata san ANNABI ya faku. Koda su Bappi ma suka fara irin wannan zargin Pa ɗinne ya gusar musu da zargin ta hanyar nuna musu babu wani sihiri uwarsa ke zugasa. Yayi hakane dan baya son suce zasu tashi tsaye akan Ramadhan ɗin, yafi son sai uwarsa taji a jikinta sannan. Amma kuma bai gaza da masa addu'ar kariya ba. 

      Abinda hankalinsu kuma ya gagara kaiwa akai su duka basuyi tunanin ko abin ya shafi Raudha ba. Dan ita dai ko sau ɗaya bata kawo wa kowa ƙararsa ba. Ta kuma hana Bilkisu faɗa duk da itama Bilkisun ba komai ta sani ba har yanzun. Kullum kuma Anne ta tambayi su Basma sukance Raudha na lafiya harma tana gaishesu tunda kullum dai suna tare a makaranta. Hakanne ya ɗan basu nutsuwa suke ganin shi kaɗai abin ke dawainiya dashi kenan.


         ALLAH sarki Raudha, sai dai kuma abinda ba'a sani ita kaɗai tasan halin da take ciki, ga yanzu kullum da zazzaɓi take kwana. Ga kasala da batasan kota minene ba. Komai da ƙarfin hali take yinsa hatta karatun. Ita Bilkisu tana ɗaukar yanayin natane kawai da tunanin maganar auren Ramadhan ɗin. Dan haka ta maida hankali wajen bata shawarwari da nasiha.

      Bazatace auren Ramadhan baya damuntaba, dan tasan wacece Aynah tasan kuma burinta akanta, dan tunda Ramadhan ya fara birkice mata Aynah da Addah Asmah suka kirata sukai mata zagin ƙare dangi saboda fahimtar ita sihirinsu bai kamataba. A tunaninsu itama bin malaman take shiyyasata ta tsira. Basu san ALLAH ne bai ƙaddara mata shan zoɓon waccan ranar ba kawai. Ranar taci kuka matuƙa dan zagine da cin mutunci da bazai taba goguwa a zuciyaba kai tsaye. A kalamansu kuma ta fahimci lallai akwai ƙullin dake kan mijinta da alama kuma sunada alaƙa da shi. Bata da abin faɗa, dan koba komai dai ƴan uwansa ne. Adda Asmah ma na amsa sunan uwane a garesa tunda yayar mahaifiyarsa ce da itama zata iya kiranta da uwa. Haka ta cigaba da masa addu'a da ita kanta abun na damunta.

      Sai dai halin da take ciki na rashin jin daɗin jiki yafi kwashe kaso mafi yawa na damuwarta. Ko mahaifiyarta batasan halin da take a ciki ba. Sai dai a duk sanda sukai waya takance Mummy kimin addu'a. Idan asabe ta nuna damuwarta cikin tashin hankalin furicin Raudhan sai ta dinga kwantar mata da hankali akan babu komaifa saboda karatu take cewa hakan.

     Ita dai Asabe hankalinta ba wani ya kwanta bane. Amma sai ta dage da bin ɗiyarta da addu'ar fatan alkairi. Itama kuma Raudha bata wasa. sosai take a kan ƙafafunta tana gayama ALLAH damuwarta akowanne dare. Wani lokacin ma tana salla tana rawar sanyin zazzaɓi, haka ta dage da azumin alhamis da litinin. Ta kuma dage da saka har Abba (M. Dauda) turama kuɗi akan ya bada sadaka yasa a mata addu'a ita da Ramadhan. Da yake shi kan babu notika ɗaurarru maimakon ya fahimci akwai matsala sai ya kama dariya yana yana faɗin.

        “Ƴar nema taji daɗin gidan gwamnati bata son suyi shekara biyar kawai. Indai addu'a ce kin tara kin samu, yau kaf almajiran dake garin hutawa saina bisu kowacce tsangaya na tattare da malamansu sun saka rokon ALLAH, dan nima inason ku koma hawa na biyun ai. Amma Raudha ya kamata kima mijinki magana ko ministan bada kuɗin fansho ya bani mana. Zamannan ya isheni haka kinga wannan sarautar ba wani kuɗi ake samu ba sai uban fama da rawani da zazzare ido a fada. Ni badan ma kar hakimi yace na raina karamcinsa ba da wlhy tuni na ajiye. Ni kuma yan kuɗina kullum kasa suke, dan ma ALLAH ya taimakeni wanda Ƴaƴan Larai suka sata an ganosu ai da yanzu hawan jini ya shanye muku ni.

     Murmushi Raudha tayi tana share hawaye. “Karka damu Abbah insha ALLAH zan san abinyi. Amma nidai gara kayi haƙuri ka cigaba da zuwa gidan hakimin”.

     “To ai duk yanda kikace haka za'ai uwata farar haihuwa farar aniya your excellency. Insha ALLAH sai kunyi goma indai mulkin NAYA ne”.

    Dariya ta ƙyalƙyale da shi babu shiri dan ya bata dariya sosai. Da ga haka sukai sallama ta ajiye wayar. Bargo ta kara ja har kanta dan wani irin sanyi mai ratsa ƙashi takeji. Ga ƙasusuwan ta kamar ana mata daka a kansu. Saboda zazzaɓin yau ko lecture ɗin karshe bata zaunaba ta gudo gida. Sai dai ta iske Bilkisu bata dawo ba. Haka shima mai gayya mai aikin da rabon dama ta sakasa a ido tun randa yay mata murzar ƴan bori. Dan ko zaune take a falo da taji shigowar motocinsa take shigewa. Ta katange duk wani abinda zai haɗasu a inuwa ɗaya saboda kare mutuncinta da nashi. Tun kusan satin baya take tunanin yanda zata fara masa addu'oin warware sihiri, idan ma shine tare da shi sai dai bata san ta hanyar da zata bashi yasha ba tunda baicin abincin gidan yanzu sai yaso. Hakan yasa ta haƙura ta barma ALLAH komai ya kawo musu mafita. 

     Barcine ya ɗan figeta da sam bama daɗi yake mata ba. Dan har a cikinsa tanajin ciwon dake nukurkusarta. Bude ƙofar ya sakata farkawa aɗan razane...........✍

     

No comments

Powered by Blogger.