Bakar Inuwa 56
*_Episode 56_*
...........“Oh oh wai duk zaɓen akwatinne ya saki tafiya tunani Mrs Ramadhan ”.
Firgigit Raudha ta dawo hankalinta. Sai kuma tai Murmushin da sauke ajiyar zuciya. Bilkisu tace “Uhm kodai mu bari sai da safe naga hankalinki nakan mijinki, nima gara na barki ki wuce kafin ya fara hararata”.
“Kai auntu Bily”.
Raudha ta faɗa cike da kunya.
“To ai gaskiya na faɗa, gashi sai murmushi kike kina tunani, kwantar da hankalinki gashi can zaune ko'ina baijeba”.
Ita dai murmushi kawai Raudha tayi ta cigaba da duban akwatinan. Wasu Silver color ta zaɓa. Bilkisu tace, “Woow kinsan kala Auntyna wlhy ni kaina hankalina na kansu tun ɗazu. Sai ki ƙara biyu wai set uku yake so, dan da biyar yace nidai nace sunyi yawa gara ayi abin hankali sauran kuɗin aba mabukata.”.
Cikin zuciya Raudha ke jinjina masu kuɗi na abinda suke so. A fili kam sai ta murmusa. “Hakan da kikai yayi aunty, da ana samun irinku da almabazaranci da dukiya ya ragu ai. ALLAH ya sanya alkairi yasa damu za'ai”.
“To amin auntyna. Inshaa ALLAH lokacin kina fama da babynmu ma”.
“Kai aunty Rufan asiri”.
Raudha ta faɗa tana mikewa. Itama Bilkisu mikewa tai tana dariya suka nufi falon inda Ramadhan ke zaune har yanzu yana kallon labaran...
A falon duk suka zauna. Bilkisu taima Yayanta sallama ta wuce ɗaki danta basu waje suma su shakata. Ganin hakama Raudha ta dubesa tana hamma. “Yaya baka bukatar komai naje nima na kwanta”.
Shiru bai tanka mata ba. Harta fidda rai da samun amsa taji yace, “Zo nan”.
Mikewa tai duk a tsorace taje gareshi. Tana koƙarin zama a kujerar gefensa ya riƙota ta zauna saman cinyarsa. Kusan tare suka sauke ajiyar zuciya. Matso da ita yay ta raɓu jikinsa har tana jin saukar numfashi sa a dokin wuyanta. Ya kama hanunta ɗaya cikin nashi yana murza yatsun a hankali. “Ameenatu baƙya tsoron wata ta ƙwace miki ni? Idan kinamin irin wannan riƙon na rashin kulawa tuni zan koma ba naki ba.”
A take idanunta suka cika da ƙwalla. Dan gani take yana mata ishara da aurensa ne kawai. Cikin rawar murya tace, “Dan ALLAH kayi haƙuri bazan sakeba. Ko zanji zafin zanyi juriya”.
Numfashi ya sauke a hankaki yana sassauta muryarsa. “Ni ba ina miki magana akan hakan bane. Ɗazu fa a gida ficewarki kikai sabgar da ba'a aikekiba kika barni ni kaɗai da shirin office, maimakon kizo muyi sallama ma sai kikaƙi. Dazan wuce ko addu'a bakiminba. Na dawo gida kuma na sameki babu wani tarba kin sake barina ni ɗaya a ɗaki kamar ba mijinkine ya dawo ba. Haka aka koya muku kula da miji a islamiyyar?”.
Kanta ta jinjina masa amalar a'a.
Juyota yay suna ɗan fuskantar juna. Ya tsura mata idanunsa masu kaifi da ƙarfi. Har yanzu yatsun hanunta na cikin nashi still dai yana murzawa.
“Amma k miyasa kike son yima mijinki haka? Ko kina so wata tazo ta ƙwace ni?”.
Ai babu zato sai kawai ta rushe masa da kuka tana faɗawa jikinsa.
Murmushi ya saki mai faɗi, yasa hannunsa ya zagayo kugunta ɗayan yana shafa bayanta alamar lallashi. Sai dai baiyi maganaba tsahon mintuna har tagaji tai shiru da kanta. Ɗagowa tai tana goge hawayenta. shiko sai faman binta da ido yake.
“Ustazah kishi fa kenan? Anya wannan zuciyar bata kamu da son Ramadhan B. Hameed Taura ba mai tsanani?”. Yay maganar yana ɗora yatsansa manuniya saitin zuciyarta. Kunyace ta kamata. Amma sai ta ɓata fuska da ture hanunsa.
“Ni ba wani kishi”.
Karamar dariya da rabonta da gani a garesa tun jiya yayi har haƙoransa na bayyana sosai. Ya shafa fuskarta da faɗin, “To shikenan naji ba'a son Ramadhan balle ai kishinsa. Sai dai ina bada shawara a gyara kafin naki ɗage kafar tafiya aljannar”.
Murmushi tayi cike da kunya ta sake sinne kanta a jikinsa. Daga haka suka shirya. Sai dai koda suka nufi ɗakinsa yayin kwanciya babu abinda yay mata sukai barcinsu lafiya.
★_______★______★
Dauriya iya dauriya Ramadhan yayi akan kin sake kusantar Raudha, sai dai salon yanda yake mata abubuwa ya ƙara shaƙuwa a tsakaninsu. Ga Bilkisu na sake ɗaurata a layi sosai ita da mama ladi. Gefe kullum Asabe cikin yima yarta nasiha take akan abubuwa da yawa da abaya tasan ita ta tafka kuskure a kansu a rayuwar nata auren.
Karatunta na tafiya lafiya cikin aminci, randa Ramadhan bai gajiba idan ya dawo sukanyi karatu ya kara faɗaɗa mata bayani akan abinda bata ganeba. Hakama Bilkisu na iya bakin koƙarinta. Acan school kuwa sun ɗinke da Queen Billy da batasan wacece Raudha ba. Har yanzu ma bata yarda ta nuna mata fuskarta ba. Duk da tasan kota nuna ɗin da wahala ta ganeta tunda dai babu wanda zaice ga ainahin fuskarta a duk hotuna dake yawo a media ita da shugaban kasa saboda facemask da take sakawa a koda yaushe idan suna tare. Su Basma ma sun karɓi Queen Billy, dan tanada shiga rai saboda barkwancinta da yawan fara'a. Ranar juma'a da take cika kwana biyar ciff batare da Ramadhan ya sake neman komai daga garetaba ta dawo school a gajiye da yamma lis. A falo ta iske Bilkisu da Ramadhan daya dawo gida da wuri yau. Dan shima Alhmdllhi komai yana tafiya masa dai-dai babu abinda gwamnatinsa keyi yanzu sai shimfiɗa manyan ayyuka da yan ƙasa keta sambarka. Irinsu Alhaji Haladu Gwandu da su forma president da God Fathers nasu kuwa na gefe sun shaka sunyi fam da takaici. balle kuma vice president da kamar ya zama hoto ga wasu al'amuran na gwamnati. Dan shegen mugun halinsa da Ramadhan ya fara fahimta ya sashi ɗan janye jikinsa da shi abubuwa da yawa sai dai ya gani a takarda. Ga kuma binciken da suke kanyi akan abinda suka fahimta game da alakar matarsa da Raudha.
Bilkisu ce kawai ta mata sannu, gogan ko ido kawai ya tsura mata yana kallonta ƙasa-ƙasa duk da fuskarta sakaye take da niƙab. Baki taɗan tura da kauda kanta daga garesa tace, “Ina yini”.
Shiru yay bai amsa ba, sai ma sake karkatar da kai yayi. Bilkisu dake musu dariya ƙasa-ƙasa ta miƙe cikin sanɗa tabar wajen. Ganin haka Raudha data yaye niƙab ɗinta tana kumbura fuska itama tabar wajen ta nufi ɗakinta. Idanu yaɗan lumshe da saki tattausan murmushi yana shafar kwantaccen gashin fuskarsa da yayma gyara ɗazun da safe san dan samun yin sallar juma'a cikin annuri da haiba.
Yana nan zaune a wajen har Raudha ta sake fitowa bayan kusan mintuna talatin. Sanye take da skirt da riga na atamfa, sun mata ƙyau sosai sun kuma kama mata jiki ɗam saboda ƙibar data ƙara. Dan sosai Raudha ke buɗewa ta ko'ina tana ƙara girma. Ga wani haske da tayi fatanta ya ƙara kwanciya luff da ɗan duhun da bazaka kirata fara ƙal ba.
Tsabar jan magana ta gaban Ramadhan tazo zata wuce kanta ko ɗankwali babu. Sai gashinta dake tsefe data ɗaure da ribbon yanata reto. Yi yai kamar bai ganta ba. Sai dai ta kusan gama giftashi ya taɗota da ƙafa sai gata a jikinsa. Ƴar ƙara ta saki mai cike da zallar shagwaɓa. yay saurin buge bakin da yatsunsa biyu.
“Wayyo Anne zai fasamin baki”.
Ta faɗa hawaye na ciko mata. Zata tashi ya maidata, kamar gaske ya wani tsuke fuska. Cikin ɗage gira da hararta ya sake kaima bakin nata ɗalli ta kare. “Na kula kin fara rainani a gidan nan. Harni zakima ƙwalele da halalina”.
Idanu ta waro sosai sai kuma ta rufe fuska. “ALLAH dai yana gani ni babu ruwana. Kawai fa wucewa zanyi ni koma ganinka banyiba”.
“Oh really?”.
Ya faɗa yana mikewa dauke da ita. Roƙonshi ta farayi tana wantsala kafafu akan itafa badashi takeba ALLAH yunwa takeji. Dan ALLAH yayi haƙuri bazata sakeba. Ko kulata baiyiba ya maida ƙofar ɗakinsa ya datse da key duk da yasan babu mai zuwa sashen. Cakulkulo ya fara mata daga kuka ta koma dariya da bashi haƙuri, bai ƙyaleta ba sai da suka dire cikin gadonsa. Salon daya fara bi da itane ya sata shagala da farko, sai da labari yay nisa a nanfa ido ya raina fata. Ta shiga magiya da roƙo akan abinda shi kuma anzo gaɓar da bazai iya ɗaga kafarba. Aiko taji ajikinta, dan har dana sanin shiga huruminsa tayi. Kuka kam ba'a magana.
Sun fito wanka yake dubanta da murmushi yanda ta lafke a gado tana sakin numfashi da ƙyar kamar wadda ke a cikin ciwo. “K kuwa yarinyanan an miki wankan jego kina jinjira? Shikenan da'an ɗan taɓaki sai ki sharɓema mutane a haka za'a haifa ƴan huɗun?”.
Shiru tai masa kamar tai kuka. Haka kawai yaji dariya ta taho masa. Bai iya dannetaba ya ƙyalƙyale kuwa. Haushine ya kama Raudha, a ganinta tsantsar muguntace ya gama wajiga rayuwarta ya dawo mata dariya. Sai kawai ta sakar masa kukan karya.
“Okay kukama kike? To bari kawai na sakaki mai dalili mana da kiyi na banza gara kiyi na lada.....”
Kafin ya rufe baki har takai ƙofa. Baki ya buɗe zaiyi magana gabansa yay wata irin masifaffiyar faɗuwa tare da kansa daya sara masa. Da sauri ya dafe kan yana ambaton sunan ALLAH. Raudha data zata wayau yake son mata tai tsaye kawai tana kallonsa da murmushi. “Ya Ramadhan na riga nasan wayonka ai. Shine harda pretending?”.
Jin shiru bai amsa mataba ga kujera ya dafe har lokacin hanunsa dafe a kansa kamar maijin hajijiya yasata daina dariyar ta tsura masa idanu. Da sauri ta ƙarasa garesa ganin ya tafi kamar zai faɗi. Tarosa tai, sai dai yanayin jiki ba ɗayaba yafi karfinta musamman da jikin nasa ya saki sai suka zube ƙasa ya faɗa kanta. Ƴar ƙara ta saki da ambaton sunan ALLAH saboda wani raɗaɗi daya ratsa mata hanunta da suka faɗi a kansa. Tai ƙoƙarin dannewa amma ta kasa dan azaba. Kuka ta saki tana son turesa sai dai ina. A take jikinta ya fara rawa, ta turashi iya karfinta yay ƙasa da ƙyar, sai dai kafin ya dire a bazata taji ya ɗauke fuskarta da mari.
“K! Baki da hankaline ni zaki ture?”.
Ya faɗa a matuƙar kausashe da muryar da ko sanda basa shiri bata taɓa ji daga garesa ba. Lallai ta maru, dan yay bala'in shigarta, zata iya rantsewa kuma shine na farko a duniya daya taɓa marinta, tsabar azaba har kifewa tai akan table sai ga goshinta ya fashe. Idanu ya waro a ɗan tsorace yay kanta yana ambaton “Ya salam Ameenat....”
Sai dai yana kai hannunsa jikinta ya sake tureta da ƙarfi ya sake dafe kansa dake juya masa. Duk yanda yaso yin addu'a bakinsa yay masa nauyi ya kasa furtawa. Duk da azabar dake ratsa Raudha a goshi da hannu haka ta sake nufarsa tana kiran sunansa a tsorace. Sai dai tana matsawa garesa ya sake hankaɗeta a matuƙar tsawace yace, “Fitarmin anan!!”.
“Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un Ya Ramadh.....”
“Nace ki fitar min anan!!”.
Ya faɗa a wani irin yanayi na fita hayyaci da tsananin ɓacin rai. Sosai jikin Raudha ke rawa kuwa yanzu. Ta fita a ɗakin da sauri kuka na kufce mata. Ga jini harya wanke mata fuska duk da taresa da tai da hanunta mai lafiya. Hanunta daya bugu kuwa wata azaba yake mata harya fara yawa da kumburi. Bata samu kowa a falon ba, sai dai karar buɗe ɗakinta da bugo ƙofar ta rufe ya fargar da Bilkisu dake gaban mirror tana kallon film a lap-top. Da sauri ta fito sai idonta yaci karo da ɗigon jini, a razane tabi jinin da kallo har ƙofar ɗakin Raudha, ai bama tasan kalar tsallen datai kawai ta ganta jikin ƙofar ba.............✍
Leave a Comment