Bakar Inuwa 48

 


Chapter 48

48


.........Duk yanda taso zamewa basa abincin fir yaƙi. Dolenta ta bashi kamar yanda ya buƙata, kunya kamar ta tsaga ƙasa ta nutse a ciki. Shiko ko'a kwalar rigarsa. Sai ma idan tayo ƙatuwar lauma ya harareta wai tafi ƙarfin bakinsa. Amma in namane dataso ragewa zai riƙe hanun da faɗin ‘Ban san mugunta Ustazah’.


    A haka dai yaci ya ƙoshi itama ya tsareta sai taci. Fuska ta marairaice tamkar zatai kuka amma yace saifa taci babu ɗaga ƙafa. Dole ta ɗan tsakura dan a takure take sosai. Bayan ta kammala ta tattare kwanikan ta fita da su. Numfashi ya sauke a hankali da barin aikin da yake a lap-top ya kwantar da kansa jikin kukerar yana lumshe ido da furzar da numfashi. Sai kuma ya kai hannu a wuyansa dan har yanzu akwai zazzaɓi jikinsa dauriyace kawai. ‘Oh Ramadhan Taura ka zama ɗan cali-cali kuma?’. Sai kuma ya sake sakin murmushi da girgiza kansa kaɗan. Shi kansa baya sanin sanda yake biyema Raudha. Abinda ya sani kawai bai son ganinta cikin damuwa kamar baya. Sannan addu'arta a koda yaushe na bashi nutsuwa. Yayinda idan tana a yanayin tsoro da kunya take hana fitinarsa zama lafiya ya dingajin kamar kawai ya...... “Ya ALLAH” ya ambata da kai hannu cikin sumar kansa. Sai kuma ya tashi zaune sosai ya cigaba da sarrafa system ɗin cike da ƙoƙarin son ture abubuwan dake neman fin ƙarfin jarumtarsa......
_______________★★_____________
     Alhmdllhi zamuce abubuwa sun fara daidaito tsakanin Ramadhan da Raudha, ta saki jiki dashi ba laifi suyi ɗan wasa da dariya. Idan kuma taga ya haɗe fuska ta kama kanta ta nutsu. kwana ɗakinsa dai bata sake yarda tayiba tun randa yay zazzaɓi. Amma yanzu tana ƙoƙarin tashi a kowace bayan sallar asuba ta haɗa masa breakfast da kanta. hakama abincin dare kafin ya shigo takai komai bedroom ɗinsa ta ajiye. Wataran ya leƙata da matsa mata tazo ta bashi abinci. wataran ya shareta yaci abinsa sai da safe idan tazo gyaran ɗaki ta tattare.


     A washe gari Ramadhan da Bappi suka gana, ganawar data zama ta farko a zahiri da har ƴan jarida suka fitar. Sai dai babu wanda yasan mi suka tattauna a zaman nasu sai ni (Bilyn Abdull cctv footage ɗin ku😉😂). Sosai kansu ya tushe da mamakin ganin rubutun Raudha dai-dai da takardar da aka turama Bappi ana jibi ɗaurin aurensa da Raudhan. An musu nuni ne da karsu yarda Ramadhan ɗin ya tare a gidan gwamnati har sai an cire ac ɗin dake a bedrooms nashi da falukansa saboda akwai poison a ciki. Ranar sun shiga tashin hankali musamman Anne datace Ramadhan bazai tare government house a kashe mata shi ba. Shi da Bappi sukaita lallashinta da mata nasiha harta nutsu, inda basuyi ƙasa a gwiwa ba randa Ramadhan ya shiga gidan gwamnati kwana biyu da aurensa da Raudha suka canja duk ac ɗin dake sashen harma dana office ɗinsa. Hakama sai da suka bincike lungu da saƙo na ɗakin barci da falukansa na sirri gudun ko an saka camaras a ɓoye. amma Alhmdllhi babu alamar hakan sai iya ta inda ya dace kawai da dole a samu a kowane gidan gwamnati saboda tsaro. Dan wani yaron Aunty Zuhrah ne yay aikin. Sun sake tsintar kansu a tashin hankali lokacin da suka samu poisons a cikin ac's ɗin. Ranar har hawaye Bappi yayi. Daga haka kuma ya ɗarsama kansa zargin akwai boyayyen al'amari. Sai dai kai tsaye bai fito ya ambaci sunan kowa ba. Babban fatansu kawai susan wanene wannan mai turo saƙo. Hakan yasa ganin wannan hand writing da yay dai-dai dana Raudha yay matuƙar ɗaure kansu.


    “Wannan ya sake tabbatar min yarinyar nan Alheri ce kuma akwai dalilin zuwanta garemu”. Bappi ya faɗa lokacin da suke ganawa da Ramadhan a office.


   Cikin sauke numfashi Ramadhan yace, “Tabbas akwai abinda bamu saniba kuma ita take ɓoye mana. Abin ɗaure kan anan kawai shine a gaba ɗaya tarihin yarinyar dana bibiya babu wani alamun alaƙarta da wani sai danginta ko anan cikin Bingo. Sai dai sister ɗin mom nata tanada alaƙa da matar forma president, a yanzu kuma matace ga Alhaji Yaro glass Vice ɗina, dama kuma sun taɓa zaman aure ta fita. Bappi inhar hasashena yana kan dai-dai akwai boyayyar manufa tsakaninka da abokan nan naka gaskiya”.


   Murmushi Bappi yayi yana ɗan jinjina kai. “Komai zai iya faruwa musamman idan akai la'akari da abubuwa masu yawa. Sai dai bana so zargin sunan kowa anan har sai muntabbar. Shawarata gareka anan lkawai ka cigaba da jan yarinyarnan Ameenatu a jiki, zaka iya jin fiye da abinda muke buƙata daga gareta. Amma tabbas ka shaida naji ƙarin ƙaunarta a raina da kimarta fiye da zaton mai zato. Dan zuciyata bata gayamin an haɗa kai da itane dan a cutar damu”.


   A hankali Ramadhan ya sauke numfashi wani abu mai sanyi na sauka masa a cikin zuciya. Jiyake kamarma ya buɗe ido ya ganta gabansa. Jin yau ɗin yake daban da kullum a rayuwarsa. Sai dai me, yana zuwa gidan ya iske ɓacin ran su Lubnah da har takaisa ga marin Lubnah ɗin. A kuma daren yasa driver maidata gida. Sai dai abun ƙarin takaici washe gari Maah tasa aka maidota.


   Wannan haushin ya sakashi tunda ya fita gida da safe bai dawoba sai dare. Washe gari kuma tafiya ta taso masa zuwa ƙasar faransa babu wani walwala tattare da shi sukai sallama da Raudha da ayanzu ta sake nutsuwa akan makaranta dan harta fara jin daɗin lectures din saboda taimakon da su Basma ke bata.


  Ta ɗan shiga damuwa da canjawar tashi, sai dai daga baya ta watsar da komai dan indai dan abinda su Lubnah sukai matane ita ya wuce a gareta basa ma gabanta. Fatanta dai ALLAH ya bata kariya daga cutar da waninsu.
   A washe garin daya wuce ta tashi da ciwon mara. Tasha azaba sauƙintama yasa Bilkisu dawowa gidan saboda ya fahimci suna ɗasawa da Raudha ɗin. Sai dai sunsha gargaɗi kamar babu gobe akan abubuwa da yawa. Hakama su Muneera sunsha nasu, dama tun marin da Lubnah tasha suka koma shiru-shiru a gidan dan sun san hali. Yanzu ko daya tafi sun ɗau alwashi kala-kala akan Raudha sai akai rashin sa'a Bilkisu ta dawo kusa da ita.  


   Bilkisu ce ta sanar masa halin da Raudha ke ciki ta hanyar massege. Hankalinsa ya tashi lokacin daya lura ta text ɗin. Sai kuma a lokacin ya tuna da zancen Dr Hauwa'u a wancan lokacin. Bai samu magana da Bilkisu ba sai dare bayan ya samu nutsuwa. Ta kwantar masa da hankali akan da sauƙi, dan Anne ta kira shine ta turo musu Maman Jabeer (Dr Hauwa) tazo ta dubata. Ta tabbatar masa tayi faɗa sosai akan ƙin zuwan Raudha ɗin bayan tun wancan karon tace taje bayan ta warke.


    Yaji babu daɗi sosai, dan kuwa akwai sakacinsa tunda shine bai nuna maida hankali akai ba matsayinsa na wadda take a ƙarƙashinsa. Bai ce a haɗashi da Raudha ɗin ba, sai dai ya tabbatar ma Bilkisu tayi ƙoƙari idan Raudha ta samu lafiya suje asibitin Maman Jabeer ɗin.
    Haka kuwa akai, bayan kwana biyu ta koma ragas kamar ba'ita ba. Dan haka sukaje asibitin da dare gudun idon mutane. Sai dai tana tare da dogaranta duk da hakan. 


   Sosai Dr Hauwa tai mata gwaje-gwaje na musamman yanda ya kamata. Cikin amincin ALLAH kuma ta gano matsalolin dake tare da Raudha ɗin harda imfection. Magunguna ta bata tare da wani bayanai a rubuce tace ta bama Ramadhan ba nata bane. 


     Kamar yanda akace shi ɗin zata bamawa kuwa bata buɗaba ta ajiye ta cigaba da sabgar gabanta. Tayi fes da ita, da alama kuma makaranta ta fara buɗe mata idanu da wasu abubuwan. Gashi bata wasa sam da karatu sosai take nuna ƙwazo dake bama su Basma dama class mate ɗin nata mamaki. Gashi taƙi yarda kowa yasan ita wacece, koda yaushe fuska a ƙunshe da niƙab. Bata shiga harkar kowa sai su Basma. Wasu na mata kallon girman kai wasu kuma tana ɗan birgesu duk da basu san wacece ita ba. Suma su Basma kuma sun kame bakinsu saboda gargaɗin Ramadhan da Anne. 
    ★Kasancewar yau juma'a da wuri ta dawo school. Ta zube a falo Bilkisu na mata dariya. “Aunty ahaka za'ai karatun kuwa?”.


   Dariya itama Raudha tayi tana ajiye ruwan data sha sosai. “Wlhy bazaki ganeba Aunty. Abunfa babu sauƙi sam. Dan masifa yau text har biyu mukayi ga submitting Assignment ɗin masifaffen malamin nan da nake gaya miki”.


    Cikin dariya Bily tace, “Haka ake shan yaƙi ai Aunty har a cimma nasara. Fatanmu dai ki fito da first class duniya tasan firt lady ɗinmu bata wasa bace”. 


  Dariya Raudha tai tana miƙewa. “Uhhm Aunty Rabani da wata first lady. bara na watsa ruwa nazo naci abinci ko breakfast banyiba yau”. 
   Bayan tayo wankan anan suka baje a falon bilkisu na sake nuna mata aikin yau da mata ƙarin bayani. Salla kawai ke tadasu har magrib. Sam Raudha batasan yau shugaban ƙasa zai dawo ba dan tunda ta shigo gidan basu buɗe tv ba. Bayan sallar isha'i taɗan sake watsa ruwa. Fitowarta kenan a toilet ɗin ta samu wayarta na ringing. Cike da zumuɗi ta ɗaga ganin Fatima. Tun jiya suka sanar mata yau zasuje Hutawa duba Abba (Dauda) da baida lafiya. Taso zuwa amma babu dama har kuka tayi. Sai dai ta ƙudiri niyyar idan Ramadhan ya dawo zata roƙesa alfarmar zuwa itama. Bayan sun gaisa dasu Fatima har dasu Inna Fatisa ke sanar mata ga ƙawarta Zubaida da tazo duba Abban su gaisa.


   Cike da mamaki tace “Zubaida fa? Dama bata mance ina duniya ba?”.


   “Ni na isa first lady ɗinmu. Ranki ya daɗe kin wuce a manta dake ai a ƙasar NAYA ”.


  Zubaida data amsa wayar ta faɗa.


“Mara kirki bazaki canjaba dai?”.


Cewar Raudha cikin dariya.


   Dariya itama Zubaida ɗin tayi, kafin su gaisa a mutunce. Zubaida ƙawartace ta islamiyya. Itama yarinyace mai ƙwazo da sanyin hali kamar Raudha. So da yawama akance halinsu yazo ɗaya ne shiyyasa suke abota. Duk da abotar tasu bawai takai mai tsanani bace da har suka san sirrikan juna musamman ma Raudha da ba'a jin cikinta. cikin tsokana Zubaida ke faɗin, “Halan kin kusa sauke mana babynmu ranki ya daɗe”.


    Raudha tai dariya tana ɗakko kayan da zatasa a Wadrobe. “Aiko gashi ma har yana motsi a ciki, ina fatan kun shirya zuwa suna”.


  Dariya sosai Zubaida keyi. Itama Raudha haka. “Uhm matsoraciya keda rakin nan naki ace cikin ya tsufa za'aji muryarki haka ragal”.


   “Tabɗi mi kika ɗaukeni. Ki shirya zuwa Bingo kiga yanda nake daram kuma ga ƙaton cikin ƴan biyunku tare dani. K cikinfa ba wani wahala kwantar da hankalinki ke huɗu zaki samo mana lokaci guda......”


    “Idan ita bata samoba ke zaki samoshi yau ɗin nan”. A mugun firgice Raudha ta juyo har towel ɗinta na ƙoƙarin kwancewa jin muryar wanda batai zatoba balle tsammani. Sanye yake cikin kananun kaya tausasa gaba ɗaya baƙaƙe. Ya ƙara wani fresh abinsa harda ɗan tumbi alamar hankalinsa kwance yake. Ga sumarsa data sake samun kulawa na gyara. Sam batasan ya dawo gidan ba balle shigowa ɗakin dan ko shigowar motocinsa yau batajiba sam kokuwa hankalintane bai a wajen, ta diririce da rasa inda zata tsoma ranta taji daɗi ganin ita yake nufowa. Har yazo gab da ita bata samu mafitar kare kanta da ko saka hijjab ba. Ta cikuykuyo wasu kaya zata yafa a jikinta ya riƙe yana mai zagayawa ta bayanta ya rungumota jikinsa.


    Wayar ya zare da kallon screen ɗin, tuni dama ta yanke kiran, sai dai hakan bai hanashi ganin da Fatima tai wayar ba. “Ai bansan kina bukatar ƴan uku ba Ustazah da tuni na ajiye ƙawancenmu gefe na baki ajiyarsu”.


   Innalillahi ina ƙasa Raudha ta shige ta huta. Ya sake kanainaiyeta jikinsa da kai hannun kan ɗaurin towel ɗinta zai kamar zai kwance. Da wani irin zafin nama ta wulƙito ta rungumesa jikinta na rawa sai ambaton “Innalillahi...” take har ƙarshe. Shiko mizaiyi inba dariya ba. Sai dai yay dauriyar gimtsewa abinsa ya sake kama towel ɗin data ƙanƙanme cikin hannu ta gaba ɗaya. “Dan ALLAH ka rufamin asiri karka cire Ya Ramadhan. Inba hakaba zan iya rasa numfashina”.


    “Sai in baki nawa mu rayu tare ai”.


Ya faɗa cikin raɗa da wata irin murya mai wahalar fassara ga Raudha.


   Raudha ta sake ƙanƙamesa saboda yanda zuciyarta ke masifar gudu cikin ƙirjinta. Tunda suke bai taɓa mata kalar abun nan ba. Iyakarsa taɓa hanunta fuskarta ya dan sumbata ko laɓɓanta. Amma bai taɓa gwada ɗora hanunsa a wani sashe na jikinta ba sai yau. Dan kuwa a bazata taji saukar hanunsa kan ƙirjinta. 


   “Na shiga uku”.


 “Baki shiga uku ba. Ai maganar kunya kuma ta kare insha ALLAH yau zamu neman ƴan huɗu............✍


No comments

Powered by Blogger.