Bakar Inuwa 55

 


_Episode 55_*..........Yau ɗin ma dai kukan tasha sosai fiye dana ranar ma, a ganinta yauɗin ma babu banbanci da shekaran jiyan. Shidai aikinsa lallashi da jinjina ragwantakarta, duda dai yasan shi ɗin bana wasa bane. Bayan sallar asuba koda ya nuna sake ziyartarta kuka ta

saka mishi iya gaskiyarta tana roƙonshi idan ya sake mutuwa zatai ita dai. Ta bashi tausayi ta bashi dariya kuma. Amma sai ya gimtse da nuna mata baifa san zancen ba a haka zata saba ai. Kuka sosai ta dingayi tana yarfe hannaye kamar wata ƙaramar yarinya. ALLAH ne ya taimaketa Bappi yay kiransa zasuyi magana, dan dama shirin office zaiyi daga Taura house can ya nufa. Ita kuma sai ƙarfe ɗaya zata wuce gaida su asabe daga can ta zarce gida.

       Badan yaso ba dole ya miƙe ya zura doguwar rigar jallabiya ya fita batare daya kalli Raudha dake maƙure cikin labule ba tana sharar hawaye. Ganin ya fice ta faɗa toilet, wanka tayi da ƙara gyara jikinta dan ita dai harga ALLAH zafi takeji sosai. Yau dai anyi jarumta an shiga ruwan zafi tanata raki ita kaɗai. Koda ta fito harta shirya ta gyara ɗakin bai dawo ba. Dan haka ta saka hijjab ta fita gaida jama'ar gidan.

     Kamar ko yaushe bata wani samu tarban arziki ga gimbiya Su'adah ba. Sai ma zageta tas da Lubnah da Aynah sukayi wai kwana uku batazo ta gaishe da Maah ɗin ba. Bata da abin faɗa dan tasan ita mai laifi ce. Yau ma da taimakon Bilkisu ta baro sashen bayan ta zage Aynah da Lubnah duk da kuwa duk sun girmeta. Masifa taitaima Raudha akan lokaci yayi da zata ƙarfafa ranta tabar zama su Lubnah na takata yanda suke so koda agaban Maah ne. Maah uwace, amma su ai ƙannene a gareta koda sun girneta tunda kanen mijinta ne. Murmushi kawai Raudha tayi amma komai batace ba.

        Ƙin komawa tai part ɗinsu duk da Anne tace Ramadhan ya baro wajen Bappi, suna nan a falon suna taya Anne shirya table Ramadhan ya fito cikin shirin office. Ɗanyar shaddace golden yollow a jikinsa daketa maiko harda babbar riga, sai dai bata cika girma ba dai-dai irin ta matasan zamani da suke yayi. Sai baƙin takalmi _chukka boot_ da hula tangaran daketa ɗaukar idanun mai kallon. Ko kunya babu ya miƙama Raudha dake ƙoƙarin gyara mayafinta agogonsa _zenith_ wai ta saka masa. Sai wani faman ɗaure fuska yake. Sai da taɗan dubi sashen da Bilkisu da Anne suke taga sun ɗauke idanunsu kamar basu san mike faruwa ba sannan ta amshi agogon ta ɗaura masa kunya kamar ta nutse.

      Kona gode babu ya raɓata ya wuce zuwa dining. Ta ɗan bisa da kallo ranta fes dan gara wannan fushin da azabar da tasan zata sake ɗanɗana a hanunsa. Anne ce ta sakata dole ta haɗa masa abinci, sannan suma suka zauna har Bilkisu da data karya anan. 

     “Yaya kamar bakajin daɗi?”.

Cewar Bilkisu cike da kulawa. Anne da tun ɗazu hankalinta na kansa itama dai kallonsa tai. Ya ɗan yamutsa fuska da sake tsuketa. Sai dai komai baice ba. Anne ce ta sake maimaita masa tambayar Bilkisun. Cikin ɗan haushi-haushi yace, “Kawai bana son fitar ne”.

     Ƴar dariya Anne da Bilkisu sukai da lallashinsa. Raudha kam da tasan ainahin fushin murmushi kawai tai taƙi yarda kuma su haɗa ido. Shi ya fara miƙewa. Harya gama sallama da Anne zai wuce ya faki idonta ya sakarma Raudha ranƙwashi akai.

    Ba shiri ta saki karamar ƙara. Gaba yay abinsa ko waiwaye babu, Anne da komai ya faru akan idonta tace, “Mugunta dai babu ƙyau wlhy Ramadhan mita maka?”.

      Ƙin tankawa yay, sai ya ɗagama Anne yatsunsa biyu alamar bye. Ita dai Bilkisu dariya kawai take ranta fal nishaɗi haƙarsu ta kusa cimma ruwa. (Batasan tuni tacin ba itace bata da labari). Bayan mintuna kaɗan suka jiyo jiniyar tafiyar motocinsa. Hakan ya bama Raudha damar bararrajewa suka daura hira da Bilkisu da Anne. Kusan ƙarfe goma baƙuwar Anne ta iso......

         Sosai kunya ta lullube Raudha lokacin da hajiya take bayanin kayan da Anne tasa aka kawo mata nagartattu haɗin sakwattawa birnin shehu tun daga ƙasar Nigeria. Hajiya. Bata wuce ba sai kusan sha biyu, a lokacin Raudha ma ta mike taje tai shirin dan lokacin tafiyarsu ya gabato. Umarnin Anne ta bi na zuwa yima su Gimbiya su'adah sallama. Bayan ta kammala da kowane part harsu Yafendo ta nufi part ɗin surukarta a ƙarshe. Ita kaɗai ta samu a falo hakimce cikin kwalliya sai zuba kamshi take, duk da tasan bata kaunarta ta daɗe da bata lambar girma da yabo na iya tsara kwalliya da ado, dan sosai jikin gimbiya Su'adah ke ɗaukar wanka, ƙyaƙyƙyawa ce itama gata fara tas masha ALLAH, matsalarta kawai bata fara'a kamar wata sojiya😖.

      Kamar ko yaushe data gaisheta bata amsaba. Ta watsar da ita a durƙushe tsahon muntina, Raudha data ga karta makara tai mata sallama zata mike amma saita dakatar da ita. Cike da gadara da tsanar data kasa haɗiyewa tata tace, “Kin dage sai kin zauna da Ramadhan duk da na nuna miki hanyar salama kin runtse idanunki. Okay fine, sai ki shirya shigowar Aynah ku goga kishi, mai sa'a ta haye”.

     Wani irin dummm kunen Raudha ya ɗauka. Ta ɗan ɗago ido ta dubi gimbiya Su'adah. Sai dai wulaƙantaccen kallon data maka mata ya sata maida idanun ƙasa dole. wani irin abune yake sukar zuciyarta mai zafi da batasan ma'anarsa ba. (Kishi?) kai ina na kishi bane, domin *_babu so miya kawo kishi?_ maybe tsoro no kawai. To amma abinda takeji baya kama da tsoro sai jin ɗaci. Dan har wata hajijiya takeji kamar tana yawo da kanta a sararin samaniya. Sai dai ta danne a nutse taima Maah godiya da sallama ta mike ta fita duk da bata amsa mata ba. 


        Gaba daya Raudha bata fahimtar komai a gidan hajiyar birni. Babu abinda ke mata kaikawo a rai da zuciya sai furucin Maah na auren Aynah da mijinta zaiyi. Tabbas ko taƙi kota so ta yarda ta fara son shugaban ƙasa Ramadhan. Irin son nan kuma mai kama zuciya da baya saki cikin sauki, duk da ita har yanzu bata da tabbacin shiɗin yana son nata. Tun tana dauriya har saida hawaye suka dinga ziraro mata, saukintama akwai ba'a gaban Asabe bane. Kagara tayi ta koma gida dan bata son tayar musu da hankali, gefe kuma tana kwaɗayin yin maganar da Mommy ko taji sanyi a ranta dai.

     Basu bar gidan ba sai bayan sallar la'asar. Driver ɗinta ta samu yana jiranta, dan hala tai sallama da su Basma da sukai mata rakkiya ta wuce. Kafin su karasa government house ma tasha kuka sosai a mota, suna zuwa ta danne ranta dai ta amshi tarbar da Mama Ladi da Mama tambaya sukai mata harma da sauran ma'aikatan sashenta da suka riski dawowar tata. 

     Duk liyafar da aka shirya musu ta abinci ita da Ramadhan ɗin da dinner bataji ta birgeta ba. Gashi shi baima shigo gidan ba har kusan tara na dare. Tana falo tsaye shayi take haɗawa koshi ta ɗan sha ta kwanata sai gashi. Tafiya yake a kasalance babbar rigarsa saƙale a hannu yana ƙoƙarin kunce agogonsa tunkan ya ida hawowa. Sai da taɗan rumtse ido ta karanto addu'a da fatan ALLAH ya bata ikon shanye halin da take ciki kafin ta juyo garesa. 

      Sannu da zuwa tai masa da nufarsa kai tsaye domin amsar kayan hanunsa. Babu musu ya mika mata komai sai dai bai amsa sanun datai masan ba. Sai ma yar harara daya sakar mata duk da a kasan ransa yaba ƙyawun da rigar jikinta tai mata yake. Rigace mai santsi sai dai sam babu nauyi tattare da ita kalar blue, sai dai an mata kwalliya da baƙi kaɗan-kaɗan, sai ta saka hula blue a kanta kamshin khumra mai sanyin daɗi na tashi a jikinta sama-sama. Cikin sauke ajiyar zuciya yabi bayanta ɗakinsa data nufa.

         Kusan a tare suka shigo, ta ajiye kayan inda ya dace da nufar fridge dan bashi ruwa. Yayinda shi kuma ya hau zame kayan jikinsa da suka damesa sosai. Kanta a ƙasa ta tsiyaya ruwan ta mika masa lokacin da yake zaune bakin gado yana kunce takalnan kafarsa. Bai dago ba har saida ya gama cirewa, kafarsa dake cikin baƙar safa ta bayyana. Ruwan ya amsa nanma yana ɗan hararta, ita dai sai tayi guntun murmushi da ƙoƙarin danne zafin da takeji a ranta.

      “Kayi hakuri dan ALLAH”.

Ta faɗa cikin sanyin murya lokacin da yake miko mata kofin ruwan daya shanye gaba ɗaya. Mikewa yay kamar bazai tanka ba. Sai da ya nufi hanyar toilet ya bata amsa kausashe...

      “Da kikaimin mi?”.

Ita dai babu bakin cewa komai, da zai tausaya matama daya barta da abinda takeji a ranta. Mikewa tai ta fice kafinma ya fito. Ta koma falo ta karasa haɗa shayinta tai zaman sha a dining dan tasan dole zai fito nan abinci koya buƙaci takai masa can........


      Shayin take sha, amma tunaninta sam baya tare da duniyar mutane. Tayi matukar yin zurfi a tunani har Ramadhan daya fito ya karaso dining ɗin bata sani ba. Yayi kyau cikin kananun kaya farare tas daga wandon har rigar. Sai baƙin Slippers daya kara fiddo hasken kafarsa. Idanu kawai ya zuba mata ransa fal mamakin mi take tunani haka da zurfi, dan shi a ganinsa yanda take da karancin shekaru kamar bata da wata damuwa da zata iya damunta a rayuwa. Hanunta da take zagayawa kan kofin ya rike cikin nasa ya matse da kofin. Zafi ya ratsata ta dawo hayyacinta firgigit. Sai kuma ta bata fuska da shagwabeta kamar zatai kuka. “Ya Ramadhan da zafi fa!”.

     Bakinsa ya ɗan taɓe da faɗin, “Ai dan kiji zafin nayi. mi kike tunani haka?”.

        Nannauyan numfashi taja a hankali, ji take kamar ta rushe masa da kuka. Amma sai zuciyarta ke tausarta akan ta daure har sai taji daga bakinsa tukunna. Cikin ƙoƙarin danne ainahin damuwarta tai ƙasa da kanta idanunta na tara kwalla. “Dan ALLAH kayi haƙuri ka yafemin, ALLAH inajin tsiro ne kawai shiyyasa. kuma akwai zafi wajen jinake kamar zan iya mutuwa”.

      Idanu ya ɗan tsura mata na wasu mintuna. Sai kuma ya lumshesu ya sake buɗewa a kanta yana furzar da numfashi.

       Jin yaki cewa komai ta ɗago ta ɗan dubesa fuska share-share da hawaye. Kauda kansa yay da rumtse idanu yana cizar lips. Sai kuma yaɗan murza goshinsa kafin ya zaro tissue dake a dining din ya miƙa mata.

     “Bani abinci barci nakeji”.

   “Baka haƙura ba dan ALLAH”.

              Fuska ya sake tamkewa. “Nifa bana son nacin magana abinci nace ki bani ko”.

     Da ƙyar ta haɗiye kukanta ta mike tai masa yanda ya buƙata. Sai dai abincin ma kaɗan yace ta zuba masa shima ta bashi shayi. Duk yanda ya buƙata haka tai masa. Kafin ta koma wajen zamanta ta cigaba da shan shayinta da duk ya huce da cokali. A haka Bilkisu da yasa ta dawo gidan da zama baki ɗaya har sai lokacin bikinsu ta fito ta samesu. Sannu da zuwa tai masa, sannan takai zaune itama dan dama bataci abincinba yau karatun alkur'ani tayi.

         “Su Muneera fa?”.

Ya tambayi Bilkisun batare daya daina cin abincinsa ba. 

     “Yaya ai muna isowa kayansu suka kwasa driver ya juya dasu kamar yanda Pa ya basu umarni”.

     Kansa kawai ya jinjina. Raudha dakema Bilkisu kallon rashin fahimta dan batasan da barin su Aynah gidanba ta nuna mata Ramadhan da ido tana ɗaga mata gira. Kanta kawai ta maida kasa dan ta gane Bilkiaun na nufin ta tambayesa.

       Haka suka kammala cin abincin kamar wasu kurame. Ramadhan ya koma falo ya ɗan zauna yana kallon labarai. Raudha kuma ta shiga tambayar Bilkiau miyyasa Su Muneera zasu koma gida?.

      Ɗan harar wasa Bilkisun ta mata. “Aunty Raudha bansan jajibe-jajibe. Kedai kawai ki godema ALLAH an rabasu da gidan kawai suje can su karata da baƙin halinsu”.

    Raudha zata sake magana ta dakatar da ita tana miƙa mata waya. “Kinga ni share waɗan can shashashun bani shawara. “Surukinkine ya turosa wai dole saina zaɓa kalar bags ɗin da nakeso”.

    Cikin murmushi Raudha ta fara bin set na akwatinan da kallo. Sun haɗu iya haɗuwa. Da gani kuma daga kasar ketare aka turosu. “Humm ni wannan ai sai nai ruwan ido. Duk fa sun haɗu aunty Bilkisu”.

     Yar dariya bilkisun tayi itama. “ALLAH nima tun ɗazun na kasa ajiye hankalina waje guda na zaɓa. Shiyyasa nace ya jira sai kin dawo kin zaɓa sai na bashi amsa.”

     Har cikin rai Raudha najin daɗin yanda Bilkiau ta ɗauketa. Sai ta tuno da Queen Billy sabuwar ƙawar datai yau a school, a massallaci suka haɗu wajen alwala ta yarda wallet ɗinta batare data sani ba. Shine Raudha ta ɗauka ta bita massallaci da shi. Sai da suka idar da salla ta bata. Cikin jin daɗi ta rungumeta. Sai kuma ta saketa tana bata hannu. “Yi haƙuri dadine wlhy ya rufeni, dan duk abuna mai muhimmanci na cikin wallet ɗin nan sunana Bilkiau amma amfi sanina da  queen billy kefa?”.

        Daga cikin niƙab Raudha tai murmuahi, dan ta fahimci queen Billy zatai ɗan karen surutu. Itama hanunta ta mika mata. “Nice name dear ni sunana Amenatu Dauda”.

      “Sunanki mai daɗi zamu iya zama kawaye? Danni bakuwace yau kwanana biyar kenan da shigowa school ɗin nan har yanzu na kasa sabawa da kowa.”

    Nanma murmushi kawai Raudha tayi, dan haka kawai queen Billy ɗin ta birgeta. Itama dai yarinyace kamarta dan bazasu wuce sa'anin juna ba. Gata ƙyaƙyƙyawa. Taso Raudha ta buɗe nata fuskarta amma taƙi, acewarta wataran zata ganine. Sun faɗama juna department sannan sukai sallama..........✍

      

No comments

Powered by Blogger.