Bakar Inuwa 21
*_Episode 21_*
.............★A ɓangaren gimbiya su'adah da fulani da Asmah suna akan bakansu na ganin sun hana auren Ramadhan da Raudha suma. Sai dai kuma hayaniyar campaign ta sakasu ajiye wannan batun gefe. Kowa fatansa a yanzu Ramadhan ya haye mulki kawai, daga nan koma miye zai biyo baya sai ayi. Dan sun ɗau alwashin yaronsu bazai auri ɗiyar
talakawa ba. Zuwa yanzu sunyi bincike mai tsanani akan Raudha har Hutawa, shiyyasa suke tunanin karya lagon su Bappi da wannan sirrin a haukarsu.★★★
Raudha kam tun kwanaki biyu da kai kuɗin aurenta aunty Hannah da First lady suka yanke shawarar ɗauketa anan gidan, tare da kafama hajiyar birni hujja da kar Asabe ta zugeta, aiko tai azamar amincewa dan ita kanta lamarin Asaben tsoro yake bata duk da tasanta da kafiyar tsiya tunba yanzu ba. Tunda itama haka tayi ga masu kuɗi na sonta a wancan lokacin amma ta dage sai M. Dauda, itako a yanzu bazata yarda Asaben tai mata baƙin cikin samun abubuwa da damaba a dalilin auren Raudhan. Sun maidata wani gida keɓantacce wai ana koya mata dabarun mulki irin na first lady. Bawai suna mata hakan danta ƙaru ba, sunayine kawai danta saki jiki dasu har idan buƙatar sakata musu aiki ya taso anan gaba tayi babu musu.
Kasancewar an haɗota dasu Yasmin kuma harda aunty Hannah duk da bata cika zama ba saboda yawon campaign sai hankalinta bai tashiba sosai, ga wata dattijuwa da sukace tana aikine a fadar shugaban ƙasar shekaru goma kenan cir na mulkinsa mama tambaya, sai ƙarin mutane biyu ƴan gayu sukuma masu koya mata abubun daya shafi gyaran jiki da dai sauransu. Sai shahararriyar mai kayan gyaran jikin nan dake gyare Raudha ɗin lungu da saƙo da ingatattun kayanta kayan ƙamshi dana sanyi *AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE 08067558902* _(guys ku garzaya dan zaku samu duk abinda kuke buƙata ga amaryar kb, daga kayan ƙamshin jiki, gida, kayan mata, maganin sanyi ingantacce😋😘😍🤗)_
Kuma akwai wata islamiyya dake anan kusa da gidan saboda matsawarta yasa suka sakata ita dasu Yasmin. Sai dai bata fita sai da dogon hijjabin Uniform ɗin makarantar harda niƙaf. Ba'a dabarun mulki kawai aka tsayaba har gyaran jiki dasu saka kaya, girki duk koya mata akeyi, dan ma Alhmdllhi dama ta iya abubuwa da yawa na aikin cikin gida sai dai bana ƴan gayu irin haka ba, ba kuma sosai take girki ba a gida saboda icce suke amfani da shi ita kuma Asthma.
A gefe kuma damuwar auren nata na nan daram a ranta. Musamman yawan ganin Ramadhan da takeyi a tv saboda campaign yanzun. Hakama idan ta fita islamiyya duk da anguwace ta manya tana ganin posters nashi. Ita kanta tasan ƙyaƙyƙyawane, yanayinsa da kwarjininsa dole ya shiga ran mai kallonsa da hanzari, sai dai ko kaɗan batajin sonsa a ranta, kamar yanda tasan itama bazai taɓa ya sota ba. ita da kanta kuma tana tilastama kanta saka ƙinsa a ranta saboda wasu dalilai
★Al'amarin campaign ya miƙa, kowa yana hangen nasara tattare da Ramadhan duk da masu iya magana kance siyasa kamar mace mai ciki ce, ba'a san mi zata haifa ba. Abubuwa da yawa masu daɗi da marasa daɗi sun faru a wajen campaign ɗin nan, wasu sun wuce an manta, wasu ko bazasu gogu a zuciyaba sai bayan mutuwa.
Da gaske Ramadhan ya manta da batun wata Raudha saboda hargitsin campaign, sai idan wani ya ambaci sunanta ko zancen auren nasa ya fita a bakin wani yake tuna wata sa rana dake kansa ta aure. Sai dai ga Bappi da Pa da Anne ba haka bane, dan sunata shirye-shiryensu na biki duk da hatsaniyar campaign ɗin da kowa ke a ciki. Ga gimbiya Su'adah kuwa tunda ta gama binciki tushen Raudha hankalinta ya sake tashi ta birkicema Pa. Ko kulata baiyiba balle ta samu amsa. Hakan ya kuma ɓata ranta ita da su Fulani, batare da sanin kowaba suka shiga ƙulle-ƙullen yanda zasu ɓadda Raudha, sai dai sunbi duk wata hanya data dace amma basu sameta ba saboda ɓoyeta da akayi. Wannan dalilinne yasa gimbiya Su'adah tun karar Pa ana gab da rufe campaign.
“Wai nikan nakega ya kamata ko sau ɗayane ai matar da Ramadhan zai aura a ganta wajen campaign, kar mutane su fassara rashin ganin nata da wani abu kuma ai”.
Shiru kamar Pa bazai amsaba duk da tasan ya jita sarai, sai da ya gama kallon rahoton da akeyi a tv game da taron campaign daya faru na Alhaji Andi ƙaura a jihar Sato sannan, cikin fushi dajin ɗacin kalaman da Alhaji Andi ƙaura yay amfani dasu a wajen da yarfen da yayma Ramadhan yasa muryarsa kausasa.
“K dake matsayin uwarsa tunda aka fara campaign ɗin kinje ne?”.
Fuska ta kumbura, cikin zafinta tace, “Miye alaƙar ganina da ganinta a wajen? Kuma ni ai inada masu zuwamin”.
“To itama ai danginta sunje sun wakilceta, dan mahaifinta campaign ɗin da yayi a yankinsu bana tunanin wani a gidan nan yayi kwatankwacinsa ma.”
“Tunda ko yana neman gindin zama da shegen kwaɗayi ai dole yayi. Imagine yarona kamar Ramadhan dake da kowane irin gata na duniya ya ƙare da auren ƴar karuwa da ɗan duniya. Jikar mai tuwo-tuwo tikari a saudia. Miyasa idan dan alkairin da tayinne baza'a bata kuɗi itada iyayen nata ba tunda su sukafi buƙata. Sai an wani ƙaƙabama yarona? Idan kuma auren nata dole ne basai a samu wani a bashiba a ma'aikatan gidan nan”.
Pa yasan ya cigaba da saurarenta zai iya mata abinda duk yazo masa a rai, dan haka ya miƙe tsam ya bar mata falon. Hakan ba ƙaramin sake ƙona mata rai yayiba, dan harda ƙwalla suka taru mata a ido, zuciyarta na ƙarajin tsanar Raudha da duk wanda ya shafeta. Tayi alƙawarin koda sunfi ƙarfinta anyi auren nan wlhy sai Raudha ta gwammace mutuwa da rayuwa.
Da wannan ɓacin ran ta yini ranar, da daddare ta buƙaci ganin Ramadhan, duk da yanda yake a matuƙar gajiye dan yau jihar Nobama sukaje campaign haka ya daure ya amsa kiran nata. Tunda ya shigo take kallonsa, duk ya rame yayi duhu saboda wahalar kai kawo, sai dai hakan bai dametaba, dan tasan yana samun mulki zai koma normal harma yafi da.
“Barka da dare Maa!”
Ya faɗa cike da girmamawa yana kaiwa zaune kujerar dake gefenta. Tab.. ɗin hannunta ta ajiye cike da ƙasaitarta tana dubansa. “Baka dai, lafiya ne na ganka sukuku?”.
Numfashi yaɗan furzar, cikin muryarsa mai ɗan faɗi yace, “Kaina ke ciwo, nasan hayaniyarnan ce kawai”.
“Basai kasha magani ba, ya za'ai mutum ya zauna da ciwo”.
“Bana son na cika yawan shan maganinne, nasan da nayi barci zan ware”.
Baki kawai ta ɗan taɓe, ta sake harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya da tsuke fuska. Dan tana so ya fahimci ba zancen wasa bane. “Ina muka tsaye game da auren wannan yarinyar da aka ƙaƙaba maka?”.
Baya ya ɗanyi da jikinsa ya kwantar a kujerar, ya lumshe idanunsa tamkar baiji mitace ba. Kusan sakan biyar sannan ya furzar da iska batare daya buɗe idanun ba. “Babu wani abu da zan iya yi akan auren nan tunda Pa da Bappi da Anne sun dage, kawai na yanke zan auretan daga baya zan san abunyi”.
“Jikar tikari mai tuwo-tuwon zaka yarda ka aura? To bara na faɗa maka idan ma baka saniba. Uwarta kanta sai da tai karuwanci, a barikinne ma ta haɗu da uban yarinyar dan shima ɗan duniyarne na bugawa a magazine, daga kakarta har ƴan uwan uwarta duk karuwai ne har yanzun. Idan ma barci kake ka farka, duk yanda zaka zame ka zame kafin cikar waɗan nan kwanakin da suka tsaida”.
Harga ALLAH maganganunta sun sokesa. Kuma dama tayi amfani dasu ne dansu soke-san tunda tasan yanda ya tsani karuwai tun yanada ƙarancin shekarunsa balle yanzun. Idanunsa dake kumbure da ɗan ja a cikinsu saboda rashin samun isashen barci ya zuba mata. Sai kuma yaɗan janye cikin taune lips. “Maa waya faɗa miki?”.
Harara ta danƙara masa tana miƙewa, “Kaje ka bincika tunda na saba maka ƙarya...” Tana faɗa tabar wajen.
“Maa Please.....”
Ya faɗa da sauri yana ƙoƙarin ganin ta tsaya amma tai masa banza ta shige. Jagwab ya koma ya zauna a kujerar yana dafe kansa daya ƙara ƙarfin gudun ciwo. _(Ƴar karuwa, jikar tikari mai tuwo-tuwo. Ubanta ma a yawon duniya suka haɗu da mamarta sukai aure, sannan duk ƴan uwan uwarta karuwaine har yanzun)._ “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un”. Ya faɗa a fili yana dafe kansa da ya sake wata irin sarawa kamar zai faɗo ƙasa. Duk yanda yaso miƙewa a wajen kasawa yay. ALLAH ya taimakesa sai ga Rafi'a ƙanwarsa ta uku ta shigo falon da shayi a hannu da waya a kunne alamar magana takeyi.
Cikin sauri tace, “Subahanallahi Yaya!”. Wayar da kofin shayin ta dire bisa centre table tayo kansa, duk yanda taso taimaka masa ya tashi ta kasa, dole ta fita ta kira Pa da sauran ƴan uwanta dake can babban falo kowa na harkar gabansa. Waɗanda ke a cikin ɗakunan barcinsu kuma suka firfito suma saboda yanda take kwakwazon kiran Pa.
Komai Pa baice masaba, sai taimaka masa da yayi ya miƙe, da kansa ya kaisa har sashen su Anne su Rafi'a biye da shi hankali tashe, wasunsu ma hawaye sukeyi duk da bawai ya suma bane ko yanayi yayi tsamari. Kawai dai idan ka kallesa kasan babu lafiya tare da shi.
Suma su Anne hankalinsu ya tashi, a take aka nemo doctor duk da yace su barshi shi lafiyarsa ƙalau, amma basu sauraresa ba. Cikin ƙanƙanin lokaci sai ga doctor Shamsu. Koda ya dubasa sai yace musu gajiyace da ƴar damuwar data saka jininsa ɗan haurawa. Sai kuma sugar ɗinsa yayi low sosai da alama kwana biyu baya kula da shan maganinsa.
Da ƙyar Ramadhan ya yarda aka saka masa drip, sai da Bappi yay masa jan ido ma, ALLAH ya taimaka bai jima da fara shiga jikinsaba barci mai nauyi yay awon gaba da shi. Su duka tausayinsane ya kamasu. Dan sun san yana matuƙar ƙoƙari akan abinda bai saba ba. Duk da yana zirga-zirgar kasuwanci ba irin wannan bace. Dan ko hayaniyar campaign ɗin nan tashin hankaline. Balle kuma akwai ƴan kunji-kunji kala-kala a gefe ga abokan hamayya dama abokan tafiyar.
Duk fita sukai suna masa fatan samun lafiya ganin yayi barci. Sai dai ran Pa a ɓace yake sanin Gimbiya Su'adah ce ta sake saka Ramadhan ɗin cikin wannan yanayin, kuma duk abin nan da akeyi babu idonta a wajen.
A ɓangaren gimbiya Su'adah kam duk taji komai, taƙi fitowane danta sake jaddadama Ramadhan fushinta ya tabbatar da zancen bana wasa bane. Dan taji daɗin yanda taga zancen yayi tasiri a ransa. Hakan yasa babu ɓata lokaci ta kira Asma data bata shawarar ta sanar mata. Cikin jin daɗi adda Asmah tace, “Su'adah ai dama na faɗa miki hakanne kawai zaisa Ramadhan yay mana biyayya. Ni yanzu ina ganin mu haɗa wani shiri da zai sake sakashi tsanarta. Suma kakannin nasa susan mike faruwa idan ma basu sani ba”.
“Okay ina saurarenki wace idea ce”.
Idanu sosai Gimbiya Su'adah ta zaro bayan ta gama jin yayar tata adda Asma. Cikin rawar harshe tace, “Anya Adda Asmah wannan shawaran yayi kuwa? Karki mantafa mulki Ramadhan ke nema. Koyaya abu yake yanzu zai ita taɓa kujerar da yake neman. Abokan hamayya na masa yarfe da ƙazafi inaga wannan ta fito......”
“Su'adah ki kwantar da hankalinki, babu ta inda wannan zai shafi Ramadhan. Sai ma ɗaga darajarsa da zai ƙara”.
“Uhm-uhm Adda kedai bari sai mun sanar ma Fulani”.
Wani irin takaici ya baibaye Adda Asmah daga can, ji take kamar ta jawo ƙanwar tata ta hau duka. Amma a fili sai tace “To hakan yayi”.
Koda Gimbiya Su'adah ta kira Fulani ta sanar mata zaginta ta hau yi. Duk da ta yabama ƙoƙarin ta na farko akan sanarma Ramadhan su waye dangin Raudha ɗin. Amma maganar fita da tsiraicin suce Raudha ce da wani wannan gangancine. “Ku miyasa baku da hankali. a tunaninku dan kunyi video na bogi kunce itama yarinyar karuwace zai hana mutuncin Ramadhan taɓuwa ne. To idan baku san siyasa ba ko mulki ku farka. Wannan abun zai iya ruguza duk wata nasarar da muka samu a campaign duk da kuwa bai aureta ba, idan ma baku sani ba zancen auren nan nata shi kansa wani mutunci ya ƙara masa ga al'umma har a wajen campaign. Idan zamu kaudashi kuwa zamuyine a sirrance bawai mu nuna wa duniya ba marasa tunani kawai. Ku fitar da video ɗin abokan adawa sujuyar da shi akan tare take da Ramadhan ɗin a ciki shashashu kawai”.
Shiru gimbiya Su'adah tai da waya a hannu dan Fulani na gama faɗa ta yanke wayarta. Itama irin wannan tunanin tayi tun farko shiyyasa ta bijirema Addar tata. Inko hakane gara ta tattara zancen Raudha gefe tukunna, dan duk abinda zai hana ɗanta hawa mulkin nan zata kwana ta yini yaƙi da shi ne.
______________________________
Badan Ramadhan ya warke ba ya miƙe ya koma filin daga, amma Alhmdllh ɗan ƙarin ruwan da akai masa yasa jikinsa yin daɗi. Ranar wata juma'a bayan sakkowa massallaci yay campaign nasa na ƙarshe a ƙauyensu Taura. Inda ɗunbin jama'a suka taru har abin ya bama mutane tsoro musamman abokan hamayya irinsu Alhaji Andi ƙaura. Su president kam ji suke kamar su goya Ramadhan a baya dan daɗi. Dan kuwa sun san burinsu na dawowar mulki garesu ya gama cika. Sai kuma fatan kauda Ramadhan a shekaru biyun da suka ɗiba masa (wa'iyazubillah. Sun manta ran kowa a hannun ALLAH yake. Sannan shike bada mulki ga wanda yaso a kuma lokacin da yaso).
Muslata irin farin cikin da Ramadhan ya shiga a yau ɓata lokaci ne. Dan kuwa ya tsorata da yawan mutanen da suka taru dominsa. Har yanaji a ransa kodai akwai aljanu kamar yanda wasu ke faɗa ne. Sai dai farin cikin nasa bai hana jin ɗacin da tsanar Raudha da ahalinta ba. Duk yanda yake turesu a ransa sun kasa gushewa.
______________________________
*_RANA BATA ƘARYA SAI DAI UWAR ƊIY TAJI KUNYA_*
A faɗin ƙasar NAYA da kewaye yau itace daren zaɓen shugaban ƙasa. Dan haka ta kowanne sashe akwai abinda ke gudana ga kowa. Wasu fatan nasara, wasu shirye-shiryen kota kwana, wasu addu'oi. A cikin masu salla da addu'a a wannan dare harda Ramadhan, Anne, Bappi, Pa, Yafendo, Inna da wasu a cikin ƴan uwan ahalin Taura. A masarautar Bino ma dai Mai-martaba ya kwana raya wannan dare. Yayinda irinsu Gimbiya Su'adah sukejin mulki kamar sun samesa ne.
Duk da Raudha bata jin son Ramadhan ta masa fatan alkairi, harta kwanta kuma zuciyarta taita zingurinta akan ta tashi tayi salla ko raka'a biyu ne. Tabi shawarar zuciyarta tayi kuma ta roƙi ALLAH samun shugaba na gari bawai Ramadhan ba.
*_WASHE GARI:_* kusan tara na safe Feena ta shigo ta sakata shiga wanka. Batare da tasan dalili cewa tai wankan ba tace ai yanzu tai wanka ita. Fita Feena tayi, babu jimawa ta dawo da kaya a hannu da makeup kit. Sam Raudha batason wannan ƙaƙale-ƙaƙalen, amma saboda Aunty Hannah ta shigo ta mata magana dole ta amine akai mata light make-up ɗin. Sannan ta saka kayan da aka kawo matan. Tabbas tayi ƙyau, sai dai bazata iya fita da gyalen da aka haɗo kayan da shi ba. Dan haka ta ɗakko gogaggen hijjab ɗinta daya shiga da kayan ta saka. Duk jarabar aunty Hannah dole ta barta dan kuka ta sanya musu.
Tana zaune fuska a kumbure tana shan tea ɗin da aunty Hannah ta tilasta mata sha Yasmin ta iso da saƙon “Mom wai ga baƙon yazo inji mama tambaya”...,
Cikin sauri aunty Hannah ta amshe kofin shayin hannun Raudha ɗin. “Sai ki tashi tunda dama haka kike so ki fita bakici komai ba. Sai ki tashi ya iso kuje ku jefa ƙuri'a muma zamuje tare da tawagar shugaban ƙasa”
Sosai gaban Raudha ya faɗi, ta ɗago da sauri ta dubi Aunty Hannah. Sai dai kafin tai magana Feena ma ta shigo.
“Hajiya suna jiranta fa”.
Da sauri Aunty Hannah ta miƙar da Raudha, bag ɗin da zata riƙe mai ƙyau ta saƙala mata a hannu, hakan sai yay matuƙar sake fito da tsarin kwalliyar tata musamman da hijjab ɗin ke iya cinyarta kawai, gashi mai hannu, ya kuma ɗau guga ya kwanta luf da haska ƙyaƙyƙyawar farar fuskarta kasancewar blue color ne, sai hakan ya ƙara bama skirt ɗin nata fitowa sosai ya buɗe. Kamar zata fasa kuka ta zura takalman da aka ajiye mata masu ɗan tudu da suka sake fidda ƙyawun ƙafarta.........✍
Leave a Comment