Bakar Inuwa 4
*_Episode 4_*
..........Ruwa kawai tasha tunda aka kai azimin na yau na kusan ashirin da ɗaya, sai dai hakan baisa ta damu ba, duk da yunwa dake cin hanjinta dan koda asuba ma batai sahur ɗin kirki ba kasancewar tuwo sukai na sahur, itako a rayuwarta sam bata shiri da tuwo
musamman miyan kuɓewa ɗanye. Sau da yawama idan taci gudawa yake sakata shi da shinkafa. Kai duk ma wani abu irinsu basu ciga damun Raudha ba. Tafi so da buƙatar abinci mai ruwa-ruwa irinsu fura, kunu, koko da sauransu. Suna fita Yasmin ta fiddo goran ruwa madaidaiciya dake ɗauke da kunu ta miƙama Raudha. “Aunty R gashi kisha”.Cak Raudha ta dakata daga tafiyar da takeyi ta dubi Yasmin ɗin, ganin abu a leda yasata daka mata tsawa dan sam bata fatan abinda zai lalata rayuwar Yasmin ɗin itama. Cikin ruɗewa Yasmin ta fara rantsuwa. “Aunty R wlhy bani akayi, baba ce ta bani (Baba Nafi) sanda naje mata aika gidan kawu Rabi'u (Ƙanin Baba Nafi) na amso mata kunun batare da Mommy ta sani ba. Niko kinga banyi azumi ba shiyyasa na ɓoye miki shi dan karsu aunty Fatisa su gani su shanye ko Mommy”.
Ajiyar zuciya Raudha ta sauke da kamo yarinyar ta rungume a jikinta hawaye na ciko mata idanu. “I'm so sorry my little girl, bana son ki fara koyon hali irin nasu Aunty Fatisa ne shiyyasa. Dan ALLAH ki kiyaye karki bari wani ya yaudareki da abinda bamu da shi ya lalatamin rayuwarki kinji”.
“Inaha ALLAH Aunty R bazan yarda ba ai”.
Yasmin ta faɗa duk da ba komai take fahimta ba da ga gargaɗin ƴar uwar tata kai tsaye, saboda ƙarancin shekarunta. Dan Raudha ta bata kusan shekara shida a duniya, bayan haihuwarta Asabe ta jima kafin ta samu ciki, harma ta ɗauka haihuwar ta kare sai kuma ga cikin Yasmin ɗin..
Kama hanunta tai suka ƙarasa massallacin batare data amshi kunun ba, can gefe ta samu ta saka musu abin salla inda bazasu takura ba, dan sam bata ƙaunar zafi ita, sanyi ma idan yay yawa yana taɓa rayuwarta.
An gabatar da sallar isha'i da asham, bayan addu'oi da malam yayi tamkar yanda ya saba kowa yay ƙoƙarin kama gabansa. Raudha bata tashi ba, sai roban kunun da Yasmin ta ajiye a gabansu ta ɗauka ta buɗe murfin, duk da ya huce haka tasha kusan rabi ta miƙama Yasmin dake gyangyaɗin barci sauran dan tasha itama. Amma sai Yasmin ɗin tace mata ta ƙoshi. Sanin kunu bai damu Yasmin ɗin ba sosai yasa Raudha ƙarasa shanyewa sannan suka miƙe.
Sai da ta gama tattare musu kayansu sannan ta duƙa Yasmin tahau bayanta danta lura barci takeji. Yarinyar ta saki sassanyar ajiyar zuciya tamkar yanda Raudhan tayi itama. Koda suka iso gidan a tsakar gida suka iske kusan kowa a ƙofar ɗakinsa. Yaran nata hayaniyar surutu iyayen kowa na sabgar gabansa. Sannu kawai tai musu bayan sallama ta shige ta kai Yasmin ɗin ɗakin barcinsu da gaba ɗaya ƴammatan gidan kan kwana musamman idan ranar Babansu a ɗakin mamanka yake. Idan ɗakin wata yake daban zaka iya kwana a ɗakin mamanka ɗin. Fitowa tai tai ɗan uzirorinta batare data tankama kowa ba ta sake shigewa tai kwanciyarta dan su Fatisa a ƙofar gida ta barsu suna hira.
*_WASHE GARI_* Raudha ta tashi da ciwon mara mai tsanani tamkar yanda takeyi duk wata. dama tun kusan jiya takejin alamarsa kaɗan-kaɗan, batai wani yunƙuri ba dan maganin da take sha ya ƙare. dama Ya-sayyadi ne ke saya mata shi kasancewar yasan lalurar tata. Idan har zatai period sai kowa ya sani. ba ƙaramar azaba take sha ba na ciwon mara dana ƙafa. Daga ƙarshe taita kwara amai. Idan ka ganta a irin wannan halin ma saika ɗauka yaron ciki ne da ita. Dan a farkon fara hakan tana jss1 secondary kowa a gidansu dama makaranta sun ɗauka ciki ne da ita, duk da lokacin batafi sa'ar Yasmin ƴar shekara goma sha ɗaya ba. Sai da aka dubata likita yace period zata fara sannan hankalin malaman ya kwanta har sukazo da ita gida akaima iyayenta bayani.
Duk murƙususun azabar da takeyi a ɗakin babu wanda ya sani, dan gidan shiru alamar yaran duk sun fice sabgogin gabansu, manyan kuma kowa barcinsa yakeyi. Sosai take cin azaba, dan tun tana kuka ma har kukan ya gagara, tsanani yay tsanani har takai Raudha da suma.
Kamar yanda ya saba shigowa gidan fagan-fagan babu ko sallama yauma haka ya shigo, dan tun fitarsa sallar asuba bai sake shigowa ba yana rumfar ƴan gulma kamar yanda ake kiran majalisarsu. Jin gidan shiru ya sashi fara ƙwala kiran Raudha, dan a rin wannan lokacin ita kaɗai zaka iya samu a gidan tana bautar gyarawa, data gama take wucewarta wajen tafsir sai sha biyu ta dawo.
Shiru babu wanda ya amsa masa, yabi gidan da kallo a harzuƙe, ko'ina kaca-kaca da kwanika da tulin tsummokaran kayansu kusufi-kusufi. Tsaki yaja yana nufar ƙofar ɗakin Asabe. “Asabe! Asabe!!” ya shiga ƙwala mata kira, dan har yanzu haushinta na jiya bai bar ransaba, musamman daya kasance yanzun nan jabiru mai shago ya sake masa maganar kuɗinsa, shine ma dalilin shigowa gidan da yay.
Cikin barci Asabe taji muryarsa bisa kai, ta miƙe a zabure tana yaye labulen daya saya falon nata matsakaici, komai babu a cikinsa sai ledar ƙasa dan duk ta siyar sun cinye kuɗin a ciki ita da ƴaƴan.
“Wai wane kalar jidaline kuma haka da wannan farar safiyar? bazaka barni nai barcin dana gagarayi ba da asubahi!”.
Tsaki yaja yana turo kai cikin falon, yaci tuntuɓe da ƙafar Fatisa dake barci a gefenta itama, da sauri Asabe ta tarosa. “Gashi nan wajen gargajigarka ta masifa zakaima kanka lahani a banza, wai nikam mike faruwa ne?”.
Numfashi yaja da ƙarfi, batare daya amsa mata ba ya kai zaune a tsakar falon yana godema ALLAH a zuciyarsa da bai faɗi ba. “Asabe ina Raudha!?”.
“Raudha kuma? Wani laifin ta ƙara maka ne?”.
Kansa ya jinjina mata cikin tausasa murya tamkar bashine ya shigo da bala'i ba yace, “Laifi kam tana da shi a gareni kema kin sani, to amma abinda ya fara kaɗoni gida yasani yafe mata zan ma biya jafarun kuɗinsa insha ALLAH. Ina Alhaji Maude Dallatu uban gidan falalu mai shagon kayan ƙwalam ɗin can na bakin titi?”.
“Eh na gane!”.
Asabe ta faɗa da sauri cikin ƙaguwar son jin inda zancen ya nufa. Fahimtar hakan ce ta sakashi cigaba da faɗin, “Wai shine fa ya aiko Falalu ɗin akan ya sameni ya faɗamin zaizo akan Raudha wajena.....”
“Ni bangane ina zancenka ya dosa ba wlhy ɗan-azumi, fito fili ka faɗamin kasan bana son wani kwana-kwana.”
Baki ya washe sosai cikin raɗa yace, “Inagafa cazai na bashi aurenta, idan ko haka ta kasance Asabe ai mun haye wlhy. Shiyyasa a koda yaushe bana gajiya da alfahari da ƴaƴanki ƙyawawa”.
Itama tuni fara'a ta baibaye fuskarta, nan fa suka shiga ƙus-ƙus akan batun wai kada magauta su jiyosu. Tun ma kan suji ta bakin Alhajin harsun gama yanke hukuncin tsaida ranar biki. Bisaga wannan shawara da suka tsaida cike da zumuɗi Asabe ta miƙe kiran Raudha.
Da sauri Larai dake laɓe tanajin komai ta afka ɗakinta har tana neman faɗuwa. Asabe kuwa da bata lura da itaba ta nufi ɗakin su Raudha.
Kururuwar ihun Asabe ne ya saka kowa fitowa a gidan har masu barci da Larai daketa faman kai kawo a ɗakinta ranta a dugunzume da zancen da taji.
Suna ƙoƙarin jin dalilin ihun nata suka hango Raudha a sanƙame tana girgizawa. A tsorace duk suka afka ɗakin, Baba Nafi tai dabarar ɗakko ruwa ta shafama Raudha ɗin. Sai gashi ta kawo wani nannauyan numfashi. Sai kuma ta ƙudundune jikinta tana ƙanƙame Asabe da sakin wani kuka maiban tausayi dako sautinsa baya fita saboda azabar da taci.
“Mommy zan mutu”.
Kawai take iya furtawa da ƙyar tana sake ƙanƙame Asabe da itama tarasa ina zata saka kanta taji sanyi, dan sun fahimci ciwonta na marane ya motsa. Fatisa ce ta bada shawaran a kaita asibiti ko za'a iske Doctor Rufa'i abokin ya-sayyadi da wani lokacin shike kawoma Raudha magungunan da ga ya sayyadi Abubakar. Amma sai ɗan-azumi ya daka mata tsawa da faɗin, “A gidan ubanwa wani keda kuɗin asibiti anan gidan?, banda jangwaloma mutane masifa a samu ɗan libiya a jiƙa a bata tasha zai faɗa mata yanzun nan, sanin kanku ne maganin da yaron can ke saya mata Sule yasha faɗa mana tsadarsa ai. Sannan ba ko'ina ake iya samunsa ba ma a garin nan. Shima yana sayo mata ne a Ɗillo”.
Fatima tai saurin cewa “Abba bafa ciwon ciki bane ba, kuma kasan kaima sai an bata maganin nan ko allura kawai take samun nutsuwa. Sai kuma last time da Doctor Rufa'in yay mata kalar sabuwar alluran nan shima da wuri ya daina mata”.
Zai fara hayayyaƙo mata itama tai saurin katsesa da faɗin, “Abba ni akaita ina da kuɗi”.
Jin haka yasa Mommy (Asabe) haɗiye maganar da take tattarowa domin fara zuba masa tujara. Amma duk da haka bawai ta barsa bane, zata dai jira taga lafiyar yarinyarta ta samu sannan ta cashe masa...........✍️
_😂Asabe ya Asabe, ɗan-azumi ya ɗan azumi. Wannan tujara da ƙauna sai ALLAH😆😹_.
Leave a Comment