Bakar Inuwa 43
Chapter 43
43
.........Ta najin shigowar motocin da suka ɗakkosa gidan ta miƙe a ɗan zabure wai zatai fitsari. Bilkisu da tuni ta gama fahimtar a tsorace take tai saurin riƙota tana danne dariyarta.
“Hi madam! sai fa Brother yaga kwalliyar nan ya shaƙi daddaɗan ƙamshin nan, dan haka babu inda zaki gudu”.
Fuska sosai Raudha ta marairaice kamar zatai kuka. “Aunty Please, kuma fa da gaske nak.......”
Sauran maganar ta maƙale sakamakon haɗa ido da sukai da abinda take tsoron gamuwar. Cak numfashinta ya ɗauke daga maƙoshinta har gangar jiki, sai da taji tana neman shiɗewa ne ta haɗiyi wani bushashshen yawu da ƙyar fuskarta na sake narkewa alamar dai da gaske a tsorace take, dan har yanzu ruwan masifar daya zuba mata shekaranjiya tana zaune daram a brain ɗinta, kowace daƙiƙa cikin bitarsu take a zuciya. Ga mai kallonta kuma a yanda tai ɗin babu maraba da shagwaɓa....
A hankali Bilkisu dake murmushi itama idonta akan Yayan nasu ta saki hanunta tana masa sannu da zuwa kafin ta ɗan zunguri Raudha ɗin alamar ta tashi ta tarbesa...
Ko gaisuwar bilkisun ma bai amsa ba, sai wata ƴar harara daya zuba mata na tabbacin har yanzu a ƙule yake da su yayi da idanunsa da sukai ɗan ja. Hakama saman hancinsa jajur yake da alamar murace ta kamashi.. wucewarsa yay zuwa bedroom ɗinsa jikinsa duk yay masa nauyi, saboda murar daya tashi da ita a safiyar yau. Gashi wahala mura ke bashi inhar ta damƙesa.
Nannauyan numfashi suka saki kusan a tare, sai kuma suka kalli juna suka ƙyalƙyale da dariya. Raudha da sosai ta saki jiki da Bilkisu a kwanakin nan tace, “Kai aunty B wlhy kema a tsorace kike fa”.
Dariya sosai Bilkisu tayi, cikin magana ƙasa-ƙasa tace, “Wlhy bazaki gane bane, Brother da kike gani ɗan daru ne bana wasa ba. Idan ya birkice babu mai iya tarosa sai Anne ko Bappi”.
Sake tsargawa cikin Raudha yayi har Bilkisu najin ƙara ƙulululu!!!, kasa daurewa tai sai da ta ƙyalƙyale da dariya. Yayinda Raudha kuma ta ɗan dafe cikin tana yamutsa fuska.
“Kinga tashi ki bisa da ruwa, naga ma kamar mai mura fa. Kuma mura na wajigashi idan ta kamashi”.
“Aunty B wlhy tsoro nakeji. Kinga kuwa harar daya bamu ko amsa sanun da kikai masa baiyiba fa”.
“Karki damu zai huce. Kedai kawai abinda zakiyi ko yayi magana yanzu karkice komai sai ban haƙuri. Ko bayani kar kice zaki masa za'a samu matsala dan ya tsani maimaita magana”.
Cikin tausayin kai Raudha ta jinjina mata kai tare da miƙewa. Dan koda bata son sa bazata taɓa son ace ta gagara sauke hakkin aure da ke a kanta ba. Idan ko ta tuno gargaɗin mahaifinta bazataso aurenta ya mutu ba har abada koda batajin daɗi a cikinsa. Ruwa da cup ta haɗa saman wani ƙyaƙyƙyawan golden tray mai yarfin fari kaɗan da fresh milk duk da tasan duk akwaisu a ɗakinsa. Ta gyara lulluɓin mayafinta har saman kai kamar wacce zata fita duk da ba wani babba bane ba. Yanda ta fahimcesa ma idan tace zata fita waje da mayafin ai zai iya halaka ta.
“Kimin addu'ar fitowa lafiya dan ALLAH aunty B”.
Ta faɗa cikin marairaicewa lokacin da tazo saitin Bilkisun. Cikin danne dariya Bilkisu tace, “Fatan alkairi aunty Babba. Insha ALLAH babu ma abinda zai faru sai alkairi da tsarabar kiss”.
Kunyar maganar ƙarshe ta saka Raudha saurin yin gaba tana ɗan tura baki. Bilkisu ta ƙyalƙyale da dariya har ranta tana sake jin ƙaunar yarinyar.
Tamkar wadda tazo sata a ɗofane tai knocking ƙofar batare da tunanin zaima jita ba. Jin shiru ya sata ƙara ɗan bugawa nan ma tsitt. Hannu ta kai zata sake bugawa a bazata aka buɗe ƙofar hanunta ya sauka saman kirjinsa da babu riga. Hasalima daga shi sai towel yana ta raɓar ruwa alamar wanka ya fito.
Da ƙarfi Raudha ta rumtse idanunta da ƙoƙarin janye hanunta daya haɗu da laushin fatarsa da laimar ruwan ɗumin dayay wankan da shi. “I...am sorry. ALLAH ban san ka taho ba”.
Ta faɗa kamar zatai kuka idanunta har lokacin a rumtse suke ji take kamar ta saki gudawa. Jin shiru ya sata ɗan buɗe ido ɗaya kaɗan. Wayam baya a wajen, gaba ɗaya ta buɗe tana haɗiye yawun da ya kasa wuce mata a maƙoshi da ɗan dafe ƙirji ta sauke numfashi. sai kuma tai saurin ɗago hanun ta kalla tare da kai masa duka da ɗayan hanunta tana cije baki kamar maiyi da wani (😂ba man kai ... Lol)
“Malama ki rufen ƙofa inba shigowa zakiyi ba”.
Ta tsinkayi muryarsa da ke nuna tabbacin mura yake. Dan baima kai ƙarshen maganar ba ya saki atishawa a cikin tissue ɗin dayay saurin ɗorawa kan bankinsa.
(Masifaffe). Ta ayyana a ranta tana ɗaukar tray ɗin data ajiye a drawer glass da akai ado da shi gab da ƙofan ɗakin nasa. Koda wasa batai gigin kallonsa ba, dan shi ya fuske abinsa duk da kuwa daga shi sai towel. A ɗan table ɗin gaban sofa's ɗin ɗakin ta ɗora, kanta a ƙasa tace, “Ina yini? an dawo lafiya?”.
Sarai ya jita, amma yay banza yana cigaba da shafa mansa lokaci-lokaci yana atishawa, yabi ya tara uban tissue a ƙasa da yake tarewa da shi. Raudha na ƙoƙarin barin ɗakin cikin takaicinsa dan ta tsani wulaƙanci duk da bata da yawan hayaniya ya katse hanzarinta da faɗin, “Bani dustbin”.
(Yadai fi). Ta faɗa a ranta tunawa da wahalar da tasha wajen gyaran ɗakin nasa lungu da saƙo. Shi kansa lokacin daya shigo yaga ɗakin sai da yaji a ransa ba gyaran Tahir bane. Yanda bai tanka ba data gaishesa itama hauka ta manna masa taki tankawar ta fice. Kallo ya bita da shi cikin jin haushin bata amsa maganar da yay mata ba (ƙarfin hali😜 lallai wanzami baya son jarfa).
Guntun tsaki yaja da cirar tissue ɗin ya sake atishawa a ciki. Idanunsa sun kara kaɗawa da ja har suna tara ruwa a ciki. Jijiyoyin goshinsa kam duk a miƙe suke alamar ciwon kai.
Yana ƙoƙarin saka shirt mai ɗan kauri ta shigo, bata yarda ta kallesa ba, cikin ɗan yamutsa fuska da bata san tanai ba tasa yatsu biyu tana a yanayin ƙyanƙyami ta dinga ɗauke tissues ɗin daya tara a ƙasa tana jefawa a dustbin ɗin. Cak ya dakata da abinda yake yana kallonta, a ransa ya ce, (Da gaske yarinyar nan ta bala'in rainani, wai ni take ƙyanƙyami?) a fili kam sai ya taɓe baki ya ɗauke kansa. Ƙarasa shirinsa yay ya ɗauka misk zai ɗan shafa dan baya buƙatar saka wani spray turare saboda mura, dai-dai Raudha ta gama kwashe tissues ɗin sai wani kwaɓe fuska take hanunta a buɗe tabbacin ƙyanƙyami. Dariya yaji tazo masa tsabar muguntar daya shirya mata. Amma sai ya gimtse kayarsa bama zaka taɓa fahimtar hakan a fuskarsa ba. Raudha na ƙoƙarin gyara mayafinta kawai taji saukar atishawa a fuskarta har biyu a jere.
“Innalillahi.....” ta faɗa cikin subutar baki tana sakin dustbin ɗin ƙasa. Misk ɗin daya gama shafawa ya ajiye saman mirror yabar wajen tamkar baima san abinda yayi ba. Yaje saman sofa ya zauna ƙafa daya kan ɗaya. Cikin bada umarni da isar daya gada ga Gimbiya Su'adah ya ɗauka jaridar dake ajiye saman stool ɗin gefen kujerar yana faɗin, “Sai kiyi ƙyanƙyamin da hujja yanzu ai ko? Ina bukatar shayi kuma”.
Wani irin yamutse fuska Raudha tai, kai kace amai ne zai kufce mata. Sai kuma ta fashe da kuka ta ɗauki dustbin ɗin ta fice.
Da kallo ya bita ta saman jaridar, sai kuma ya saki guntun murmushi da taɓe baki lokaci ɗaya yana ɗage kafaɗa irin ko'a kwalar rigarsa ɗin nan.
Cikin sa'a Raudha ta samu bilkisu bata falon, kitchen ɗin dake falon ta shiga, kuka tayi sosai dan har cikin rai taji zafin abinda yay mata, yayinda wani gefe na zuciyarta ke ƙoƙarin nusar da ita abinda yayi ɗin ba komai bane, sai dai taƙi saurarensa. Sai da ta fidda duk wani takaicinta sannan ta wanke fuskar tas har kwalliyar tana faɗin “Anma fasa kwalliyar ALLAH bazaka sake gani ba”. Shayin da yace ta haɗa masa ta haɗa cikin flask mai ƙyau bayan taje ƙasa ta ɗibo kayan data san ana dafa masa shayi da su da yawa.
Maimakon a ɗaki data barsa sai ta iskesa a falo zaune yanzun. Bilkisu na daga zaune ƙasan carpet itama kusa da ƙafafunsa da alama haƙuri take bashi. Dan yanda tai kalar tausayi ya isa tabbatar da haka. Shiko yayi wani kicin-kicin da fuska har yanayin nasa yasa Raudha sake shiga hankalinta. Bayan ta ajiye a gabansa ta zuba shayin tare da saka masa sugar ɗinsu na masu diabetis da yake amfani da shi. Komai baice ba ya ɗauka abinsa ya fara sha.
Kanta a ƙasa tana ɗan wasa da yatsun hanunta tace, “A kawo abincin nan?”.
Cikin mamaki da al'ajab ɗinsa taga ya wani zuba mata idanunsa da mura ta gama firgatawa. Dan harsun kumburo fatarsu tai jaa ga ƙyallin ruwan a ciki, tsaf ya fahimci kuka tayi, sai kuma ya ɗanji babu daɗi. Amma a fuskarsa bazaka taɓa fahimtar hakanba. Dan wani yamutse fuskar yayi ma ya ɗauke kansa bayan ya zuba mata nunanniyar harara.
“Zan sha wannan, idan da buƙatar hakan daga baya na ci”. Ya faɗa bayan yaja wasu sakanni.
Baki ta taɓe zata bar wajen Bilkisu ta ƙyafta mata ido alamar karta tafi. Ta marairaice fuska kalar tausayi da alamar roƙo wa Bilkisun. Da ido Bilkisun tai mata nuni da Ramadhan da ya maida hankalinsa ga jarida... Sai kuma ta ɗauke kanta da faɗin, “Yaya dan ALLAH fa nace, i promise hakan bazai sake faruwa ba. Wannan ma kuskure ne wlhy kuma nice nayi banda Aunty Raudha dan batama san na ɗaura ba”.
Shiru kamar bazai tanka ba sai kuma ya ajiye jaridar yana furzar da huci kaɗan. A takaice ya ce, “Tashi kije”.
Ta san ya haƙura kenan, dan haka cikin jin matuƙar daɗi ta miƙe fuskarta washe da murmushi tana faɗin, “Thanks you Yaya. ALLAH yasa aunty Raudha ta haifa mana ƴan biyu”.
Hannu ya ɗaga kamar zai kai mata ranƙwashi ta kwasa da gudu tana dariya. Shima dai murmushi ne ya subuce masa a bazata. Yana matuƙar son Bilkisu a duk cikin ƙanensa. dan tanada hankali da nutsuwa. Gata da addini, wani lokacin akance halinsu na kamanceceniya da juna. Hakama a fuska suna matuƙar kama. Har lokacin da ɗan murmushi a fuskar tasa ya maida dubansa ga Raudha da mamakin dama yana wasa haka ya narkar da ita. Haɗa idon da sukai ya sata janye nata tai gefe da shi tana tura baki, dan har yanzu a fushi take. Sai kuma tai saurin yunƙurin barin wajen itama......
“Ina su Muneera?”.
Tambayar tasa ta sakata tsayawa cak, sai kuma ta juyo kanta a ƙasa. “Inaga suna can gida, Yau kwanansu biyu”.
“Kinaga? Bamaki da tabbas kenan?”.
Yanda yay maganar a dake ya sata ɗagowa ta ɗan kallesa. kasancewar idanunsa a kanta suke saita janye. Duk da zafi da zuciyarta ke mata sai ta danne. Banda ma ya raina mata hankali su Lubnah dake manyanta ne zai nuna kamar laifintane barinsu fita. A fili kam cikin sanyin murya da ɗan fushi-fushi tace, “Nasan can ɗinne kawai zasu je. Kuma ni da zasu wuce basuyi sallama da ni ba ai miye nawa”.
Yanda taɗan tunzura baki ya fahimci haushi taji. Batare da yace mata komai ba ya ɗauke kansa kawai gareta ya maida ga jaridarsa. Itama ganin haka ya sata barin wajen tai wucewarta bedroom.
*BAYAN SALLAR ISHA'I* tana zaune a ɗaki ita kaɗai dan bilkisu na ɗakin da su Lubnah suke tana waya da saurayinta ne. Yunwa takeji sosai shiyyasa tana idar da salla taje falo ta ɗibo abinci....
A hankali ya turo ƙofar waya manne a kunensa, kan agogon ɗakin ya fara sauke idanunsa kafin ya maida kan Raudha da mamakin shigowar tasa ya sakata shagala a kallonsa.
Takawa ya cigaba dayi inda take a hankali, tsabar yanda ta tafi wani tunani daban yasa harya iso gabanta bata sani ba. Firgigit ta dawo hayyacinta jin an hure mata idanu. Yanda ya ɗan ranƙwafo fuskarsa gab da tata har yana busa mata numfashinsa ya sata ƙoƙarin jan jikinta baya amma sai ya saka hannunsa jikin kujerar ya tokare. Koda ta matsar da kan nata sai ya sauka akan hanunsa. Saurin ɗagawa tai hakan kuma sai ya ƙara basu kusancin da take gudu. A haka ya cigaba da wayarsa cikin harshen turanci idanunsa cikin nata, yayinda yatsansa ke shafa girarta.
Fuska Raudha ta ɓata kamar ta fasa ihu da wannan dabaibayi nasa data gagara fassarawa, acan kuwa zuciyarta na liguden daka, sai dai duk yanda taso ɓoye firgicinta ya riga ya gama karantarta, dan duk ta daburce. Hatta cokalin da take shan farfesun gabanta ya suɓuce a hanunta ya faɗi saman table ɗin. Duk yanda ya fahimci takurata yay yaƙi janye jikinsa. Sai ma cigaba da wayarsa yay hankali kwance numfashinsa na sauka saman fuskarta itama yanajin nata a wuyansa, ta rasa yanda zata fassara lamarin nasa.
“Ina yini”.
Ta faɗa kamar zatai kuka dai-dai yana sauke wayar a kunensa alamar ya kammala wayar, dan wannan kusanci nasu ya matuƙar sakata cakwalkwalin ruɗani. Kaɗan ya rage dariya ta suɓuce masa amma ya danne. Janye jikinsa yay da ga gareta ya kai zaune a kujerar gefenta cikin basar da gaisuwar tata.
Da ƙyar ta iya sakin numfashin data riƙe a ƙirji. Fitsari ne kawai ya ragema Raudha ta saki itakam dan al'ajabinsa. Bata gama dawowa hayyacintaba ta tsinkayi muryarsa still da wani furicin.
“Har yanzu kina ƙyanƙyamin nawa?”.
Babu shiri ta kallesa ido a zare. cikin marairaicewa ta ce, “Ni yaushe nace ina ƙyanƙyaminka?”.
Yanda tai maganar ya sashi tsura mata idanunsa da mura ta cika. Sai kuma ya janye yana sake tamke fuska. Kamar yanda itama ta ɗaure tata tamau.
Fuskarsa ya ɗan sake matsarwa gab da tata, still yanzu ma suna shaƙar numfashin juna. “Idan ma baki faɗa da baki ba ai sirrin zuciyarki ya fito, shiyyasa na baki numfashina naga idan kin ɗauka ke kuma yaya zakiyi da kanki?”.
“Ya ALLAHU!”. Ta faɗa cikin subutar baki da waro idanunta waje gaba ɗaya kansa. Yatsun hanunsa biyu ya ɗan kaɗa mata, sai kuma ya duba bowl ɗin gabanta mai ɗauke da farfesun kayan cikin da Bilkisu tai musu. Yunwa ce ta addabeta dan tun safe rabonta da abinci, fargabar dawowarsa da tuna azabar masifar da yay mata a waya ya hanata sake cin wani abu. Dama da safen Bilkisu ce ta takura mata........
“Ammafa wannan cin amana ne, aci nama ina gidan nan babu ni, wannan ƙawancen dake tsakaninmu kuwa na tsoron ALLAH ne Ustazah?”.
A yanda yay maganar ya sata kasa daurewa sai da ta kallesa. Ganin idonsa a kanta ya sata ɗauke nata da sauri tana tura baki. (Na shiga tara ni Raudha, ALLAH yasa dai da gaske ya huce kenan) ta faɗa a ranta, a fili kuwa sai ta ja kwanon namanta gabanta da faɗin, “Naji a kwance, idan na gama ci sai mu shirya”.
“Ko? to andai ji kunya Ustazai da rowan nama, idan kina son kanki da arziki muje ki bani nawa naci kokuma na ɗiba rabona a can”
Yay maganar cikin ɗage mata gira ɗaya yana miƙewa. Batare da ya jira cewarta ba ya fice abinsa. (Uhm, su Ramadhana an fara zama ƴan is...😏🚶🏻)
Filo Raudha ta ɗauka ta balla masa cizo tana matsesa a ƙirjinta. Sai kuma ta tillashi ƙasa tare da dafe kai tana faɗin, “Ni Raudha yama haukatar dani”.
Babu yanda ta iya dole ta miƙe ta ɗau mayafinta na ɗazun dan kayanne a jikinta har yanzun ma ta fita. Tsaye ta samesa a falo hankalinsa gaba ɗaya akan television da ake nuna labarai. Koke-koke da taji anayi a tvn ya sata saurin kallo gabanta na faɗuwa. Jikinta ya kama rawa, domin kuwa rahotone na wani ƙauye a ƙaramar hukumar Gaman dake jihar Kuddo faɗa ya ɓarke a tsakanin ƙabilun dake ƙauyen. Gawarwakine zube na yara da manya harma da dabbobi, wasu jina-jina da raunika abin babu daɗin gani. Ga wasu nata kuka durkushe gaban gawarwakin ƴan uwansu da aka kashe ko aka raunata.
Kuka da Raudha ta fashe da shi ne ya maido Ramadhan da ga ɗaukewar numfashi da ya tafi na tashin hankali. Ya kai zaune jib cikin kujera hajijiya na neman ɗibarsa. Ba yau ne aka fara irin wannan rikicin a ƙauyen ba, sai dai bai taɓa gani ba kamar yau, ga shi yau ɗin daya gani kuma yana amsa sunan shugaban kasar NAYA ne da hakkin kowa ya rataya ne a ƙarƙashin mulkinsa..... Yanda jikin nasa ke rawa ya sakashi riƙo Raudha data kai dirƙushe a gabansa tana kuka ya rungume, itama ƙanƙamesa tayi kawai tana sakin wani sabon kukan.....
Wayarsa ya fara laluba da hannu ɗaya a aljihu, yayinda ɗayan ke tallafe da Raudha. Yana cirota kafin ma ya aiwatar da abinda yake shirin yi kira ya shigo masa. Da ƙyar ya iya controling kansa tsabar ruɗani ya ɗaga, da ga can hankali tashe cos ya ce, “Ranka ya daɗe kaga abinda ake nunawa a tashar Q-TV kuwa? Kodai halin ƴan adawa ne kawai....”
“No Jafar, karka kawo wannan, ka bincika yanzu abun ke faruwa ne ko tun ɗazun?”.
“Okay sir ina zuwa”.
Wayar ya jefa saman kujera, ya kai zaune shima har yanzu Raudha na jikinsa tana sharɓar kuka. Ji yake kamar shima ya fashe da kukan, amma ya daure ya ɗago Raudha, cikin dakiya yake faɗin, “Please Ameenatu relax mana. Kukanki sake tadamin hankali yake, bayan daga gareki ya kamata na samu ƙarfin gwiwa”.
Hannu tasa tana sharar hawayen, “Kayi haƙuri”. Ta faɗa tana ƙoƙarin tashi daga saman cinyarsa da take zaune ɗare-ɗare gudun kar Bilkisu ta fito, kuma a karankanta ma dai da kunya ai.
Komai baice mata ba, sai wayarsa data fara ring ya kai hannu ya ɗauka ganin cos ne.
“Ranka ya daɗe a yanda suka faɗa su dai yanzu ne. Amma dai yanzu I.G ya tabbatar min tun kusan magrib ne abun ya fara faruwa kamar yanda C.P ɗin jihar Kuddo ya sanar masa. Sai dai ka kwantar da hankalinka ya tabbatar min komai ya dai-daita zuwa yanz.......”
A matuƙar tsawace shugaban ƙasa Ramadhan ya katse cos, “Taya zan kwantar da hankalina Jafar? mutane na cikin irin wannan tashin hankalin!! Ka duba fa kaga mata ne da yara kanana a cikin jini saboda rashin imanii!!! Yanzu da akan familyna ya faru zakace na kwantar da hankalina ne? Na shiga uku ni Ramadhan!........”
A yanda yay maganar dole ne ya baka tausayi ya kuma tayar maka da hankali, dan abun al'ajabi sai ga hawaye na sakko masa. Wayar yay jifa da ita tare da dafe kansa yana yamutsa gashinsa da duka hannayensa biyu.
Sosai Raudha ta sake rikicewa itama, dan yanda yake birkita sumarsa yana hawaye da ambaton ya shiga ukun itama sai ta sake fashewa da kukan da zuwa gabansa ta durƙushe hannayenta duka biyu akan gwiwoyinsa............✍
Leave a Comment