Bakar Inuwa 40

 


.........Ba sai an mata wani explanation ba tasan shine. Dan mayataccen ƙamshinsa tuni ya ƙara ƙarfi a ƙofofin hancinta. Kasa buɗe ido tayi ta kallesa dan kunya, ga shi bata da ƙarfin da zata ƙwace jikinta a nasa. 

      “Kina ganin jiri ne?”.

   Ya faɗa a hankali yana tallafo fuskarta cikin tafin hanunsa. Bata yarda ta buɗe idanunta ba, sai ta jinjina masa kanta, zuciyarta babu abinda take sai luguden daka kamar zata fito waje, ga tsigar jikinta sai yamutsawa take. Dan wannan shine karo na farko da ya taɓa mata irin wannan riƙon a cikin jikinsa sosai kamar haka. Shi kansa danne yanayin kawai yake a zuciyarsa, yay ƙoƙarin kaita zaune a bakin gadon....  

         Dai-dai lokacin Mama Ladi da batai zaton samunsa a ɗakin ba ta turo ƙofar da sallama ta shigo saboda tasan Raudha ɗin ma ta barta ne tana wanka batai tsammanin ta fito ba. Shigowar tata baisa ya janye jikinsa da ga na Raudha ba, sai ma itace data ɗan dabirce har ta samu ƙarfin yin mutsu-mutsu amma sai ya shareta. A ɗan rikice Mama Ladi ta juya zata koma ya dakatar da ita

      “A gafarce ni ranka ya daɗe wlhy bansan kana ciki ba”.

     “Is ok”. Ya faɗa tamkar baya so yana matsar da jikin nasa daga na Raudha ya zaunar da ita da ƙyau ya miƙe akan ƙafafunsa, nuni yayma Mama ladi data ajiye kayan hanun nata. Cikin girmamawa ta ƙaraso ta ɗora tray ɗin saman table da alama abinci ta haɗoma mata.

         “Babu dai wata matsala zuwa yanzu ko?”.

       “Eh ranka ya daɗe Alhmdllhi. Likitama da tazo ɗazun tace komai ya dai-daita sai dai a cigaba da kula da maganinta, ta kuma dinga cin abinci sosai dan ƙarfin jikinta ya dawo”.

      Baice komai ba sai kallon Raudha da yayi. Sosai ta rame, ƴar ƙibar da tayi duk ta zube. Idanun ya janye yana ɗan furzar da iska. Sai kuma yace, “ALLAH ya ƙara lafiya”.

        Mama Ladi ta amsa da “Amin”. Raudha ma data kai kwance saboda rashin ƙarfin jiki ta amsa a laɓɓanta. 

        Bai sake cewa komai ba ya fita a ɗakin ya barsu, dan Taura house yake son zuwa amma a ɓadda kama zai fita gidan. Ɗakinsa ya koma ya ɗaura jacket saman kayansa da p-cap ya fita, odilan ɗinsa dake jiransa dan dashi kaɗai zasuyi fitar yay saurin risinawa yana masa barka da fitowa. Kansa kawai ya jinjina masa. 

       “Saifu muje lokaci yaja”.

   “Okay sir, odilan Saifudden ya faɗa da sauri yana buɗe masa back sit.


*_★★TAURA HOUSE★★_*


        Gaba ɗaya ranta a ɓace yake tun jiya a gidan, tsabar bala'in dake cin ranta ko barcin kirki batayi ba da daddare. Yinin yau kuwa babu wanda zai ce yama ganta a gidan har ƴaƴanta, sai Adda Asmah data shigo da yamma ta ƙara fanfata matuƙa saboda cikin nan na Raudha ya matuƙar tsaya musu arai duk sun san ya zube kamar yanda sukaji bakin su Lubnah da Anne. Ɗazun da rana Hajiya Shuwa da Hajiya Mufida sunje har government house sun duba Raudha. Koda Anne taga babu gimbiya Su'adah batace komai ba, saboda ɗaukar hakan matsayin kawaici ga abokan zaman nata.

        Knocking ƙofar bedroom ɗin nata ya katse mata wayar da takeyi da Fulani. “Ammy zan kiraki inaga gashi nan ma yazo mara mutuncin”. Daga haka ta yanke kiran da miƙewa ta buɗe ƙofar dan a kulle take kasancewar bata buƙatar kowa ya shigo mata.

          Barin wajen tai, Ramadhan da yaga tsantsar ɓacin rai a yanayin nata ya ɗan furzar da iskar bakinsa yana ambaton sunan ALLAH a zuciyarsa. Ko ɓangaren su Anne bai shigaba ya wuto nan. Koda ya kai zaune yana gaisheta bata amsa masa ba, sai kawai ya saki ɗan murmushi da zame p-cap ɗinsa ya ajiye shima yay shiru. 

       Tsahon mintuna uku ɗakin ya ɗauka shiru, sake ɓaci ranta yayi fiye da wanda take ciki. A zafafe ta watsa masa harara tana magana a kausashe, “Yanzu ai ka fara ganin abinda muketa nuna maka akan wannan shegen auren, matarka tayi yanda take so na zubar da ciki saboda ta fito a gidan marasa tarbiyya. Tunda ta nuna bata shirya haihuwa ba kasani ni bazan amince ba. Dan haka dole ne ka ƙara aure nan da wata ɗaya, kuma Aina'u zaka aura.....”

       “Maah!. Aina'u?”.

   “Eh ita, idan kuma ban isa ba kamar yanda ubanka da kakaninka suka isa har suka aura maka zaɓinsu ka amsa ba tare da bijirewa ba sai naji.”

       Iska ya furzar da ƙarfi yana ɗan rumtse ido da buɗewa lokaci guda. “Maah Please calm down. Kibar zancen wata Aina'u a beg. S.......”

      “Anƙi a bari ɗin, kai yanzu Ramadhan dan baka da mutunci har kana da bakin faɗamin nabar zancen ɗiyar ƴar uwata akanka? Aka saka kama auri karuwa....”

      (Ya ALLAH) ya faɗa a zuciyarsa yana rumtse ido da murza goshi. Cikin zafin rai gimbiya Su'adah ta cigaba da sauke masa takaicin Raudha da shi kanshi da dama take ƙullace da shi tun lokacin first night da suke tunanin ya faru tun a waccan ranar. “Ita ga ƴar iska mara mutunci, tasan bata shirya haihuwa ba miyasa ta yarda da kai dan ubanta, nama godema ALLAH data zubar ɗin kuma mahaifar tata bazata sake ɗaukar wani cikin ba. Bani da rabon haɗa zuri'a da jinin karuwai!!”.

       Sosai ransa a dagule yake. Amma ya daure dan mahaifiya ta wuce wasa. Babu abinda yake sai haɗiyar zuciya. Babbar matsalarsa auren Aina'u da ta ambata, koma mizai faru sai dai ya faru babu auren Aina'u a cikin tsarinsa. Yariyar daya gani da idanunsa a cikin tsakkiyar club a America ana lesbians da ita, ƴan iska na ihu suna ɗauka a waya (Wa'iyazubillah). Ta rufe fuska da mask, shiyyasa tai tunanin babu mai ganeta, sai dai tayi rashin sa'a shi ya ganetan da idonsa. Dan ya tabbatar mata ya ganeta ɗin kuma ya cire mata mask ɗin. A wannan rana baiyi barci ba dan tashin hankali, dan koba komai itaɗin jininsa ce. Da uwarta da tashi fa uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Sannan mahaifinta shima ɗan masarautar su Maah ɗinne ɗan uwa na jini matsayin Uncle yake garesa. Amma itace yanzu Mahaifiyarsa ke tabbatar masa zai aura. Ji kawai yake ana ambaton Raudha da ɗiyar marasa tarbiyya amma shi har yanzu bai tabbatar ba tunda bai taɓa ganinta tana aikata wani fasiƙanci ba. Itako Aina'u da idonsa ya ganta ba labari ba.......

          “Tunda ga ƴar iska ina magana kamin shiru ko!!”.

     Gimbiya Su'adah ta faɗa cikin dawo masa da hankalinsa gareta. Ajiyar zuciya ya sauke yana gyara zamansa. Cikin tausasa harshe yace, “Maah Please relax. Ki bari ki huce sai muyi magana daga baya. Indai dan haihuwa ne insha ALLAH jikoki har sai kin rasa yanda zakiyi da su a gidan nan.....”

        “ALLAH ya tsareni samuwarsu da ga wannan jinin karuwan da talauci. Dan haka karka sake min irin wannan maganar zan ɓata maka rai”.

     “Ok. ok!. shike nan kiyi haƙuri Please”.

    Tsaki taja tana ɗauke kanta gefe. Kaje dare yayi, amma ka tabbatar ka samu kakaninka da mahaifinka da maganar Aina'u dan wlhy babu fashi saika aureta, sai dai in mutuwa kayi ko ita ta mutu”.

     (Oh oh, shikam yau ya zaiyi da tsohuwar nan) ya faɗa a ransa yana dafe kai.


*_GOVERNMENT HOUSE_*


        Tunda ya shigo ya zube a falon upstairs ɗin ransa duk a jagule. Kansa harya fara ciwo tsabar rasa ina zai kama. Magana da yake ji ƙasa-ƙasa kamar ana raɗa ya sashi sake nutsuwa da hasashen ta ina ne. Fahimtar da ga inda sautin ke tashi ya sakashi miƙewa. Kansa tsaye ya tunkari wajen, amma tsabar shagala da Aina'u tai a wayar da take yasa sam bataji motsinsa ba balle ƙamshin turaren sa.

       “Amma naji daɗi Ummi da kika sake tunzurata, duk da dai wlhy a tsorace nake. Har zuciya ina son Yaya Ramadhan, amma nasan akwai matsalar da tai mana katangar danne zumuɗina. Gani nake kamar tursasawarku ma bazatasa ya amince ya aurenin ba......”

     Shiru tai alamar an katseta daga can. Sai kuma ta sauke numfashi. “Wlhy zan jure Ummi, nidai yanzu burina ya amince ɗin, indai na zama matar tasa komai mai sauƙi ne. Sannan ƴar iskarnan nasan da wahala ta sake ɗaukar ciki kamar yanda doctor ya sanar mana. Kinga sanadin barinta gidan yazo kenan ƴar karuwai”.

     Dariya ta ƙyalƙyale da shi sai kuma ta dumtse bakinta tana ɗan waige irin kar ajitan nan. Hakan yasa Ramadhan sauri ɓoyewa dan karta gansan. Janye hanunta tai a baki tana cigaba da faɗin. “Nifa harma mamakin yanda akai cikin nake Ummi, wlhy kinga wancan zaman har muka bar gidan nan bamu taɓa ganin ta shiga ɗakinsa ba ko shi ya shiga nata. Hakama yanzu banda randa muka gane tana da ciki datai pretending ya ɗakkota daga falonsa bamu taɓa ganinsu tare ba. Ni anyama cikin nan bada shi tazo ba....”

        Shiru ta karayi na saurare. Sai kuma tace, “Wlhy Ummi komai zai iya faruwa. Ke dai ki cigaba da fanfa Maah dan ALLAH ayi-ayi nima na shigo wannan daular ta mulki a dama dani. Hhh Ummi nice nafi dacewa da first lady ba wannan ƙwailar yarinyar da ko ƙirar mata bata da shi ba”.

       “Ok Ummi kije wajen Abban karya jimu kin sansa. Da safe ma karasa”.


        Da kallo ya bita daga inda take tsaye harta shige lungun corridor ɗin bedrooms ɗin Raudha. Babu abinda ke masa turereniya a rai sai zantukanta da ya fahimci alaƙarsu da birkicewar mahaifiyarsu a yau. Wato Addah Asmah na tunzura Maah akan matarsa dan ya auri ƴarta. Wani murmushi ya suɓuce masa a bazata ya kai hannu ya shafo ƙeyarsa.

         Maimakon ɗakinsa da ya kamata ya nufa sai ya wuce na Raudha kamar yanda zuciyarsa ke tunzurashi. Kansa tsaye ya murɗa ƙofar ya shigo. Mama Ladi da ke lallaɓa Raudha ta sha ko farfesu ne da shayi tai saurin kallon ƙofar tana amsa sallamar da yay a hankali. Tunkan ya karaso ta risina tana gaisheshi. Amsawa yay idonsa akan Raudha data dafe kanta saboda ɗan nauyin da yay mata.

        “Wani abu ya sake faruwa ne?”.

   “A'a ranka ya daɗe babu abinda ya faru, bayan fitarka ne ta sake komawa barci sai yanzu ta tashi. To tace tanajin yunwa ne an kawo abincin kuma tace ta ƙoshi. Shine nake lallashinta taci kodan ta samu ƙarfin jikinta kamar yanda likitar tace”.

        Komai baice ba, sai alama da yayma mama ladin akan taje abinta. Cikin girmamawa ta risina da faɗin, “A fito lafiya ranka ya daɗe”.

      Kamar zaiyi magana kuma sai ya fasa. Yana tsaye hannayensa duka a aljihu har Mama Ladi ta fice ta rufo ƙofar. Raudha da har yanzu hanunta ke dafe da kanta cikin rashin ƙarfin jiki tace, “Ina yini”?.

       Karon farko taji ya amsa mata gaisuwarta da “Lafiya, yaya jikin naki?”.

      “Alhmdllhi naji sauƙi”.

Nanma baice komai ba ya taka zuwa bakin gadon ya kai zaune kusa da ita gab. Hanunta data tallafe kanta da shi ya janye da faɗin, “Oya ci abinci”.

        Batare data yarda ta kallesa ba ta marairaice fuska kamar zata fasa kuka. “ALLAH na ƙoshi”.

       “Ashe zan miki ɗura kenan ok! Bana son gardama maza ɗauka”.

            Bata da zaɓin daya wuce bin umarninsa. Dan yayi kicin-kicin da fuska babu alamar wasa tattare da shi. Badan yana mata daɗi ba ko ɗanɗano ta fara tsakurar abincin, yayinda shi kuma ya ciro wayarsa a aljihu ya fara dannawa. Da wannan ƴar damar ta ɗanci tea ɗin ma kaɗan. “ALLAH na ƙoshi”. Ta faɗa a marairaice dan yaji tausayinta. 

        Wayar ya ajiye tare da ɗagowa yana kallonta. Yanda ya ɗan tsura mata ido kamar mai nazari ya sata fara wasa da zoben hanunta......

      “Yanzu mike miki ciwo?”.

Kanta ta girgiza masa. “Ba ko'ina, sai dai ɗan jiri shima ba wani mai tsawwalawa bane”.

         “Kina sakaci da abinci ne shiyyasa shima bai tafi ba. Idan ALLAH ya kaimu gobe inada tafiya zuwa UK, zan samu kamar 4 to 5days kafin na dawo. So bayan na dawo inada sharuɗɗa na canja tsarin zaman gidan nan”.

     Wani irin ƙuuuu cikinta ya bayar amma batace komai ba. Shima bai damu da cewar tata ba ya cigaba da maganarsa a kausashe babu alamar wasa. “Dole ne ki koma tsayawa a kan masu girkin nan inhar zasu mana abincin da zamu ci ni da k. Zaki koma kwana ɗakina dan Maah tana buƙatar jikoki saboda tana tunanin ta rasa wani ne a yanzun......”

       Cak numfashin Raudha ya tsaya a aiki, cikin rashin fahimtar zancen nasa dan ƙwalwarta ma jitai ta toshe baki ɗaya ta ɗago tana kallonsa. Shima kallon nata yake cikin sarƙe idanun nata a nashi. A hankali ya kai fuskarsa gab da tata ya hure idanun nata. Saurin rumtsesu tai da ƙoƙarin jan jikinta baya amma sai ya ɗaura hanunsa a fuskar gadon kanta ya sauka akai. Jikinta ya sake matsowa a nata shima idanunsa na ƙara ƙanƙancewa. Cikin wani sautin murya da shi kansa baisan ta suɓuto da ga ƙirjinsa zuwa harshe ba yace, 

        “Idan kaka taso ganin jikokinta laifi ne?”.

       Ruɗanin da Raudha ta shiga ne ya sata fara girgiza kai jikinta na tsuma. Ya kashe mata ido ɗaya da janye fuskarsa a tata ya maida saitin kunenta “To ki shirya bata madadin babyn da take tsamanin ta rasa a jiya”. Ya ƙare maganar da ɗan sumbatar gefen kuncinta ya miƙewa lokaci guda da ɗaga mata yatsunsa biyu “Good-night”.

           Fitsari ne kawai ya ragema Raudha ta saki dan al'ajabinsa, amma hatta da kayan cikinta sai turereniyar dunƙulewa suke waje guda. da ƙyar ta iya sake numfashin data riƙe a ƙirji lokacin daya maida ƙofar ya rufe alamar ya fita. Gaba ɗaya kalamansa sai suka saka hajijiyarta sake dawowa sabuwa dan jinin daya batan ma ƙasa ya dinga zirarewa ta cikin jijiyoyi yabi numfashi ya fice fit. Hannu takai taɗan mari fuskarta dan gani take kamar a mafarki take dai, sai dai jin tabbacin a zahiri ne komai ya faru ba mafarki ba ya sata faɗin, “Inaga bashi bane aljani ne”.


(🤣🤣saifa aljanin kam).


★★★★★


      *_WASHE GARI_* kamar yanda ya faɗa kusan 8am ya shigo ɗakin nata cikin kwalliyar suit baƙaƙe da suka fiddo masa ainahin tsarin halittarsa da ƙyawun haiba da ƙuruciya. Duk ramar nan ta campaign ta ciko fatarsa ta sake fresh sai ƙyalli yake yi. 

        Kamar ko yaushe gaisheshi tayi sai dai taƙi yarda su haɗa ido dan har yanzu kalamansa na jiya basu bar bitar kansu a brain nata ba. Tsaf ya fahimci halin da take ciki amma sai ya basar. ATM card ya ajiye mata da wasu takardu guda biyu batare da ya mata wani bayani ba. Ya ɗan kalla agogon hanunsa yana furzar da iska a hankali....

      “Zaki iya fara fita school idan kinji ƙarfi, idan kikaiwa gargaɗina ɗaukar wasa zaki iya rasa karatun baki ɗaya. Abota da wani namiji ko ɗan uban waye bana buƙata. Tarkacen ƙawaye bana ra'ayi. Kiyi abinda ya kaiki”.

       “Insha ALLAH bazaka sameni da ƙinjin magana ba. Sai dai ina roƙon alfarmar securitys ɗin nan basai na dinga zuwa da su school ba, hakan zai iya nisanta idanu a kaina na zauna lafiya ga kowa dan ALLAH. Sannan ina son.....”

     Sai kuma tai shiru ta kasa ƙarasawa.

      “Bana son kwana-kwana, idan zakiyi magana kiyita kai tsaye”.

    Nanma kanta kawai ta jinjina masa. sai kuma ta ɗan ɗago a marairaice yanda zaifi tausayinta ta ce, “Dama ina son ne naje gyaran kai da kitso na kuma je naga Mummy i miss her”.

       Miƙewa yay yana gyara necktie ɗinsa, a ɗan daƙile yake faɗin, “Well kina da damar hakan, sai dai bako yaushe nake buƙatar ganin kitso a kan matata ba. Idan nai buƙatar hakan zance ayi”.

     Sototo tayi tana kallonsa baki buɗe har yaje ƙofa. (Oh dama yana mata kallon mata ne wai dama? Ba ƙawance yace kawai suy.....) ganin zai fice tai saurin katse tunaninta. “Dan ALLAH zuwa wajen Mummy fa to?”.

          Yanda tai maganar cike da zalama ya sashi ɗan waigowa ya dubeta, sai kuma ya ɗauke kansa “Zamuyi waya”. Ya faɗa yana ficewa gaba ɗaya..............✍


No comments

Powered by Blogger.