Bakar Inuwa 53
*_Episode 53_*
..........*_JIHAR ƊILLO (HUTAWA)_*
A Hutawa kam kowa yaga M. Ɗan-azumi yanzu sai yay matuƙar mamaki. Dan kamar yanda ya ƙudiri ƙara sabon aure ya auro dalleliyar budurwa sabuwa dal a kwali. Kai daka ganta kasan ƴan kuɗin ta biyo.
Baƙaramin tashin hankali Larai ta shiga ba, dan saika ɗauka ma wani sabon haukane ya hau kanta. Data nema birkice masa sai ya aikata gida taje ta huta. Roƙo iya roƙo ita da danginta amma ya birkice musu ƙememe dama fitinarta ta isheshi, ga baƙin cikin rabasa da masoyiyarsa Asabe da har yanzu ko ɗigon sonta baibar zuciyarsa ba. Ganin haka Baba Nafi ta ƙara kama kanta da mutuncinta a gidan, dan tun dawowar Inna da ƙaninsa da matarsa dama gidan ya sake zama sai a hankali. Gadai jin daɗi yanzu a cikinsa amma kowa zaman haƙuri yake da ɗan uwansa saboda fitinar sirikarsu dabance a rayuwa, shi kuma M. Dauda na biye mata dan duk haukarsa yana ƙaunar Innarsa.Tun auren Raudha alaƙar zuminci mai ƙarfi ke tsakaninsa da hakimi, hakama jama'ar gari sosai suke respecting nashi kowa burinsa ya zama abokin mu'amularsa (kaiko sirikin shugaban ƙasa fa ba wasa ba😝). Da wannan damar M. Dauda kan samu na hura hanci sai ya zaɓi wanda yaso ayi zumincin, shi da M. Gambo ne dai ana nan tif da taya, sai dai baisan M. Gambo nata masa zagon ƙasan ƙoƙarin kiran Asabe a wayaba kullum, wani lokacin harda mata ɗan text na soyayya dan ƴar sakandire ɗin nan dai shi da M. Dauda sunyita. Ita Asabe har zuwa yanzu batasan wanene ba. Dan tun tana sharesa da masa masifa idan ya kirata harta ɗan fara kulashi.
Hakimi daya fahimci rawar kan M. Dauda bata risinaba saima giyar kuɗi dake neman ɗorasa a wani layin bayan wanda yake kai yasa shi ƙara jansa a jiki yana masa nasiha, ya kuma bashi sarautar data tilastashi kullum zuwa gidan Hakimi ayi fadanci dashi. Koda yake mugun ɗagawa da faɗi yake da sarautar, inma ka kira sunansa baka haɗa da sauratarba to kuwa kaji barbaɗin jaraba daga sama har ƙar zai zugeka yana hura hanci da kiran shi ya wuce raini ai. Surikin shugaban mai ƙasar yake baki ɗaya, Baba sama baba ƙasa yake kiransa kuma saiya risina yake gaisheshi koda a wayane balle wani ƙaton ƙawai da talauci yayma katutu. (😂🤣ALLAH ya bar mana Man Dauda).
Ya sayi ƴar kwariɓar motarsa ana yanga da ita kwana biyu ta birkice, cike da masifa ya maidawa bakaniken daya saida masa yace wlhy koya dire masa kuɗinsa kokuma yasa azo daga Bingo a cukuykuyesa yasan dai uban matar shugaban ƙasa yake. Da farko makanike ya ɗau abin wasa, dan mahaukacima suka maida M. Dauda shi da yaransa. Saiko gashi ko mintuna ashirin baiyi da barin wajenba motar ƴan sanda har uku sunzo sun yayesu gaba ɗaya har yaran nashi. Dan kuwa M. Dauda yana zuwa police station d.p.o da ayanzu ya gama haddacesa shi da yaransa koda ɗunbin alkairin da suka samu a ranar auren ƴarsa da shugaban ƙasa sukai masa tarbar mutunci. Harda matsar kwallan munahinci wajen faɗa musu abinda akai masa a gareji. Rai ɓace d.p.o ya bama yaransa umarnin zuwa a kwasosu yana bama M. Dauda haƙuri.
“Baba ai kun wuce ko kallon banza yanzu a ƙasarnan, kunefa iyayen masu ƙasar. Gamu nan tunda ɗanku ya hau mulki albashinmu ma ninkashi akai tsabar adalci na wannan shugaba. Ai mu babu abinda muke sai fatan alkairi a garesa, mun kuma tabbatar lallai matasa masu jini a farce ƙasar NAYA ke buƙata irinsa.. ALLAH ya ƙara masa zaman lafiya da matarsa nan da watanni asake zuwa taron suna NAYA muci musha muyi warkan. Dan muna alfahari first lady tamuce wlhy”.
Daɗi kamar zai kar m. Dauda, ya dinga washe haƙwara yana sake baje babbar rigarsa dan ɗinkunan alfarma da Alhaji Hameed Taura yay masa na biki har kala goma sune suka zama na faɗi yanzu a gari. Lokacin da aka shigo dasu Gali a ɗage M. Dauda yake kallonsu da watsa hannaye gaba. “A rufeminsu har sai na manta da wanzuwarsu sannan a tunamin”.
Cikin roƙo da magiya kanikawan nan ke roƙon Alhaji Dauda (dan tunifa dama gargaɗi yake abar kiransa M. Dauda😂😜). Amma ko kallonsu baiyiba. Cikin takun ƙasaita ya buga babbar rigarsa aka fice dan d.p.o ya bada motarsa a maidashi gida.
Kwanakin kanikawan nan huɗu a ofishin ƴan sanda sannan ya bari aka sakesu da sharaɗin maido masa kuɗaɗensa nanda sati guda. Hakan kuwa akai sai gasu da kuɗaɗensa cif sun kawo, ya dinga antaya musu harara yana sake baje riga da hura hanci. Bayan ya koma gida ne ya nema kuɗin ya rasa da kwana biyu shine ya yanke jiki ya faɗi har saida aka kaisa asibiti. Wannan ne dalilin zuwa su Fatisa dubashi har suka sanarma Raudha, to ayanzu haka dai ya haɗa duk yaran gidan nasa da matan ya tabbatar musu idan kuɗinsa basu dawoba nera dubu ɗari bakwai wlhy suma cell zaisa a zubasu har sai sun magantu.
(🤣😂To bara muga ta inda kuɗin Alhaji Malam Dauda surikin shugaban ƙasar NAYA zasu fito).
*_BINGO CITY (TAURA HOUSE_*
Barci sukasha sosai kamar yanda Ramadhan yaso. Ga Anne daga falo na musu gadi dan koda su Basma suka taho wai anan zasuyi breakfast korasu tai duk da tasan da wahala hayaniyarsu takai ga sashen Ramadhan ɗin. Dama tunda ya shiga ya gaisheta bayan sallar asuba yace kar ai musu breakfast da wuri. Dan haka ba'a ɗora ɗinba kuwa sai kusan sha ɗaya na safe. Zuwa sha biyu an kammala komai an kawo falon part ɗinsa an shirya bayan an gyarashi yanata ƙamshi duk da bawani datti yayi ba.
A yanzu ɗinma kusan tare suka farka sai dai motsintane ya tadashi. Tai ƙoƙarin janye jikinta ya hana hakan. Cikin yanayin kasalar barci ya mika hannu ga side drawer ya ɗakko agogonsa yaɗan kalla time cikin lumshe idanu da buɗewa. Har sha biyu ta gota. Agogon ya ajiye da kai lips nashi a goshin Raudha da taƙi buɗe ido ya sumbata. Kafin ya saketa ya sauka baki ɗaya batare da yayi magana ba.
Bata iya motsawaba sai da taji ya rufo toilet ɗin. Ta miƙe da ƙyar itama dan barcine da bata sabayi ba ace tun sallar asuba har kusan 1. Gadon ta shiga gyarawa a ɗan gurguje, ta maida net ɗin yanda ta gansa, sosai yake birgeta dan ya sake kawata gadon da ɗakinma baki ɗaya. Har falo ta fito neman kayan shara, cikin sa'a ta samu a cikin kitchen bayan ta karema falon da kitchen ɗin kallo. komai akwai na buƙatar ɗiya mace har tana mamakin sai kace mai mata.
Shara ta gama tana tsaka da mopping ya fito. Bata yarda ta kallesa ba, sai shine dake binta da kallo ya nufi mirror yana faɗin, “Waya saki wannan aikin?”.
Amsa ta bashi batare data yarda ta kalla inda yakenba dai.
“Ba kowa”.
Komai bai sake cewaba harta kammala ta fita da kayan, taɗan jima kafin ta dawo da fatan ALLAH yasa ya saka kaya. Sai dai addu'ar tata bataci ba dan har lokacin ɗaure yake da towel tsaye a gaban Wadrobe da alama kaya yake nema. Kaita kauda cikin sauri ta faɗa toilet.
Baki yaɗan taɓe dan duk yana kallonta ta gefen ido. Ta jima bata fitoba, har sai da ta leƙo taga baya ɗakin. Da sauri-saurin tai shirinta cikin atanfa datai mata ƙyau matuƙa, ga ɗinkin ya fidda jikinta tsaf kamar ka saceta ka gudu. Ɗauri tai mai sauƙi amma ya mata ƙyar ta saka ƴan kunne kawai harda yafa mayafi sannan ta fito da nufin zuwa gaida mutanen gidan duk da kunya da nauyin ƙin zuwa akan lokaci na cinta. A tunaninta Ramadhan ma nacan, sai dai tana fitowa falo taci karo da gogan nata zaune cikin kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallon labarai a television da alama sallar azhar yaje yayo kawai ya dawo.
Tsamm tayi a ƙofar ɗaki kamar bazata karaso ba. Sai kuma cikin dauriya ta cigaba da takowa har inda yake. Kanta a ƙasa tana wasa da zobon hanunta tace, “Ya Ramadhan zanje naje na gaida su Anne”.
Maimakon ya amsa mata duk da idonsa ba'a kanta yakeba sai taji ya riƙota ya zaunar saman cinyarsa. Mutsu-mutsu zata fara ya dakatar da ita ta hanyar yaye veil ɗinta gaba ɗaya. “Banda ƙauyanci miye na zuwa gaban miji da veil?”.
Duk da maganar ta bata haushi sai ta dake. A sanyaye tace, “Wajensu Anne fa zanje”.
Wasa yake da jelan kitsonta idonsa a tv, “Sunce sun yafe yau ko ƙofar corridor ɗin can bazakije ba nayi gaisuwan da taki ai tun ɗazun”.
“Kai Ya Ramadhan wlhy bai kamataba ace banje na gaishesu ba. Gashi dama lokaci ya gama shigewa ai da kunya”.
Maimakon amsa mata maganar ko barinta tafiya sai ya ɗagata daga jikinsa shima ya tashi, dining ya nufa da ita dan shi ta yunwar cikinsa ma yakeyi. Dolo ta haɗiye komai dan yaci serious kamar bashi ba. Tsorone yaɗan fara kamata na gudun karfa mutumin nan ya juya mata baya bayan ya rabata da mutuncinta. Dan taga tun jiya ya koma sha mata ƙamshi irin yanda yakeyi mata a baya. Da wannan tunanin tai saving nashi komai, zata zuba nata ya hanata yay mata nuni data zauna kawai. Dole tabi umarninsa zuciyarta fal tsoron abinda ba haka bane. Shi Ramadhan yana ɗan ɗaurewa ne kawai dan gujema abinda zuciyarsa ke kwaɗaita masa game da ita. Dan tausayinta yakeji matuka. Amnah mai shekaru da suke gab da nashi duk da tanada lalura bata iya jure ɗaukarsa akoda yaushe balle ita. Dan sauda dama idan yaje gareta sai tayi kuka balle Raudha da yakema kallon jaririya. Shi kansa yasan yayi juriyaa shekarun da babu Amnah, amma ya tabbatar ɓacin rai da tashin hankaline suka girmama juriyar tasa, yanzu ko daya ɗan ɗana bayajin zai ɗaga ƙafa duk da ƙoƙarin hakan da yakeyi.
Tare sukaci abincin Raudha nata sinne-sinne. Shi dai bai kulataba. Daga ƙarshema ya amshe cokalin ya koma bata da kansa. Ina ƙasa ta shige amma babu damar gardama dan ya haɗe girar sama data ƙasa........✍
Leave a Comment