Bakar Inuwa 38


 *_Episode 38_*..........Hijjab ɗin ya ajiye gefe idanunsa akan hanunta data matse pants biyu da ledar part da Bilkisu ta ɗakko mata. A hankali ya kai zaune gefenta, sannan ya kamo hanun nata ya zare abinda take ɓoyon. Kai tsaye ya gane ko minene, ya ajiyesu gefe da ɗan sake tsura mata ido. Yanda ta ɓata fuskar alamar batajin daɗi har a cikin barci ya sashi sakin

ƙasaitaccen murmushi yana kauda idanunsa. Sai kuma ya miƙe ya gyara mata kwanciyarta batare da yace uffanba ya nufi toilet bayan ya lulluɓeta da lallausan duvet nashi dake ta tashin ƙamshin turarurrukan sa.

        Kusan ƙarfe goma na dare Ramadhan ya kai kwance bisa katafaren gadon nasa bayan kammala komai na al'adar rayuwarsa kafin kwanciya. Addu'a yay, harya shafe iya jikinsa zai kwanta sai kuma ya ɗan dubi Raudha dake gefensa. Miya tuna oho masa ya karanta mata addu'ar itama ya tofa mata sannan ya kwanta zuciyarsa na masa wani irin kaikawo na son tuna baya. Amnah tamkar mage take a wajen son jiki, a duk sanda yake gida zaka sameta manne da shi. Tun hakan na takura rayuwarsa har ya saba. Shiyyasa bayan rasuwarta ya jigatu matuƙa da kewa. Taunar lip ɗinsa ya shigayi da ƙarfi idanunsa na tara ƙwalla, a hankali ya shiga ambaton sunayen ALLAH dan yasan zurfafa tunanin wani motsawar ciwone daga zuciya zuwa ƙwaƙwalwa. Cikin amincin ALLAH batare da ya farga ba sai barci yay awan gaba da shi.

     Kasancewar allurar da akaima Raudha yasa barcinta yin nauyi harya tashi yay salla bata farka ba. Bai tadata ba tunda yasan bata salla. Barcinta ta sha sosai har kusan bakwai da wasu mintuna. Ta buɗe ido a hankali tana ambaton addu'ar tashi a barci. Taja ƴan mintuna kafin ta tashi zaune, ta riga bin ɗakin da kallo a ɗan firgice dan tama manta a ina take. Duk abinda take Ramadhan na'a ɗakin zaune bakin gado ta bayanta yana dalle-danne a lap-top da alama aiki yake mai muhimmanci.

      Sam bata lura ba, dan ta juya masa baya. Ji take tamkar jikinta ya ɓaci, dan haka ta fara laluben kayanta na jiya da bilkisu ta ɗakko mata. Ganinsa zaunen a bazata ya sakata waro idanu waje tasa hannu tana kare jikinta kunya tamkar ta nutse. Zuciyarta har wani gudu take kamar zata fito. (Na shiga tara ni Amina ina zanga Hijjab ɗina?) ta faɗa a zuciyarta tana ɗaga duvet ɗin da sauri-sauri.

        Duk abinda take bai ko nuna yasan tanai ba, amma kuma yana lure da ita ta gefen ido. Abinda yay tunanin tana nema dake a gefensa ya turo mata da hannu batare da ya ɗago kansa da ga lap-top ɗin ba. Wani irin takaici da kunya suka sake lulluɓe Raudha taji tamkar taita tsala ihu kawai. Da sauri tasa hannu ta kwashe, tsabar rikicewa batama san ta nufi hanyar fita ba.

      Yatsunsa ya murza suka bada sautin ɗas-ɗas da ya tilastata tsayawa ta juyo, har yanzu kansa naga lap-top, amma sai yay mata nuni da hanyar toilet ɗin ɗakin batare da yayi magana ba.

       (Wayyo ni Aminah na shiga uku na) ta faɗa a zuciyarta kamar zata fashe da kuka. Dole ta nufi hanyar toilet dan bata da zaɓin daya wuce hakan. Bazata iya bijirema umarninsa ba, sannan bazatama iya fita da kayan jikinta ba. Ɗazunma ruɗewa ta sata nufar can da rashin zaɓi.

      Yau kam ba kamar jiya ba, tsaf ta zauna ta kalle toilet daya lashi kuɗaɗe, da ga ƙarshe ta fara wanka zuciyarta cike da mita dole shuwagabanni su shagala da son mulki da mantawa da talaka. Sai da ta kammala wankan tana ninke kayan barcinta taci karo da jinin daya ɓata mata wando, cikin rumtse ido ta dafe kai dan ta tabbatar ta ɓata masa gado kenan.. Ita kam taga takanta yau da a gidan nan. Duk da kunyar da take na fito ɗaure da towel haka ta daure dan gara fitowa da towel tunda ta yafo wani akan yaga jinin data ɓata masa gado.

      Saɓanin ɗazun yanzu tsaye ta samesa saitin inda ta tashi yana ɗage-ɗagen duvet. Kai tsaye zuciyarya ta ayyana mata yana dubawane kota ɓata masa gado. Sosai Raudha tama manta waye shi a wajenta. Dan batasan tai tsalle ta dire ba a gabansa ta damƙe duvet ɗin hanunsa ta cikuykuyesa a hannu. Mamaki ya sakashi dubanta daga sama zuwa ƙasa. Sai dai kuma baice komaiba ya kai zaune da miƙa hannu zai sake amsar duvet ɗin dan bai buƙatar yawan magana yau ransa a ɓace yake. Tsam ta matsesa a jikinta kamar zatai kuka....

        “Ni wlhy bansan hakan ta faru ba”...

     Mamakinta ya sashi sake ware idanunsa a kanta. 

    “Are you okay?”.

Kanta ta jinjina masa kawai tana sake matse bargon a jikinta. Dan koba komai yana sake bama jikinta kariya da towel ne kawai. sannan bata son yaga yanda ta ɓata masa gadon. 

     Shi saima abun ya girmesa da bashi dariya amma ya gimtse. Cikin takaicin ɓata masa lokaci da take ya kama bargon zai fisge saita biyoshi itama, kawai sai gata a cinyarsa ɗare-ɗare zaune.

      (Ya ALLAH yarinyarnan kuwa tanada lafiya?).

     Ya ayyana a ransa da mamaki jininsa na yamutsawa da sauri-sauri. Tuna abu zaiyi mai muhimmanci da wayar da yake nema ya sashi ƙoƙarin fisgar bargon batare da ya cemata komai ba a zahiri, amma kuma ya harɗe mata ƙafa da tasa yanda ta kasa tashi a jikin nasa duk da tanata ƙoƙarin hakan. Wajen fisgar bargo towel ya kwance. Ai bama tasan ta fasa ƙara ba da ƙadandanesa gaba ɗaya. Dan duk hannayenta ta harɗo wuyansa da su ta kife ƙirjinta a nashi jikinta na rawa. Babu shiri ya saki bargon ya toshe kunnensa.

         Jin yanda take sake matsesa tana neman harmutsa masa tunani ya sashi cire hanun a kunnensa. Sai kuma a bazata ya saki murmushi jin ɗumin hawayenta a jikinsa alamar kuka takeyi. Yay ɗan gyaran murya idonsa akan gashinta dake ɗaure cikin ribbon duk ya sukurkuce wani ma ya jiƙe a gaban goshinta. So take ta ɗagashi amma bazata iyaba. 

       (Oh oh yau naga takaina). Ya ayyana a ransa, a fili kam cikin raɗa yace, “Ustazah jikina kar yay ciwo kin cika nauyi”. Yana maganar ne yana kama jelar gashin nata dan ya tabbatar dai nata ɗinne ko sakawar take kamar yanda yake zargi. Tabbatar da natane ya sakashi tura yatsun hanunsa duka cikin sumar ya zare ribbon ɗin....


        Saurin sakinsa Raudha tai baki ɗaya jin wani kuma baƙon lamarin daga garesa, ta fisgi bargon ta cukuykuye jikinta a ciki. Da ƙyar ya iya danne dariyarsa, yanda ta cukuykuye ɗin ya bashi damar ganin wayarsa da yake nema, sai dai tana kusan rabin kanta. Gyara murya yayi, ta buɗe idanunta kaɗan sai suka haɗa ido. Ganin zata maida ta rufe ya sakashi mata nuni da wayar da ɗan yatsa. Wajen ta kalla dai-dai yana miƙo hanunsa zai ɗauka. Ta ɗan ɗaga jikinta tana tura baki. Duk yanda yaso dannewa ya kasa sai da murmushi ya suɓuce masa har haƙoransa na bayyana. 

         (Masha ALLAH) ta ayyana a ranta ganin yanda murmushin yay masa bala'in ƙyau. Shi dai tuni ya ɗauka wayarsa ya bar wajen. So take ta tashi taje ɗakinta amma ta kasa, haka ta cigaba da kwanciya a wajen nannaɗe a bargo harya kammala shirinsa cikin ɗayar shadda milk color datai masa ƙyau sosai. Ya murza brown hula mai kwalliyar milk kaɗan-kaɗan.

          Ƙaruwar ƙamshin turarensa _Sauvage dior_ cikin hancinta ya sata ɗan buɗe ido. Tsaye yake a side drawer ɗin gefen da take yana ƙoƙarin saka link ɗin hanu. Duk yanda taso janyewa kafin ya kamata ta kasa, haka ta cigaba da binsa da kallo harya juyo hanunsa ɗauke da takardu suka haɗa ido. Saurin rufewa tai shi kuma ya ɗan taɓe baki yabar wajen dan tun ɗazun dama yake ji a jikinsa ana kallonsa.

         “Ni na wuce office kinsa na makara yau. Saura ki batamin gado da wannan abun naki”. Ya faɗa yana ƙoƙarin barin ɗakin. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana ɗan harar bayansa, yana ƙoƙarin murɗa handle ɗin ƙofar tace, “ALLAH ya tsare ya bada nasara”.

       Bataji ya amsa ba, sai dai tasan zai amsa ɗin saboda da wuya tai masa addu'a yaƙi amsawa balle yanzu da suke ɗasawa kuma. Yauma ta fahimci kamar akwai abinda ke damunsa ko kuma ƴan girman kanne a kusa. Gaisuwa ce dai sai ya gadama. Bayan ficewar tasa taja kusan mintuna 2 sannan ta miƙe, ita kanta sai yanzu abinda ya farun ke bata dariya. Taita sakin murmushi tana ƙoƙarin gyara masa gadon bayan ta nema towel ɗinta daya koma gefe ta saka.

     Tsaf ta gyara ko ina har toilet. Ta tattara kayanta ta fice bayan ta saka hijjab. Tayi mamakin cin karo da su Aynah a falon, sai dai ta ɗauke kanta kawai da niyyar wucesu batare data nuna tasan da zamansu ba.

        “ALLAH dai ya rabamu da karuwanci ni Aina'u. Tsabar jaraba baza'a iya riƙe kai ba saboda an saba da maza tun a titi tamkar uwa da danginta. Ni ALLAH ma yasa cikin na Yaya Ramadhan ɗinne ba wani yayisa ba tun kan a shigo.”

        Har cikin rai maganganun Aina'u sun soki Raudha, amma sai ta wuce abinta batare data tanka  mata ba. Kai ko kallon inda suke batai ba ma balle ta nuna tasan da zamansu tai shigewarta ɗakinta.

   

      Sai da ta kammala shiri  tana ɗan kimtsa ɗakin nata maganganun Aynah na ƙarshe ke mata kaikawo a rai. (Ciki? Wa take nufi nada cikin?) ta tambaya a zuciyarta batare da tunanin lalubo amsa ba. Haka dai ta ƙarasa aikin da wannan tunanin tai zaman cike takardun jiya dan ta jona wayarta a caji tunda ta shigo.

     

★★★★


      A office kam murmushi ya kasa barin face ɗin shugaban ƙasa Ramadhan. Dan babu abinda ke masa kai kawo a rai sai hidimarsa shi da Raudha na safiyar yau. Shigowarsa office da cos ya fara ganawa akan tsare-tsaren abinda zaiyi a yau. Amma shi kansa cos sai satar kallonsa yake ganin yau babu ɗacin ran nan sam tattare da shi. Hakama a zaman meeting da yay da sabbin ministers fuskarsa ƙawace da fara'a tamkar bashi ba. Bayan sallar azhar ya samu hutun awa biyu shi kaɗai a office. Jiyay tamkar ya kirata a waya. Sai dai zuciyarsa na gargaɗinsa akan idan ya kirata mizaice mata to? Karma ta ya yake rikitata duk da dai yanzu Alhamdulillahi sun saki jiki da juna sosai. Yau ma sama-sama yake jin kansa shiyyasa bai biye mata ba.


(Humm🤳🏻).


*_TAURA HOUSE_*

        

         Tun wayar da tai da su Munirah ranta yake a ƙololuwar ɓace. Koda ta kira Adda Asmah ta sanar mata itama ɓacin ran ta nuna sosai, hakama Fulani. Kai tsaye shawarar Adda Asmah sukabi akan zubda cikin jikin Raudha kota halin ƙaƙa ita da fulani. 

       Tana gama waya da su ta kira Safina.

        “Maah lafiya kuwa kira a wannan lokacin!?”.

      Tsaki gimbiya Su'adah tai idanunta na sake rufewa da ɓacin rai dan ba ƙaramin fanfata Asmah ta sakeyi ba, ita kuma ta riga ta yarda da ita tsakani da ALLAH. “Maganin zubda ciki nake so mai tsananin ƙarfi da zai rikito a cikin mintuna goma”.

      “Na shiga uku Maah waye da ciki?!”. Ta faɗa a cikin tashin hankali da tunanin cikin ƴan uwantane wata ta yayo musu abin kunya.

      “K dalla ba abinda kike tunani bane. ALLAH ya tsari zuri'a ta da fasiƙanci. Wannan ƴar iskar yarinyar ƴar karuwai ce, wai harni Ramadhan zai yaudara Safina ya lallaɓa yay ma shegiya ciki”.

      “Innalillahi... Anya Maah kun tabbatarma nasa ne? Kinsan fa yanda Brother yake da taurin kai akan abinda bashi yaso ba. Kuma kowa yasan Bappi ne ya manna masa auren nan bawai yana so bane, ƙilama asiri sukai masa wlhy inhar ya kasance cikin nasa ne ma.”

     Sosai maganganun Safina sukai tasiri a zuciyar gimbiya Su'adah. Takai zaune tanajan numfashi mai nauyi. “Safina maganarki kuma nakan hanyar wlhy. Da harna ƙullacesa a raina. Tabbas inhar cikin nan ya kasance nasa yarona baya cikin hayyacinsa sun masa asiri. Nasan wacece kakar yarinyarnan komai zata iyayi dan tayi a baya akan mahaifina”.

      “Humm kin gani ko Maah. Nidai nasan Brother bazai taɓa son yarinyarnan ba. Idan ma ƙyau ne ai yanada shi, sannan akwai tarin mata dake binsa wanda suka fita ƙyawun amma bai kula ba sai ita banza ƙaramar alhaki sa'ar Basma fa. Autarmu, inagama Basma ta girmeta wlhy”.

              “Aiko zataci ubanta, zan tabbatar mata damu asiri baya cinmu, dan na kula saka mata idon da nayi ban ɗauka wani mataki a kanta bane ya kawo hakan. Yanzu ki aikomin da sunan maganin”.

      “Indai magani ne kwantar da hankalinki, zansa doctor Wali ya kawo miki ma har gida. Sai ma nakejin dama kar a zubar da cikin mu nuna kawai bana Brother bane mu kunyata ƴar iska nasan zaima iya sakinta....”

      Ɗan jimmm Gimbiya Su'adah tai tana nazari, sai kuma ta girgiza kai kamar Safina na ganinta. “Ina bazai yuwuba baki da hankali. Idan kuma yace cikinsa ne fa? Ramadhan da shegen kafiya kema kin sani. Sannan tsoffin nan zasu iya cewa bazataje ko'ina ba ta zauna a wajensu har sai ta haihu anyi DNA test. Ke dai kawai mu ɓarar da ɗan iska mukuma san matakin ɗauka da zai hanata damar ɗaukar wani”.

     “Okay Maah duk yanda kikace haka za'ayi. Bara na kira Dr Wali ɗin. Amma ya za'a bata maganin?”.

       “Wannan mai sauƙi ne ba su Lubnah nacan ba, ai na sake maidasu zama can bayan na tsara tsoffin nan akan zasuje suɗan dinga ɗebe mata kewa injisa. Bayan na masa gargaɗi shi kuma”.

      Safina tai ƴar dariya daga can tana faɗin, “Kai wannan shegiya ta zame mana *ƘARFEN ƘAFA*”.

       “Nikuma zan zame mata *BAƘAR INUWA* kuwa da sai ta gwammace zaman ranar data baro dani dan ubanta”.

        “Shiyyasa nake sonki Maamana”.

Kashe wayar Gimbiya Su'adah tai tana murmushi. 


         Mintuna arba'in ba'a cika ba Dr Wali ya iso da maganin, tsabar muhimmancin maganin har falon baƙi gimbiya Su'adah tasa aka saukesa taje da kanta suka gaisa ta amso. Tafiyarsa babu jimawa Munirah da zata amshi maganin ta iso. Duk yanda Dr Wali yay mata bayani haka taima Munirah. Tai mata gargaɗi akan su lura da abinda zasuyi.

      Munirah ta tabbatar mata da sai tayi alfahari da su insha ALLAH. Da ga haka ta shiga mota driver da tasa ya kawota ya juya da ita government house.


*_GOVERNMENT HOUSE_*


      ALLAH sarki Raudha batasan mike faruwa ba. Bayan ta kammala cike takardu ta nemo littafin data ajiye numbers na Mommynsu da ƴan uwanta ta loda a sabuwar wayarta da har credit cart sai da Ramadhan yasa aka loda mata a layin nata. Cikin farin ciki tai kiran number Mommynsu. tana ɗagawa taji muryarta sai ta sa kuka dan daɗi. Ita Asabe ma sai abin ya bata dariya. Amma tunanin ko Raudha na cikin wani ƙunci ne data guda tun farko yasa dariyartata kasa fitowa ta hau jera mata tambayoyi. Da ƙyar Raudha ta haɗiye kukanta ta tabbatar mata da babu komai jin daɗin jin muryartane ya sata kukan kawai.

      Ajiyar zuciya Asabe ta saki, sai kuma ta hau saka mata albarka. Sunyi hira sosai ta sanar mata zancen makarantarta ta tayata murna. Daga haka ta gaisa da sauran ƴan uwanta har hajiya mama da hajiyar birni da yanzu ta daina zuwa shago sai su Fatisa. Sai dai tana zuwa taga yanda komai ke tafiya ta koma gida.


     Bayan kammala wayar ne taji yunwa na ƙara damunta dan bata karya ba. Mikewa tai ta fita da fatan ALLAH yasa akwai abinci table. Addu'arta kam ta karɓu, dan haka babu ɓata lokaci tai zaman cin abincin da tunanin idan ta kammala ta ɗan sauka downstairs dan duk yau basu haɗu da su Mama ladi ba.

      Wani irin cafkewa su Munirah dake laɓe sukai lokacin da Raudha take haɗa shayi. Sun tsiyaye ruwan flask ɗin duka suka bar dai-dai kofi guda suka saka ƙwayoyin maganin fiye ma da yanda akace su bata. Maimakon 2 sai suka saka har 6 dan basu da hankali. Wai yanda cikin zai rikito da wurwuri kowa ya huta.

       Tsaf Raudha ta shanye shayin ta ɗan sha farfesu saboda bakinta babu daɗi. Dama ita idan tana period tata kwaɗayi kenan tamkar mayya. Ko abinci bata cika so ba tafi son nama a irin wannan lokacin. Riƙewar da mararta tayi ya sata ɗan dakatawa da ga shan farfesun kamar mai hasashe. Kirjinta yay wani irin yankewa tamkar ana kiɗa a kan zuciyarta. A take kanta ya fara juyawa cikin ficewar hayyaci ta kife fuskarta akan kwanon farfesun tana ambaton sunan ALLAH. Ba tare data fahimci mike faruwa ba taji abu na ɓulɓulowa ta kasanta da gudun tsiya yana sauka jikin ƙafafunta...........✍


No comments

Powered by Blogger.