Bakar Inuwa 50


 Episode 49 & 50_*



..........Da asuba daya tadata suyi salla kuka ta dinga masa sosai. Duk sai tausayinta ya lulluɓesa. Shi kansa yasan ya tsaurara mata da yawa, dan dukan fushinsa na shekarun nan babu ƙwange sai da ya sauke shi tsaf. Bata wani yarda ya taimaka mataba tace zata iya. 

       Koda ya haɗa mata ruwa sai ya fita a toilet ɗin ya barta. Zafin ruwan ya sata harar ƙofar tana ƙunkuni ta surkeshi ya koma salaf. A haka ta gyara jikinta ta fito tana faman sinne kai. Ga dariya ga tausayi duk suna cin Ramadhan lokaci ɗaya. Amma sai ya gimtse dan karya sake tunzurata.

      Da ƙyar ta yarda suka sake komawa barci bayan ta idar da sallar. Acewarsa su ɗan ƙara rage barcin idonsu dan anguwa zasuje. Taura house yake son suje hutun nan na kwanaki biyar da akai, amma bai sanar mata ba. Dan kuwa bazai yarda amarcin nan ya wucesa bai ɗana gadonsa na Taura house ba. 


(Mutumin nan ko😂😜)


         ★Tun a daren jiya dama ya sanarma ƙanensa yau zasu wuce Taura house hutu gaba ɗayansu. Dan haka da safe ya turama Bilkisu text ta haɗama Raudha abinda duk tasan zatai amfani da shi su wuce su sai zuwa anjima zasu zo. Murmushi kawai Bilyn tayi. Sai dai kafin su fita tai ƙoƙarin haɗa breakfast ta ajiye musu. Mama Ladi kuwa ta zauna gadin abincin nan dan kuwa Anne ta kirata tun sanda suka gane Raudha ce ta aika musu takarda akan saka poison a ac ta ce mata ta dinga saka ido akan kowa na gidan kar'a cutar mata da su Raudha. Duk da tasan bata isa hana zartar da ƙaddarar UBANGIJI akansu ba.


        Yanzu kam Raudha ce ta fara farkawa. Ta buɗe idanunta da sukai mata nauyi matuƙa. Akan fuskar gogan nata ta saukesu. Idanunsa a lumshe, ƙyaƙyƙyawar fuskarsa tayi wani fayau. Duk da haushinsa na murzar da yay mata jiya babu tausayi da takeji haka ta shagala a kallonsa. Itama kanta tasan shiɗin ƙyaƙyƙyawa ne, ga yanayin jin daɗin rayuwa daya tashi a ciki, bai san wahalar komai ba sai ta karatu. Ahankali takai yatsanta saman girarsa data daɗe tana kwaɗayin taɓa tsagar wajen da zuciyarta ke bata wanzami yay masa. Sai dai me, koda ta shafa wajen sai taji santsi irin na tabon ciwo. Mamaki ya kamata, a zuciyarta tace, (Ashe ba tsaga masa akeba tabon ciwo ne) a fili kam mamaki ƙarara ya bayyana gareta da sake girmama sunan UBANGIJI, dan babu mai kallon wajen yace ciwone. Sosai tsagar ta fita da tsari kamar yimasa akai akan sani. A hankali ta sauke numfashi da maida gashin girar data yamutsa masa ta maidashi ya kwanta. Tana ƙoƙarin sake janyewa taji an riƙe hanun. Babu shiri tai saurin rumtse ido tana fisgewa amma yaƙi saki. Nasa lumsassun idanun dake cike da barci ya buɗe a hankali a kanta. Sai kuma ya sumbaci hanun nata daya riƙi ya turashi ƙasan kuncinsa yay filo da shi.  Ɗayan hanunsa kuma ya ɗaura a jikinta saitin ƙugunta.

     “Good morning sweetheart”.

  Wani bala'in kunyane da yafi na ɗazun da asuba ya lulluɓeta. Tai ƙoƙarin kauda kanta yay azamar tallafosa da hanunsa dake a ƙugunta ya hanata hakan. Cikin ɗan marairaicewa yace, “Ki amsa min mana Baby luv”.

        Da ƙyar ta iya buɗe baki tace, “Ina kwana”.

      Ahankali ya shafo kanta tun daga sumar gaban goshin har zuwa ƙeya yana ɗan murmushi. “Ya jikin ki? Duk da nima dai ya kamata a tambayeni nawa kodan yaƙushi da cizon dana sha”.

      Ina ƙasa Raudha ta shige ta huta. Tai ƙoƙarin jan hanunta da yay filo da shi amma ta kasa. “Kibar wani gulma Ustazah, nasan kina son mijinki kar kiyi sake wata ta ƙwace miki ni”.

      Kanta tai ƙoƙarin sinnewa a jikinsa. Yay murmushi yana riƙeta ya hana hakan. “Gara na faɗa miki gaskiya matsayina na abokinki babban amininki. Bazan so a miki kishiyaba kina ƙawata ta hanun damar, dan sai na fiki kishi kilama kullum dani zaki dinga cin dabe da ita a gidan ga muna lakaɗa mata duka ko ya kikace?”.

       Duk yanda taso riƙe dariyarta ta kasa. Ta saki murmushi tana turesa. “Kai Ya Ramadhan....”

      “K nifa bana wani kalar dangi ƙannena sun isheni, inama laifi da muke abota niba yayanki bane”.

   “Toni ai bazan iya faɗar sunanka ba”. Tai maganar tana sake son cusa kanta a ƙirjinsa. Haɓarta ya riƙo ya ɗago fuskar tata da sumbatar laɓɓanta. Cikin sake ƙanƙan da murya yace, “To basai ki canjamin da wani ba. Amma sam bana son Yayan nan kamar wani zamanin iyaye da kakanni, bayan kuma jiya na gama turmusheki a gadon na....”

       Dariya ta ɗan ƙyalƙyale da shi tana kaimasa ƙaramin duka a ƙirji. Shima sai ya rungumeta yana murmushi. Zuciyarsa fes da farin ciki.


       Duk yanda taso zamewa kar suyi wanka tare bai bata damarba. Amma kuma taƙi sakin jiki haka ya gama nashi ya barota a bayin. Sanda ta fito yana zaune yana waya. Dan haka tai wuff ta fice a ɗakin bayan ta saka hijjab.

       Ciwo take ɗanji kaɗan-kaɗan a ƙasanta amma ta daure ta shirya cikin wani material da yay mata ƙyau sosai da fiddo kalar fatarta. Tayi fayau da ita daka ganta kaga amarya, sai dai fuskar babu walwala sosai ga idonta duk wanda ya kalleta yasan taci kuka. Yunwa takeji amma batajin son cin abinci kuma. Bakinma ɗaci takeji yana mata kamar mai malaria. Tana fesa turare ya shigo, sanye yake cikin shadda ash color datai bala'in masa ƙyau. Sai maiƙo take da ɗaukar iadanun mai kallo. Ya murza hula baƙa data fiddo ainahin hasken fatarsa da ƙyallin angwanci. Duk da waya ya shigo yanayi hakan bai hana Raudha shiga jin kunya ba, ya ƙaraso inda take yana riƙe kwalban turaren da kunya tasata cigaba da fesa ƙasa-ƙasa dan karya tada mata asthma. Ajiyewa yay saman mirror ɗin ya riƙe hanunsa cikin nata idanunsa a saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta da yakeji kamar ya haɗiyeta. Ga ɗaurin datai ya sake fiddo ƙyanta kamar dai ya haɗiyetan ya huta kawai. Ita dai kanta a ƙasa tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa na _Dolce & gabbana_ daya gauraya da _burberry brit_. shiko yanata wayarsa da murza yatsun hanunta.

      Tsawon lokaci harta fara gundura da tsaiwar kafin yay sallama da wanda yake maganar wanda ta fahimci kamar akan harkar kasuwanci ne. Saman mirror ya ɗaura wayar da kamo fuskarta cikin tafukan hanunsa ya sumbaci goshinta, sai kuma ya sakko a hankali ya sumbaci lips ɗinta dake ƙallin lips gloss. Shima ya duƙo kaɗan yana nuna mata nasa kumatunsa da goshi. 

       “Kai Ya Ramad......”

Sai kuma ta kasa karasawa saboda ɗallin daya bama bakinta. “Dole na fara hukunta wannan bakin idan yaya ɗin nan bai fita a cikinsa ba”. 

     Hannu tasa ta rufe laɓɓanta da zafi ya maimaye idonta na cika da ƙwalla. Hannunta ya kamo ya zuba mata link ɗinsa da agogonsa _hublot_ dayay mata ƙyau sosai kalar ash. Batai musu ba, dan koba komai tasan aiki garesa lada ne. Links ɗin ta fara saka masa sannan agogon. 

     “Thanks bestie”.

Ya faɗa a hankali idonsa a kanta. Sai kuma ya janye yana ƙoƙarin barin wajen mirror ɗin. “Ƙarasa mu wuce so nake na more gida sosai lokaci nata tafiya”.

       Duk da batasan ina zasu ba cike take da ɗokin tafiyar. Ta ɗauka hijjab da zai shiga da kayanta ta saka tare da haɗa abinda zata iya buƙata a karamar handbag. Tana duba takalmi a akwatin lefenta ya sake shigowa. Bai yi magana ba yabi duk kayan wutar ɗakin ya kashe komai. Dai-dai tana gamawa yake faɗin, “Ko breakfast bazamu tsaya yiba mayi acan kawai”.

     Kanta ta jinjina masa, sai dai har yanzu taƙi yarda su haɗa ido. A hankali ya matsa gefenta yay musu hoto bayan ya faɗi abinda ya sakata ɗagowa ta kallesa a ɗan tsorace. Sai hoton ya bada wani style mai ƙayatarwa kamar anyisane da shiri.


        Bayan sun sallami su Mama Ladi suka fito compound inda jerarrun motocin da zasu fitan suke. Yau ce karo na farko da zasu fita tare da shi a bayyane. Sai gaisuwa ake miƙa musu cike da ɗunbin girmamawa wadda har Raudha takejin babu daɗi akanta. Dan kuwa da yawansu sun haifeta da girmarta. A motar da tafi kowace mota ƙyau da ɗaukar idanu ga tutocin ƙasar naya a jikinta suka shiga. Kafin wanda zasu musu rakkiya Taura house ciki harda cos da wasu ministers uku suma suka shiga. Ba wani tafiya mai tazara bace ba, amma ta fahimci an bama fitar muhimmanci matuƙar dan har a redion motar da driver ya kunna saiga sanarwar yau shugaban ƙasa Ramadhan B. Hameed Taura zaije hutun ƙarshen shekara gidansu a karo na farko tun bayan hawansa mulki na watanni kenan. Anan aka saka zantukan mutane daban-daban daketa masa addu'a shi da iyalinsa akan yasha hutu lafiya cikin farin ciki.

     Sosai ya ƙara samun nutsuwa a ransa dan kuwa zuwa yanzun ayyukan daban-daban da suka faro na talakawa sun kankama matuƙa. Abinda zai matuƙar birgeka duk wani mai kwangilar gwamnati sunansa da aikin da zaiyi a bayyane yake ga al'umma. Hakan yasa yake ƙara samun addu'a ga talakawa dan kuwa babu wani ƙunshe-ƙunshe balle a cucesu a ƙiyi musu aiki kuma su rasa daga ina matsalar take. Kai hatta kuɗin da aka bama masu kwangilan da wanda sukebin bashi sai sun kammala a cika musu duk an sanar da duniya babu wani rifa-rufa. Hakan da yay ya matuƙar taimakawa da saka tsoro a zukatan masu kwangilar dan sun san kam inma basuyiba sune a ruwa tsundum. Gashi har adadin watanni ko shekarun da aikin zai ɗauka kowa ya sani a bayyane. Bashi kaɗaiba hatta da gwamnoni da ƴan majilusu, ciyamomi, kansiloli duk aikin da zakai ma ƴan yankinka a jihohin nan 41 dolene ka sanar da komai talakawa su sani.


        Tarba ce ta musamman tawagar shugaban ƙasa ta samu a Taura house, dan kuwa wannan shine karo na farko da yazo gidansu a bayyane kuma da shirin kwanaki. Sosai bakin Anne da su Yafendo ke a buɗe, ganinsa ya musu wahala yanda suke buƙata tunda ya hau mulkin nan. Raudha dai gaba ɗaya a takure take. Jitake kamar kowa zai iya gabe abinda ya faru a tsakaninsu jiya. Ga anne da su Yafendo sai nan-nan suke da ita kowa na saka mata albarka. Bayan gaishe-gaishe da addu'oi Ramadhan da su Bappi suka fita salla dan tawagar datai masa rakkiya sun koma. Sai dai Taura house tako ina zagaye yake da securitys kai gaba dayama anguwar. Dole ne ka shaida shugaban ƙasa na nan koda matakan tsaron dake kewayen anguwar baki ɗaya, kai kace ko ƙuda bazasu bari ya gitta ba.

           Da ƙyar Raudha ta iya tsarki da ruwan sanyi tsabar zogin da wajen ke mata zuwa yanzun. Har jin kanta take kamar wadda zazzaɓi zai saukarmawa. Anne na lure da yanayin nata sai dai batace komai ba dan zuciyarta bai kai ga zargin abinda ke faruwa da Raudha ɗin ba kai tsaye. Gashi tunda suka shigo dama yanayin idanunta na wadda taci kuka ya tsayama Anne a rai. A ɗakin Anne sukai salla duk da kuwa an gyara sashen Ramadhan ɗin tsaf domin su.

      Bayan idar da salla gaba ɗaya gidan ƴaƴa da iyaye aka haɗu domin yin lunch a katafaren falon Bappi. Abincine mai rai da lafiya da gamsarwa a wajen iri-iri. Anyi hakanne kawai domin walimar zuwan Ramadhan ɗin da Raudha. Sai yanzu Raudha taga gimbiya Su'adah da sauran matan gidan, dan kuwa bata shiga gaishesu ba Anne tace sai zuwa yamma sun huta. Sai dai shi Ramadhan ya shiga ya gaida Gimbiya Su'adah ɗin kawai ganin bata a masu fitowa tarbarsa. Kasancewar salla zai fita yasa bayan gaisuwa babu wani abu daya shiga tsakaninsu ya fito suka fice massallaci.

     Har ƙasa Raudha takai tana gaishe da iyayen. Kowa ya amsa mata cike da kulawa banda gimbiya Su'adah da ko kallon inda take bataiba. Ƙasan ranta wani takaicine da baƙin ciki da kishin yanda Raudha ta kara murjewa komai na halittar jikinta ya ƙara girma sai kace ƴar 25years. Ga tsadadden material ɗin dake jikinta wanda ta tabbatar za'a iya sayen abincin watanni na gidansu Raudhan da kuɗinsa. Ita saima taga kamar yarinyar tana wani jin kanta.

     Oho Raudha batasan tanai ba. Ita abinda ya dametama ya isheta. Komai yinsa take cike da dauriya. Abincinma tana matuƙar bukatarsa amma ta kasa ci saboda bakinta babu daɗi. Sai juya spoon take a ciki tana ɓata fuska. Ramadhan na lure da ita. Kuma hankalinsa na kanta. Burinsa su haɗa ido amma taƙi kallon ko inda yake. yana zaune ne tsakkiyar Bappi da Pa. Sai Anne a gefensu da Yafendo da Inna. Ita kuma tana kusa da Bilkisu da Zainab ne. Su Lubnah sai faman jan tsaki suke ƙasa-ƙasa suma kamar su halaka Raudha sukeji musamman ganin suturar data sanya kosu da suka tashi gidan kuɗin basu saka ba. Tsadajjen agogon hanunta da zabba da bangles kawai duniyane. Balle ita kanta data kara wani kyau na musamman da su sam basa lura da shi sai yau duk da kuwa suna tare da ita.

          Da gangan Ramadhan yay kamar ya sarƙe yaja gyaran muryar data saka kowa maida hankalinsa a kansa ana rige-rigen jera masa sannu. Bappi dake shafa masa baya kamar wani ƙaramin yaro ya kai masa kofin ruwa bakinsa yana masa sannu. Kaɗan yasha yana jinjina musu kai da satar kallon Ustazahr tasa. Sai dai bata yarda ta kallesa ba tun bayan ɗagowar datai kamar yanda kowa ya ɗago lokacin daya sarƙe. Ita sanun tatama a kan laɓɓa tai masa ta tsuke bakinta. Ganin dai ba samun yanda yakeso zaiyi ba sai ya haƙura. Takaici ya cika Aynah da duk hankalinta ke akansu. Hakama Muneera da idonsu akan yayan nasu da abinda yake yawan kallo. Jin hawaye na neman zuboma Aina'u itace ta fara mikewa wai ta ƙoahi. Babu wanda yace mata komai, hakan sai ya ƙara baƙanta ranta. Dan a ganin bai kamata aƙi bata kulawaba kodan mata ta biyu da take shirin shigowa ga ɗansu kuma ɗan uwanta.

        Raudha da dama ba abincin take ci na kirki ba itace ta ukun tashi a wajen. Ramadhan ya ɗan bi yanda take tafiya da kallo. Hannu ya kai ya dafe goshinsa a zuciyarsa yana ayyana (Yarinyar nan zata tonamin asiri fa). Bayan sun kammala kowa ya tashi a wajen yaso janta sashensa dan ya fahimci mugunta taima kanta bata shiga ruwan zafin daya haɗa mataba da asuba, bayajin kuma da safe ta sake kula da kanta. Takaicin kansa yaji dabai tsaya akanta ya taimaka mataba duk boranta. Sai dai duk yanda yaso ya keɓe da ita ɗin hakan bata yuwuba dan su Basma na zagaye da ita a falon Anne suna hirar school duk da ba wani saka musu baki take sosai ba. Sai dai ganin Inna da Yafendo da Anne na wajen ya sashi haƙura ya shige shi acewarsa zai ɗan huta...........✍

        

No comments

Powered by Blogger.