Bakar Inuwa 19


 *_Episode 19_*

............. *_BINGO CITY_*

      Ƙananun magana da surutan dake faruwa a gari dama wasu manyan kafafen yaɗa labarai dana yanar gizo baisa Alhaji Hameed Taura ya damu ba ko janye maganar auren Raudha da Ramadhan. Dan cecekucen jama'a yayi dai-dai ne da cin primary election da

Ramadhan yayi zancen tsayawarsa takara ta fito fili. Aifa jama'a da ƴan siyasa ƴan bani na'iya suka samu nayi, yayinda magoya baya keta faman murna. Ƴan jam'iyyun hammaya kuwa tuni suka fara cece kuce akan sam Ramadhan bai cancanci fitowa takarar shugabancin ƙasar NAYA ba. Saboda dalilai masu yawa.


     Ɗan jarida dake hira da wani riƙaƙƙen ɗan siyasa a jam'iyyar hamayya ya gyara zama da faɗin, “Ranka ya daɗe miyasa kuke ganin bai cancanta ba bayan shiɗin matashine mai jini a jika da ba'a taɓa ko kwatanta shugaban ƙasa mai ƙarancin shekarunsaba a ƙasar NAYA? Sai nakega kamar wannan wani al'amarine daya kamata kowa yay murna da shi tare da yabama jam'iyya mai mulki data kawosa dan sunyi abinda ba'a taɓa yiba suma. Sannan Ramadhan B. Taura kowa yasan gidansu akwai kuɗi, a cikinsu ya tashi babu yanda za'ai ya handame kuɗin Al'umma tunda ba baƙonsa bane kuɗin”.

     Wata ƙasaitacciyar dariya Alhaji Andi ƙaura ya sake. Kafin ya haɗe fuska da faɗin, “To ai kuɗin daya tashi a ciki suna ɗaya daga cikin abinda yasa bazai iya ba. Banda matsala da ƙarancin shekarunsa dan koba komai muma muna buƙatar matasan ayi dasu. Sai dai kuma Ramadhan B. Taura bai cancantaba saboda baisan komai ga wahalar talaka ba. Idan baka saniba bara na faɗa maka. Shekaru biyar da suka wuce an kashe matar Ramadhan B. Taura da ƴarsa ta hanyar kai musu guba har gida cikin fridge sukasha suka mutu. Idan har wanda bazai iya bama iyalansa tsato da za'a halakasu har gidaba, tayaya zai bama ƴan ƙasa? Maimakon fa a tsaurara binciken gano wanda ya aikata sai ma yabar ƙasar gaba ɗaya ya koma America da zama. shine bai tashi dawowa ba sai yanzu wai shi yazo yay mulkin ƙasa. Inama laifin ya fito kansila ɗin anguwarsu ko ƙauyen Taura, amma ba NAYA ba dan babu abinda zai iya. Kai kana gani ko primary election ɗin nan ba kuɗi daliget sukaci ba da sauran ƴan takarar da suka janye masa tunkan fara jefa kuri'a?. Hutu da jin daɗi ya iya, yaje yayi kayarsa yabar wanda suka san wahalar talaka suyi mulkin ƙasar NAYA”.

        “To amma ranka ya daɗe sai nake ganin kamar jama'a zasuce kana faɗar duk wannan ne saboda kaima ana zargin takarar zaka fito a jam'iyyar hamayya?”.

      (Dariya). 

“Dan kawai zan fito takara sai a danganta zancena da ita. To nabama duk mai saurarenmu damar zuwa ya binciki, shin a zancena akwai ƙarya kuwa?”.

         “To amma ranka ya daɗe idan za'a duba a yanzu haka Ramadhan B. Taura yana shirin angwancewa ne da ɗiyar talakawa, wadda kowa ke ganin halaccine garesa bisa itama nata hallaccin data nuna akan kakansa wanda taima garkuwa aranar salla a filin idi. Shin wannan bai kai a yaba masa ba kuma a ƙara tabbatar da yasan kishin talaka da darajarsa ba?”.

        “To ai wannan maganar auren nasa ga kowa ma abayyane take. Dama sunyine domin duniya tai irin tunaninka, inba hakaba taya kake tunanin yaro kamar Ramadhan B. Taura young millioner da tun yana ciki ake tara masa kuɗi a accaunt zai auri ɗiyar talaka mai wahalar neman na masara a kullum. Kai ita kanta yarinyar ma a majiya mai ƙarfi tayi abinda tayine dama saboda an biyata. Sune suka sakata tayi hakan domin ayi irin tunanin da kayi. ka auna mana, dayin abun da fitar sunansa matsayin ɗan takara gaba ɗaya sati biyu kenan”.

        Ɗan jarida ya jinjina kansa yana kallon fuskar camara man. “To jama'a kuna dai jin tattaunawarmu da Alhaji Andi ƙaura acikin shirin SIYASA RIGAR ƳANCI dake zuwa muku anan gidan tv na G tv. Gashi mun kwararo bayani kuma lokaci ya ɗaga mana hannu, amma ku mana afuwa sati mai zuwa zakuji ƙarashen wannan fira insha ALLAH, zakuma kuji amsoshin zantukan Alhaji Andi ƙaura daga bakin makusancin ko nace jam'iyya mai mulki shima insha ALLAH”.

   

         Ɗauke hotunansu ya saka Raudha cusa kanta cikin ƙafafu ta fashe da kuka. Tun farkon fara hirar ta zauna kallo sakamakon cin karo da hotonta da tayi tare da na Ramadhan. Da farko rikicewama tayi dan bata gane shi bane, sai da hajiya mama dake zaune a falon tana kallo ke faɗin, “ALLAH dai ya kaimu randa zanga wannan zuƙeƙen surikin namu ya zama shugaban ƙasar NAYA ɗiyata first lady, ɗiyata da zakimin baƙin cikin zama uwar first lady”.

      Cikin rashin fahimta Raudha ke duban hajiya maman, sai kuma ta maida hankalinta ga tvn dan itako batama san wanda ake kira da mijin nata ba ya fito takarar shugaban ƙasa. Sosai hankalinta ya sake tashi dajin wannan hira musamman abinda Alhaji Andi ƙaura ya faɗa akanta. ALLAH shine shaidarta batayi dan a yaba mataba. Hasalima batasan wanene Alhaji baba ba alokacin. Amma gashi nan ta shiga bakin duniya yau harda masu fassara al'amarin da cewar an biyatane dan tayi, wasu na faɗin neman suna da neman gindin zama ne dama. Wasu na faɗin dan kuɗi tayi.

     Surutu dai iri-iri gasu nan marasa daɗin ji, ita kanta zuwa yanzu harta fara ganin gaskiyar zantukan mutanen, dan tana da tabbacin Ramadhan yafi ƙarfinta. Musamman da zancen fitowarsa takarar shugabancin ƙasar NAYA ya bayyana. Sannan ita tun da ake maganar auran nan batajin ma shi ya sani, tunda tun randa yaje asibitin nan bata ƙara ganinsa ba. Sai ma hannunka mai sanda dayay mata akan zame mata *_BAƘAR INUWA_*  inhar bata faɗi dalilinta na bama kakansa kariya ba. Idan har shi zaiyi irin wannan tunanin dan jama'ar gari sunyi mizaisa ta zargesu.......

      “Raudha!”.

Asabe ta sake kiran sunanta a karo na biyu. Ɗagowa tayi tana dubanta dan bataji na farkon ba. Cikin tausayin ƴar tata tasa hannu ta ɗagota ta rungume. “Haba Raudha kukan nan ya isa mana. Kina sake tayarmin da hankali wlhy. Ni nasan bakison auren nan, bansan miyasa kika amsa musu ba.....”

      “Wlhy ko bataso saita yisa”.

Cewar Hajiyar birni dake fitowa daga ɗaki a fusace. Dan yau da wuri ta baro shago saboda tana shirye-shiryen daina zuwa wai dan zata zama kakar matar shugaban ƙasa (🤔😝😂lol).

       “K dan ubanki saketa kitsaya da ƙafafunki!!”.

     Raudah ta saki Mommynta da sauri saboda gigitacciyar tsawar da Hajiyar birni tai mata. A take hajiyar birni ta haɗasu su duka ita da Asaben ta zage tas Hajiya mama na tayata. Sai da Aunty Hannah ta shigo gidan kusan goma na dare sannan tasa baki dan har lokacin sunata mita. 



*_TAURA HOUSE_*


     A ɓangaren Ramadhan ma da duk ƴan gidansu sunga hirar da akai da Alhaji Andi ƙaura, hakan kuma yasa Gimbiya Su'adah jin wa ɗanta zai aura. Dan tayi-tayi Pa ya sanar mata dama yaƙi. Sai gashi yau taji a shanun ƴan talla.

         Cikin lokaci ƙanƙani ta birkice, su Lubnah na tambayarta amma bata sauraresu ba. Da suka cigaba da damunta ma tsawa ta daka musu tai wurgi da wayar da take neman Fulani taƙi shiga ta fice zuwa sashen Pa duk da yau ba itace da girki ba. Zaune ta iskesa shi da Hajiya Mufida sunata hirarsu. A kallo ɗaya da sukai mata suka fahimci babu lafiya. Dan kowa a gidan yasan shegen girman kai da isar Gimbiya Su'adah. Duk da tanada tsananin kishi kishiya bata isa fahimtar komai daga garetaba. Dan batayin wani abu da za'a samu kafar rainata, ko kallon banza bata amince zamanyi da kishiyaba dan tace zubar da mutunci ne. Hakan kuwa da takeyi yayi tasiri, dan kame kan nata yasa ko shirmensu suke yakan tsayane iya su biyu, ballema suma ɗin kowa ji take da kanta abunka da kowa ubanta ya tara kuma akwai ilimi, dama hayaniyar tasu bata wuce ta harara ko rainin wayo anama juna yatsine-yatsine ko ɗaukar kai.

      Tsam hajiya Mufida ta miƙe tana tattare wayoyinta, cike da kulawa ta dubi Pa. “Bara nayo shirin barci kafin ku kammala”.

    Kansa kawai ya ɗaga mata idonsa akan Gimbiya Su'adah datai zaman ƙasaita a gefensa fuskarta tamkar zatayo aman wuta. Sai da ta tabbatar Hajiya Mufida ta bar sashen saboda akwai cctv da ake ganin shiga da fitar kowa daga nan falon sannan ta dubi Pa.

       Kafinma tai magana yace, “Lafiya?”.

         Idanunta da suka kaɗa zuwa ja ta zuba masa, cikin son nuna isar tata tace, “Abban Ramadhan ban yarda da wannan auren na Ramadhan ba”.

      Kansa ya ɗan girgiza ya ɗauke ya maida ga tv. sai da yaja numfashi ya fesar kafin yace, “Komi yasa?” batare da ya sake kallonta ba.

          Bata damu da yanda yay ɗin ba, cikin kaushi da nuna a wuya take tace, “Saboda bata dace da shi ba. Taya za'ace duk ƴaƴan sarakunan ƙasar nan dana attajirai da masu mulki arasa matar da za'a bashi ya aura sai wannan?! Wad......”

      Cikin sauri ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu. “Su'adah bana son hayaniyar banza. Shin ɗanki aure bautar ALLAH zaiyi? Ko auren kuɗi ko mulki?. Sannan ma ina zuwa, kina nufin Bappi bai isa zartar da hukunci bane a kan ɗayanmu? Ita yarinyar kuma kinsan ƴar waye da kike wannan hanƙoron.”

      Zatai magana ya sake dakatar da ita. “Karma ki ɓata lokacinki a banza. babu abinda zai hana wannan auren sai idan Ramadhan ne ya mutu, ko ita yarinyar insha ALLAH”.

       “To ashe kuwa lallai zata mutun”.

Ta faɗa a harzuƙe tana miƙewa zata fice batare data san katoɓara da suɓutar bakin da tayiba. Wadda ta saka Pa binta da kallo ƙirjinsa na bugawa. (Gimbiya Su'adah ta manta har yanzu akan binciken wanda ya kashe matar Ramadhan da ƴarsa akeyi, tun kuma a wancan lokacin an tabbatar musu wanda ya ajiye gubar suka sha sai dai idan yanada alaƙa dasu ne tunda duk wanda yazo birthday ɗin Haseenah makusancinsu ne. Sannan kafin wancan auren ma ta nuna borenta na ƙin Amnah saboda tanada sikila).

        “Ya ALLAH mi Su'adah keson faɗa ne?”.

    Pa ya faɗa a razane yana miƙewa zaune sosai. Zuciyarsa fal fargaban kar dai Su'adah nada alaƙa da kisan Amnah. Da sauri ya girgiza kansa. Dan a halayenta babu mai kamanceceniya da iya kisan rai. Barta dai da gadara da girman kai wannan kuma ya tabbatar jinin mulki ne ke yawo a jikinta. To amma miye ma'anar furucinta na yanzu? Anya kuwa babu lauje cikin naɗi.

      Hankalinsa ya tashi matuƙa da wannan tunane-tunanen, harta kaisa ga fitowa daga sashen zuwa sashen iyayensa. A falo ya iske su harda ƙannen kakannin nasa su Inna sunata hira hankalinau kwance. Yanayinsa ne ya saka Yafendo tambayarsa ko lafiya?.

      Da ƙyar ya iya haɗiye kaso sittin cikin ɗari na tashin hankalin daya shigo da shi, ya ƙirƙiri murmushin dole ya aza a fuska yana girgiza kansa. “Ba komai Yafendo, dama nazone akan batun Ramadhan”.

       Bappi ya sauke ajiyar zuciya a hankali, “Dama muma shi muke tattaunawa anan, dan munga dukan hirar da akai da Alhaji Andi ƙaura, nasan kuma itace kaima ta hargitsoka. Karka wani damu, dama wannan itace siyasar, duk wani abu da zasu masa yarfe damu kanmu yanzu bazasu gajiya wajen bincikosa ba. Sai dai mu mun riga munsan kanmu, addu'a kawai za'a dage da ita. Insha ALLAH a cikin satin nan za'a kai kuɗi a tsaida magana, sai a ɗaura auran bayan an gama zaɓe hankalinmu ya kwanta.”

        “Bappi haka shine dai-dai amma idan son samune dama a ɗaura auren kawai yanzu, sai ta cigaba da zama a gidan nasu bayan zaɓen sai ta tare ɗin”.

     Ɗan jimm Bappi yay yana tunani, kafin yay magana Anne tace, “Ya kamata ku fara jin ta bakin iyayenta dai, ku basu haƙƙinsu har sai sun yanke muku lokacin da sukaga ya dace da su. Da campaign da zaɓe har zuwa rantsarwa inaga watanni uku ne zuwa huɗu ai. To idan kunji ta bakinsu kunga yayi nisa sai ku roƙi alfarma. Kokuma shi uban gayyar ku tuntuɓesa ko yanada wani lokaci daya tsara”.

          Bappi yace, “Masha ALLAH hakan yayi kuwa. insha ALLAH zanyi magana da Ramadhan ɗin da safe idan ALLAH ya kaimu, na tabbatar yanzu yay barci. Ni bammasan yanda za'a kwashe da shi akan wannan barcin wurin ba yanzun. Dan kuwa ba nasa bane ba barci inhar da gaske ƙasar NAYA zai riƙe da ƙyau”.

     Ƴar dariya suka ɗanyi su duka.


__________________________________


        Alhmdllhi kamar yanda su Bappi suka yanke shawara an kai kuɗin auren Raudha Hutawa, dan Bappi ya dakatar da M. Dauda sake zuwa Bingo da yay niyyaryi akan son lallaɓa Asabe ta koma aurensa, yace yay haƙuri suɗan kammala wasu abubuwan. Shima M. Gambo ya bashi shawarar ya zauna su taya Ramadhan campaign anan daga baya sa san dabarar lallaɓa Asaben, sai shima ya gamsu.

      An amshi kuɗin auren Raudha harda hakimi, hakama dangin M. Dauda kowa so yake ace da shi akayi. Anba M. Dauda zaɓin tsaida lokaci, babu wani tunani ya yanke watanni huɗu. Duk da ba haka Bappi yaso ba sai baice komaiba sukai fatan ALLAH yasa haka shi yafi alkairi. Dan shima Ramadhan ɗin koda ya tuntuɓesa cayay wata huɗun, dan yafi son maida hankali akan wannan maganar campaign ɗin, ya kuma kawo hujjar idan akai auren yanzu za'aga kamar yayine dan amfani da Raudha wajen campaign. Sai dai abinda Bappi bai sani ba Ramadhan so yake ya zamewa auren, so yake kafin wata huɗun ya samu wani ya aurama Raudha ɗin batare da sanin su Bappi ba. 


  ★★★


    A ɓangaren ƴan jam'iyya babu ɓata lokaci aka hau campaign ta kowanne ɓangare bayan an bada damar hakan ga ƴan takara ta kowanne fanni. Duk wani ɗan uwa da abokin arziƙi ya fito domin tallata *_ Brr Ramadhan B. Hameed Taura (Young millioner)_* kamar yanda matasa ke kiransa. Ta ko ina posters nashine ke yawo. Matashi na matasa kenan. 

       Duk wani ƙarfin halin Ramadhan da tunanin zai iya sai abin ya koma bashi tsoro, lallai siyasa ba wasa bace ba. Ƙoƙari yake yaga ya hana duk wani ɗora matasa akan ta'addaci na basu ƙwaya da makamai da wasu manya keyi amma hakan ya gagara. Dan su Alhaji Yaro glass sun rigada sun kammala shirinsu tsaf a bayan fage. Hasalima Ramadhan baida maraba da hoto game da kowanne irin tsari nasu. Sai dai duk wani tsari nasu mara kyau sun binne iya su. Mai ƙyawunne kawai suka fiddo garesa. Hakan yasa yake cigaba da musu kallon mutanen kirki.


      Tabbas an kaɗa gangar siyasa. Mutanen ƙasa kuma sun amsa. sannan Alhmdllhi ta ko ina Ramadhan ya samu karɓuwa musamman a wajen matasa ƴan uwansa. Dan suna ganin wannan karonfa yaƙin nasune bana kowaba. A gefe kuma ƴan siyasa nata yarfe ga abokan hamayya. Musamman Ramadhan da tako'ina aka sakashi tsakkiya akan bai cancantaba. Ta yaya wanda ko aure baida shi zai iya riƙa ƙasar NAYA. Taya mai ƙarancin shekaru irinsa zai iya riƙa ƙasar NAYA? Taya ɗan gata irinsa zai iya riƙa ƙasar NAYA? Taya... Taya... Tay.... Dayawa suketa faman lissafi.    

       Sai dai kuma masu iya magana kance _zakaran da ALLAH ya nufa da cara ko ana mazuru ana shaho sai yayi_. To hakanne kam ga Ramadhan, dan tako ina bakajin sunan kowa sai na _Young millioner_ ga ƙuruciya ga kuɗi ga gayu ga ƙyawu.

      A ɓangaren ƴammata suma ba'a barsu abaya ba wajen yaƙin ganin sun ture gwamnatin Raudha sun maye gurbinta. Wasuko gani suke koda ita babu abinda za'a fasa fatansu dai Ramadhan ya amshi tayi kawai. Dukan saƙonsu da shishshiginsu yana hankalce da shi. Sai dai kuma basune agabansaba yanzun. Ita kanta da aka saka masa ranar auren da ita bata gabansa. Dan yakanma manta da wata saranar aure dake a kansa gaba daya. Shi hatta sunan Raudha sai abakin ƴan siyasa ma ya fara jinsa. Kuma bazaice ya riƙeba duk da ana yawan ambata saboda yarfe da ake masa akan batun aure dama auren nata da mutane kan fassarasa a siga kala-kala.

        Kallo ɗaya zakai masa ya baka tausai, duk ya rame yayi duhu saboda wahalar campaign da rashin barci. Duk ƙoƙarinsa nason ganin kowa ya fahimcesa hakan bai hana wasu jifansa da kalmar *Mai girman kai ba* susukance ya cika girman kan tsiya da izza. Duk lokacin da kalmar nan ta fito a bakin wani ɗan siyasa yakanyi murmushi, dan shi dai wannan girman kai nasa da aketa faɗa har yanzu bai ganinsa..........✍


No comments

Powered by Blogger.